Showing 33001 words to 36000 words out of 45829 words

Chapter 12 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

ya wuce suna dagawa juna hannu, sai da ya fita da motan kafin Safna ta koma cikin ɗaki ta soma shirin haɗawa kanta abin karyawa.


****


Bayan sallar La'asar Rashida ta ɗaura sanwar abinci da wuri, dan haka ta fito tsakar gida tana wanke uniform ɗin su Aslam, su kuma suna wasa da kwallo, tsautsayi yasa Ilham ta buga kwallon ya daki window ɗin Safna da ƙarfi, Safna dake bedroom a kwance a razane ta farka daga barcin data samu ya ɗauketa, dan jiya bata samu barci mai kyau ba, ta tashi cike da ɓacin rai sai ta saka hijab saman rigar barcinta ta fito tsakar gida tana cewa su Ilham.


Wanene ya buga mini window? Ilham meyasa bakwa yin abu cikin natsuwa ne ina barci kun tashe ni.


Malama dakata! ta yaya zaki hana yara sakewa suyi wasa saboda karsu tashe ki a barci, wannan ai ba magana bace.


Cewar Rashida data ɗago cikin faɗa, Safna ta cigaba da kallonta cike da mamakin ta.


Amma kin san ya kamata ayi musu faɗa karsu sake, duba da window ɗin glass ne karsu fasa, sannan ban hanasu wasa ba amma suyi shi cikin natsuwa.


Ba za suyi ɗin ba, yara da gidan ubansu ki nima saka musu dokar yin wasa, in ma sun fasa window ɗin babansu ne ya saka kuma shi zai gyara bana son takura.


Hmmm Safna tace kana ta koma ɗaki dan sosai taji kanta na sara mata ga bugun kirjinta yana yi da sauri da sauri, saboda jinnun jikinta sun motsa shiyasa ta wuce kar ayi rikicin da bai dace ba. Rashida ta bita da ƙananun magana tana jan tsaki tare da cewa yaran suyi wasa son ransu ba wanda ya isa ya hana su, sai ta cigaba sa wankinta, Safna kuwa tashar karatun Al-Qur'ani ta saka tana saurare ga wani hawaye mai zafi yana sauka daga gefen idonta na hagu kuma tanan kanta ke ciwo, ta jima a haka kafin daga bisani ta shiga fidda numfashi mai nauyi tare da zufa daga goshinta, alamun aljanun sun tafi sai ta miƙe jiki ba ƙarfi ta wuce kitchen ta ɗauko ruwa a fridge tasha kana ta samu sauƙin zafin data ke ji a ƙirjinta.


***


Da dare.


Bayan sallar isha'i Zayyad ya dawo, ya riƙo musu nama tsire tare da fruits ya aje nasu sai ya wuce sashin Safna ya buga ƙofa tazo ta buɗe masa, ya bita a baya ya zauna yana tambayarta jiki tace da sauƙi, ya ɗaura da cewa.


Na sanar da Ammi ba kya jin daɗi shine tace ko zata aiko yarinyar yaya Hauwa tazo ta zauna miki na kwana biyu ta taya ki aiki.


Ikon Allah, ba dai ka gaya mata ciki gareni ba kasa naji kunyar zuwa gidan.


A'a ban faɗa ba nace dai kunne kike fama da shi.


Ai tun ɗazu naji sauƙinsa sai dai toshewar ne har yanzu kuma ni bazai hanani aiki ba, kar a takurawa yarinya.


Ba wani takura ta kammala secondary ne tazo zan nima mata admission anan KASU.


Kace ta dawo Kaduna da zama kenan to Allah yasa a dace.


Ameen. Ina ganin wannan juma'ar zaki je can gidanmu kiyi musu wuni in wata juma'ar ta zagayo sai ki je gidanku.


Wato dai sai da nayi wata biyu kan zan fara fita.


Banda Ammi tace in barki da ba zaki je ko ina ba sai kinyi wata uku.


Buga ƙofarta ya dakatar da hirarsu, ya miƙe yaje ya buɗe yaga Aslam ne.


Mamanmu tace kazo.


Wuce kaban guri.


Ya faɗa a tsawace.


Yaron ya tafi da gudu, Zayyad ya juyo yana ce mata yana zuwa, sai ya wuce sashin Rashida yana shiga ya soma cewa.


Bana son irin abinda kike yi mini wlh, taya zaki dinga aika mini yara in zo.


Gani nayi dole sai ina tuna maka da girki na ne, dan na kula mancewa kake yi dani.


Amma ke bana zuwa ɗakinki na daɗe kafin in koma can, wani lokacin sai na fara zuwa nan na ganku kafin in je ɗakinta kuma itace da girki, sannan bata taɓa yi mini ƙorafi ko nuna damuwa akan haka ba, wlh zan ɓata miki rai in baki bari ba.


Ato daga faɗar gaskiya sai kuma ya zama laifi. A saka abincin ne ko sai anjima.


In kin gadama zaki iya sakawa.


Zayyad ya bata amsa yana samun guri ya zauna, Rashida ta taɓe baki da ɗage kafaɗa ko a jikinta sai ta miƙe ta wuce Kitchen ta haɗo masa abinci ta kawo masa, dafadukan shinkafa da wake na mangyaɗa tayi, gashi nan fari bai ji kayan haɗi ba, ba kayan miya sosai balle curry, Zayyad yana kai loma ɗaya yaji baiji gishiri bane ko maggi oho, ya haɗiye yana kallon Rashida.


Ɗauko mini yaji.


Aiko yaji na ta ƙare ban daka wani bani.


Ke Ilham jeki ɗakin antynku ki amso mini yaji.


Yayi maganar yana kallon Ilham, ta miƙe da sauri ta fita, ba jimawa sai gata ta dawo da yaji a cikin ƙaramin kwano plastic ta miƙa mishi, ya amsa ya zuba ya cigaba da cin abincinsa, Rashida cikin ƙufula tace.


Yanzu dan Allah miye na amso yaji a gurinta, komai dai sai ka nuna mata ni ban iya ba, ai da sai ka bada kuɗi yanzu na saka hijab na amso nan maƙota suna sayarwa.


Zayyad abincinsa ya cigaba da ci bai tankata ba, ya kula Rashida abin ƙorafi baya yi mata kaɗan, a dalilin yajin kuwa yaci abincin sosai ya kora da ruwa tare da kankana kana ya miƙe ya bar mata kayan a gurin ya wuce ɗakinsa dan yayi wanka, Rashida ta ɗauke kayan abincin ta mayar kitchen ta samu leda ta juye sauran yajin ta ƙulle, kana ta kife kwanon a ƙasa ta ɗauko taɓarya ta bugawa gefen kwanon, nan take ya tsage dan kaɗan ya rage ya rabe biyu, ta ɗauka ta adana da nufin da safe in Zayyad ya fita zata aika yaran da shi su kaiwa Safna.


*Duk mace mai yawan mita, ƙorafi da kai ƙara wallahi tana ragewa kanta matsayi ne a zuciyar miji har ta gama fita a ransa. Koda ita ce da gaskiya akan abu to ba za a gani ba domin yawan ƙorafinta. Allah yasa mu dace. Ameen*
[22/09, 8:31 pm] null: https://chat.whatsapp.com/KiimXR7QoIVAe8V8rnGWhC




ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUH KUNA INA NE MUTANNAN ARZIKI KUHANZARTA KUSHIGA WANNAN GROUP MAI ALBARKA KADA AYI BABU KU , MUNA ARHA MUNA HANA BASHI💕MUNA TURA KAYA KO INA DA YARDAR ALLAH CIKIN AMINCI. DA MUTUNTA JUNA , MUNA KASUWANCI DA AMANA , ZAKUJI DADIN KASUWANCI DAMU .

Ga abubuwan da muke siyarwa kamar haka 👇🏻:
KAYAN KITCHEN
WRAPPERS
JAKUNKUNA
TAKALMA DA KUMA SUPPLEMENT.


MASU KYAU DA INGANCI , YAR UWA ME KIKE JIRA? MAZA HANZARTA KI SHIGA LİNK DON SAMUN KARIN BAYANI KO KUMA KU TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER DAN SAMUN KARIN BAYANI . 08033938993 .


UA_ENTERPRISE suna maraba da masu siyan d’ai d’ai ko sari.


*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 15.


Rashida bayan ta kammala komai ta sallami yara suka kwanta kana tayi shirin barci ta zauna jiran Zayyad ya dawo daga ɗakin Safna, tana yi tana duba lokaci a wayarta har ya kai kusan minti ashitin da biyar, shi da bai wuce minti sha biyar a kowani ɗakin wacce ba ita ke da miji ba, ta miƙe ta isa ƙofa ta buɗe ta tsaya, ta shiga loda masa kira dan gabaɗaya tunaninta ya gama bata ya tsaya cin amanarta ne, Zayyad kuma kallon wani action film ya shagaltar dashi bai san lokaci ya ƙure ba, kiran Rashida daya gani ya sashi miƙewa yana yiwa Safna sallama, ta rakoshi bakin ƙofa ya wuce sai ta rufe ƙofarta ta koma ta cigaba da kallo.


A ƙofar ɗaki yaci karo da Rashida fuskar nan a haɗe tana cewa.


Ai wlh daka ƙara minti biyu sai dai ka ganni a nazo ina buga muku ƙofa, Allah Zayyad baka yi mini adalci tunda kayi auren nan idonka ya rufe akan Safna, ba ka ɗaukeni a bakin komai ba.


In dai haka tunaninki ya baki to kije a haka, wannan kanki kike yiwa, ban guri na wuce kafin in saɓa miki.


Ya faɗa a hasale, Rashida ta koma ciki tana ƙananun magana bai kula ta ba ya rufe ƙofar ya wuce zuwa ɗakinsa tana binsa a baya, koda suka shiga wajen kwanciya ya nima ya juya mata baya.


Abban Ilham ina da magana, amma naga ko lokacina ba kada shi.


Kin san dai dare yayi, ki bari gobe In Allah ya kaimu mayi maganar bana son damuwa a yanzu.


Dama dole kace haka ita kana da lokacinta amma ni ba kada nawa. Dama ina so ka jawa matarka kunne ta fita a sabgar yarana naga take takenta burinta tatakura musu, to bazan ɗauka ba dan nasan zafinsu.


Zayyad rufe idonsa yayi dan bai tanka mata ba, idan ya cigaba da biye mata ba zasu kwashe ta daɗi ba dama yasan maganar nata baya wuce ƙorafi, Rashida ganin bai kulata ba yasa ta yi kwafa ta nima gurin kwanciya tana mitar ya daina sonta.


...


Safna.


Ganin sha ɗaya yayi hakan yasa ta haƙura da kallon ta kashe komai ta wuce ɗaki ta kwanta, a wannan lokacin ta tuna da duk abinda ya faru a ranar, musamman na zancen cikin da take da shi sai ta samu kanta tana murmushi, ta shafa mararta tana ambaton.


Ya Allah ka albarkaci abinda ke cikin cikina kasa ya zamo rayayye mai jin ƙai a garemu, kasa ya kasance ma'abocin addinin musulunci. Ka shiryar da shi shiriya dauwamammiya. Ameen.


Ta ƙare tana lumshe ido tunawa da cewa yanzu lallai dole ta kauncewa wasu abubuwa dan in ganta tarbiyyar abinda ke cikin cikinta, domin tarbiyya tun daga samuwar ciki ake fara shi, dole mace ta daina jin kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe, ta zamo ma'abociyar sauraren karatun Al-Qur'ani ko karantawa, tare da sauraren wa'azin malamai, duk wata shagala ta nisanta kanta da shi, sannan a duk lokacin da cikin ya dameta ko take jinta a takure ko kuma wahalar laulayi, akan ta riƙa yawan ƙorafi wannan ciki ya dameni, dan abu kaza kaza a bishi da zagi, kamata yayi tana faɗin kalmomi kamar subhallahi ko hamdala ko wani tasbihi tare da roƙan Allah ya bata juriya akan jarabawan daya yi mata na abinda ke cikinki, ta riƙa sallah akan lokaci tare da yin azkar safiya da maraici, ta riƙa kamewa da zarar magrib tayi. sosai Safna ta lula duniyar tunani wanda ya ɗauketa kusan sha biyu saura, daga bisani tayi addu'ar barci ta gyara kwanciya ba jimawabarci ya ɗauketa.


Da gari ya waye har sai da ta makara sallar asubahi, data idar ta saka ruwan wanka tayi shi da zafi dan taji ƙarfin jikinta, Alhamdulillahi ta samu sauƙi daga ciwon kunnen duk da yana mintsilinta sai dai ba kamar jiya ba, ta shafa mai sai ta sauya wata rigar barci mara nauyi mai wando ta koma gado ta kwanta tana karanta azkar ɗin safe, data gama ta rufe ido ba ɓata lokaci barci ya kwashe ta.


****


Rashida.


Da yake yara suna hutun makaranta a ranar teachers day ne, hakan yasa taƙi tashi haɗa breakfast da wuri sai wajen ƙarfe takwas ta shiga kitchen, Zayyad yana kwance shima dan ya san yara ba zasu makaranta ba, sai ya bari wajen ƙarfe goma ya fita shago shima ya ɗan samu barcin Safe, Rashida ganin ba mangyaɗa ga kuma kwai ya ƙare sai ta fito ta shiga ɗakin Zayyad yana tsaka da barci ta tashe shi tana cewa.


Abban Ilham me zamu karya dashi ne? ba mangyaɗa da kwai.


Ok bari na fita na siyo biredi sai mu sha da tea. Anjima zan aiko da mai da kwai ɗin.


Ni dai ka siya mana ko kaɗan ne mu samu wanda za muci yanzu bana jin daɗin shan tea da biredi ba kwai.


Allah ya bawa waɗanda ruwan koko ne kaɗai suke sha ba mahaɗi, kin samu wannan amma kike ƙorafi bayan kusan koda yaushe kina ci.


Kai dama ba damar na faɗi magana sai ka cini gyara, abu ne da ka riga ka sabar mana kaga ai banda laifi. Ni dai ka siwo mana kwai in kai ba zaka ci ba to mu zamu ci.


Tana gama faɗar haka ta fice, Zayyad ya girgiza kai halin Rashida sai ita, barcin da bai koma ba kenan ya sauko ya sauya kaya dama tun asubahi yayi wankansa, ya samu yaran suna falo ya kama hannun Aslam akan ya rakashi shagon unguwarsu ya siyo musu kayan kari sai suka fita, ita kuma Rashida ta shiga kitchen ba jimawa ta fito riƙe da kwanon Safna data fasa tace Ilham takai mata tana cewa.


Idan ta tambayeki waye ya fasa mata kice ya faɗi ne a hannunki baki sani ba.


Yarinyar ta gyaɗa kai ta amsa ta wuce, buga ƙofar Ilham yasa barcin Safna ya yanke wanda nan take taji wani ciwon kai ya dirar mata, ta taso da kyar tazo ta buɗe ƙofar, Ilham ta miƙa mata kwano ba gaisuwa balle sannu, to ba a koya mata ba dan ko babansu ba gaisheshi suke yi ba, Ilham harta juya Safna ta dakatar da ita tana cewa.


Ke zonan ya aka yi kwanon nan ya fashe haka duk ƙarfinsa.?


Faɗuwa yayi a hannuna.


Haba Ilham haka fa kwanaki dana baku sauran abinci kuka kawo mini plate a tsage, yau kuma kin fasa wannan. Inna roba ne halan yagalgala shi za kuyi.


Safna ta isa gareta ta kama kunnenta ta murɗa tana cigaba da cewa.


Wannan ya zama na ƙarshe dan Wlh kika kuma saina zaneki tunda kun iya ɓarnatawa mutum abu ba zaku bayar da haƙuri ba. Wuce ki bani guri.


Ta ƙare maganar tana rankwashinta, Ilham ta wuce sif sif tana kumbure kumbure kamar zata ce mata Allah ya isa, tana zuwa sashinsu ta isa gurin maman dake falo tana cewa.


Mama sai da ta murɗe mini kunne ta rankwasheni. Wallahi naji zafi sosai.


Muje wlh saina rama miki dama abinda nake so kenan.


Rashida ta fita buguzum buguzum riƙe da hannun Ilham ta isa ƙofar Safna ta fara bugashi cike da rashin mutunci, Safna tunda taji dukan ƙofar haka taji wani yar a jikinta, kanta ya sara tasan cewar Rashida ce, dan haka ta isa ɗaki ta sauya kayan barcin ta saka wata doguwar riga mai guntun hannu mara nauyi ta saka kajeran wando a ciki kana ta nufo ƙofa, har lokacin bata daina buga ƙofar ba sai da Safna ta buɗe ta fito gabaɗaya ta rungume hannunta a ƙirjinta, ta ƙanƙance ido tana kallon Rashida da masifa ke cinta.


Narance da girman Allah baki isa ki saka yarana a gaba ba, daga aikota sai ki duketa dan ta fasa banzan kwanonki, ai da saiki faɗi kuɗinsa a biyaki kuma...


Bata ƙarasa ba Safna ta juya dan wani irin wuta taji yana tafasa a ƙirjinta, hakan ya tabbatar mata mutanen jikinta suna son tashi, sai ta juya dan ta rufe ƙofar saboda ta kaucewa tashin hankalin, Amma Rashida ta wani jawo mata kafaɗa da ƙarfi.


Ke har kin isa ina magana ki juta mini baya zaki tafi, waye ubanki.


Safna wani irin juyowa tayi ta shararawa Rashida kyakkyawar mari, bata bari ta dawo daidai ba ta shaƙe mata wuyanta da ƙarfi da duk hannunta biyu, Rashida ta shiga kwarma ihu.


Jama'a ku kawo mini ɗauko Zayyad ya auro mahaukaciya zata kashe nieee.


Ya ƙarasa ƙarshen da ƙarfi saboda shaƙar da Safna tayi mata wanda ba ita bace, Rashida ta shiga kokawar kwace kanta amma ina ta kasa sai da Safna ta kaita ƙasa duk girman jikinta kuwa, ta hau ruwan cikinta ta shiga naushinta a fuska tare da yin gurnani wanda daga ji kasan ba ita bace, dukanta sosai take yi tana kurma ihu a lokacin mai gadi ya rugo a guje ya rasa yadda zaiyi ya kwaci Rashida a hannunta, dan tun tana ihu ana jin muryarta har ya fara disashewa duk ta fasa mata baki sai jini yake yi da kuma gefen idonta daya fashe ya kumbura, a wannan yanayi Zayyad ya shigo mai gadi ya isa gareshi.


Yallaɓai kazo ka raba su faɗa suke yi.


Ya faɗa cikin rawar murya, Zayyad bai san sadda ya yarda ledan hannunsa ba ya nufi lungun da Kofar Safna yake yana ganin ta akan Rashida yayi kukan kura yasa ƙarfi ya damketa ta baya, tare da riƙe mata hannu gam sannan ya ƙara ƙarfinsa ya ɗagata daga jikin Rashida, ya shiga janta tana tirjewa da kyar ya iya sakata a cikin ɗaki ya kwantar a ƙasa, sai yayi saurin fitowa ya rufeta da makulli ta waje, Safna ta shiga ihun kuka tana buga ƙofar akan ya buɗe ta amma bai bi ta kanta ba, ya koma gurin Rashida da ta gama galabaita ya tallafota ta miƙe, Allah yasa siket ne a jikinta amma da zani ne da tayi mata tsirara, haka Zayyad ya kamata tana marayan kuka tare da ɗingishi dan duk jikinta ciwo yake yi, ya ajiyeta a kujera kana ya fito ya nufi sashin Safna ya buɗe yaga tana zaune a kujera ta saka tashar karatun Al-Qur'ani dan aljanun sun tafi sai kuka take yi mai sauti, tunda yaga haka yasan Aljanun sun sauka dan haka ya fito yabar ƙofar a buɗe ya koma ya ɗauki siyayyar daya yi ya wuce ɗakin Rashida, ya samu ta kwanta tana rusa kuka ya aje ledar hannunsa a center table ya shiga nuna Rashida da yatsa cike da tsantsar ɓacin rai.


Naji daɗin abinda tayi miki domin tunda naga faɗan a ƙofar ɗakinta kuka yi ke ce kika je kika tsokaneta, dan haka yanzu ba sai anjima ba ki shirya ki tafi gida sai na nimeki.


Duk irin wahalar data bani baka tausaya mini ba sannan kace in tafi gida.


Rashida ta faɗa cikin sanyi tana matsar kwalla, Zayyad ya ɗage kafaɗa.


Na gama maganata.


Sai ya fice daga falon ya koma ɗakin Safna ya tsaya a tsakiyar falon yana dubanta.


Kin bani mamaki Safna, meyasa zaki biye mata kuyi dambe sai kace wasu karnuka.


Wallahi ba laifina bane.


Safna ta faɗa cikin kuka Zayyad ya ɗaga mata hannu.


Dakata bana son jin komai, kema yanzu ba sai anjima ba ki shirya ki tafi gidanku sai na nimeki.


A gigice Safna ta ɗago kai tana dubansa tare da miƙewa tsaye jikinta har rawa yake yi.


Wata guda da sati na uku da aurenmu zaka ce in tafi gida, tunda muka yi aure banje gida ba sai in je a silar tashin hankalin nan, dan Allah ka rufa mini asiri wlh gidanmu babu wanda zai mini uzuri, ba laifi na bane ita taja har aljanuna suka tashi suka yi faɗa.


Zainab bari na kiraki da sunaki na asali wlh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login