Showing 12001 words to 15000 words out of 45829 words

Chapter 5 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

tayi amfani dasu.


Sai ta miƙe tsaye ta mayar da hijab ɗinta Anty Shafa ta miƙe itama ta kama hannunta suka shiga bedroom ɗinta, sauran 'yan uwa suka cigaba da kallon ɗakin wasu har Kitchen suka shiga suna kallon jere, Maryam ma binsu bayan Safna tayi data same su a gefen gado sun zauna tace.


Safna ki cigaba da amfani da magungunarki karki yi wasa dan gaskiya banji daɗin yadda jinnunki suka tashi ba. Da kinji jikinki ba daɗi ki kira ki faɗa dan ayiwa tufkar hanci bana fatan su hanaki zaman ɗakinki.


In Sha Allah zan kula.


Sannan wancen kayan dama ba amfani dasu zaki yi ba duk da bana tunanin kishiyarki zata cutar dake duba da yadda taketa haba haba da auren nan.


Nima dai haka na gani, amma tunda kin ce a kaiwa umma shikenan duk hukuncin data yanken akan kayan zaki ji.


Cewar Shafa, Safna ta turo baki tana cewa.


To in Umma tayi amfani da su ai kamar nice nayi amfani da shi, kuma ban zargi komai ba wlh.


Masha Allah gwara ki tsarkake zuciyarki. Mu zamu tafi ki tashi ki ɗauro alwala ki zauna da ita a jikinki In Sha Allah wani aljani ba zai sake tashi ba.


Cewar Maryam kana ta juya zata fita.


Ni kaɗai zaku bari? .


Eh mana, to ƙawayenki duk matan aure ne ko wacce tayi gidanta balle su zauna wani siyan baki, koda yake an bar yayin wannan, ki taso ki rufe ƙofar zan kira Zayyad ɗin na faɗa masa mun fito yazo ya sameki.


To tace mata kana Shafa ta miƙe itama suka fita, ba ɓata lokaci suka tattara suka tafi aka bar Amaryar Zayyad ita kaɗai cike da kewan gidansu tare da tunanin sabon rayuwar da zata fara a cikin gidan aurenta.
[09/09, 5:44 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 6.


Safna tana kwance tayi lamo dan har barci ya fara fizgarta sai taji wani irin bugun ƙofa kamar tarar aradu, a razane ta tashi ta zauna dan ƙirjinta saida yayi wani irin bugawa saboda zazzafar tsoro daya dirar mata, jin an cigaba da buga ƙofar ya sata saukowa daga gado ta fito falo, sai ta isa ƙofar ta kara kunnenta dan ji hira sama sama data fito, nan ta tsinkayi muryar wata tana cewa.


Wannan 'yar iskar amaryar 'yar rainin wayo ce, ji yadda muke buga mata ƙofa amma taƙi ta buɗewa.


Anisa muje kawai tunda bata buɗe ba dama sai da nace ki bari mu ganta zuwa gobe amma kika nace sai kin zo.


Na ƙosa ne naga wacce tafi Anty Rashida da Zayyad taketa rawar ƙafa akanta, amma taci bashin wannan wulaƙancin data yi mana.


Safna tana jinsu amma taƙi buɗewa dan hirarsu ya tabbatar mata da 'yan uwan Rashida ne, banda niman fitina taya daga kawota zasu zo suce zasu ganta ai koma miye sabari washe gari tunda yanzu ango ne ya dace ya shigo ɗakin ba wasu ba, imma ganinta ne zasu gaji da ita tunda zamane na dindindin. Sai ta koma cushing ta kwanta tana tunanin su, ashe gwara data rufe ƙofar da Anty maryam ta ce mata, bata san da wanne ma suka zo ba a cikin wannan daren.


Anisa suna shiga falon Rashida ta tsaya tana zagin Safna, Zaliha tana tayata tare da wasu 'yan uwansu da suka je tare, dan zasu kai kusan su biyar waɗanda suka je sashin Safna da niyyar su ganta, Rashida ta kallesu tana cewa.


To kuma uban waye yace kuje, ai gwara data yi muku haka gobe kwa ƙara.


Amma meye laifinmu dan munje muyi mata hira kafin angon yazo. Wannan ai wulaƙanci ne tana ji ana buga ƙofar tayi banza damu.


Rashida ta ƙanƙance idonta tana cizon yatsa ta miƙe tana faɗin.


Aiko saita san ta wulaƙantaku dan daren yau In Sha Allah ba zata kwana cikin farin ciki ba, sai nayi amfani da wannan damar na bar mata tarihin da har ta koma ga Allah ba zata manta da shi ba. Miko mini wayata na kira Zayyad.


Ta faɗa tana nuna inda ta saka chargy, Nan suka saki shewa Anty Wasila tana cewa.


Yauwa 'yar gari gwara ki fara nuna ikonki na uwargida, tasan cewa kece da gida bata isa ta samu yadda take so ba sai in kin so hakan ya faru, komai sai da makirci gwara ki hau kan layin dana ɗauraki shima zai miki amfani sosai matsawar kin iya takunki.


Murmushi Rashida ta saki ta koma ta zauna tana ɗaura ƙafar damanta akan center table.


Ai tunda ta yarda ta auri mijina ita da farin ciki sunyi sallama.


Sai ta amsa wayar da Zaliha ta ɗauko mata, dama falon ba kowa sai su dan duk mutane sun watse wasu baƙin kuma suna can ɗakinta sun kwanta wasu kuma sunje gidansu, sai ta shiga wajen kira a wayarta ta danna number ɗin Zayyad, bugu biyu ya ɗauka zata yi magana ya rigata.


Gani nan na kusa ƙarasowa gida ina hanya.


Cikin yanayi na rauni da sanyin murya tace.


To sai ka ƙaraso.


Rashida lafiya kuwa naji muryanki cikin damuwa.


Ka bari dai ka ƙaraso ɗin.


Tana kaiwa nan ta kashe wayar tana sakin wani shu'umin murmuahi, Zayyad kam kasa haƙuri yayi ya shiga kiranta amma taƙi ɗagawa, hakanan ya samu kansa cikin damuwar yadda yaji muryarta, dan sosai yake tausayinta ba ƙaramin jarumta tayi ba da auren nan nasa yana jinjina mata akan haka. Rashida ta kalli Anisa tana cewa.


Ko ki tafi gida yanzu ko ki shiga ɗaki ki ɓoye kanki dan abinda na shirya akanki ne bana so ya ganki.


Wani irin na tafi ai sai dai na ɓoye dan wlh ina gidan nan har sai amarya ta gama kwanakinta kafin mu tattarara muyi gida.


Ta faɗi haka tana wani fari da ido sai ta yi gaba ta shiga ɗakin Rashida ta sanya wayarta silent ta kunna data ta fara chart, nan kuma sauran dake falon suka shiga shewa da cigaba da hira. Lokacin da suka ji dirar motar Zayyad sai duk suka shanye fara'arsu suka yi fuska tamkar waɗanda aka yiwa mutuwa, har ya shigo da motarsa cikin gida yayi parking sai ya ɗauko ledar kazar daya siyawa Rashida yabar nasu a cikin mota, akan in ya fito daga side ɗinta zai tsaya ya ɗauka sai ya wuce. Yana isa ƙofar ya murɗa handle ya shiga da sallama suka amsa masa amma yadda yaga fuskokinsu cikin damuwa yasa shi tsayawa tare da amsa gaisuwarsu, Rashida ta miƙe ta iso inda yake ta amsa ledar hannunsa.


Sannu da zuwa.


Lafiya na ganku haka?


Muje ɗakinka sai nayi maka bayani.


Tace tana wucewa gaba sai ya bi bayanta ya saka makullin ya buɗe ɗakin ya shiga ta bishi a baya tare da rufo ƙofar.


Rashida ya na ganku duk cikin damuwa ko wani abu ya faru ne.?


Zayyad ban so faɗa maka ba saboda ganin yau ranar farin cikinka ne, ka bari zuwa gobe In Allah ya kaimu sai nayi maka bayani.


Kinga Rashida ki faɗa mini kawai dan hankalina bazai kwanta ba ganinki cikin damuwa.


Hmmmm dama su Anisa ce suka je side ɗin Safna domin su yi mata hira kafin ka shigo saboda 'yan uwanta sun tafi sun barta ita kaɗai, amma abin mamaki sun yi mata sallama sun buga ƙofar shuru bata buɗe ba tayi banza dasu, ban taɓa tunanin Safna zata yi haka ba duba da yadda na ɗauketa, wlh har cikin raina yadda Anisa da Zaliha suke a gurina haka na ɗauketa amma ita ga dukkan alamu da wata manufar tazo gidan nan. Ace yadda na dinga zuzuta kirkinta ga 'yan uwana amma lokaci guda ta gwasaleni tasa naji kunya, in zata wulaƙanta kowa ai bai dace ace tayiwa 'yan uwana haka ba kodan yadda na ɗauketa.


Ta ƙare maganar cikin zubda kwalla saboda kasa danne baƙin kishinta daya zo mata wuya, in ta tuna da Zayyad zai kwana da wata ji take yi kamar ta haɗiyi rai ta mutu, Zayyad jikinsa yayi sanyi yana dubanta yama kasa magana saboda tsantsar mamakin Safna dan bai taɓa kawo zata yi irin haka ba, sai ya nisa ya kamo hannun Rashida.


Kiyi haƙuri kuma In Sha Allah zan tsawatar mata dan ba zan taɓa yarda ta wulaƙanta ki ba saboda kina da matuƙar muhimmanci a gareni.


Abinda yayi mini ciwo har nasan dagangan tayi haka, sunce suna jin ƙarar waƙa daga wayarta a falo har ma tana rerawa, hakan ya tabbatar da ta sane daga ɓangarena ne aka je gunta, ashe yadda na ɗauki Safna ba haka ta ɗaukeni ba, nayi haƙuri na danne damuwa da kishina na kwantar da hankalina ganin nasan wacce zaka ɗauko mini, ba zamu samu matsala ba amma daga zuwanta ta wulaƙantani, to eh mana ni tayiwa ba 'yan uwana ba.


Ta ƙare tana rusa kuka mai cuma zuciya, ran Zayyad in yayi dubu to ya ɓaci dan har ga Allah ya yarda da duk bayaninta, duba da yadda yasan halinta da yadda ta bada haɗin kai ga aurensa. Jayota yayi jikinsa yana buga bayanta tare da bata haƙuri akan zai ɗauki mataki, ɗagowa tayi tana danne kukanta.


Nifa bana faɗa maka bane dan ka yi mata magana ba, kawai na kasa danne abin a raina ne dan ta yi matuƙar bani mamaki banyi zato ba sam, kuma saboda su Anisa sunyi fushi sosai har ta kasa zama a gidan ta wuce gida, dama tun ɗazun da yan uwanta suka kawo ta nan sashinsu bayan fitarsu munji suna ƙananun magana, amma ban kawo komai ba tunda ni da gaskiya zan zauna da Safna.


Haba Rashida meyasa zaki bar Anisa ta tafi, Allah yasa ba zata faɗa a gida ba.


Saida na kwaɓeta nace su bar maganar a iya tsakaninmu dan kar wasu suyi mini dariya.


To shikenan bari zan samu Safnar, wannan kazarki ce kici ɗaya keda yara sai ki bawa 'yan uwanki suci ɗaya. Bari naje sai da safe.


To Allah ya tashe mu lafiya.


Ta faɗa a raunane, Zayyad ya fito tana biye dashi har ya rufe ƙofarsa ya nufi waje, ta tsaya a ƙofar daki ya isa motarsa ya ɗauki kazarsu da lemu ya wuce part ɗin Safna yana ɗaga mata hannu, murmushin yaƙe tayi masa tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki yana taso mata, bata taɓa jin tsanar Safna ba irin na yau dan ji tayi kamar ta babbaka musu wuta su ƙone akan ya kasance tare da ita, hakan yasa ta saki ƙofar ta fito a hankali ta lallaɓa ta isa windon Safna ta ƙara kunnenta dan jin wainar da zata kaya.


Zayyad kuwa yana isa ƙofar ya buga yana ambaton sunan Safna, dama tana falo sai ta aje wayarta da sauri ta miƙe ta isa ƙofar ta buɗe kanta a sunkuye ta kama ledar hannunsa mai makon ya sake mata sai ya riƙe gam, ya juya ya rufe ƙofar tare da wuceta ya samu kujera ya zauna yana cire hular kansa fuskarsa a matuƙar haɗe, Safna bata ga fuskarsa ba shiyasa bata gane da wani yanayi ya shigo ba, ta samu one seater ta zauna tana matsa yatsunta.


Samnu da zuwa.


Safna!


Ya ambaci sunanta cikin kausasa murya ba tare da ya amsa mata sannu da zuwan ba, yadda taji muryarsa yasa ta ɗago kai da sauri taga fuskarsa a murtuke sai taji gabanta ya faɗi tana dubansa, ya ɗaura da cewa.


Ina so ki sani idan zaki wulaƙantani ko 'yan uwana ko wani nawa kiyi amma banda Rashida da 'yan uwanta, Domin banda kamarta macece mai haƙuri da kawaici ta yi matuƙar bani haɗin kai wajen auroki, bazan lamunci cin mutunci ko cin zarafinta ba dan wlh zan iya yin komai akanta saboda ba dan bana sonta bane na auro ki. Haba daga zuwanki zaki fara nuna halin da ban taɓa zatonki da shi ba, ace 'yan uwanta sun zo gunki dan suyi miki hira kan na dawo amma sunyi miki sallama da buga ƙofa suna jin motsinki a falo kinyi banza dasu, to daga yau karki ƙara bazan ɗauki wulaƙanta mutane ba.


Ya ƙare maganar cikin nunata da yatsa, Safna kam tunda ya fara magana ta sunne kai ta soma zubda hawaye, jikinta har zafi yayi dan nan take taji zazzaɓi take ji, ace a ranar daren amarcinsu su fara da faɗa wanda bata san hawa ba bata san sauka ba, ta san dai wannan makirci ne kawai suka shirya mata amma yadda suke buga ƙofar kamar tarar aradu ba zaisa ta buɗe ba dan ta tsorata dasu, sannan ba suyi mata sallama ba balle tace cikin lumana suka zo. Zayyad ya miƙe ya cire babbar rigarsa ya aje a cushing ya wuce kitchen dan ɗauko plate, bai damu da yanayinta ba ko ya lallasheta dan shima yaji zafin abinda tayi kuma dole ne ya nuna mata kurenta yadda ba zata kuma aikata hakan ba, ya dawo da plate da kofi a hanunnsa ya zauna a carpet ɗin tsakiyar ɗakin ya ciro kazar a leda wanda aka ƙunshe a foil paper ta ɗaura a plate ya buɗe ya fara ci yana cewa.


Ki sauko mu ci abinci.


Ya ƙare maganar ba tare da wata kulawa ba, Safna miƙewa tayi bata ce masa komai ba ta wuce zuwa bedroom ɗinta, tana shiga ta kwanta a can ƙuryar gado tana kuka mai tsuma zuciya, ga mugun ciwon kai daya addabeta ga kuma zazzaɓi da ɓacin rai daya dirar mata a lokaci guda, ta rasa tunanin me zata yi haka ta lumshe ido ta rufe sai ruwan hawaye ne ke zuba. Zayyad a zatonsa ko ta shiga danta yi wani abu ne ta fito amma shuru bata dawo ba, har ya gama cin kazarsa ya naɗe sauran ya aje plate a kan center table da ragowar lemun kwalin, ya miƙe ya ɗauki hula da babban rigarsa ya shiga cikin bedroom ɗin, koda ya ganta a kwance bai kulata ba dan ya kula fushi tayi shi kuma akan Rashida zai ɓata da ita dan ba zai lamunci haka daga gareta ba, ya aje rigarsa ya fito falo ya isa kitchen ya sauko da butar kattle ɗinta da yake cikin kwali ya ciro shi sai ya wanke butar ya zuba ruwa ya jona ruwan wanka, sai ya dawo falo ya zauna yana duba saƙonni a wayarsa wanda duk na mutane ne da suka yi masa fatan Alkhairi da aurensa.


Rashida lokacin data ji Zayyad yana korowa Safna faɗa, wani sanyin taji a ranta dan haka ta bar jikin window ta koma ɗakinta zuciyarta cike da farin ciki, addu'a kawai ta shiga jerowa akan Allah yasa su kwana suna faɗa kar wani abu ya wakana a tsakaninsu, haka ta sake taci kazar daya kawo tare da 'yan uwanta waɗanda ba suyi barci ba. Sun kai kusan sha biyun dare suna hira kafin daga bisani ko wanne ya nima gurin kwanciya.


Zayyad bayan yayi wanka sai ya zo kan gadon ya kwanta yana duban Safna da take sauke ajiyar zuciya da alama barci ya ɗauketa, ba haka yaso daren farkonsu ya kasance ba, dan ya jima yana mafarkin yadda zai kasance tare da ita da irin kyakkyawar tanadin da yayi musu, sai dai kash Allah bai nufi haka ba dan har lokacin bai yi nadamar abinda yayi mata ba saboda laifinta ya gani, kuma a tunaninsa ta wannan hanyar ne kawai zai magance ɓarakar data ke shirin kunna masa a gida, daga zuwanta zata fara haddasa damuwa wanda bai zaci haka daga gareta ba, da tunani barkatai barci yayi awon gaba dashi.


****


Da asubahi kiran sallar wayar Safna shine ya tayar dasu duka su biyun, dan dama tana da app ɗin da ke kiran sallah duk in time ɗinsa yayi, ta farka amma ta kasa kwakkwaran motsi saboda ciwo da jikinta ke yi mata, ga kuma wannan ciwon kai har yanzu dan a cikin barci ma tana jinsa dan dai barcin yaci ƙarfinta ne, Zayyad ne ya miƙe ya shiga toilet ya ɗauro alwala ya fito yana ambaton sunanta, kamar ba zata amsa shi ba amma ta cije ta amsa tana tashi zaune.


Ki tashi kiyi sallah zanje masallaci na dawo.


To tace masa sai ya fice ita kuma ta sauko ta wuce falo ta shiga kitchen, ta ga yayi amfani da kettle sai ta zuba wani ruwan ta kunna ta jira ya fara zafi sai ta dawo ta ɗauki buta a bayi ta koma ta zuba ruwan zafin a ciki sai ta ƙara wani ruwan a kettle wanda in ta idar da sallah zata yi wanka, ta koma ɗaki tayi alwala da ruwan zafi dan yadda take jin jikinta ba zata iya yi dana sanyi ba, data gama ta fito ta gabatar da sallah.
[10/09, 6:08 pm] null: https://chat.whatsapp.com/D5ISXoMOGGR9PPoswkybsj


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 7.




Safna tana zaune a dadduma tana lazumi, Zayyad ya shigo bedroom ya sameta bisa sallaya, zama yayi a gabanta yana duban fuskarta, ita kuma ta sunne kai ƙasa tana cewa.


Ina kwana.


Bai amsa ba sai ya ɗago fuskarta yaga idanunta a kumbure wanda yasa shi jin ba daɗi a ransa, Safna lumshe ido tayi hawaye ya soma zuba a kuncinta.


Saboda nayi miki faɗa shine zaki hukunta kanki da kuka har idanunki suna kumbura haka.


Kayi haƙuri ba faɗar daka yi mini bane ya sani kuka, kewar gidanmu da su Umma ne yake sani zubda kwalla. Kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login