Showing 36001 words to 39000 words out of 45829 words

Chapter 13 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

bazan yi miki uzuri ba kuma bana son naji meya haɗaku, tunda ni ban isa ki jira na zo ki faɗa mini abinda tayi miki ba na yi mata hukunci, to tunda kina da zarafin ɗaukar mataki ba matsala amma ki sani ba dai a gidan Zayyad ba wlh, ki tafi gida kawai.


Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, safna ta faɗa tana duƙawa ƙasa kan guiwarta, ta haɗe hannunta guda biyu tana kuka mai ban tausayi.


Na yarda nayi laifi amma wlh ba yin kaina bane, ba dani tayi faɗa ba da aljanuna ne, kamin rai Zayyad ka tuna ni amarya ce wacce ko wata biyu bata rufe ba, wlh daga yau ko me Rashida zata yi mini bazan bari raina ya ɓaci ba balle aljanuna su tashi.


Zayyad wani irin bushewar zuciya yaji daga ƙirjinsa, duk wani tausayi da jin kai yaji kamar an cire masa, dan haka bai ce mata komai ba ya fice daga ɗakin fuskarta a matuƙar murtuke, Safna ta ɗaura hannu biyu a kai tana cewa.


Innalillahi wa inna ilaihir raji'un Allahumma ajirnee fee musibati wa akliflee khairan minha. Allahu Allahu rabbi laa ushrika bihi shai'a, Allah kaine mahaliccin kowa da komai baka kada abokin tarayya ka jiɓanci lamarina ka zame mini gatanaaa.


Ta ƙarasa cikin matsanancin kuka jikinta sai rawa yake yi, ta miƙe ta shiga zagaye ɗakin takai ta dawo, tsananin tashin hankali ta shiga akan zuwa gidansu dan tasan halin babansu ba yida wasa, idan ma taje me zata ce musu, bata taɓa faɗa musu tana fuskanta wata matsala ba amma ace lokaci guda taje musu da wannan maganar, ta ina zata fara?.


Akwai ƙura, akwai turka turka...


_Zaku iya fara biyan kuɗinku domin muna gab da gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. ₦500 ne kuɗin, dan Allah ku mara mini baya._


Pay ₦500 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.
[23/09, 8:26 pm] null: https://chat.whatsapp.com/KiimXR7QoIVAe8V8rnGWhC




ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari.


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 16.


Safna nan take ta nima ciwon kunne da nauyin jikin da take fama dashi ta rasa, dan wani tashin hankalin yakan mance mutum wani yanayin rashin lafiya da yake ciki, haka ta isa bedroom ɗinta ta cire kayan jikinta ta saka baƙar jalabiyar jiya, sai ta saka hula akanta tare da zura dogon hijab ɗinta ta ɗauko safa ta saka ta ɗauki niƙaf ta ɗaura, kana ta dauko fos ta saka dubu dayan da Zayyad ya bata jiya da wayarta, ta fito ta kashe duk hasken ɗakin ta duba kitchen babu abinda yake a kunne sai ta fito ta kulle ɗakin ta saka key a pos, ta nufi hanyar gate ta fice daga gidan ko waiwaye bata yi ba, haka ta nufi titi tana jan ƙafa tare da fidda hawaye dan duk ta jika nikaf ɗinta, har ta isa babban titin bypass bata ji ta gaji da tafiyar da tayi mai ɗan nisa ba, ta samu ta tsallaka titina guda biyun kafin ta tare mashin ta faɗa masa in da zai kaita ta hau suka wuce.


***


Rashida.


Tun sadda Zayyad ya fita ta rikice dan bata taɓa zaton rashe zai juyewa mujiya ba, tunaninta Zayyad zai shigar mata faɗan yadda Safna ta yi mata duka har da fitar mata da jini, ko kuma in ya tashi yanke hukunci akan ita Safna zai yi, sai kuma taji yace ta tafi gida bai duba ma halin da take ciki ba, hakan yasa tayi saurin miƙewa ta ɗauki wayarta ta kira mamansu bugu biyu ta ɗaga tana cewa.


Mamanmu na tsokani Safna munyi faɗa sai dai ban samu damar dukanta ba, itace tayi mini dukan tsiya har da fasa baki, shine wai Zayyad yace na tafi gida sai ya nime ni.


Wlh karya yake yi ba inda zaki je. Rashida ki saurareni da kyau, kinga yanzu wata dama ce ta samu in kin tuna maganar dana yi miki jiya, dan haka maza ki kwanta a ƙasa male male kiyi tamkar mara lafiyar da ko hannu baki iya ɗagawa, kisa yaranki suna jijjigaki suna ambaton sunanki har yazo ya taddaki a haka, sauran abun ki san yadda zaki ƙarasa da kanki.


To mama zaku ji kira dan zan saka ya kiraku.


Daga haka Rashida ta kashe wayar tana shu'umin murmushi, in yasan wata bai san wata ba! dole ne tayi amfani da wannan damar dan ganin ta gurɓata tunanin Zayyad akan Safna, babban burinta bai wuce Zayyad ya saki Safna ba dan ba ƙaramin baƙin ciki taji ba lokacin daya sanar mata tana da ciki, ko da bata samu nasarar zubar da cikin ba to ta buɗe ido taga ba Safna a cikin gidanta har abada. Nan take ta aje wayar a center table tayi sauri ta kwanta a ƙasan tiles ta kwanta rigingine tana fidda numfashi da kyar, yaran suna zaune a kujera kamar ruwa ya cinyesu, sai ta daka musu tsawa tana cewa suzo su riƙa jijjigata suna ambaton sunanta, da sauri suka iso gareta suka shiga yin abinda ta saka su. A lokacin da Zayyad ya baro ɗakin Safna taji buɗe ƙofarsa sai ta yi sama da kwayar idonta tana fafar fafar dasu kamar wata me farfaɗiya, ga wani gurnanin mumfashi da take fitarwa, yaran suna jijjigata suna kira sunanta, Zayyad cikin hanzari ya ƙaraso yaga halin da take ciki sai ya shiga tsananin tashin hankali, da sauri ya isa kitchen ya ɗibo ruwa yazo ya shiga yayyafa mata, a lokacin ne Rashida ta sauke ajiyar zuciya da ƙarfi kana idanunta suka dawo dai dai, sai dai ikon Allah duk yadda taso ƙaƙalo hawaye yaƙi fita sai dai ta shiga raba kwayar idonta, Zayyad ya dubeta yana ambaton sunanta amma ba magana, ya tsuguna yana cewa ta tashi, sai a lokacin ta iya buɗe baki da kyar tana cewa.


Jikina yayi mini wani irin nauyi da ko hannu ba zan iya ɗagawa ba, ka taimakeni Zayyad mutuwa zanyi, ga yarana ka riƙe su amana kuma na yafewa Safna duk abinda ya faru domin nice na jata da rikici sai dai ban zaci abin zai zama haka ba, ashe tana da aljuna ban sani ba.?


Zayyad nan jikinsa ya ɗauki rawa hankalinsa in yayi dubu to ya tashi ya shiga cewa.


Babu abinda zai faru In Sha Allah bari na kaiki asibiti.


Ka ɗaukeni ka mayar dani kan kujera sanyin tiles har cikin ɓargona nake jinsa, ka kira mamana su zo yanzu.


Zayyad jin haka ya miƙe a kiɗime ya ɗagata ya ɗaura kan kujera, ya koma gefe ya shiga niman number ɗin Anisa, tana ɗagawa ya rigata magana.


Anisa kuzo gida yanzu, Rashida ba tada lafiya.


Ya faɗa a kiɗime duk ya susuce dan samun kansa yayi da tsananin fargaba tare da jin tausayin Rashidan yana bin duk wani ɓargon jikinsa, Anisa bata amsa masa ba ta kashe wayar. Zayyad ya koma ya risina a gabanta yana jera mata sannu ita kuma sai gyaɗa kai kawai take yi tare da lumshe ido, haka ya miƙe yana kai komo tare da jin dole sai ya ɗauki tsastsauran mataki akan Safna, saboda ba zai yarda da aljanunta suna tashi ba, gwara kawai ya sanar da iyayenta su nima mata magani dan ba zai iya ba. Ganin yaransa sunyi jugum da alama yunwa suke ji gashi kusan ƙarfe tara basu karya ba, sai ya shiga kitchen ya haɗa musu tea ya zo ya basu suka zauna suka fara karyawa, shi dai zama yayi yana karanta wasikar jaki, dan ji yayi ma a ƙoshe yake, duk wani haushin Rashida da yake yi, ji yayi ya ragu sosai a zuciyarsa sai tausayinta.


Wajen ƙarfe goma da kwata sai ga su Maman Rashida da ƙannenta mata tare da Haruna ƙaninsu daya tuƙosu a motar gidansu, a kiɗime suka faɗo falo Mama ko gaisuwar Zayyad bata iya amsawa ba ta nufi inda Rashida ke kwance ta shiga dubanta cike da kulawa.


Mama! mama jikina yayi mini nauyi ko hannuna bana iya ɗagawa, faɗa nayi da Safna aljanunta suka yi mini duka.


Aljanu kuma? to wlh ba zamu yarda ba ina ita Safnar take? kai Zayyad kana ina haka ta faru ana niman sabauta yarinya, kasan dai masu aljanun nan ba hankali garesu ba sai su nima kashe mutum har lahira.


Mama ta ƙare maganar tana duban Zayyad wanda ya ke a ruɗe dan shi bai san ma Safna ta tafi gida ba, haƙuri ya shiga basu akan zai ɗauki mataki ya ɗaura da cewa.


Yanzu ma asibiti nace zan kai ta tace in kiraku ku zo.


Wannan bana asibiti bane, sai dai mu kaita wajen masu maganin islamic ko gargajiya.


Maman tace cikin haɗe rai, Anisa ta ce cikin damuwa.


Mama mu kaita gurin malam na kan kwana kinsan yana bada maganin aljanu sosai, gwara a yiwa abin tufkar hanci tun kafin jikin yayi tsamari. Wlh dana san haka zai faru dana zo na kwana muyi mata taron dangi, kuma Wlh taci bashi ba zamu yarda ba sai mun rama mata, waya sani aljanun ƙarya ne tsabar mugunta ne da iskanci, dama ai naga take takenta ba tada mutunci, idan kuma mayya ce to naman Anty Rashida ba zai ciwu mata ba.


Shi dai Zayyad haƙuri kawai yake basu, nan mama tace su shiga ɗaki su ɗaukowa Rashida hijab dan yanzu zasu wuce gurin mai magani. Dama tun kafin su ƙaraso Mama ta kira Malam na kan kwana ta shaida masa zasu zo da mara lafiya amma fa ciwon na ƙarya ne, kawai dai zai yi wasu 'yan bayanai ne da zai rikita mijin mara lafiyar, malamin ya amince dan dama ta saba amso maganin farin jini a gunsa nasu Anisa, dan babban burinta su auri mai abin hannu kamar yadda Rashida ke cikin rufin asiri, kuma tana amsar maganin Hawan jini da yake damunta, hakan yasa suka saba sosai dashi wani lokacin sai dai ta kirashi tayi masa bayanin abinda take so ta aika yaran su amso magani.


Zayyad shi ne ya ɗauki Rashida ya ciccibeta zuwa motarsa ya kwantar da ita a gidan baya, Zaliha ta shiga ta zauna tare da ɗaura kan Rashida a cinyarta, su kuma su mama da anisa suka shiga motar gidansu da Haruna ya tukosu, Su Ilham suka zauna a gaban motar Zayyad suka rufe ɗaki tare da wucewa gurin mai magani.


Malam na kan kwana babban shago ke gareshi yana sayar da maganin gargajiya da kuma abinda ya shafi sammu kona aljanu, yana bayar da sarin magani saboda ya shahara har tallarsa ake yi a wasu gidan tv. Koda suka isa plazansa sunyi sa'a ba cikowar mutane, da yake yana da babban office na ganawa da jama'a, tunda mama ta kirashi yaki sauraren kowa akan yana jiran su ƙaraso, nan mama ta kirashi ta shaida masa sun iso, sai yace su shigo da mara lafiyar, Zayyad shine ya kinkimi Rashida ya shigar da ita ciki ya kwantar a kan wata doguwar kujera, ya ja ya tsaya a gefe mama data biyoshi a baya ta samu kujera ta zauna, suka gaisa da malam ya tambayi asalin abinda ya faru, nan mama ta sanar dashi faɗa tayi da kishiyarta mai aljanu daga nan kuma jiki ya rikice, malam ya miƙe ya iso inda take kwance ya dafa kanta sannan ya gwale mata ido yana dubawa, sai ya shiga tofa mata addu'a na tsayin minti goma, daga bisani ya koma ya zauna yana dubansu.


Ina mijinta?


Gani nan malam.


To madalla, matarka anyi mata jifa ne dan a lalata garkuwar jikinta, har ku gaji da jinya ka rabu da ita. Tuntuni aka yi shi amma da yake jininta yana da ƙarfi asirin baiyi tasiri ba sai a yanzu da aljanun matarka suka shafe ta.


Innalillahi wa inna ilajir raji'un. Malam asiri kuma? Rashida me ta tsarewa mutane da har za ayi mata asiri, anya kuwa? ka dai ƙara bincike malam.


Cewar Zayyad cike da damuwa dan harga Allah zuciyarsa bata gamsu asirin bane, yafi tunanin aljune ne suka shafeta, dama tunda zuka zo wajen zuciyarsa bai wani kwanta ba yafi yarda da masu maganin Islamic, amma ba yadda ya iya tunda cewar maman Rashida ne shiyasa yayi musu yadda suke so.


Hatta kaima cutar nata zai iya shafarka, amma in baka yarda ba zaku iya kaita wani guri a bincika muku.


Haba malam wani irin mu kaita wani guri bayan mun saba amsar magani a gurinka kuma mun samu waraka, nan nake amsar maganin hawan jini na dana jinnun Zaliha dan haka itama anan za a bata magani. Kai Zayyad da kake maganar me ta tsarewa mutane ka manta tanada kishiya kuma ai mugu bai da kama.


Cewar maman Rashida, Malam ya ɗage kafaɗa yana cewa.


Mijinta bai gamsu ba kinga kuwa sai ku sauya guri ni bani da matsala.


A'a malam ni tuna ni na ko aljanu ne suka shafeta. Amma ayi mata duk abinda ya dace fatanmu ta samu lafiya.


Cewar Zayyad, malam ya gyara zama yayi rubutu a takarda kana ya ɗago yana cewa.


Dama irin wannan asirin dole da aljanu ake amfani, shiyasa zaka ga kamar aljanu ne, dan haka zan ɗaurata akan magani wanda na sha ne da hayaƙi In sha Allah za a samu waraka. Hajiya ga wannan in kun fita sai ku bayar a haɗa muku magani dubu dari ne kuɗin. Allah yasa a dace.


Mama ta amsa takardan tana godiya ta miƙe tana cewa.


Yanzu haka zata cigaba da zama malam ko ruƙiyya ayi mata ta samu taka ƙafarta.


Karku damu ina kyautata zaton tana fara amfani da maganin zaku ga sauyi In Sha Allah.


Nan duk suka yi masa godiya Zayyad ya ɗauki Rashida ya fitar da ita zuwa mota, ya dawo ya biya kuɗin magani aka haɗa musu suka kamo hanyar gida zuciyarsa cike da wasi wasi, har lokacin ya kasa yarda asiri ne a jikin Rashida, kuma bai yarda Safna zata cutar da ita ba.


*****


Safna.


Koda ta isa ƙofar gidansu ta tsaya jikin wani falwaya ta kasa shiga sai asa asa take yi da fargaban shiga cikin gidan, Yusuf da aka aika ya siyo sugar da zasu karya shine yayi kiciɓis da ita a waje, yadda ya ga tsayuwar da ta yi ya gane ita ce, sai ya isa da sauri yana cewa.


Anty Safna ya baki shigo ba.


Ta juyo a zabure dan ta tsorata da jin muryarsa, ta kasa cewa komai sai matsar hawaye take yi daga cikin nikaf, Yusuf juyawa yayi cikin gida ya shiga falonsu wanda duk iyayen suna zaune Umma ta tareshi da cewa.


Ina sugar? ba dai har ka dawo ba.


Anty Safna na gani a waje jikin falwaya taƙi shigowa gida, nayi mata magana bata ce mini komai ba.


Da sauri babansu ya miƙe yayi hanyar fita, umma ma ta miƙe ta kwance ɗankwalinta ta warware shi ta yafa a kanta ta fito, a lokacin ne Mudan ya fito daga ɗakinsa ya shiga tambayar meke faruwa ba wanda ya bashi amsa shima sai yabi bayansu zuwa wajen.


Ke Safna zo nan lafiya?


Cewar Abba yana isa gurin da take tsaye, Umma tana daga ciki tana leƙo kai tana kallonsu, Safna ta soma ja da baya tana kuka sai kawai ta juya da nufin ta ruga da gudu, Yaya Mudan yayi kukan kura ya kamo hijab ɗinta, wanda a lokacin ne ta ɓarke da kuka mai sauti duk hankalinsu in yayi dubu to ya tashi, Safna tana turjewa Yaya Mudan yana janta har suka shiga cikin gida ya fincike niƙaf ɗin idonta wanda tuni hawaye ke bin kuncinta, yadda taga fuskar mahaifinta ya tamke yayi gaba zuwa cikin falo yasa taji fitsari cike da fargaban hukuncin da zai yi mata.


_Zaku iya fara biyan kuɗinku domin saura page ɗaya mu gama season 1 mu tsunduma a season 2 wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku cigaba da samun cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa. ₦500 ne kuɗin, dan Allah ku mara mini baya._


Pay ₦500 to 9034940106
RAMATU MUHAMMAD KABIR
OPay Digital Services Limited
Hajiyoyi masu son vip group su tura ₦1000. Sai a tura shaidar biya ta number 09034940106.
[24/09, 8:36 pm] null: https://chat.whatsapp.com/KiimXR7QoIVAe8V8rnGWhC




ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 17.


Bayan sun shiga falo kowa ya zauna kukan Safna ne ke tashi a ciki, babu wanda yace tayi shuru ko ya tambayeta abinda take yiwa kuka, har ta gaji dan kanta ta yi shuru tana ajiyar numfashi, a lokacin ne Yusuf ya shigo ya miƙawa Umma sugar ta amsa ta saka a cikin kunun tsamiyar data dama musu, data gama juyawa ta zubawa babansu a kofin jug tasa Yusuf ya miƙa masa tare da kular ƙosai data zuba masa, daga nan ta sakawa Mudan sai Yusuf, a lokacin ne ta kalli Safna da take zaune a takure a carpet.


Kin karya?


U-um ta bata amsa haɗe sa girgiza kai, umma ta zuba mata a wani kofi da ƙosai a plate tasa Yusuf ya miƙa mata sannan ya koma ya cigaba da karyawa, falon ya ɗauki shuru sai cin abincinsu suke yi sai dai ko wanne zuciyarsa cike yake da damuwar ganin Safna, amma da yake sun san dokar Abbansu yasa kowa yayi shuru har sai shi ya buɗe baki ya fara magana, Umma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login