Showing 39001 words to 42000 words out of 45829 words

Chapter 14 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

ma dauriya kawai take yi tana tusa abin karin ba dan tana jin daɗinsa ba, ace yarinya ko wata biyu bata cika a gidan aurenta ba amma matsaloli suna biyowa baya irin haka, duk ta ƙosa taji meke faruwa, ɓangaren Abba kuwa yana sane yaƙi cewa kowa har sai ya karya tukuna, shiyasa daya kammala ya miƙe ya shige ɗakinsa ya shirya cikin manyan kaya har da malum malum kafin ya fito yana gyara zaman hularsa ya samu guri ya zauna, wanda a lokacin duk sun gama karyawa Safna ce dai data kasa cin komai tana wasa da yatsunta babu kuma wanda yace taci dole, Abba yayi gyaran murya yana dubanta wanda yasa Safna tattaro duk natsuwarta.


Mamana meya kawo ki gida a irin wannan yanayin? Bana so kiyi mini karya ki faɗi duk abinda ke faruwa muna saurarenki.


Safna bata taɓa zaton Mahaifinsu zai tambayeta cikin sassauci haka ba, hakan yasa ta samu damar sauke ajiyar zuciya abinda take ji ya tokare mata a wuya ya sauka, sai ta shiga basu labarin irin matsalar data fara fuskanta da Rashida har kawo abinda ya faru yau, sai ta ja fasali tare da sauraren me zasu ce, umma tace cikin damuwa.


Ban zaci haka daga gareki ba Safna ina yabonki da haƙuri ashe ba kida shi, meyasa zaki biye mata? Kenan duk jan kunne da faɗar da muka yi miki ya tashi a banza ko, wannan ba shine tarbiyyar da muka baki ba, sai ki biye mata kunyi faɗa keda nasan aljanunki bama sa tashi. Me yasa sai yanzu zasu yi haka kuma anata magani.


To mugunta suka shirya mata mana, ace anyi maganinsu sai da aka yi aure zasu riƙa tashi, ashe maganin ya zama aikin banza. Sannan Safna meye dan sun fasa miki plate, saiki rabu dasu in ma kina buƙatar wasu ne saiki kira ki faɗa a siya miki, kuma bai dace ki hukunta yarinya ba tunda har uwarsu tanuna ki daina takurawa yaranta, wataƙila da su zata riƙa amfani dan ganin tana tunzuraki aljanunki na tashi, kinga in hakane to ta samu nasara akanki tunda gashi tayi sanadin da Mijinku ya koro ki gida kuma ko wata biyu baki rufa da aure ba, wannan kinga ya zama kin zubar mana da mutunci da ƙima, dan haka daga yau wannan ya zama na farko da ƙarshe, na rantse da Allah idan har kika sake biye mata kuka yi faɗa koda ta baki ne Zayyad ya koroki gida to ki sani sai na yi miki dukan da tunda kika zo duniya ba ayi miki irinsa ba. Idan ma tayi miki wani abu ki jira ya dawo ki faɗa masa shi ya ɗauki mataki, amma zanfi so karki zama mai kai ƙara ki zama mai haƙuri juriya da kawar da kai, ki tashi cikin dare ki faɗawa Allah ki sata a addu'a akan Allah yayi miki ganinta ya kawar da saɓani a tsakaninku, in kinyi haka In Sha Allah zaki ga kyakkyawar sakamako, dan haka yanzu zan fita bazan jima ba zan dawo ki shirya zan mayar dake gidan mijinki. Ke kuma sai ki ƙara ja mata kunne dan wlh bazan ɗauki wannan shegentakar ba.


Abba ya ƙare maganar akan umma, to tace masa kana ta yi masa a dawo lafiya ya wuce ya fita, a lokacin Mudan ya soma magana.


Gaskiya idan kika ƙara faɗa da kishiyarki wlh har gida zan zo in miki shegen duka, haba Safna ya za ki biye mata kuyi abu sai kace a zamanin jahiliyya, karki kuma aikata haka dan ban sanki da rikici ba, yau da Maryam ce aka ce tayi haka bazan musa ba dan ita tana da zafi da gatsali.


Faɗa mata dai danni wlh mamaki ma ta bani, in ance min Safma ce tayi haka zan karyata amma da yake da bakinta tayi bayani shiyasa na gasgata. Nasan baki san ya zaman kishi yake ba tunda nan ba ita gareni ba, kuma suma 'yan uwanki ba mai kishiya amma kuma mun baki tarbiyyar da zaki iya zama da kowa duk mugun halin mutum, karki biyewa zuciya Safna dan ba tada ƙashi ƙarshe ya sauke ki a tudun dana sani. Ko wannan koroki da yayi ai ya zama cin mutuncin gidan nan dan haka karki ƙara, tunda har ta nuna miki halinta na son rashin zaman lafiya sai ki tura mata aniyarta ki zuba mata ido, ki kama kanki ki kula da mijinki kawai, yaranta in kin kinji zaki iya kyautata musu kiyi amma ki kauce duk wani abu da zaisa yaran su samu abin faɗawa Mamansu kinyi musu dan a zauna lafiya.


In Sha Allah Umma zan kiyaye nima wlh ba a son raina hakan ta faru ba.


Ki dai kiyaye, sannan In Sha Allah za a kawo miki wasu magungunar kina amfani da su dan su daina tashi. Ki kuma cigaba da kyatatawa mijinki iya iyawarki. Sai hankalinki ya kwanta yanzu, ki samu ki karya kafin babanku ya dawo.


Safna tace to tana mai sauke ajiyar zuciya dan bata taɓa zaton zasu yi mata da sauƙi haka ba, kunun ta iya sha bata ci ƙosai ba. Bayan ta gama umma ta jata ɗakinta ta cigaba da bata bayanai na yadda zata zauna da Rashida lafiya, Safna ta baza kunne tana saurare kuma sosai ta gamsu da kuma ɗaukar alƙawarin aikata hakan.


******


Bayan sun isa gida nan Zayyad ya barsu maman Rashida suka shiga hidima da ita da magani, ya fito ya nufi sashin Safna sai ya tadda bata nan, shuru yayi yama rasa tunanin da zaiyi daga bisani ya fito ya shiga motarsa sai ya wuce gidan hajiyarsa danya shaida mata abinda ke faruwa. Yana fita Rashida ta miƙe da gudunta ta nufi ɗakinta ta faɗa tiolet tayi fitsari, data gama ta fito tana sauke numfashi sai ta samu guri ta zauna tana cewa.


Tun ɗazu fitsari ya matseni amma ina tsoron na motsa na ɓata shirinmu.


Ai magana ma ta ƙare tunda mun je gurin magani kuma yaji komai da kunnensa, ko zuwa anjima zaki iya yin tafiya sai dai kiyi shi a hankali tunda sauƙi bai samuwa lokaci guda sai a hankali, kuma kinga wannan abinda ya faru shine abinda zan iya ɗauraki akai da zaki samu sassauci daga Zayyad ɗin, kuma na tabbatar dole hankalinsa yafi karkata akanki saboda jinyar da zaki yi, to sai ki san yadda zaki ja ragamar zaren ki kama shi a hannu, ni zan wuce su Anisa sai su zauna miki Allah yasa daga can ya bita da takardan saki.


Cewar maman su, Zaliha suka amsa da amin kana ta miƙe, Anisa ta tareta da cewa.


To yanzu malam yaci dubu ɗari kenan a bilis.


Rabonsa ne ya tsaga mu dai buƙatarmu ta biya shine kawai, ko bai yarda da kishiyarta zata yi mata asiri ba mun dai saka masa shakku da kokwanto a zuciyarsa, kuma daga haka komai zai kankama.


Tana kaiwa nan a maganarta ta yi hanyar fita suka rakata har mota ta shiga suka wuce kafin suka dawo ciki suka tadda Rashida zaune ta ɗaura ƙafa daya kan daya tana danna waya.


Sai kinyi ko ba fosta uwargidan Zayyad, duk wanda ya shiga gonarki sai kin ga bayansa da izinin Allah.


Cewar Zaliha, Rashida ta saki wani shu'umin murmushi.


Ai yanzu wasan zai fara, ba dai ta yarda ta auri mijina ba hmmm, cikin ruwan sanyi zata bar gidan nan da ƙafafunta, dama hanya nake nima kuma mama ta ɗaurani a kai.


Ta ƙare maganar tana turo ɗankwalinta gaban goshi, Zaliha ta miƙe ta nufi ƙofa ta saka key ta dawo ta zauna.


Saboda tsaro kar muna cikin hira muga Zayyad ya dawo ido ya raina fata.


Ta ƙare tana 'yar dariya, nan suka cigaba da hirarsu Anisa ta miƙe ta shiga kitchen dan haɗawa Rashida abin kari saboda tace yunwa take ji bata karya ba.


*****


Zayyad yana isa gidansu ya samu Hajiya a baranda bisa tabarma ta kishingiɗa da filo, tana ganinsa ta miƙe ta zauna tana murmushi har ƙaraso ya zauna ya shiga gaisheta, ta amsa tare da tambayarsa iyali, Zayyad yace lafiya lau kafin ya soma bata labarin duk abinda ya faru, hajiya ta riƙe haɓa cike da mamaki.


Amma banji daɗin wannan labari ba, meyasa Safna zata biye mata ina yi mata kallon mai hankali da tarbiyya.


Wlh Ammi abinda ya bani haushi kenan nace ta tafi gida. Kuma abinda yake bani mamaki yadda aljanunta suka tashi dan tace lokacin tana gisa basa tashi saboda suna magani kuma har yanzu ma ana aiko mata da magani daga gida.


Zai yuwu ɓacin rai ya kawo su, tunda da yawan masu aljanu in ana faɗa ko tashin hankali yana saka su tashi, amma ni maganar da kace wai asiri aka yiwa Rashida shine hankalina bai ɗauka ba, taya daga faɗa sai kuma ta zube ace wai asiri ne, sai dai in itama tana da aljanun ba a sani ba.


Wlh Ammi nima abinda na gani kenan shiyasa naso muje islamic chemist, amma mamanta ta ce can gurin malam na kan kwana zamu.


Ai tunda sune suka zaɓi haka shike nan sai a jira a ga aikin maganinsa tunda an zuba kuɗi har dubu ɗari, Allah ya kyauta gaba amma banji daɗin da kace su tafi gida ba kaga iyayen Safna ba zasu ji daɗi ba dan ba a kyauta musu ba, tunda har ka iya haƙuri da matsalolin rashi meye zaisa ba zaka yi mata uzuri ba tunda wannan ne na farko kuma faɗan bada ita aka yi ba da aljanunta suka yi. Gaskiya karka sake yin haka ko nan gaba domin hakan ke nuna baka fi ƙarfin gidanka ba ka kaza tsawatarwa.


In Sha Allah zan gyara kuma nima sai daga baya naga bai dace data tafi ba, na duba ta a ɗaki naga ko tana nan muyi magana sai na tadda ta tafi.


To ba dole ta tafi ba tunda kai kace hakan, Dan Allah Zayyad ka zama tsayyen namiji a gidanka, kasa a ranka irin haka zai faru koma fiye da haka tunda ka haɗa mata biyu a gidanka, idan kuma zaman lafiyar bazai samu ba ina ga gwara ka raba musu gida hankalin kowa ya kwanta.


In Sha Allah zan kula sosai, kuma ni yanzu inna ce zan raba musu gida hayar ne bana so tunda Allah ya rufa mini asiri da gidana. Zan cigaba da lallaɓawa haka.


To shikenan Allah ya shiga lamarin ya baka ikon Adalci a tsakaninsu, bari na kimtsa sai ka kaini na duba jikin Rashida.


Ameen ya ce mata sai ta miƙe ta shiga ciki ba jimawa ta fito cikin shigar doguwar rigar atamfa da hijab suka wuce suka shiga mota sai ya jasu. A hanya Ammi ke ce masa lallai zuwa yamma yaje gidansu Safna ya bawa iyayenta haƙuri ya maido da matarsa, yace mata to, nan dai ta dinga yi masa faɗa da shawarwarin yadda zai zauna da su cikin hikima.


Lokacin da suka isa Zayyad yayi parking a ƙofar gida kana suka nufi sashin Rashida, sai da suka buga ƙofar dan sun tadda shi a rufe, Zaliha tazo ta buɗe musu suna ganin Hajiyarsa ce suka shiga yi mata sannu da zuwa har suka ƙarasa cikin falon suka zauna, suka gaishe da Ammi ta amsa tana yi musu ya mai jiki.


Da ɗauki bata jima da samun barci ba.


Cewar Anisa, Ammi ta shiga yi mata addu'ar samun sauƙi cike da tausayinta, dan shimfiɗa suka yi mata akan carpet suka ɗaura kanta bisa pillow, duk tana jin hirarsu dan idonta biyu suka yi karyan tana barci, kiran daya shigo wayar Zayyad shine yasa shi miƙewa ya fita danya amsa, ya barsu da Ammi tana tambayarsu yanayin jikin nata.


...
Safna.


Abba bai jima ba ya dawo nan yace ta fito su wuce, ba musu ta fito har waje umma ta rakota tana ƙara ja mata kunne, suka shiga motar Abban suka wuce, shima a mota faɗa da nasiha ya dinga yi mata har suka ƙaraso ƙofar gidanta, yayi parking a waje yace ta shiga ta kira Zayyad in yana ciki in kuma baya nan ta shiga ɗakinta ta zauna anjima zai dawo, Safna tace to kana ta sauko a motar ta buga gate mai gadi ta buɗe mata ta shiga, wanda a lokacin ne Zayyad ya fito ya amsa waya, yana jin buga gate ya mayar da hankalinsa can sai ga Safna ta shigo ya ganta, nan take yasha kunu dan har lokacin bawai ya sauko daga fushin daya ke yi da ita bane, har inda yake tsaye ta ƙaraso ta tsaya a gabansa ya gama wayar kafin ya dube ta.


Dama ashe kinfi son ki tafi gidan, kika sa ƙafa kika tafi ko.


Bani kaɗai bace tare da babanmu nazo yana waje yana jiranka.


Ta bashi amsa tare da kaucewa maganarsa, dan itama har lokacin haushinsa take ji saboda ya raina mata wayo shi yace ta tafi amma yana ƙorafin ta tafi, Zayyad bai ƙara magana ba ya nufi gate ya fita, sosai yaji kunyar ganin babansu Safna dan baiyi zaton zai dawo da ita ba, ya isa inda yayi parking ya risina yana gaida shi, Abba da yake jikin motarsa a tsaye ya miƙa masa hannu akan su gaisa, Zayyad yaji kunyar miƙa masa hannu sai ya noƙe, haka suka gama gaisawa Zayyad ya shiga bashi haƙuri akan abinda ya faru tare da faɗin dama ya bari anjima yaje ya dawo da ita, Abba yace ba komai nan shima ya bashi haƙuri ya kuma tabbatar masa da za a cigaba da nima mata maganin aljanunta, sannan sunyi mata faɗa sosai ba zata kuma aikata abinda ya faru yau ba, sosai Zayyad yaji kunyar Abba kamar ƙasa ta buɗe ya shiga, sai yanzu ya gane bai kyauta ba daya turata gida, daga bisani Abba yace zai tafi Zayyad yayi masa godiya yaje jikinsa yana rawa ya buɗe masa mota ya shiga ya tuka yana tsaye har ya bar unguwar, a lokacin ne ya samu damar sauke ajiyar zuciya kana ya juya ya shiga gidan cikin sanyin jiki.




_Zaku iya fara biyan kuɗinku domin saura page ɗaya mu gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. ₦500 ne kuɗin, dan Allah ku mara mini baya._


Pay ₦500 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.


Masu matsalar turawa ta Opay saiku tura ta nan.
0106956864
Ramatu Muhammad Kabir
Access bank
[25/09, 7:00 pm] null: https://whatsapp.com/channel/0029VafY1c50LKZI3eXehh3Y


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 18.


Ght products me Maida Bora mowa💃🏻💃🏻💃🏻 Mai maida mazaje jarumai uwar gida da Amarya suyi ta alfahari da shi shima na alfahari da su🙈😂


Wai haryanzu kina zaune baki gwada ba? Kaima kana zaune baka gwada ba? mata da Maza nata k'ara martaba da kima adalilin ght products, wai kun tsaya kallo? Shin ko sai gwad'o yayi muku k'afa ne?🤔🤥


Yar uwa da d'an uwa ku garzayo in hada muku kayan gyara iya kudinku iya shagalinku.


Mrsjmoon bata tsauwalawa ku dai ku zo musa labule in gyaraku ciki dawaje kuyi tsaf tsaf kuyi cif cif kuyi zaqwai zaqwai kunsan dai zaki na zuma baya illah😋 hakkun duk wanda bai tab'a amfani da kayan GHT ba anbarshi a baya Maza da Mata kada ku bari a barku a baya dan dan Allahb👏🏻 ku ka sance a kan gaba wurin mallakan naku ba jiran ana baku labari ba😍🏃‍♀️🏃‍♀️ Mai so zai iya tuntubar wannan number 08132166848 a Whatsapp ko kira. Nagode sosai.👏🏻👏🏻 Indiawa suka ce bahut bahut shukhriya🥰🥰


Safna koda ta shiga ɗaki ruwan wanka ta fara sakawa domin ta samu ta watsa ko zata ji daɗin jikinta, sai ta ɗauko maganinta a ɗaki ta fito falo ta zauna a cushing ta sha, a lokacin ne Zayyad ya shigo falon dan ta barshi a buɗe, yace ta fito suje part ɗin Rashida Mahaifiyarsa tazo tana ciki, daga haka ya fice sai ta miƙe ta mayar da hijab ɗin data cire ta fito ta nufi sashin Rashida. Da sallama ta shiga wanda idonsu Zaliha ya dawo kanta harta ƙaraso ciki ta zauna a carpet tana gaishe da Ammi, a lokacin Rashida ta farka ta soma zaro ido tana nuna inda Safna ke zaune tana fuzzar da miyau, su Anisa suka yi kanta suna salati, haka shima Zayyad miƙewa yayi ya isa gareta yana tambayarta lafiya, bata iya cewa komai ba sai nuna Safna, wanda ita kuma kallonsu kawai take yi tana jin wani hayaƙi yana yawo a kanta, sarai ta fahimci meke maruwa amma har cikin ranta bata yarda da Rashida ba sharri kawai take so ta yi mata, Ammi ma tana zaune tace su kawo ruwa su shafa mata a fuska dan itama kallon lamarin take yi kamar a drama, bayan sun shafawa fuskarta ruwa sai ta shiga sauke ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta, Anisa ta miƙe cikin faɗa.


Gaskiya Safna ki tashi ki fita mun samu ta fara dawowa hayyacinta karki ɓata mana maganin da muka fara yi mata, kuma In Sha Allah aniyarki zata biki.


In Sha Allah aniyar kowa kuwa zata bishi, kuma Allah baya barci.


Cewar Safna cikin kwarin guiwa dan sosai taji zuciyarta a dake babu fargaba ko tsoro. Zayyad ya dubeta rai ɓace.


Tashi ki fita bana son tashi hankali.


Babu inda zata je ta zauna zanyi magana daku duka.


Cewar Ammi cikin haɗe rai, ba wanda ta ƙara magana ta cigaba da cewa.


Anisa da Zaliha dole zasu bar gidan nan a samo wata wacce zata yi jinyar Rashida, dan na kula in dai kuna gidan nan ba zaku bari a zauna lafiya ba, ko kuma su ɗauki Rashidar su koma gida ta yi jinya a can bana son tashin hankali. Sannan wannan ciwon nata alamu ya nuna Aljanun dake jikin Rashida basa shiri dana Safna dan haka sai an tsaya tsayin daka wajen yin maganinta, itama Safna a dage mata, na rasa wannan abu ace girki ba ɗaya ba ko wacce da side ɗinta ba ruwan wani da wani amma ku kasa sakawa zuciyarku salama akan kishi, to gaskiya ba zai yuwu ba duk wacce ba zata zauna lafiya ba to zata tafi gidansu.


Amma Hajiya ita Safna da Anisa tayi magana meyasa zata biye mata, ba sai tayi shuru taga hukuncin da zan ɗauka ba.


Tunda na zo gidan nan mutanen nan suke bina da rigima, na kawar da kai nayi haƙuri amma ba zasu fasa ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login