Showing 9001 words to 12000 words out of 45829 words

Chapter 4 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

a fakaice ba tare da kin fito kin nuna zafin kishinki akan auren da zanyi ba.


Haka dai kake gani, amma kasan da zan ɗaga maka hankali da tuntuni nayi, kuma Safna a matsayin 'yar uwa na ɗauketa duba da yarinya ce mai hankali da tarbiyya.


Gaskiya ne Allah ya ƙara haɗa mini kanku, yanzu dai kin huce ko?


Zan dai huce.


Ta faɗa a dakile, murmushi yayi ya fara yi mata cakulkuli tun tana ture hannunsa har sai da ta saki dariya, daga haka kuma ya sauke nauyin daya kwana biyu bai sauke ba, duk da ba wani dogon kulawa da take bashi yawancin ma nuna ƙosawarsta take yi ayi a gama dan ta gaji, ya saba da haka shiyasa bai wani damu ba, a daren ya tsarkake jikinsa dan yana fatan gobe Alhamis ya tashi da azumin nafila daya zame masa jiki.


Tun daga lokacin Zayyad ya cigaba da lallaɓa Rashida yana haƙuri da jure duk wani shirme da take yi masa, sannan baiyi ƙasa a guiwa ba yana yi mata duk abinda tace tana so daga kuɗi har abin kuɗin, dan hatta ankon Safna data nuna masa ya siyo mata ta bada ɗinki, sannan ya kawo mata akwatin faɗar kishiya kamar yadda yayi niyya guda biyu da kit ya saka kaya masu kyau dai dai ƙarfinsa, suma yara yayi musu ɗinki kala uku uku da takalmi. Duka ɓangarorin shirye shirye suke yi ba kama hannun yaro, dan har an kai akwatin Safna guda huɗu da kit kuma yaji kaya na zamani Masha Allah, sai dai angon da gani yana da kishi dan yaƙi sanya gyale ko ɗaya duka manyan hijabai ya saka, Safna bata damu ba dan bata saka gyale sosai kuma yanzu aure zata yi wa zata yiwa kwalliya in ba mijinta kaɗai ba. Fannin gyara kam ta sashi dan sosai ta sauya har wani haske ta ƙara saboda zaman guri ɗaya ba fita take yi ba, ko rabon kati ta online tayi bata yi yawo ba tunda yanzu zamani yazo na waya. Can gidansu Zayyad suma danginsu sun hallara ana ta shirya shagali, yaya Bilki da Asiya sune kan gaba a komai dan Ammi sakar musu ragamar bikin tayi sai dai in abu yazo na shawara su sameta.


Ana gobe ɗaurin aure sun gama shirinsu tsaf na zuwa walimar da Zayyad ya gaya musu Safna zata yi a babban masallacin unguwarsu, wanda zasu yi a harabar Masallacin, sun gayyaci wani babban malami da zai gabatar da wa'azin aure, hakan yasa danginsa suma suka ce zasu je ayi komai dasu tunda bikin babu wani bidi'a party ko taron raye raye, suka yi sallama da Ammi mota ta ɗibesu ƙananun bus guda biyu suka wuce gidansu Safna. Kyakkyawar tarba suka samu wanda tuni aka ware musu gefensu daban cikin rufar kanofi da kujeru suka zazzauna suna hira ƙasa ƙasa kafin a gama taruwa Malam ya fito dan gabatar da wa'azin, kwatsam sai suka hango Rashida da tawagarta wato 'yan uwanta mata ƙenne da yayyi na family ɗinsu sun shigo, Bilki da Asiya suka kalli juna cike da tsantsar mamaki, sai dai sun kasa cewa komai suka yi gum da bakinsu, wasu daga cikin danginsu ne suke ambaton ga Rashida sunyi mamakin ganin zuwanta, har suka ƙaraso runfar da suke ciki aka shiga gaisawa cike da fara'a a fuskokinsu kamar ba wani abu a tsakakinsu, suma suka samu guri suka zauna 'yan uwan amarya suka zo suka gaggaisa kowa ya cika da mamakin ganin kishiyar Safna a gurin taron walimar, wasu na ambaton gulma ya kawota wasu kuma ta burgesu yadda take da sauƙaƙƙiyar kishi, haka dai gurin walimar ya gama cika da mata wasu ma basu zamu gurin zama ba, a haka amarya ta shigo ta zauna a mazauninta da aka tanadar mata ba jimawa malam ya fito ya fara gabatar da wa'azi. An ɗauki tsayin awa biyu ana yi daga bisani aka rufe taro da addu'a malam ya tafi tare da kayan arziki, su Anty Shafa da Haajara suka bi matan dake gurin da kayan sovenears, nan fa aka ga dangin Rashida suma sun miƙe suna nasu rabon a gurin turaren wuta a roba fari ƙarama da sitika a jiki sunan ango da amarya da sunan Ilham da Aslam a ƙasa domin sune suka ɗauki nauyin haka, wannan abu ya ƙara shayar da mutane gubar mamaki wanda da yawa wasu na sambarka da Rashida tare da hango tsantsar kirkinta da mutane suke yi, wasu kuma suna ganin na ciki na ciki wataƙila da biyu tayi hakan, wanda tunanin dangin Zayyad kenan sam hankalinsu bai kwanta ba da yarda da abinda Rashida tayi ba, haka taro ya watse kowa cike da farin ciki tare da kwasar tsarabar tunatarwar da Malam Inuwa yayi akan zamantakewar aure, har gidansu Safna Rashida da 'yan uwan Zayyad suka shiga tare da gaisawa da su Umma daga bisani suka yi sallama dasu suka fito kowa yaja tawagarsa ya wuce. Dangin Safna sai yabon Rashida suke yi da kyawun halinta, hatta anty Maryam da take adawa da Rashidar ta sauko ta yarda da halinta ne na kirki, haka dai kowa keta yiwa Safna sambarka.
[08/09, 6:29 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗




*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 5.


'Yan uwan Zayyad kuwa suna isa gida suka sanar da Ammi yadda taron ya kasance tare da ƙorafin basu yarda da abinda Rashida tayi ba, Ammi ta kwaɓesu da cewa.


Bai dace kuce haka ba ina ganin farin ciki ya kamata ku yiwa ɗan uwanku daya samu ya shawo kanta, wannan abinda Rashida tayi shine yake nuna za a samu zaman lafiya a gidansa. Ku riƙa kyautata niyya da fatan alkhairi akanta.


Idan zaman lafiyar ya kasance zamufi kowa farin ciki, Allah ya haɗe kansu ya kaɗe fitina.


Cewar ƙanwar babansu Haj. Samira, nan suka cigaba da tattaunawa akai suka saki komai a ransu, wataƙila dalilin auren Rashida ta yi hankali ta gyara kuskurenta, da haka suka bar maganar suka shiga zancen abincin da za a girka goben In Allah ya kaimu ɗaurin aure.


Ɓangaren Zayyad shima ba ƙaramin farin ciki yayi ba da yaji labarin abinda Rashida tayi a gurin walimar Safna, yasha mamaki dan baisan da duk wannan shirin nata ba, hakan yasa daya koma gida da dare ya tareta da zancen, dariya tayi ta zauna a gefen gadonsa tana cewa.


To meye a ciki? ai mun zama ɗaya, Allah ya baka ikon adalci.


Ameen ya rabbi.


Ni ina ganin zan tattara na koma gidan Ammi domin na baku dama keda 'yan uwanki, sai dai zan rufe ɗakina gudun ayi mini ɓarna.


To shikenan ba damuwa dama a kwai masu kwana a falo yanzu haka dan gidan a cike yake da 'yan uwana, kaima zaka fi sakewa a can gidan Hajiya, na tabbatar gobe dole ka dawo saboda amarya tunda an gama jere ba kwana.


Dominku gabaɗaya zan dawo zaki ce, ni naga ma sai wani basar dani kike yi hala kin daina sona ne Rashida? ko kaɗan bana ganin kishina a tare da ke.


Ina kishinka mana amma ban isa na hana abinda Allah ya ƙaddara mana ba, sannan da kayi mini kishiyar waje gwara ta gida, dole ne na koyi haƙuri da juriya wata rana sai labari.


Nagode sosai da kika kasance haka, ina fatan koda Safna tazo zamanku ya ɗaure a haka ba tashin hankali.


Allah yasa.


Tace tana guntun murmushi, amin yace ya miƙe ya isa waldrobe ɗin kayansa ya ciro abubuwan da yake buƙata ya saka a wata ƙaramar jaka, ya saka komai a ciki kana ya dawo ya miƙa mata kuɗi dubu hamsin.


Ki riƙe a hannunki koda ana buƙatar wani abu bana kusa.


Godiya tayi masa sai suka fito ta raka shi ƙofar fita falon, ya wuce ya shiga mota kana ya fice daga gidan cike da farin cikin sanyin kishin Rashida.


***


Washe gari duka ɓangarorin anata hidimar girki gidajen sun cika da al'umma, kowa yana cike da farin cikin wannan biki. Bayan sallar juma'a aka ɗaura auren Zayyad da Safna a bisa sadaki dubu ɗari biyu, ɗumbin jama'a sun shaida tare da binsu da fatan alkhairi. Zayyad duk da yana cikin taron mutane bai hana shi komawa gefe ba ya kira Safna, cikin yanayin sanyin jiki ta ɗaga ba tare da tace komai ba.


Zainab an ɗaura fa, daga yanzu kina ɗauke da igiyar aurena uku a kanki.


Wani irin abu taji ya tsirga mata tun daga tsakiyar kanta har zuwa kan babban yatsarta na ƙafar hagu, jikinta ya ɗauki wani irin rawa tare da jin zazzafan sanyi ya rufeta.


Safna kina jina kuwa?


Zayyad ya ambata yana buɗe murya, Safnah ta runtse ido tana ambaton sunan Allah a zuciyarta da kyar tayi jarumta ta haɗiye miyau tace cikin sanyin murya.


Allah ya bamu zaman lafiya.


Safna meke damunki ko baki da lafiya ne?


Zazzaɓi nake ji.


Sannu Allah ya baki lafiya yanzu haka stress ɗin bikin nan ne ki samu kici abinci da panadol, In Sha Allah anjima da kin ganki a cikin gidana zaki warware dan sai nayi yadda zanyi zazzaɓin ya sauka.


Murmushi ta saki mai sauti bata yi magana ba.


To sai anjima, amma da anyi sallar La'asar zamu zo ayi hotunan tarihi.


Allah ya kaimu.


Tace daga haka ta kashe wayar tana duban ƙawayenta.


Yau dai na zama Amaryar Zayyad.


Ihu suka saka suna yi mata tsiya, murmushi kawai take saki sai dai can ƙasar zuciyarta wani irin zullumi da karaya take ji, haka suka cigaba da hira masu bata shawara nayi musamman waɗanda suka jima da yin aure.


Zayyad yana gama yin waya da Safna sai ya kira Rashida amma ta kasa ɗaga wayar, sai ta miƙawa Anisa ta cigaba da tsayuwa tana dubanta dan hankalinta a matuƙar tashe yake, Anisa ta ɗaga wayar tace Rashidan bata kusa, sai Zayyad yace ta sanar da ita an ɗaura, daga haka ya kashe wayar Anisa ta ƙundumo wani ashar ta faɗa tana huci.


Wlh Zayyad mugun ɗan rainin wayo ne, wai ya kira ne ya faɗa miki an ɗaura aurensa.


Rashida da take tsaye kusa da miro wani irin jiri ne taji ya ɗibeta da sauri ta dawo gefen gado ta zauna tana dafe kai da hannu bibbiyu, sai ta cire ɗankwalin dake kanta ta shiga firfita, dan sosai gumi ya gama rufeta jikinta har rawa yake yi, Anty Wasila tace.


Wlh ki ɗaure ki danne zuciyarki a gama bikin nan kar ki karaya, ke ce fa uwargidansa sai abinda kika so zai gudana a cikin gidanki.


Anty wai fa an ɗaura auren, yanzu kenan Safna ta tabbata matar Zayyad, duk wani abu na auratayya zai wakana a tsakaninsu babu tsamaki ina ji ina gani. Na shiga uku bazan iya ba wlh zuciyata zata buga, ina son mijina bazan jure ganinsa tare da wata mace da sunan matarsa ba.


Sai ta rushe da kuka mai ƙarfi da gunji, Anisa ko jingina tayi da jikin waldrobe tana jijjiga cike da takaici, sosai abin ya bata haushi wai ya kira ya faɗa an ɗaura auren, Anty Wasila ce ta dafa kafaɗar Rashida tana bata baki, ana cikin haka ƙanwar Mamansu ta shigo ɗakin, ganinsu ko wanne rai a ɓace ga Rashida na kuka ta shiga rafka salati.


Meke faruwa ne naganku ba yadda kuke?


Zayyad ne ya kira Anty Rashida wai an ɗaura aurensa.


To shine me? Sai ku ɗaga hankalinku akan wannan, Rashida ki ware kiyi shagalinki dan babu abinda za a fasa tunda an ɗaura aikin gama ya gama, karki yarda maƙiyanki su samu labarin karayarki suyi miki dariya, dan ga dangin ubanku can sun hallara kuma kunsan ƙiris suke jira su samu abin yi muku dariya tunda ba ƙaunarku suke yi ba.


Inna zuciyata raɗaɗi take yi mini kamar zai faso ƙirjina ta fito. Shikenan Zayyad ya zama mallakin mu biyu.?


Ehen ya za ayi tunda ƙaddara ta riga fata, dole ki danne ki jure ki bawa mara ɗa kunya, ina ce kece kika bar tarihi akan yadda kika nuna sauƙin kishinki a auren, dan haka jaruma zaki zama tunda an ɗaura ki karɓi ragamar uwargidan Zayyad.


Inna Fati ta faɗa tana share mata hawaye, haka dai suka dinga bata baki da kyar ta daina kukan, ta shiga bayin ɗakinta ta wanke fuska ta fito Anisa ta ƙara yi mata wani kwalliya kana suka fita falo wajen baƙinsu, duk da ana ganin idonta sai an gane taci kuka amma fa haka ta dage tana yiwa mutane dariyar yaƙe sai dai na ciki na ciki.


Kamar yadda Zayyad yaje yayi hotuna da Amarya haka ya dawo gidansa aka yi masa da uwargida harma da yaransu da 'yan uwanta, daga bisani suka fita can zuwa gidan su Ammi nan ma aka yi masa hotuna da 'yan uwansa, Alhamdulillahi an ɗaura lafiya tare da yinin biki lafiya kowa ya tafi da farin ciki, sai sauran dangi na jiki ne suka rage. Bayan sallar Isha'i motocin ɗaukar Amarya suka dira a ƙofar gidansu Safna, anyi komai kamar yadda ake yi a al'adan Hausa Fulani, dangin ango sun kawo abincin biko da komai da ake yi. Amarya Safna tasha nasiha da faɗa a gurin 'yan uwa kafin aka fito da ita tsakar gida, umma har ƙofar gida ta rakata ta kama hannunta duka biyu tana cewa.


Daga ni har babanku munyi miki faɗa tuntuni, dan haka abinda zance miki yanzu shine ki shiga gidanki da zuciya ɗaya ki zauna da kowa da gaskiya, ki riƙe ibadarki ki kuma kula da al'amarin mijinki, ki zama mai juriya da haƙuri da kawaici, kiso duk wani abun da mijinki ke so ki ƙi duk abinda mijinki ke ƙi matsawar bai saɓawa Shari'a ba, addu'a ya zama shine makaminki a duk wani damuwa, ɓacin rai, baƙin ciki da zaki samu kanki a ciki, domin zaman aure akwai jarrabawa kiyi ƙoƙarin kai kanki zuwa ga cin nasara, Allah ya baku zuri'a nagari yasa gidanki ya zame miki hanyar samun aljannarki.


Umma ta ƙare maganar cikin rawar murya kana ta saki hannunta, Safna ta juya tana wani irin kuka mai karya garkuwar jikin duk wani mai tausayi, haka Anty Shafa ta kama hannunta ta jata zuwa wajen mota suka shiga driver ya jasu zuwa gidan Zayyad dake Askolaye.


Da suka isa har cikin gidan motarsu Safna ta shiga sauran ne aka sauke su a ƙofar gate haka suka shigo mata na guɗa, Safna kuwa tunda ta zuro ƙafarta ƙasa sai taji zuciyarta ta kuma tsinkewa tana fidda hawaye mara sauti, Anty Shafa ta kama hannunta ta fito sai suka fara isa ɓangaren uwargida Rashida, suka shiga da sallama matan dake ciki suka amsa kana suka basu guri wasu suka zauna wasu kuma dole tsayawa suka yi domin falon ya cika ba guri, bayan gaishe gaishe sai Mama Najah ƙanwar babansu Safna tace.


To uwargida ga amana mun kawo da fatan zaku yi haƙuri da juna Allah ya baku zaman lafiya, Safna sai ki zama mai biyayya a gareta domin ta girme miki dan ita kika zo kika tadda, Allah ya kaɗe fitina.


Duk matan falon suka amsa da amin, Inna Fati tace.


Ai rayuwar ma gabaɗaya haƙuri ne ku kyautatawa mijinku wajen haɗe kanku, dan in har baku haɗa kai ba to babu yadda za ayi ya samu farin ciki, Allah ya baku juriya da juna. Ga wannan a bawa amarya inji uwargidan Zayyad ba yawa, duk da mun so yi mata tanadi mai kyau amma abun yazo a ƙurƙure.


Wannan ma an gode, Allah ya saka da alkhairi.


Cewar Anty Maryam tare da amsar ledar da Inna Fati ta miƙo, Turmin atamfa ce da kuma turaren jiki na kanti guda biyu duk suna cikin kwalinsu, haka suka ɗan tattauna wanda duk shawarwari ake basu, Safna dake cikin Hijab ta ƙosa su fita saboda zafin da take ji, Rashida kuwa gyale ta saka ta ɗan jawo shi ya rufe mata saman fuskarta ta kasa cewa komai sai matsa yatsunta da take yi, haka su Anty Shafa suka yi musu sallama suka fito da Amarya, wasu daga dangin Rashida suka rakosu tsakar gidan kafin suka koma. Anan ne aka shiga kiciniyar buɗe ƙofar ɗakin amarya, bayan an buɗe Anty Shafa ta kamo hannunta tace ta shiga da ƙafar dama da addu'a, Safna wani irin jiri ne taji ya ɗibeta wanda nan take ta ƙanƙame hannun Anty Shafa tana ambaton sunan Allah.


Anty jiri nake ji.


Ta faɗa cikin sarƙewar murya.


To Safna shiga ciki tukunna sai ki zauna ki huta duk gajiya ce.


Safna ta ɗaga ƙafarta da kyar wacce taji tayi mata nauyi sai ta shiga ciki da sallama tare da koro addu'ar tsari a taƙaice, duk da haka sai da taji kanta ya sara mata, nan take ta saki wani irin kuka wanda ya tabbatar da ba ita ɓace jinnun jikinta sun tashi, Anty Shafa ta kamata ta zaunar da ita a Cushing ta cire mata hijab tana cewa.


Haba dan Allah ya zaku yi mana haka, ace ku rasa lokacin da zaku tashi sai a wannan lokacin.


Gurnani kawai Safna take yi tana kuka, Anty Maryam tace duk matar da ke da aljanu to ta fita saboda gudun damuwa, haka masu shi suka fita can waje, Anty Maryam ta matso kusa ta kama kan Safna da ƙarfi ta shiga tofa mata addu'a, Safna ta fara ture hannunta amma ina taƙi sakinta, ɗan so take su tafi kafin su tona asirin Amarya nada jinnu subar abin faɗe, Allah yasa ango bai riga yazo ba, motocin wasu abokansa ne da suka ɗauko su suna waje suna jiran su fito su mayar dasu, motar su Yaya Bilki ana shigo da amarya gidan suka juya aka mayar dasu domin su isa gida da wuri tunda gobe zasu dawo, shiyasa su Anty Shafa suka ji daɗin ba wani bare sai su danginta, haka Maryam ta shawo kan jinnun suka tafi Safna ta sauke wani nannauyan ajiyar zuciya kana ta kalli Anty maryam tace.


Kayan da suke hannunki ki bawa umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login