Showing 42001 words to 45000 words out of 45829 words

Chapter 15 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

yayarsu tayi mini suma suyi mini, ina ce a ranar da aka kawo ni cikin gidan nan bayan 'yan uwana sun watse sai da suka haɗani faɗa da kai, buga ƙofa da sassafe bani da sukuni a cikin gidan nan, Rashida ta takura mini bayan ni bana shiga lamarinta, yarinya ta fasa mini kwanon dana saka maka yaji jiya ta kawo sai naja mata kunne akan karta ƙara, saboda sau biyu kenan suna fasa mini kwano, amma ba halin na yiwa yaran nan faɗa Rashisa zata zo har ɗakina tana gaya mini maganar da yayi mata, ya kake so nayi.


Safna ta ƙare maganar tana matsanancin kuka, daga bisani miƙewa tayi ta bar ɗakin da gudu ta wuce ɗakinta, nan ko Ammi ta shiga surfa musu masifa tayi musu tatas tare da jawa su Anisa kunne akan in dai zaman lafiya bazai kawo su ba to karsu ƙara zuwa gidan, dama tasan duk abinda ya faru laifin na Rashida ce kuma in taso ta gyara in taƙi kanta zata yiwa, ta miƙe rai ɓace tayi mata Allah ya sauƙe kana ta fito zuwa sashin Safna.


Koda ta shiga ta sameta tana ta kuka Ammi ta zauna ta shiga yi mata faɗa, tace daga yau in yaran sun yi mata abu ta riƙa faɗawa Zayyad ne tunda in ta yi musu magana ita yana zama rikici, tayi faɗa sosai tare da nasiha tace in har Rashida ko 'yan uwanta sun sake yi mata wani abu ta kira ta faɗa mata ita da kamta zata zo ta ɗauki mataki, tayi mata nasiha sosai da shawarwari wanda yasa Safna ta ji sanyi a ranta, ko ba komai tasan Hajiya tana sonta dan haka ta share hawayenta, Ammi ta miƙe akan zata tafi Safna ta rakota har waje kana ta koma cikin ɗaki ta rufe dan sosai Zayyad ke bata mamaki yadda ƙiri ƙiri yake niman ɗaura mata laifi. Ammi ta leƙa tace ya fito ya mayar da ita gida yace to kana ta wuce waje shi kuma ya cigaba da bawa Rashida haƙuri, dan tun fitar Ammi take kuka akan ta nuna mata bata sonta ƙiri ƙiri dan tafi ƙaunar Safna da ita, dan haka ita gidansu zata koma da jinya, ganin ta rikice masa yasa ya susuce ya dinga lallashi kana ya bawa su Anisa haƙuri yana cewa ba inda zasu je sune zasu kula da Rashida ran Ammi ya ɓaci ne kuma zai fahimtar da ita, haka ya fito ya ɗauki hajiya a motarsa, ta cigaba da yi masa faɗa dan ta kula hankalinsa yafi karkata akan Rashida wanda hakan bai kamata ba, tunda a zahiri itace ba tada gaskiya amma saboda ta langwaɓe yake rawar ƙafa akanta, ita sam ma bata yarda da ciwon da Rashidan ke yi ba gani take yi duk makirci ne, Zayyad haƙuri yake bata da alƙawarin zai daidaita gidansa, har ya sauketa a ƙofar gida tana ƙara jaddada masa akan ya kamanta adalci, yayi mata godiya ta shiga gida shi kuma ya koma gida kansa a cunkushe yama rasa tunanin da zai yi, duk da yasan Rashida ce ba tada gaskiya amma ya zama wajibi ya tausaya mata kodan lalurar da take fama da ita, kuma da Safna bata biye mata sunyi faɗa ba da duk haka bai faru ba, shiyasa yake jin hauahinta sosai tunda yace mata duk abinda yaran suka yi mata ta faɗa masa ya yi musu hukunci da kansa amma bata ji ba.


Koda ya dawo sashin Rashida ya shiga ya samu tana kwance kan kujera, ya cigaba da bata baki akan komai zai yi daidai kana ya tambayi me suke buƙata, ta faɗa masa sai ya yi mata sallama ya wuce ya fita ba tare da ya shiga sashin Safna ba. Bayan fitansa Rashida ta tashi ta zauna tana ɗaukar alwashin saita ci uban Safna cikin ruwan sanyi, kuma Hajiyarsa sai tasan ta nuna mata ƙiyayya, su Anisa banda zugata ba abinda suke yi, har mamansu sai da suka kirata suka bata labarin abinda ya faru, cewa tayi ta kwantar da hankalinta tunda ko a yadda Zayyad ke rawar ƙafa da ita sun fara samun galaba ta fita batun mamanshi.


***


Safna


Shiru shuru tana jiran Zayyad ya shigo amma bata ganshi ba, har ya dawo daga kai Ammi ya kuma fita bai leƙo ba, abin yayi matuƙar ɓata mata rai amma ya zata yi dole ta sauko tunda ita ce ranar zata amsa girki. Wajen ƙarfe uku na rana ta kirashi ya kai sau uku amma yaƙi ɗauka, hakan yayi matuƙar baƙanta mata rai amma saboda ta fita haƙƙinsa kuma ta saba tambayarsa abincin da zata girka yasa ta tura masa text kamar haka.


_Assalam na kira shuru baka ɗauka ba Allah ya huci zuciyarka, dama ina so naji me zan dafa mana anjima._


Ta tura masa amma ba reply, ganin har bayan La'asar bai kirata ba kuma bai tura mata saƙo ba yasa ta shiga kitchen ta ɗaura tuwon shinkafa miyar kuka da busasshe kifi dan tasan yana so, harta kammala ta zuba taci ta ƙoshi dan ba wani abincin kirki taci ba a ranar, wajen gabda magrib ta yi wanka ta shirya cikin ƙananun kaya riga mai guntun hannu da siket iya rabin cinyarta, ya kama jikinta duk wani halittarta ta fito, dan ranar ne farkon data fara saka kayan duk dan tayi amfani da wannan damar ne wajen jawo hankalin Zayyad ya daina fushi da ita.


...
Bayan sallar magrib Zayyad ya dawo daga shago, ya yiwa Rashida siyayyen kayan marmari da kuma nama tsire, sashin ya fara shiga ya taddata tana zaune ƙafafunta suna ƙasa ta jingina bayanta da jikin kujera, da sauri ya ƙarasa ya aje ledojin hannunsa akan Center table yana duban Rashida cike da fara'a a fuskarsa.


Alhamdulillah kice sauƙi ya fara samuwa.


Wlh kuwa ka ganni ina motsa jikina tafiya ne ya rage mini, gaskiya maganin mutumin nan yana da kyau.


Sosai kuwa dan ga alamu mun gani, saboda har abinci taci fa sosai.


Cewar Zaliha data fito da plate a hannunta daga kitchen tana cin abinci, Anisa ta fito da ƙaton tire da abinci a kai da ruwa ta dire a center table tana cewa.


Abban Ilham ya aiki, nasan ka shigo da yunwa ga abinci ka rage hanya kafin ka isa gurin Amarya.


Wlh kamar kin san yau haka na yini banci abinci ba sai drink da cincin ne a ciki na.


Ya faɗa yana samun guri ya zauna, Anisa taja center table ɗin a gabansa ta buɗe masa abincin fried rice ne data girka dan ba laifi ta iya girki, Zayyad ba tunanin komai ya soma cin abincin, su kuma suka shiga shan kayan fruit ɗin daya shigo dashi, ya ɗiba tsiren ya saka a saman abincinsa yana ci su kuma suka raba sauran tare da ɗibarwa Rashida nata, haka Zayyad ya shagala har aka kira sallar isha'i kafin ya miƙe dan ya kammala cin abincin, ya kama hannun Aslam suka fita masallaci, Anisa ta kalli Rashida tana sakin dariya.


Anty fa ga dukkan Alamu kin samu akalar Zayyad, dan gabaɗaya ma ya mance da cewar ba ke ce da girki ba.


Hmmmm ba kuga komai bama dan yanzu aka fara wasan.


Cewar Rashida cike da tsantsar farin ciki, haka suka dinga hira cike da nishaɗi dan ko ba komai yadda Zayyad ya share Safna yayi matuƙar faranta musu rai.


....
Safna tun tana duba lokaci har ta gaji ta koma ta zauna a cushing ta rafka tagumi tana tsumayen shigowar Zayyad, saboda taji ƙarar shigowar motarsa sannan yanzu ma da zai tafi masallaci taji yana cewa Aslam yayi sauri, faɗar damuwar da ta shiga ɓata lokaci ne haka ta miƙe jiki a sanyaye ta shiga bedroom ɗinta ta gabatar da Sallah, tana zaune a dadduma taji dawowarsu da saurinta ta miƙe har tana haɗawa da gudu danta buɗe masa ƙofa saboda tasan yanzu dai dole ya shigo ɗakinta, amma ga mamakinta sai taji shuru har saida ta buɗe ƙofarta ta fito tsakar gidan ta tsinkayi maganarsa a falon Rashida, kamar zata je ta same shi sai kuma wani zuciyar ya gargaɗeta akan kar ta kuma wani laifin, sai ta juya ta shiga ɗaki tana matsar kwalla, tabbas Abin da ciwo a zuciya dan babu wanda zai fahimci ya Safna taji a wannan lokacin sai wacce ta samu kanta a irin wannan halin, ace kina da kishiya kuma ke ce da girki amma namiji ya nuna baisan da ruwan halittarki ba, zama tayi a carpet tana wani irin kuka saboda wani abu mai nauyi daya tokare mata maƙoshi, a buɗe tabar ƙofar amma har kusan goma saura Zayyad bai shigo ba, haka ta miƙe da kyar ta wuce bedroom ɗinta ta kwanta tana ambaton sunan Allah, duk addu'ar data faɗo a bakinta shi take yi domin kawai ta samu sassaucin halin da take ciki, a haka har taji zuciyarta tayi sanyi sai dai damuwar yana nan daram, hawaye kuma da kanshi ya ƙafe ya daina zuba dan kansa, har barci ya fara ƙoƙarin ɗaukarta.


Zayyad ko tunda ya shiga falon Rashida ya tadda suna cuku cukun ɗaukarta su shigar da ita ɗaki akan zata yi wanka, sai ya ce su bari shi da kansa ya ɗauketa ya kaita bayi yayi mata wanka ya fito da ita ya kwantar a gado, ya shirya ta cikin kayan barci kana ya gyara mata kwanciya ya miƙe da nufin tafiya yana ce mata sai da Safe, Rashida ta marairaice fuska ta kamo hannunsa.


Ji nake yi in ka tafi kamar ba zan sake ganinka ba sai dai na ganni a kushewata.


Dan Allah ki daina wannan maganar.


To ka zauna kayi mini hira in samu barci sai ka tafi.


Ba musu Zayyad ya zauna ya cigaba da yi mata hira, har saida barci ya kamata kusan ƙarfe sha ɗaya kafin ya miƙe ya fito lokacin su Ilham suma sunyi barci, sai su Zaliha da suke kallo a tv yayi musu saida Safe kana ya wuce sashin Safna. Yana shirin buga mata ƙofa sai ya tadda ƙofar a buɗe yake ya shiga da sallama ya wuce ɗakinta ya cire kayan jikinsa, Safna duk tana jin motsinsa koda ta fito ta shiga ɗakin ta samu ya shiga wanka, sai ta ciro masa kayan barcinsa ta aje a gadon ta koma ta zauna, harya fito ya taddata, tace masa sannu da zuwa ya amsa a daƙile, sarai yaga kayan data ciro masa amma sai ya wuce wardrobe ya ciro wasu ya saka, Safna ta miƙe tana cewa.


In saka maka abincin ne?


A ƙoshe nake, zaki iya zuwa ki kwanta dan barci zanyi.


Daga haka ya ƙarasa saka kayansa yabi lafiyar gado ya kwanta, Safna da jikinta ya ɗauki rawa bata ce masa komai ba ta fice daga ɗakin, ta koma ɗakinta ta kwanta tare da jan bargo dan zazzaɓi taji ya rufeta. A wannan daren wani irin ƙunci Safna ta samu kanta a ciki wanda ƙiri ƙiri barci ya kauracewa idonta, sai gabda kiran sallar farko ta samu ya ɗauketa.


****
Washe gari wajen bakwai saura ta farka taga gari ya yi haske, da sauri ta sauko ta shiga toilet ta dauro alwala ta gabatar da sallar asubahi, data idar ta fito ta duba Zayyad amma baya ɗakinsa kuma baya falo hakan ya bata yana sashin Rashida, hawaye taji ya sauka a kuncinta sai kawai ta wuce kitchen ta shiga haɗa musu breakfast. Wajen takwas saura ya shigo ya sauya kayansa tana sauri ta cimmasa a ɗakinsa sai gashi ya fito falo yana saka links ɗin hannun rigarsa.


Ina kwana.


Lafiya, ni zan kai yara makaranta daga can zan wuce shago.


Na gama haɗa breakfast ba zaka dawo kaci ba.


Kici kawai dan sauri nake yi.


To anjima me zan dafa?


Ki dafa abinda ya sauwaƙa.


Yana kaiwa nan ya juya ya fice, da ido Safna ta bishi har ya fita tamkar wani baƙon mutum haka ya zame mata, dan fuskarsa a tamke yake yi mata magana, sosai Zayyad ya shayar da ita gubar mamaki bata taɓa zaton haka yake ba, jiki a sanyaye ta koma kitchen ta ɗiba breakfast ɗin soyayyen arish da kwai ta fito ta nufi wajen maigadi Zayyad yana tsaye tazo ta wuce, ta miƙa masa yana zabga mata godiya, Safna tace.


Anjima akwai sauran tuwo zan kawo maka, sannan in ka samu almajiri ka yi mini magana shima na saka masa dan yana da yawa kuma kar ya lalace.


To 'yar baba nagode Allah ya saka a mizani.


Ta amsa da amin ta zo ta wuce su lokacin yaran sun fito sun shiga mota ga Anisa tana yi musu bye bye, ta shiga ɗakinta ta rufe da key ta ɗauko sauran abin karin tazo ta zauna, da kyar ta iya cin kaɗan ta mayar da sauran ta koma ɗakinta ta kwanta ta shiga karanta wasiƙar jaki.


A takaice haka Safna ta fita girki Zayyad bai ci abincinta ba, sannan tunda Rashida ta amsa girki in ya leƙota da safe to bata sake ganinsa sai wata safiyar, tayi kuka har ta gode Allah ga ciki ga ciwon kunne da har lokacin yana mintsilinta ga damuwar Zayyad, bata iya cin abinci sai ta tilastawa kanta sai yawan shan ruwa, nan da nan ta rame ta yi wani haske, taƙi faɗawa kowa halin da take ciki face Allah dan shine kaɗai gatanta.


****


Bayan kwana biyar.


Wanda ya kama ta amsa girki ta fita, Rashida ma ta amsa hatta fita itama, Safna ta kuma tq amsa har tayi kwana ɗaya jiya, kuma har lokacin Zayyad bai daina fushi da ita ba kusan mako guda suna abu guda, a ranar ne ta yanke shawarar tunkararsa da maganar dan ta bashi haƙuri su shirya, saboda ita ce ke cutuwa saboda shi yana walwalarsa a sashin Rashida wacce har ta ji sauki Anisa ta tafi gida sai Zaliha ce ta rage tana ɗan tayata aiki. Ranar ta tura masa text akan tana so a kawo mata fulawa zata yi ɗan wake, duk da in ta tura saƙo baya yin reply amma yana aikowa. Can wajen ukun rana ya aiko da fulawa haɗe da kwai da mangyaɗa, nan ta soma haɗa ɗan waken saboda bata ci komai da rana ba shi take jira, kafin La'asar ta gama dan haka ta zuba taci haɗe da kayan miya data yanka da kwai data dafa, taci sosai kuwa dan ta jima bata ci abinci haka ba, ta tsame sauran a matsami akan anjima zata ci in kuma yace zaici duk sai ishesu tunda har lokacin baya cin abincinta, ta samu ta gabatar da sallar La'asar sai ta zauna a adduna tana jan hasbulallahu wa ni'ima wakil ƙafa 450, Ya hannu Ya mannanu ya bidi'assamawati wal ardi ya zaljaluli wal ikram shima ƙafa ɗari, tare dasu salatin annabi dubu da Bisimillahi dubu, haka ta kai kusan ƙarfe biyar tana lazumi daga bisani ta yi addu'a ta miƙe ta fito falo ta kwanta a doguwar kujera ta soma kallon MBC bollywood.


Yauma kamar kullun Zayyad bai shigo sasshinta ba koda ya dawo sai wajen ƙarfe tara da rabi, ya shigo ya sameta a falo tana kallo tana ganinsa ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa, ya amsa ba yabo ba fallasa sai ya wuce ɗakinsa ita kuma ta wuce kitchen dan shirya masa abinci, ta gama haɗa komai a babban tire ta fito dashi falo ta ɗaura a table sai ta wuce zuwa ɗakinsa, koda ta shiga taji saukar ruwa alamar ya fara wanka, sai ta zauna gefen gado tana jiransa amma me? ƙarar saƙon WhatsApp ya cika mata kunne dan datarsa a buɗe yake, kamar ance ta ɗauki wayar taga saƙonni yana shigowa ta sama, abinda idonta ya gani na saƙon Saima sai da taji kamar anbuga mata guduma a kai, wanda yasa aljanunta motsawa saita samu kanta da danna PIN ɗinsa wanda ita bata sansu ba amma aljanunta sun yi amfani da hannunta sun buɗe mata, ta shiga WhatsApp ɗinsa tare da shiga number ɗinta Saima nan taga hirarsu na batsa da yawa, sai ta fito ta shiga duba sauran numbers ɗin, nan taci karo da Zuby itama dai kusan hirar da yake yi da Saima suke yi, sai dai yadda suke roƙonsa da magiyar yazo su haɗu ya bata mamaki, kuma a hirar taga yasha tura musu kuɗi, sosai gumi ya gama rufeta dan hankalinta yayi mugun tashi. A lokacin ne Zayyad ya fito daga bayi ɗaure da towel ga wani ƙarami a hannunsa yana goge kansa, Safna ta ɗago tana kallonsa cike da tuhuma shi kuma wani faɗuwa gabansa yayi ganin wayarsa a hannunta, da sauri ya yarda towel ɗin hannunsa yazo ya kwace wayar yana hucci.


Uban waye yace ki taɓa mini wayata.?


Ya ƙare maganar yana kifa mata mari cike sa borin kunya, Safna ta miƙe jikinta babu inda baya rawa tama kasa magana, ta fashe da matsanancin kuka tare da dafe mararta data ɗaure mata, nan take kuma jini ya ɓalle mata.


Last freepage.


_Labari ne ƙirƙirarre mai taɓa zuciya za kiji tamkar kina kallon tv in kina karanta shi, wataƙila kuga labarin yayi kama da labarinki ko na wata to arashi ne, amma na tabbatar irin haka yana faruwa musamman a cikin rayuwar Bahaushe. So da dama matsalolin da mata suke fuskanta acikin gidan aurensu to mata sune suke jefa su a ciki, mu da kanmu muke cutar da 'yan uwanmu mata bisa son zuciya da son kai. Idan kuka bibiye ni a wannan tafiyar akwai faɗakarwa da yawa wanda zaku ilmantu dashi sosai akan zaman aure, tare da ƙarin wasu abubuwan da zaki amfani gobenki._


Don samun cigaban labarin ku biya ₦400 discount daga nan zuwa ranar Lahadi In Sha Allah duba da mutane sunata niman ragi da rokon in duba halin da kasar ke ciki, normal group update sau biyar a sati Monday to friday. VIP ₦1000 zasu samu update duka 7days tare da yuwuwar samun 2pages amma ba kullun ba.


Pay ₦400 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.


Masu matsalar turawa ta Opay saiku tura ta nan.
0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank
[27/09, 10:10 pm] null: *AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 19.


Ght products me Maida Bora mowa💃🏻💃🏻💃🏻 Mai maida mazaje jarumai uwar gida da Amarya suyi ta alfahari da shi shima na alfahari da su🙈😂


Wai haryanzu kina zaune baki gwada ba? Kaima kana zaune baka gwada

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login