Showing 18001 words to 21000 words out of 45829 words

Chapter 7 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

haƙuri damu domin mu ƙannen Anty Rashida ne in da ƙara kuma kema kin zama yayarmu.


Wlh kuwa ai a hankali zata wayemu, gaskiya ɗakinki ya tsaru gwanin burgewa Allah ya nuna mini aurena haka.


Cewar Amina ɗiyar ƙanwar mamansu Rashida, nan suka cigaba da zama suna hira cikin sakewa kamar ɗakin uwarsu, Safna ganin abin nasu bana ƙarau bane gashi tana fama da ciwon kai ga barci na damunta, tasan kuma har zata runtsa kafin 'yan uwanta su zo hakan yasa ta ari jarumta tace.


Dan Allah kuɗan yi mini haƙuri zan kwanta ina fama da ciwon kai zuwa anjima sai ku dawo muyi hirar.


Kallon juna suka shiga yi ko wacce da magana akan fuskarta, Zaliha da yake ba kunya ke gareta ba ta miƙe tana cewa.


Sai ku tashi mu tafi tunda bata yi farin ciki da ganin ba, dama tun ɗazu naga sai wani haɗe rai take yi, wannan amaryar da gani sai Anty Rashida ta sha fama da ita dan alamu sun nuna ba kirki zata yi ba ni kunga tafiya.


Ta ƙare maganar tana yin hanyar ƙofa, suma sauran duk suka miƙe suna ƙananun magana.


Allah ya baku haƙuri bani nakar zomon ba, amma kam ina buƙatar na kwanta bazan kuma tauyewa kaina hakki ba dan na faranta muku, da alama baku san kawaici ba.


Ta faɗa tana bin bayansu tare da rufe ƙofarta garam ta ɗan ƙarfi sai tasa key, su Anisa tsayawa suka yi suna kallon ƙofar tare da mamakin maganar data yi musu basu zata tana da baki haka ba, hakan sai ya ƙara wutar tsanar da suke yi mata dan sosai suke taya yayarsu kishi, gashi Rashida ba zata gwadawa Safna komai ba illa ta fita ƙiba da haske, amma batun kyau Safna itace matar nunawa sa'a gata ba tada ƙiba sai kumari da dan tsayi kaɗan, tana da hips da mazaunai wanda nan gaba in taji daɗin auren zasu ƙara bayyana, ga boobs ɗinta Masha Allah ba irin na Rashida ba da suke ƙananu kuma duk sun kwanta. Ita Rashida hasken fata gareta ga tayani muni da idanu ƙanana kamar an tsomawa teba tsaya, sauƙinta tana da ƙaramin baki da hanci wanda sune suka ɗan ƙarawa fuskarta kyau kaɗan, haka suka nufi sashin Rashida suna surutai, suna shiga falo suka ga su Rashida a zaune Amina ta fara da cewa.


Anty Rashida Wlh kishiyar nan taki saikin tashi tsaye da ita dan wlh idanunta a tsastsaye suke da gani ba tada mutunci balle kunya, wai fa koromu tayi ita zata yi barci.


Aini ta gama shayar dani mamaki yadda naganta a fuska kamar ba zata yi surutu ba, ashe kallon kitse nakewa rogo, ni ai ta sagar mini da duk wani kwarin guiwa ta, shegiya gata da kyau na ɗauka mummuna ya kwaso.


Cewar Anisa data samu guri ta zauna tana cika tana batsewa, nan fa suka cigaba da zagin Safna, Rashida dai ta cika tayi fam kamar zata fashe, tunaninta Allah ya bata damar da zata nakaɗawa Safna dukan tsiya ko ƙila ziciyarta zai rage mata raɗaɗin abinda take ji dangane da ita, ta cigaba da lissafin yadda zata hana mata kwanciyar hankali a gidan har sai ta bar mata gidanta.


****


Safna.


Tana rufe ƙofar ta dawo ta zauna a cushing ta tallabe kuncinta da hannu biyu tana mayar da numfashi, dan sosai taji fargaba da maganar da tayi musu bata ma san tana da jarumta har haka ba, koda yake tunda taji zuciyarta da numfashinta yana wani iri tasan mutanen jikinta sun motsa, wata ƙila suna ɗaya daga cikin taimakon da suka bata ta samu damar korasu, ta sauke hannu tana cewa a fili.


Allah ka haɗani da dabbobin mutane wanda basu san zuru ba, aiko wlh su kai ƙarata gurin Zayyad ɗin in yaso yayi min faɗan, duka ne dai bai isa ba wlh sai dai ya tsaya a bambami, dan bazan ɗauki wannan rashin hankalin nasu ba ina dai dai da lissafinsu.


Tana gama faɗar haka tayi ƙofa ta miƙe ta haɗa kayan gabaɗaya takai kitchen, sai ta tattara datti ta saka a dustbin ɗin da suka aje mata a kitchen, ta wanke kayan da suka ɓata ta dawo falo ta gyara, kana ta kunna turaren wuta na tsinke ta aje shi a cikin ƙarfensa, sai ta koma ɗaki ta cire kayanta ta saka na barcin da 'yan uwanta suka ciro mata akan tayi amfani dasu jiya, tabi lafiyar gado tana mai koro addu'ar safiya da bata samu yi ba tana kammalawa ta rufe ido, cikin ikon Allah sai barci ya ɗauketa ba jinawa.


Itace har kusan ƙarfe sha ɗaya da rabi tana barci, wanda kiran wayarta ne ya farkar da ita tana dubawa taga yaya Mudan ne, bata ɗauka ba ta tashi ta fito falo ta shiga kitchen ta kunna gas ta saka ruwa a tukunya dan tuni aka ɗauke wuta, kana ta dawo ta zauna bakin gado ta kira Yayanta, koda ya ɗauka suka gaisa ce mata yayi.


Dama Maryam ce ta kiraki da wayata nata wayar ba kuɗi, ina ga sun kamo hanya zasu zo dama tambayarki za suyi ko a tawo miki da littafan makarantarki, nace su barshi tukuna ko daga baya Yusuf ya kawo miki.


Allah sarki to ba damuwa ka gaida su Umma.


Zasu ji Allah ya baku zaman lafiya kanwata ayi ta dai Haƙuri.


Murmushi tayi tace amin kana ta yi masa godiya suka yi sallama. Ko kafin su anty Shafa suzo tayi wanka ta mayar da rigar shaddarta, sosai taji ƙarfi a jikinta dan dama ta kula rashin barci mai kyau da gajiyar jiya shine ya saukar mata da zazzaɓi, sai dai ciwon kai ne yana yi mata kaɗan kaɗan amma shima a hankali zai tafi in dai zata samu barci isasshe. Da su Anty Maryam suka shigo basu ga kowa a tsakar gida ba sai suka nufi sashin Safna, suka buga mata ƙofa ta buɗe kana suka shiga tana murna da ganinsu, Anty Zainaba matar ƙanin Umma tace cikin kulawa.


Ayya takwarata har kin faɗa wlh, aure akwai saka damuwar rabuwa da iyaye ba sauƙi saina Allah, Allah yasa gidan zamanki ne.


Suka amsa da amin sai duk suka samu guri suka zauna, nan ta gaishe su suka amsa fuska sake anty Maryam tana cewa.


Ya kewar gida da baƙunta, naga ma komai tsaf ba wani gyara da za muyi ƙilan dai zaman hira za muyi yau.


A'a fa ina so ku sauya mini zaman kujerun nan sannan ɗayan ɗakin baku gama haɗa gadon ba, ina so ya zama ɗakina wanda muka kwana ya zama na Zayyad.


Safna tana faɗa cikin shagwaɓa, Anty Shafa ta fara dariya.


Iye Safna masu miji anyi gidan kai fa sai iya yi da tsurfa kala kala, to dama ba zamu bar gidan nan sai mun gyara miki ko'ina dan Umma tace kar mu bar miki aiki.


Allah sarki abar ƙaunata Ummata nayi kewarta da Abba wlh sosai.


Ai Safna haka saki saba dan zama in yayi zama dole rashinsu yabi jikinki.


Cewar wata dangin babansu, nan dai suka cigaba da hira wasu kuma suka miƙe suka fara gyara ɗayan ɗakin, dama daki ciki uku ne a cikin falon kuma ko wanne da bayinsa sai kitchen da store a haɗe a falon. Bayan sun shiga ɗakin Safna dan su aje mata akwatinanta da kayan gara na cincin da diblan, anty Maryam ta zauna a gefen gado tana cewa.


Safna babu wata matsala ko?


Safna ta sauke ajiyar zuciya kamar ba zata faɗa musu abinda ya faru ba, amma kuma tana buƙatar shawararsu dan lamarin ba zata iya ita kaɗai ba, nan ta gyara zama ta basu labarin abinda ya faru tun daga jiya har yau sai dai ta ɓoye kusancin aurayyarsu da Zayyad dan wannan sirrinta ne, Anty Maryam ta kalli Shafa tana cewa.


Kinji ba ai wlh biri yayi kama da mutum dama wannan shige matan da tayi da akwai manufarta, dan haka wannan turarukan da Umma tace a dawo mata dasu tayi amfani dasu to ba zata yi ba, dan mutum mai fuska biyu baka iya sanin alƙiblarsa.


Gaskiya kam Maryam ko atamfar da umma tace mu ɗinkawa yara shima ba zamu yi ba, ajewa zata yi a hannunta in wata ta haihu a dangi tayi biki da shi, Allah yace tashi in taimakeka.


Cewar Shafa tana mamakin sauyawar Rashida, Safna tace.


Nifa dama ba zanyi amfani dasu ba, balle ma yadda ta nuna makircinta a kaina ƙiri ƙiri gwara na kama kaina nasan irin zaman da zanyi da ita, ɗan wlh ta tsoratani da halin ɗan Adam.


Ai mun ɗauka soyayyar gaskiya take nuna miki shiyasa umma tace sai dai mu ɗinkawa Hafsa ɗiyar Anty Shafa da kuma Labeeba 'yar wajena atamfar, In yaso turarukan kuma mu kawo miki kiyi amfani da abinki, amma yanzu shawara ta sauya dan mugu baida kama.


Cewar Maryam, nan dai suka tattauna suka bata shawara akan yadda zata yi taka tsantsan da duk wani rikici da Rashida zata kunno mata, ta kuma kama azkar da yawaita karatun Alqur'ani da addu'a, tunda har ta fara nuna mata haka to lallai itama ta iya takunta.


******


Zayyad.


Wajen abokinsa Saminu ya nufa yayi sa'a ya same shi a ƙofar gidansa ya fito shan hantsi, nan suka zauna suka gaisa yana tsokanarsa amarya, tare da cewa.


Yanzu fa shikenan kayi mana zarra, da muna da ɗai ɗai yanzu ka ƙara ka barmu a baya, nima dai dana samu wasu kuɗi Allah auren nan zan ƙara kasan matanmu sai sunga anyi musu kishiya suke gyara wasu ɗabi'unsu. Yanzu yaushe zaka saka mana rana muje muci girkin amarya.?


Haba abokina sai kace wani auren fari, ba wani girki da zaku ci tunda kunci na Rashida ya wadatar, sannan wlh abokina in ka samu dama kayi auren nan dan kuwa gida biyu maganin gobara, kaga kuwa yau ɗin nan zan fara cin girkin amarya dan nace tayi mana na dare.


Haba abokina baiyi wuri ba, ai bata gama hutun gajiyar biki ba, kuma da alama zaka fara yiwa mutane rowa dan kayi sabuwa.


Hmmm Samuni kasan matsalata bana samun abinci a gidana sai na fi sati banci ba, shiyasa naketa ɗokin na amarya wlh, nasan In Sha Allah tanan na huta da cin abincin waje, Rashida zata san yanzu duk abinda zata yi mini ba zai bani haushi ba tunda ina da madafa.


Gaskiya ne kuma, amma duk da haka daka ɗaga mata ƙafa zuwa jibi.


Ina da mata biyu in cigaba da cin abincin waje, nasan Safna tana da juriya zata yi kuma iya na dare ne, sannan da safe ni zan riƙa yi mana kafin na fita.


Zama da masoyi daɗi in andacewa... Wani waƙar 'yan hausa film, banga laifinka ba dan duk wanda ya samu rana dole yayi shanya, Allah ya saka mu a danshinku.


Saminu ya faɗa yana ɗan murmushi, Zayyad yace Amin suka cigaba da hira sai wajen ƙarfe goma kafin suka rabu ya wuce gidan Amminsu.




_Kuyi haƙuri rasuwa aka yi mana shiyasa Allah ya jikan dukkan Musulmi ya gafarta musu. Mutanen Maiduguri ina miƙa saƙon jaje gareku Allah ya shiga lamarinku ya kawo muku agaji ya mayar muku da alkhairi. Ameen_
[14/09, 8:35 pm] null: https://chat.whatsapp.com/LJ0A2QRC2OM2XlDG6Q1qdH


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari 🤗🤗🤗


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 9.


Zayyad koda ya isa gidansu ya tadda suna ta hada abin karyawa sai ya wuce sashin Ammi ya sameta da 'yan uwanta ya gaishe su kana ya fito ya wuce ɗakin Mukhtar ya samu baya ciki sai ya rage rigar jikinsa ya kwanta a gado dan ya huta, dama ya bawa yaran aikinsa hutun kwana biyu sai monday zasu koma aiki. Dangin Zayyad sai wajen ƙarfe ɗaya da rabi suka isa gidansa, sashin Rashida suka fara isa sai dai basu samu tarba mai kyau ba, dan gaisuwarsu ma sama sama matan dake falon suka amsa kuma babu wacce ta basu gurin zama, hakan yasa suka fito suka nufi sashin amarya nan suka tadda karamci dan an yi musu tarba mai kyau kamar sun jima da sanin juna, haka suka saje suka shiga hira dama sun tawo da abinci a ƙaton kula dafadukan shinkafa da naman rago soyayye a sama kuma da ɗan yawa, haka suka ci abinci suka ƙoshi, Safna dai tana bedroom ɗinta da aka gyara mata tare da ƙawayenta su Haajara sunata hira, anan ne ma Haajara take cewa Saleema ƙawarsu.


Kin ce in mun zo zaki amsa number ɗin mai maganin gyaran nono da ƙarin kumarin da Safna tasha, gatanan a kusa sai ta ƙara yi miki bayani, dan kinga ramarki tayi yawa ga shi kince kin kusa yaye Ammar.


Saleema ta muskuta da yake an sosa mata inda yake yi mata ƙaiƙayi.


Yauwa Safna bani sirrin gyaran da kika yi dan wlh har baban Ammar ya fara mini ƙorafi, cewa yake ko nawa ne zai bani nayi gyara dan yana son ya ganni nayi dumur dumur.


Maza mutanenmu yanzu fa akan wannan sai kiji yana zancen ƙara aure.


Cewar wata daga cikinsu Hafsa, nan Safna ta ɗaura da cewa.


Sabayar Maman Khadija nasha ya ciko mini da komaɗa, shine sirrin kyau na.


Ina uwar gida da amarya, zawarawa, 'yanmata da masu Shirin amarcewa hadda ke Ƙanwata, shin kuna son abunda zai ciko maki da ramarki Kuma ya gyara maki fatar ki? to haƙiƙa kukan ki ya ƙare da yaddar Allah, Dan maman Khadija ta tanadar maku d garin kunun Sabaya wanda zai ciko maku da duk wata rama ya gyara maki Fatarki ba tare da cutarwa ga lafiyan kiba, maman Khadijah tana zaune a Zaria Kaduna State Muna aikawa ko Ina a fadin Nigeria: Dan Neman Karin bayani kuna iya tuntubarta ta number waya kamar haka. 07037777442, 08033411249.


Sai Tula Tula 3 in 1 maganin nono, infection, da ƙarin Ni'ima.


Tula tula maganin nono ne, yana gyara nono komin lalacewarsa ya cicciko dasu suyi tula tula. Masu yaye in suka sha kafin su yaye yaron da sati 1, to ba zasu yi ciwon nono ba kuma nono baze lalace ba. Uwa uba yana wanke mara ya cire infection, sannan ya ƙara miki Ni'ima da test. Zallar magungunan gargajiya da gadalin Fulani, daga manbila ake kawo mun babu na bature ko kaɗan a ciki, sannan bayasa ƙiba maganin nono ne kawai, sai maganin mata da sanyi da yake yi wato 3 in 1. Idan kina buƙata ina zaune a Kawo Kaduna ku tuntuɓeni a wannan number 08135613021 muna turawa ko ina a faɗin Nigeriya harda ƙasashen ƙetare


Aiko ba Saleema kaɗai ba hatta ni zan yi ƙoƙarin nimansu dan na kwashi garaɓasa, kin san mace sai da gyara ballw mazanmu na yanzu suna son ganin mace kullun 'yar cakaras.


Cewar Hafsa, sai duk suka saka dariya haka suka cigaba da hira gwanin sha'awa. Zuwa yamma lis mutane sun fara watsewa waɗanda suka rage suka gyarawa amarya ɗaki suka saki turare, su Anty Maryam suka ɗiba kayan gara suka kaiwa uwargida nata, daga bisani sai ga Zayyad yazo da mota ya ɗibesu harda Safna zuwa can gidan Ammi, sun samu tarba mai kyau nan suka danƙa amanarta ga mahaifiyarsa tare da kayan gara da atamfa mai kyau da turaren wuta haka suma dangin ango suka haɗawa amarya kuɗi dubu goma sha biyu kamar dai yadda ake yi a al'adar malam Bahaushe, sai gabda magrib Zayyad ya mayar dasu suka yiwa Safna sallama suka tattara yanasu yanasu suka koma gida. Ɗaki ya rage daga ita sai halinta, a sannan ne na tuna da miyar tuwon da bata yi ba, dan tuwon ma Haajara ce tayi mata, miyar ne tace in an watse sai ta ɗaura, ba ɓata lokaci ta shiga kitchen ta soma aiki data gama ɗaura sanwa sai ta fito ta yi alwala ta gabatar da sallar magrib kana data idar ta koma kitchen ta ƙarasa miyarta, ta sauke ta ɗumama miyar stew da umma ta aiko mata dashi wanda yaji tsokar naman sa a ciki, ta sauke ta kashe gas, sai ta juye ruwan wanka ta mayar da wani taje ta yi, da ta fito ta shirya cikin wani leshi riga da siket ɗinkin ya zauna a jikinta, duk wani saƙo da lungu ta saka turare sannan ta yi kwalliya a fuskarta tayi kyau, a lokacin an kira sallar isha'i sai da ta gabatar da shi kafin ta ɗauki wayarta ta fito falo ta zauna ta fara kallo a tv, ba jimawa Zayyad ya ƙaraso gida yayi parking mota, da gudu yara suka isa gareshi suna yi masa oyoyo ya fito ya kama hannun Aslam suka wuce sashin Rashida, ya samu guri ya zauna a falo dan baƙin sun tafi sai Anisa da Zulaiha ne suka rage suma suna ɗakin yara suna danna waya, Rashida ta fito daga ɗakinta sanye da ƙananun kaya riga da wando sun matseta, da fara'a ta ƙaraso ta zauna kusa da shi tana ƙamshin turare.


Madam kinyi kyau fa, yaushe rabon dana ga kin saka waɗannan kayan.


Kai Abban Ilham banda sharri, ina sawa fa Allah.


To shikenan yanzu kije ki saka hijab muje sashin amarya na haɗa kanku.


Ko dai ita tazo ta same ni ba, haba Zayyad ya kake abu sai kace baka san yadda ake yi ba, ai nice babba.


Afwan ganin ita baƙuwa ce yasa nace muje amma bari naje na yi mata magana ta zo.


Da dai yafi, dan wutsiyar raƙumi yayi nesa da ƙasa.


Ta faɗa tana cuno baki, girgiza kai Zayyad yayi yana dariya ya miƙe suka fita tare da yaran zuwa sashin Safna, sallama ya fara yi kafin ya buga ƙofar a hankali, da sauri ta miƙe ta isa ƙofar dan tasan shi ne ta buɗe, ƙamshinta ya gauraye da iskar shaƙarsa kallonta ya tsaya yi cikin wani irin shauƙi, dan sosai tayi masa kyau ga ƙamshinta da ya soma gigita tunaninsa.


Sannu da zuwa Sirrin Safna.


Yauwa Ƙaunata. Ɗauko hijab muje sashin Rashida na haɗaku.


To tace masa kana ta juya zuwa bedroom ɗinta ta ɗauki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login