Showing 6001 words to 9000 words out of 45829 words

Chapter 3 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

waya tana jiransa. Zayyad ji yayi kamar ya fashe da kuka ko hakan zai sama masa kwanciyar hankali amma koda yayi kukan ba zai yi masa maganin halin da yake ciki ba, sai ya sauka daga gado ya ɗiba ruwan flaks a marfinsa ya shiga shansa yana kurɓa a hankali har ya shanye farin ruwan ya rufe ya koma ya zauna yana mayarda gumi, daga haka kuma yaji sauƙin ƙullewar marar, sai miƙe ya kashe wuta ya koma ya kwanta ya rufa da bargo ba jimawa barci da ɗauke shi.


*****


Washegari Zayyad sai da ya makara sallar asubahi dan wajen shida da kwata ya tashi, ba ɓata lokaci ya juye ruwan flaks ɗinsa yayi wankan tsarki dan jiya yayi makarfi bar katai kuma ikon Allah da Safna yayi saboda ya kwana da ita a ransa, daya fito wanka ya shirya ya gabatar da sallar asubahi a ɗaki ya cigaba da zama yana jan lazumi har gabanin ƙarfe bakwai, kafin ya kwanta a gado ya kunna data yana duba shafinsa na Facebook, bayi da sauran yin barci dan zai kai yara makaranta ga kuma yana so ya biya gidan mahaifiyarsa ya gaisheta kafin ya wuce shago. Yana a kwance yana jin hirarsu Rashida sai hidimarsu suke yi dan ba tashi take ba, yana matuƙar mamakin sakarcin Rashida tare da ganin wautar yayarsu da ba zata iya ɗaurata a hanya ta gyara ba, ya kula haka rayuwarsu take tun daga gida tarbiyyar da suka samu kenan, tsaki yaja yayi Allah ya kyauta a ransa kana ya sauko daga gado ya shirya cikin ƙananun kaya ya kimtsa ɗakinsa kana ya fito lokacin wajen ƙarfe bakwai da Rabi.


Ina kwana.


Anty Wasila ta ambata.


Lafiya kalau Alhamdulillahi kun tashi lafiya.


Ta amsa da lafiya lau, sai ya wuce zuwa kitchen dan can yaji motsin Rashida, Aslam ya isa ga Abbansa da gudu ya rungume shi yana cewa.


Abbanmu.


Na'am Aslam ɗin Abba, ya naga ba kuyi shirin makaranta ba ina Momynku?


Momy tace uniform ɗinmu yayi datti kuma bamu karya ba.


Ran Zayyad ne ya ɓaci sai ya saki hannun Aslam ya nufi kitchen ya shiga ya tsaya yana ce mata.


Rashida ya naga yaran nan basu shirya ba?


Abban Ilham ashe ka tashi, ina kwana?


Lafiya lau, ina tambayarki baki bani amsa ba.


Rashida ta shiga sosa ƙeya.


Dama uniform ɗinsu yayi datti ban samu damar wankewa ba na manta, amma yanzu nake shirin naje na duba in zai yuwu su saka haka in sun dawo na haɗa na wanke.


Amma nasan uniform ɗinsu kala biyu ne, kuma sun saka ɗaya shekaran jiya monday da jiya talata, yau laraba ya kamata ace ɗayan yana wanke sawa zasu yi tunda sau bibbiyu suke saka kayan friday su saka sport wear.


Wlh ranar Lahadi guda ɗaya na wanke da tunanin washe gari zan wanke ɗayan shiyasa.


Ta faɗa a sanyaye, Zayyad daga hannu ɗaya yayi ya dafe goshinsa dan tsananin takaici, ya sauke hannu yana hura iska mai ɗumi daga bakinsa ya girgiza kai ya fice, a nan ƙofar Kitchen ya tsaya ya shiga kwalawa yaran kira nan suka zo da sauri, ya dubesu.


Kunyi wanka?


Ba muyi ba dama sai mun dawo makaranta muke yi.


Ok kuje yanzu ku sauya kaya masu kyau ku ɗauko jakunanku na makaranta ina jiranku a mota.


To suka ce masa suka isa ɗakinsu da gudu, Zayyad ya koma kitchen ya duba lunch box ɗinsu yaga an aje a gefe ba a jima da wanke su ba, ya isa ya haɗasu cikin kwandonsu ya ɗauka ya fice ya isa ƙofar ɗakinsa ya saka key ya juya ya fita daga falon, a mota ya jira yaran har suka fito suka shiga sai ga Rashida ta fito da gudu.


Abban Ilham basu karya ba ga arish ɗin na gama soyawa yanzu zan haɗa musu tea.


Bai kulata ba ya tayar da motarsa ya ja baya tare da buga hon mai gadi ya buɗe masa ya cilla motarsa waje ya hau hanya ya wuce, Rashida taɓe baki tayi tana jan tsaki ta koma ciki anty Wasila tana cewa.


Wai ke haka kuke rayuwa a gidan nan gabaɗaya bai ɗaukeki a bakin komai ba, anya amaryar da zai aura bata nima shiga tsakaninku ba.


Ke dai anty kya faɗa amma kuma yadda na karanci yarinyar tana da hankali da ilimi bana tunanin zata yi wani abu, halin namiji kawai yake gwada mini.


Amma wlh ke shashasha ce an gaya miki masu ilimin basa shagala ne to su suka fi iskanci ma, dan haka bana tantama yarinyar nan tana niman shiga tsakaninku Allah.


In tayi wani abu ma to kanta ta yiwa ba ni ba, dan Zayyad ɗin ban ɗauke shi a bakin komai ba, bai isa ya wulaƙanta ni ina kallonsa ba ni da shi kar tasan kar.


Allah ya kyauta ni in kin gama haɗa abin karyawa ki kawo muci dan cikina karta yake yi.


Anty Wasila ta faɗa tana yamutse fuska, Rashida tace.


Ai na gama bari na ɗauko.


Sai ta shiga kitchen ta cigaba da aikinta.


**


Zayyad rastaurant ya wuce da yaran ya yi parking suka shiga ciki, yasa aka haɗo musu breakfast mai kyau soyayyan arish da kwai tare da miyar albasa, sai ruwan lipton da kayan ƙamshi, nan suka ci suka ƙoshi daga bisani ya bada lunchbox ɗinsu aka zuba musu abinci jelop ɗin shinkafa da nama duka su biyun ya biya kuɗi suka fito suka shiga mota ya wuce dasu makaranta, ya kashe kusan dubu ashirin a wannan abincin da suka ci. Suna isa makaranta suka ɗauki kajunansu da kwandon abincinsu suka wuce ciki, office ɗin headmaster ya kaisu sun samu ba kowa a ciki sai shi kaɗai, yana ganin Zayyad ya miƙe suka gaisa dan sun saba da juna sosai, suka zauna sai Headmaster ya dubeshi yana cewa.


Ya naga ɗalibanmu da kayan gida Allah yasa lafiya.


Malam kayan nasu ne an wanke musu basu bushe ba, shine naga da suyi fashin makaranta gwara na zo dasu na siya musu wasu, Allah yasa akwai uniform a ƙasa.


Akwai su ai bama bari su yanke saboda masu siye da sabbin shiga. Ina zuwa.


Headmaster yace tare da miƙewa ya shiga cikin wani ƙaramin ɗaki dake cikin office ɗin ya duba uniform ya ciro musu size ɗinsu, nan ya miƙa masa yana cewa.


Gashi nasan zasu yi musu ita bata wuce shekara takwas ko? shi kuma biyar.


Basu ma kai ba, tsayin ƙafa garesu amma wannan zai yi musu.


Cewar Zayyad yana ɗaga kayan yana dubawa, nan ya umarci yaran su cire kayansu su saka uniform ɗin, ba musu suka yi tuɓe suka saka yace su ɗauki jaka da abincinsu su wuce class, suka yi masa bye bye suka fice nan Zayyad ya biya kuɗin uniform suka yi sallama da headmaster kana ya fito ya shiga motarsa ya nufi gidan Amminsu.


Yana shiga falon gidansu ya samu Hajiya zaune a carpet tana ta aikin ɗura dambun Nama a robobi, ta amsa masa sallama tana cewa.


Dan halak kaƙi ambato, yanzu nake zancen Muktar dole ya jira na gama sakawa ya kai muku shago daga can ya wuce makatanta.


Ai tunda nazo sai yayi tafiyarsa. Ina kwana Ammi kun tashi lafiya.


Lafiya kalau Alhamdulillahi ina mutane na su Ilham da fatan kowa lafiya.?


Alhamdulillah yanzu na sauke su a makatanta.


Haba Zayyad meyasa kuke barin yaran nan suke lattin zuwa makaranta, wannan zai iya saka karatunsu yayi ta baya.


Ya zanyi Ammi kema kinsan halin Rashida ba sai na faɗa ba.


Nan ya kwashe komai daya faru da safen ya faɗa mata, Ammi ta girgiza kai tana cewa.


Allah ya kyauta ya shiryata, dama shi mugu bazai cika mugu ba sai yayiwa kansa mugunta, gashi duk abinda take yi ya fara shafar rayuwar yaranta. Shiyasa nake fatan Safna ta shigo ta kula da kai kota fannin Abinci ka huta da zaryar Rastuarant.


Allah yasa mu dace, ashe kinyi dambun naman, kwana biyu masu saye suna ta tambaya.


Ai jiya nace bari na ɗaure nayi nasan za ayi ta tambaya, to jikin namu ne na tsufa yau lafiya gobe ba dama.


Hakane Allah ya ƙara afuwa, Ina Salame mai aikinki bata nan ne?


Ta tafi kula da 'yarta data haihu, shiyasa aikin ke mini yawa amma tace cikin kwanakin nan zata dawo.


To Ammi ko za a sake samo wata ne su zama su biyu.


A'a itama ta wadatar kuma ai yanada kyau ina motsa jikina. Matso kusa ka zuba dambun a leda roba saba'in ne ba sai ka sha wuyar ƙirgawa ba.


To yace mata ya matso yana sakawa a katon leda.
[06/09, 8:54 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 4.


Sai ga Mukhtar ya fito daga ɗakinsa yana ganin Zayyad ya washe baki yana cewa.


Yauwa shikenan ma bari nayi fijo na wuce inda nafi wayo. Yaya Zey zan samu wani 'yan chanji a gunka? kasan gaye ba kwabo yawane.


Nan kafi auki ai, kana gama karatun nan shago zan buɗe maka ka fara sanin yadda ake kasuwanci kasan muhimmamcin kuɗi.


Dako ka kyauta Zayyad, dan kam wannan shiryayyen in ba anyi masa da gaske ba malalaci zai zama.


Haba Ammi jifa yadda na tara kwanji, ai ko yanzu zan iya saɓa yaya a wuya nayi yawo dashi saboda ƙarfina.


Zayya ya ɗauki ludayin da Ammi ta gama amfani dashi ya wurga masa, Mukhtar yayi tsalle ya koma gefe yana kwasar dariya suma dariyar suke tayashi, Zayyad yace.


Allah ya shiryeka kowa ma ka mayar dashi abokin wasanka. Ga dubu biyu nasan zata isheka fafa.


Yasin tayi mini kaɗan, ina laifin ka bani dubu biyar a matsayina na autan marigayi Alhaji Ahmad da Hajiya Halima mai dambun nama, ƙanin Bilki da Zayyad da kuma Asiya.


Innalillahi! Muktar Allahu yahadika.


Cewar Ammi tana murmushi, Zayyad ko murmushi shima yayi yana girgiza kai dan ƙanin nasu in dai wajen barkwanci ne lamba ɗaya yake, ya ƙara masa dubu uku ya zama dubu biya ya amsa yana godiya.


Zaka yi Albarka dan gidan Ammi In Sha Allah, Allah ya kawo Anty Safna gidanka lafiya muci rayis.


Yana gama faɗar haka ya fice yana kwasar dariya, suma dariyar suka yi suna yi masa fatan shiriya.


Ammi ta miƙawa Zayyad wani robar takeway.


Ga naka sai ka aje kaci abinka a hankali harya ƙare.


Yauwa nagode, a office ɗina zan aje shi dan inna je da shi gida sai dai naga robar a bola, amma wannan baiyi mini yawa ba? kar in karya jalin.


To Zayyad in ka cinye kaine mai bayarwa, sannan ma Alhamdulillahi na fidda uwar kuɗi da riba. Ɗazun nayi waya da Kamal yace mini jibi Juma'a zai zo.


Eh munyi waya jiya, amma kinyi magana da Yaya Bilki yaushe zata zo ita.


Wai in biki saura sati biyu, zasu fara sauka a gidansu can daga baya su dawo nan ayi bikin.


Allah ya kaimu.


Zayyad ya ambata, Ammi tace amin suka cigaba da tattauna yadda suke fatan bikin ya kasance.


*****


Safna.


Tana zaune a ƙaramar kujera tana wanke wanke sai ga Haajara ta shigo gidan da sallama, da murmushi kan fuskar Safna tace.


Sannu da zuwa ƙawalli na ɗauka sai anjima zan ganki.


Ke gwara na fito kafin rana tayi zafi na kasa fitowa, kin san na fara zama ajebo.


Eh ba shakka ɗan baba ya fara mulki dai, ya nauyin jiki.


Alhamdulillahi, umma fa?


Cewar Haajara tana waige waige, Safna ta sanar da ita taje islamiyya ita ce kawai a gidan kowa ya fita sabgarsa, nan ta zame hannunta a ruwan wanke wanke ta shiga kitchen ɗin tsakar gida ta ɗauko mata kujera ta aje a innuwa tana cewa.


Bisimillah, ina kwana ya Amir da mai gidanki.


Lafiya lau, Amir yana gidan Mamanmu yaje hutu.


Kice ke kaɗai ce a gidan kina buga sarauta.


Ya son ranki Amaryar Zayyad, ya shirye shirye? Wai menene sirrin dana ga kinyi wani kyau kin ciko kamar ba amarya ba, ko ramar fargaba ban gani ba a tare da ke, ga ƙirjinki sunyi Masha Allah kuma keda na sani ba abin 'yan fiƙil fiƙil.


Dariya Safna tayi mai sauti tana wanke tukunyar data rage bata wanke ba tace.


Ba zaki gane ba madam, an gaya miki haka zanje gidansa kamar wacce aka yiwa aure dole, komai fa sai da gyara aka ce in kana da kyau to ka ƙara da wanka, Sabayar Maman Khadija na siya ya zama abincina na safe da yamma shine yasa na ciko nayi ɓulɓul sannan fatata tayi kyau da sheƙi.


_Ina uwar gida da amarya, zawarawa, 'yanmata da masu Shirin amarcewa hadda ke Ƙanwata, shin kuna son abunda zai ciko maki da ramarki Kuma ya gyara maki fatar ki? to haƙiƙa kukan ki ya ƙare da yaddar Allah, Dan maman Khadija ta tanadar maku d garin kunun Sabaya wanda zai ciko maku da duk wata rama ya gyara maki Fatarki ba tare da cutarwa ga lafiyan kiba, maman Khadijah tana zaune a Zaria Kaduna State Muna aikawa ko Ina a fadin Nigeria: Dan Neman Karin bayani kuna iya tuntubarta ta number waya kamar haka. 07037777442, 08033411249._


Haajara ta jinjina kai tana 'yar dariya tace.


To shi kuma breast ɗinki da naga sun ciko Masha Allah fa?


Sai da Safna ta kife tukunyar data wanke kana ta juyo tana dubanta.


Wani magani na siya mai suna Tula Tula, shine sirrin da kika ganni gwanin sha'awa, ga shi abin burgewa yana maganin Infection da kuma ƙarawa mace ni'ima, a takaice dai triple action ne amfaninsa.


_Tula tula maganin nono ne, yana gyara nono komin lalacewarsa ya cicciko dasu suyi tula tula. Masu yaye in suka sha kafin su yaye yaron da sati 1, to ba zasu yi ciwon nono ba kuma nono baze lalace ba. Uwa uba yana wanke mara ya cire infection, sannan ya ƙara miki Ni'ima da test. Zallar magungunan gargajiya da gadalin Fulani, daga manbila ake kawo mun babu na bature ko kaɗan a ciki, sannan bayasa ƙiba maganin nono ne kawai, sai maganin mata da sanyi da yake yi wato 3 in 1. Idan kina buƙata ina zaune a Kawo Kaduna ku tuntuɓeni a wannan number 08135613021 muna turawa ko ina a faɗin Nigeriya harda ƙasashen ƙetare_


Haajara ta tafa hannu cike da farin ciki tana cewa.


Habawa shiyasa gabaɗaya naga kin sauya ƙawata kinyi kyau sosai Tubarakallah, lallai nima zan nima nawa kar a barni a baya.


Ki bari ki juye sai kiyi gyaran da hujja, dan kin san yanzu kin fara nauyi bata gyara zaki yi ba, ta kula da tarbbiyar abinda ke cikinki za kiyi.


Hakane kuma.


Cewar Haajara, nan suka cigaba da hira har Safna ta gama aikinta ta tattare tsakar gidan suka shiga ɗakinta suka yada zango, zancen dai na maganar biki ne, har Safna ta sako mata labarin matar Zayyad, Hajara ta riƙe haɓa.


Ikon Allah, wlh ta burgeni da haka mata suke sauƙaƙa kishi da an zauna lafiya, amma fa ni bazan iya ba kin sanni da zafin kishi.


Niko wlh zan iya, ai yadda Rashida ta nuna mini ya tabbatar mini da za muyi zaman lafiya.


Allah yasa.


Cewar Haajara, Safna tace amin suka cigaba da tattaunawa. Hajara ita ce aminiyar Safna dan tare suka yi makarantar boko har zuwa poly, sun shaƙu sosai tamkar 'yan biyu duk inda zaka ga Safna to zaka ga Hajara, duk da unguwar su ba ɗaya ba saboda ita Hajara suna ɓangaren geto ne, ita kuma Safna suna GRA, Haajara tayi aure shekara biyu da suka wuce har ta haihu ɗaya Amir yanzu ga cikin na biyu nan kuma duk da tayi aure ba abinda ya taɓa zumuncinsu, suna shawara da juna duk abinda ya shigewa junansu duhu.


Sai bayan La'asar Haajara ta tafi akan sai biki ya rage sati guda zata kuma zuwa taji ya lamarin bikin zai kasance, har titi Safna ta rakata cike da kewar juna suka rabu.


******


Zayyad.


Sai dare wajen sha ɗaya ya dawo gidan, saboda ya biya ta gidan Hajiya sai wajen ƙarfe goma ya baro can, daga bisani ya tsaya shagon abokinsa Saminu tela da yake yin dinkin maza, nan ya ƙarar da sauran lokacin kafin ya nufo gida, falon suru ba kowa hakan ya bashi damar dafawa kansa ruwan wanka yayi kana yabi lafiyar gado ya kwanta. A da yayi niyyar share Rashida amma kuma in yayi haka shine zai cigaba da cutuwa, sannan a wannan gaɓar dole ne yayi mata uzuri ya cigaba da lallashinta tunda laifi zaiyi mata na ƙara aure, sosai maganar Saminu Abokinsa ya tsaya masa a rai da ya bashi shawarar akan ya yi haƙuri ya cigaba da yi mata uzuri tunda har ta iya kwantar da hankalinta bata yi wani abu da zai ɗaga masa hankali ba da ƙarin aurensa, hakan ya sashi sauke gauron numfashi ya dubo number ɗinta ya kirata sai dai bata ɗaga ba, duk da haka bai yi ƙasa a guiwa ba ya sauko daga gado ya nufi ɗakinta ya kwankwasa, ganin shuru ba motsi ya sashi tura ƙofar ya samu tayi ɗai-ɗai tana barci kuma basu Anty Wasila ashe sun tafi ma bai sani ba, ƙila shiyasa tayita kiransa da rana shi kuma saboda haushin abinda tayi masa yasashi ƙin ɗauka, ganin ita kaɗai ce sai ya juya ya wuce ɗakin yara nan ma su biyu ne sunata barcinsa, ya shiga ya gyara musu kwanciya tare da tofa musu addu'a ya kashe wutan ɗakin ya fito ya rufe ƙofar ya koma ɗakin Rashida wacce tun sa'ilin daya buga ƙofar taji amma ta share shi dan yayi mugun ɓata mata rai ɗazun daya ƙi ɗaukar wayarta, ya tura ƙofar ya shiga ya rufe sai ya kashe wutan ya haska da hasken wayarsa ya ƙarasa gadon ya kwanta tare da matsawa kusa da ita ya rungumeta ta baya, kiciniyar kwace kanta ta shiga yi ya saki murmushi.


Dama kina jina kika yi min banza ko.


Ni ka cikani barci nake ji, ko kuma ka jira zuwan amaryarka da zata zo ta kula da kai tunda ni ban iya komai ba.


Kema kinsan duk wata mace a bayanki take sai dai yadda kike hukuntani yana sa mini karaya sosai a zuciyata, sai nake ganin kamar hukunta ni kike yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login