Showing 24001 words to 27000 words out of 45829 words

Chapter 9 - Amaryar Zayyad Complete Book By Rahma Kabir.txt

sai taga ya raɓeta ya shigo ita kuma ta mayar da ƙofa ta rufe tana yi masa sannu da zuwa, ko kafin ta yi aune ya fizgota zuwa jikinsa ya rungumeta yana shaƙar ƙamshinta, ita sai yanzu ne ta tuna daga ita sai underwear, Zayyad ya ɗago fuskarta cike da tsantsar kewarta.


Kaunata ƙamshin ki ya gigitani, ji nake yi kamar zan suma dan daɗi.


Siirin Ruhi shifa nake shafawa in zan kwanta.


A'a wannan ya bambanta dana kullun ban yarda da guda ɗaya kike amfani ba, gaskiya zaki tsammini wannan ƙamshin daga jikinki yadda zanyi barci cike da begen ki.


Ka rufa mini asiri kar Anty Rashida ta ji ba daɗi, ni cikani ka tafi anjima ka dawo.


Korata kike yi saboda kin daina sona umm?


Ya ƙare maganar cikin marairaicewa, Safna ta saki dariya ta wuce zuwa cushing ta zauna tare da ɗaukar cokali tana cewa.


Ni ɗin banzana zan kori Ruhina, kawai dai bana son shiga hakki ne.


Amma ai ke halas ɗina ce zan iya aikata komai dake ba haramci. Sannan da in fita waje in nima a gurin wata banza fa bayan ina da ke.


Gamu dai zaka ce dan Anty Rashida itama macece.


Na kula kina mugun ji da yayar nan taki.


Ya fada yana ƙarasawa gaban center table ɗin ya zauna gefenta ya jawo shi gabansa ya amshe cokalin ya fara ciki yana cewa.


Cin abincin ba tayi saboda kin fara koyan rowa ko, to wallahi wannan rabona ne ki tashi ki shiga kitchen ki dafa wani.


Haba Zayyad ya zaka yi haka wlh bazan ji daɗi ka ci abinci anan ba bayan kasan bani ce da girki ba.


Safna kiran sunana gatsai haka ba ko sirki, gidana kuma ɗakin matata babu wanda ya isa yayi mini sharaɗi akan duk abinda zan aiwatar.


Yana gama faɗar haka ya cigaba da cin indomie ɗinsa, Safma dai shuru tayi ta rasa me zata ce masa sai tunanin zucci, amma har ga Allah bata ji daɗin haka a ranta ba dan ba zata so a ranar girkinta yayi mata haka ba, Zayyad ya kusa cinye abinci sai suka ji bugun ƙofa da mugun ƙarfi wanda yasa Safna sai da ta miƙe tsaye a tsorace tana dafe da ƙirjinta dan ba ƙaramin tsorata tayi ba kuma dama da tunanin Rashidan a ranta, Zayyad ya dubeta yace.


Koma ki zauna.


Ba musu ta koma ta zauna, ya cigaba da cin abincinsa kuma Rashida bata fasa buga ƙofar ba, sai da ya gama tas ya cinye komai dan hatta kwai da naman bai ragewa Safna ba, ya kora da ruwa ya miƙe yana dubanta.


Allah yayi miki albarka sai na shigo anjima.


Yana kaiwa nan ya juya yayi hanyar ƙofa ita dai Safna da kallo ta bishi dan sosai buga ƙofar nan ke razanata, ya buɗe ya fita tare da jan ƙofar, nan ta tsinkayi muryar Rashida tana cewa.


Zayyad ni zaka wulaƙanta kana ji ina buga ƙofa baka buɗe ba, sannan daga zaka miƙa mata abu shine zaka yi zamanka wannan adalci ne.


Bai kulata ba ya wuce abinsa.


Na rantse da Allah ban yafe ba kuma wlh sai ka faɗa mini mai ka tsaya yi?


Bata rufe baki ba ya juyo a fusace ya wanke ta da mari ya ɗaura da cewa.


Abinci na tsaya ci ko kin isa ki hanani ci ne, idan ke bakya buƙatar lada ita tana buƙata kuma tasan daraja na, wlh daga yau muddun na dawo baki gama girki ba to a ɗakin Safna zanci abinci baki isa ki cigaba da jana a ƙasa ba saboda kin raina ni, na wuce zama da yunwar da kike hukunta ni dani da yarana, ni yanzu ina da madafa. Idan kinyi zuciya ki gyara.


Yana gama faɗar haka ya wuce abinsa.


Ni ka mara akan hakkina, Wlh bazan yafe wannan ba.


Rashida ta faɗa cikin kuka ta bi bayansa, Safna dake jikin window duk taji komai jikinta ba bubu inda baya rawa, daga zuwanta ace sun fara samun matsala, ba zata so ace ita ta zama sila ba, ta koma jiki ba kwari ta zauna a cushing.


Dama ya auro ni ne domin na zame asa sanyin idaniyarsa, ashe Rashida bata cika macen da ake buƙata ba, taya zai dawo iyanzu bata gama girki ba wannan ai sakarci ne, ni dai bana so ta ƙullaceni wlh.


Duk wannan maganar a zuciya take yinsa, data ga ba zai fissheta ba ta miƙe ta isa kitchen ta ɗaurawa kanta wani indomie zuciyarta sam babu daɗin abinda ya faru.


...


Rashida tunda suka shiga falonta ta shiga surfa masa masifa tana yi tana kuka, Zayyad bai iya ce mata komai ba yayi shuru yana saurarenta har sai da ta gaji dan kanta kafin ta wuce kitchen ta duba girkinta, a lokacin Zayyad ya miƙe ya kamo hannun Aslam ya cewa Ilham ta tashi, ya kama hannunsu suka fito suka shiga mota, sai dai Rashida da Safna suka ji tashin motarsa mai gadi ya buɗe masa gate suka fice daga gidan.


Bai zame ko ina a sai wani joint na masu sayar da tsire ya siyawa yaran, kana ya wuce suka siya yoghurt sai ya samu wani guri a cikin wani layi yayi parking yace yaran su ci, haka suka riƙa ci a yunwace dan rabonsu da abinci tun da rana a makaranta, dan ko da suka dawo gida basu samu abinci ba sai cake data basu suka ci. Sai da suka cinye komai tas suna gyatsa ya tabbatar da sun ƙoshi kana ya tada mota suka kamo hanyar gida, ko kafin su ƙaraso yaran sunyi barci, da ya shigo da mota yayi parking ya tashi Ilham sai ya ɗauki Aslam suka wuce ciki, a falo suka tadda Rashida ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza ƙafar data ɗaura a cinya.


METAFORCE
Tsari ne mai matukar kyau daya zo mana a saukake, dan samun kudin shiga ta hanyar amfani da wayar hannunka. Kana kwance a gadonka zaka tare 'yan daloli bisa jajircewarka.


MENENE METAFORCE ⁉️
Kasuwanci ne na network marketing da ake gudanar dashi da wayar hannu, kasuwanci ne wanda kowani reshe ka ta6a kudi ne, kasuwanci ne wanda yake biya 💯percent, kasuwanci ne wanda kowa ma zai iya yinsa, kasuwanci ne da yake da tsaro da kuma tsari wanda yake akan blockchain technology. Project ne me zaman kansa saboda decentralized ne, babu Wanda ze iya HACKING, DELETING KO EDITING. Wani abu daga kasuwancin koda kuwa founder na METAFORCE ne wato Mr.lado saboda an riga an tsara shi Kuma a haka zai ci gaba da tafiya💯 Alhamdulillahi
Alhamdulillah metarforce ana samun arziki da shi sosai. Duk wanda ya shirya dm 09034940106
[16/09, 7:13 pm] null: https://chat.whatsapp.com/EXMdpLPMP2l61mV0W7pXVF




*AMARYAR ZAYYAD*


Na


©®Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir


Page 11.


Zayyad ko da ya shiga ɗakin yara sai ya kwantar da Aslam, Ilham ma ta kwanta a gadonta yayi musu addu'a ya kashe musu wuta kana ya fito ya nufi sasshin Safna, duk Rashida tana falo ya fice basu tanka juna ba, haka ya yi minti sha biyar a sashin Safna kana suka yi sallama ya fito ya dawo, bai ga Rashida a falon ba sai ya rufe ya shiga ɗakinsa ya kwanta tare da kunna data, yasan halinta in tayi fushi to sai ya bita yana rarrashi, yanzu ko rabuwa yayi da ita tunda ba wani abu yake nima a gurinta, dan yana da Safna koda yaji shi a matse zai je can ya sauke nauyi ya dawo dan bata isa ta juya shi ba.


Da safe bayan ya kai yara makaranta kasantuwar Sunday ne baya fita sai da rana, haka ya dawo ya shiga kitchen ɗin Rashida ya tadda bata yi breakfast da shi ba sai ya shiga fere dankalin turawa yana yankawa har ya kai yadda zai iya cinyewa kana ya ɗaura mai daya gani a fan a gefe, ya soya dankalinsa ya fasa kwai shima ya soya sannan ya haɗawa kansa ruwan tea, daya gama ya fito falo ya zauna ya cinye kayansa, sannan ya mayar da kayan kitchen ya wuce ɗakinsa ya shirya dama tun asuba yayi wankansa saboda ya saba da yi koda bai yi wani mu'amalar aure ba ko mafarki, wajen goma saura ya fito ya nufi sashin Safna bai nima Rashida ba kamar yadda itama bata nimeshi ba, tana ɗaki tana jin motsinsa amma fushi yasa ta watsar da shi. Ya samu Safna cikin kwalliyar doguwar riga ready made kanta ba ɗankwali tayi parking gashinta, ya zauna suka gaisa yana dubanta.


Ya kamata kannan kiyi kitso.


Ban san ina zan samu mai kitso ba a unguwar nan, nima kan ya isheni amma nafi so saina ƙara wankewa.


Ya kamata, kuma can saman titi akwai wata mai saloon kamar har da kitso suke yi sannan musulma ce.


In ka lamince mini za je nayi In Sha Allah amma sai zuwa goben.


Allah ya kaimu ni zanje gidan Ammi daga can zan wuce shago.


Ka gaisheta, ni yaushe zan fara fita ne?


Sai kinyi wata uku.


Ido Safna ta waro waje, tana 'yar dariya.


Sai kace auren mutanen da, ina laifin in nayi waya guda dai na je gida ina son ganin su Umma.


Uhum tukuna dai bari muga zuwan lokacin, anjima ki dafa abinci dani.


Kallonsa tayi sheƙeƙe alamar tambaya, sai ya kanne ido ɗaya yana murmushi.


Eh kin ji me nace ai, kiyi abinci dani ko miye zanci sai na dawo.


Ya miƙe yana gyara zaman hularsa tace Allah ya tsare sai ya amsa da amin kana ya wuce ya fita, taje ta kulle ƙofarta da key dan sosai take jin tsoron Rashida bata son abinda zai haɗasu domin bata son faɗa. Zayyad ya kunna mota kenan Rashida ta fito da sauri ta isa window motar ta tsaya tana cewa.


Nifa zan je gidanmu ka bani kuɗin mota.


Bai ce mata komai ba ya ciro kuɗin motan dubu ɗaya ya bata, tana amsa ya ja motarsa ya fice ita kuma ta koma ciki ta sauya kaya dama tun ɗazu tayi wanka, bata tsaya gyara gidan ba sannan ko wanke wanke bata yi ba ta shirya ta fito ta rufe ƙofar ta kama hanyar gidansu.


Koda ta isa gida ta samu Zaliha tana nan amma Anisa ta fita, ta zauna a falonsu tana duban Mamansu da suka gama gaisawa.


Mama na gaji da auren Zayyad wlh wulaƙantani kawai yake yi saboda yayi auren nan.


Hauka kike yi halan da kaka ce kin gaji da aurensa, to me akayi da 'yan maza ai zama ba fashi.


To ya zanyi Mama? gabaɗaya na rasa ta ina zan karkato da hankalinsa kaina.


Har yanzu da sauranki Rashida shi namiji ai sai annuna masa da gaske ana sonsa shine za a zauna lafiya, dan haka zama bai ganki ba.


Shiyasa nazo dan naji ta ina zan shawo kan matsalata, sannan ma ina so naje asibiti a cire mini implant ɗin nan.


Ba dai kin biye masa ba kina wani tsarin iyali, aiko ga amarya nan tana fara zuba kwai zata kamo ki, dafa yanzu kinyi haihuwa ya kai huɗu zuwa biyar amma saboda kin biye masa gashi ba a je ko ina ba ya yi aurensa, kuma in baki wasa ba haka zaki cigaba da zama 'yar kallo.


Cewar mamanta tana taɓe baki, Rashida tayi kwaɓa kwaɓa da fuska kamar zata fashe da kuka.


Mama ya zanyi?


Bari in shiga bayi inyi wanka ina zuwa.


Maman ta bata amsa tana miƙewa ta wuce, Zaliha ta muskuta gurin Rashida.


Anty wlh sai kin cigaba da haɗa mata makirci kamar yadda Anty Wasila tace dan na kula wannan kishiyar taki a tsaye take.


Rashida ta tallabe haɓarta tana jin wani tuƙuƙin baƙin ciki a cikin ranta, tama kasa magana dan takaici.


****


Safna.


Tunda Zayyad yayi mata maganar kitso sai ta fara shirin wanke kanta dan sai ta wanke tayi driying ɗinsa gobe In Allah ya kaimu sai taje kitso, duk da tana da shampoo amma bata yarda tana wanke kai da ruwa mai haske ba sai da ruwan haɗin kayan islamic, shiyasa tun kafin aurenta taje ta siyo kayan buƙatarta ta adanasu dan tafi gane ta riƙa yin gyara dakanta, hatta hand dryer ta saya sabo wanda zata riƙa busar da gashinta koda ya jiƙe, shiyasa kullun kanta yake fidda ƙamshi tunda aka kawota to tana kula dashi tare da shafa masa mai da busar dashi. Ta shiga ɗaki ta ɗauko Ganyen magarya, Ganyen dalbejiya, Habbatus sauda 'ya'yan Hulba, ta shiga kitchen tayi giretin albasa da tafarnuwa, sai ta haɗa wannan kayan duka a babban tukunyarta ta ɗaura a gas ta kunna tare da zuba ruwa mai yawa ta barshi domin ya tafasa. Sai ta kuma yin giretin albasa ta tace ruwan ta zuwa a ƙaramin kofi ta fito ta shiga ɗakinta ta samu kibiya tana tsaga kanta tare da yayyafa ruwan albasan a ƙasan gashinta, tana cuɗawa har sai da ta tabbatar da ruwan albasan ya gauraye kanta sai ta samu leda ta saka akan, ta ɗauki kofin ta mayar kitchen ta wanke kayan data ɓata kana ta dawo falo ta kunna kallo tana yi tana charting, har sai da ruwan nan data dafa ya tausa dan taji ƙamshinta har falo, taje ta sauke ta kashe gas, kana ta dawo dan ruwan ya huce. Ta ɗauki kusan awa biyu a haka kafin ta ɗauko bokitin bayi ta juye ruwa nan tare da tace shi, ta ɗauka ta wuce toilet ta cire ledar data rufe kanta da shi ta ɗauki shampoo ta soma wanke kan da wannan ruwan maganin, har ta gama tas kafin ta samu ƙaramin towel ta ɗaure kanta dashi ta mayar da komai inda yake ta wanke bayin, sannan ta fito falo ta zauna towel ɗin ya tsane ruwan kanta sai ta fito ƙofar ɗakinta da kum ta taje kan, sannan ta koma ɗaki ta ɗauki hand dryer ta jona a wuta ta busar da gashin, sai ta samu haɗaɗɗen manta mangyada pure one wanda bana gida ba, da man kaɗe data gaurasu ta haɗa su sosai shiga shafawa akan, ta kuma ɗauko man kitsonta da aka saka mata a akwati ta ɗauka ta saka a kai, wanda shima ta saka masa haɗin mangyaɗa da man kaɗe a ciki ta gaurayasu, ta shafa kan yaji mai sai ta kuma saka hand dryer ta narkar da man ya gauraya gashin sai ta taje ta yi parking ɗinsa sai sheƙi yake yi, wannan shine sirrin sumar Safna tana ɓata lokaci gurin gyaransa, wannan haɗin data yi yana taimakawa wajen maganin amosanin kai da dandrop da kuma maganin karyewar gashi ne da kuma ƙarin tsayin sumanta. Ta dawo ta zauna tana tunanin me zata ci da rana, a lokacin ne aka kira sallar azahar ta miƙe taje ta gabatar ta fito ta shiga kitchen ta ɗaura sanwar taliya dan taci da sauran miyarta, ta dawo kenan taji sallama a ƙofarta taje ta buɗe sai taga wata mata ce baƙuwar fuska, da fara'a ta tarbeta suka shiga ciki suka zauna tare da gaisawa.


Ni maƙociyarku ce nace bari na leƙo naga amaryar Rashida.


Allah sarki nagode ya yaran.


Lafiya lau sai naga kamar Rashida ta fita ko, dan nata sallama ba a buɗe ba.


Gaskiya ban sani ba amma da alamar ta fitan tunda har bata buɗe ba.


Safna ta faɗa tana miƙewa ta wuce kitchen ta ɗauki plate ta fito zuwa Bedroom ɗinta da ta aje cincin da diblan ta ɗibo mata sai ta fito taja mata center table a gabanta tana cewa bisimilla, matar tayi mata godiya.


Ai yara ma sun shigo an basu, da alama anyi miki kayan gara da yawa, ace har yanzu bai ƙare ba duba da wannan rayuwa da muke ciki.


Aiko dai da yake ba mutane sosai da suke shigowa shiyasa.


Nan a miƙe dai ta koma kitchen ta saka taliya a ruwan daya tausa, ta fito ta zauna matar tana cewa zata tafi, Safna tace ta tsaya ta shiga ɗaki ta ɗauko leda ta juye mata cincin ɗin ta bata ta yi mata godiya ta fice bata tsaya tambayarta wani gida take ba, dan ba lallai ta shiga ba tunda ita tun asali ba mai son mutane bace kuma tasan duk suna mu'amala da Rashida bata son damuwa. Lokacin da taliyar tayi ta saka ta fito ta zauna tana ci, a lokacin ne su Ilham suka dawo direct ɗakinta suka nufo dan dama Rashida ta faɗa musu in sun dawo su je sashin Safna, suka shiga buga ƙofa tayi sauri ta miƙe ta buɗe, ganin su ne ta ce cikin kulawa.


'Yan makaranta kun dawo, kamata yayi kuyi sallama ba buga ƙofa ba koda ina bedroom zanji ku.


To suka ce mata sai ta matsa suka shiga ciki, Aslam yana ganin abinci ba magana yaje ya zauna ya soma ci, da kallo Safna ta bishi tana mamakin wannan lamari, sai ta isa gurin plate ɗin ta ɗauka tana cewa.


Ka bari ayi maka tayi mana malam Aslam, ina zuwa.


Ta wuce Kitchen ta zuba musu sauran taliyar data rage akai ta juya musu ta ɗaukowa Ilham cokali ta fito falon ta aje musu a carpet tace suje su ci, sai suka sauko suka soma ci ta ɗauki plate ɗin data zubawa matar nan cincin ta je ɗaki ta ɗibo ta aje a hannun kujera, sai ta shiga kitchen ta haɗa tea ta fito ta zauna ta ci badan ranta yaso haka ba, yunwa take ji kuma ba zata iya jiran ta dafa wata taliyar ba haka ta tusa cincin da tea kuma ta ƙoshi, yaran da suka gama suka bar mata wanda suka zubar a caepet ko wanne yaja kujera ya zauna yana mayar da numfashi dan sun ƙoshi sosai, da kallo ta bisu bata ce komai ba ta miƙe ta tsince wanda suka zubar ta ɗauki plate ta mayar kitchen ta tsaya wanke kayan, a lokacin ne Aslam da Ilham suka miƙe suka wuce bedroom ɗinta suka ga robar cincin a can jikin bango, suka isa gurun suka cicciko hannunsu suka fito falo suka zauna suna ci, Safna data fito ta gansu da cincin sai ta tsaya ta kama ƙugu.


Kai waye ya baku cincin?


Mun shiga ɗakinki mun ɗiba ne.


Da izinin waye kuka shiga har Sakina kuka ɗiba? Ina wasa da ku ne, taya zaku ɗiba abu ba tare da ance muku ba, wannan wani irin tarbiyya aka baku? to bazan ɗauka ba matsawar kuka ga abu ban baku da hannuna kuka ɗaukar mini Allah sai na bigeku.


Ta ƙare maganar ta wuce bedroom ɗinta, nan taga marfin robar akan gado suka barshi ba su rufe ba, tayi ƙofa ta je ta rufe kana ta dawo falon ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login