Showing 1 words to 3000 words out of 43291 words
RAMIN MUGUNTA
Ka gina shi dai-dai da kai
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN MMN HIBBA
SADAUKARWA
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA
ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)
AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljanna yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
GARGAƊI
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
07073193332
1-2
Ƙarfe sha biyu na dare dai-dai babu abin da kake ji se kukan tsin tsaye daga can kuma se harbin bindiga ta ko ina ji kake tau tau darammmmm har sashi se wuce wa yake kamar ruwan sama nan da nan garin ya kuma yin shiru, a daidai wani tanƙa meman gida ƴan fashin suka tsaya dukkan su fuskokonsi arufe suke wasu daga cikinsu ne suka ɗa ne katangar gidan ɗakin me gadi suka shiga inda suka rakumi shi se gashi atsaye yana rarraba ido ya buɗe baki ze yi ihu ɗayan yace. “idan ka kuskura kayi mana ihu sena sa bindiga na fasama ƙwa ƙwalwa wallahi” tsutt me gadin ya tsuke magan sa kamin wannan lokacin tini ya fitsare wandan sa da firsari jikin sa se kyar ma yake janyo shi suka yi xuwa harabar gidan biyu daga cikin su ne suka buɗe wa sauran gett suka shigo inda suka yiwa gidan ƙawanya me gadi suka sa a gaba suka ce ya nuna musu sashin me gidan tiryan tiryan ya kai su duka ɗaya oga su ya yiwa Ƙofar ta buɗe suka shiga farlon, nan ya bawa yaran nasa izinin da su taso masa masu gidan cikin mintina ƙalilan suka tasosu bayin allah dik sun ruɗe musamman me gidan , yana kuka yana basu haƙuri tara da cewa in dai kuɗi suke so xe basu amma su kai ƙema da gass suka ce su ransa suka zo ɗauka kuma turosu akayi. “gwaja” “na'am” oga “miƙo min bindiga ta” miƙa masa yayi ya amsa tara da saita kan alhajin kalmar shahada ya Shiga yi yana kaiwa ƙarshe. harasashi ya fasa kansa take ya faɗi ƙasa wata ƙara matar ta saki bata gama ƙarar ita ma ya sakar mata bulet nan da nan jini ya wanke ɗakin, MANAL wacca take ɗakin ta ta jiyo ƙarar bindiga tayo waje a zatan ta wani gurinne taji tsoro ta fito dai-dai lokacin da ɗan fashin nan ya harbi mahaifiyar ta ƙara ta saki tara da yin wurin iyayan nata wanda suke kwance cikin jini, “ABBA MOMY ABBA ku tashi ku tashi dan Allah MOMY ki tashi kufa kuka min alƙawarin zaku kaini gurin wasa gobe shine.. se kuma tayi shiru tara da juyawa gurin ƴan fashin cikin zafin nama ta warci bindigar... “kun kashe min iyaye na kun rabani dasu me suka muku na san iyaye na masu kirki ne amma yau gashi kun raba ni da su dan Allah ni ma ku kashe ni se ta saita kanta da bindigar data ƙwata a hannun su , ogasu ne yayi saurin amshe bindigar yace “ ba a ce muka sheki ba dan haka mungama ai kin mu se an jima” yana gama faɗar haka yayi waje ragowar suka mara mai baya aka bar ta daga ita seme gadi wanda tini yayi suman tsaye, itama MANAL faɗuwa ƙasa tayi sumammiya gari na waye wa unguwa ta ɗauka ƴan fashi sun kashe ALHAJI SA'AD ME DALAH kan kace kwabo zance ya yaɗu gidan rediyo talabijin kai har A jarida a buga dik wanda yaji labarin se yayi kuka yayi ala-wadai da dik wanda yake da sa hannu acikin kisan domin kowa ya san ALHAJI SA'AD mutumin kirki ne ga temakon, talakawa haka itama matarsa hajiya ZARAH. mutuniyar kirki ce ga faran faran da mutane, ƴan jaridu da masu bincike sunyi iya ƙoƙarin su wajan binciko wa inda suka yi wannan ta asar amma basu samu wata Hujja ba MANAL kuwa da ƙyar aka samu kanta dan tayi doguwar suma bayan an haɗa su aka ce tazo tayi musu addu'a dan a kaisu makwan cin su anan ne MANAL ta kuma shiga wani sabon tashin hankalin kan gawar iyayan nata ta faɗa tana kuka me ban tausayi se da ta bawa kowa tausayi da kyar aka janye ta aka saikace su sannan aka kaisu makwan cinsu., tin da aka fitada gawar wani su MANAL ta kuma suma har aka dawo daga Kai su bata far faɗo ba se da aka dan gana da asibiti shima da kyar a kasamu kanta sannan akayi mata allurar bacci, se magariba ta farka tana ƙarewa ɗakin da aka kwantar da ita kallo hawaye na bin gefen idonta, “haƙuri zakiyi MANAL haka Allah ya ƙaddara musu ta wannan hanyar Allah ya karɓi rayuwar su su kuma wa inda suka kashe su Allah ya ganar dasu”
ko bata juya ba ta san waye me magana wato ALHAJI BUKAR ne ƙanin mahaifin ta uwassu ɗaya ubansu ɗaya, wani sabon kukan MANAL ta ƙara fashewa da shi ganin ƙanin mahaifinta amma babu mahaifin ta agurin nan suka yo kanta shi da matar sa da ƴa ƴansa suna rarrashin ta “ki dena kuka MANAL in sha Allahu ba zaki yi rashin iyaye ba zan maye miki gurbin ɗan uwana kuma ga maman su NABILA nan itama zata nake miki uwa kinji ƴa ta, ni dai fatana kirki sa damuwa aranki wani abin ya same ki ina so naga jinin ɗan uwana dan Allah MANAL kiyi haƙuri ki fawwalawa Allah komai kinji” kai ta gyaɗa mai alamar to ta juya ta kalli su NABILA da ZAINAB wa inda suka yi jugum murmushin ƙarfin hali tayi tara da yi musu alama da su matso gare ta nan kuwa suka ƙaraso ta ruƙo hanna yansu tana kallansu ba tara da tace komai ba.
To
bayan sadakar bakwai dik wasu kadarori na ALHAJI SA'AD ME DALAH suka zama mallakin MANAL tin agurin ALAJI BUKAR ya nuna ƙin amince warsa, se dai a raba dukiyar biyu A bashi rabi inda aboka nan margayi wato ALAJI SA'AD suka ce a ah hakan baze yu ba yayi haƙuri ƙarshe dai aka rabu baran baran har alaji bukar yana cewa, kila ma su suka kashe mai ɗan uwan sa ..
BAYAN ANYI ARBA'IN.
Gaba ɗaya alaji bukar da ƴaƴan sa suka kwaso kayan su suka dawo gidan kowa ya zaɓi inda ze zauna tin daga nan MANAL ta fara ganin sauyin rayuwa babu wanda yake bi ta kanta idan gari ya waye akayi abin kari babume kiran ta se dai ta jiyo hayaniyar su suna shewa ita kuwa tana ɗaki kullum cikin karatun alƙur'ani take. tana nema wa iya yanta rahama wajan ubangiji tina nin iya yanta ya dame ta kullum se ytayi mafarki dasu musamma MOMYN ta yau ma kamar kullum cikin bacci tazo mata tana yi mata nasi ha da taji tsoran allah kada ta kus kura ta saɓa mai idan ta tsinci kanta awani yana yi dik yanda tasamu kanta tayi haƙuri ta kuma gode masa dan wata rana se labari, firgigit ta tashi daga baccin da take saka makon dukan da taji an ɗala mata NABILA ta gani tsaye akan ta tana binta da wani irin kallo wanda ta kasa gane ma'anarsa “ idan kin gadama kixo in ji DADY " daga haka NABILA ta fice daga ɗakin gami da banko mata ƙofar kallan mamaki MANAL ta bita da shi bata kawo komai a ranta ba ta miƙe tare da shiga tolet tayi wanka ta sauya kayan jikin ta ta saka hijab ɗin ta har ƙasa ahankali take tafiya kamar ba itaba, canjin yana yin data gani akan fuskokin su ya bata tsoro musamman DADY, kusa da shi taje ta zauna akan kafet tace “ina kwana DADY” “da ban kwana ba zaki ganni tin ɗazu na aika akiraki se yanxu kika gadamar zuwa?” girgiza Kai tayi gamida cewa “kayi haƙuri DADY” tsaki yayi yace. “so nake ki bani dik wasu takaddu da aka baki wanda akace kinci gado” da sauri MANAL ta ɗago kanta tana duban sa. “ eh ai na san kinji me na ce ” ya faɗa cikin tsawa wadda ta ƙara firgita ta . “to DADY bara na kawo maka” ta faɗa cikin muryar kuka da razana tin da take ba'a taɓa yi mata tsawa ba sega shi yau bayan ran mahaifan ta taga sauye sauye, cikin mitina ƙalilan ta kawomai jakar takar dun da dik wasu kadarori da aka bata karɓa, yayi yana washe baki „zan ajiye miki a guri na dannaga ke biki ɗauke su da mahimmanci ba” to kawai tace mai dik da bahaka taso ba.
Ahankali rayuwa tayiwa MANAL ƙunci dik wannan ƙibar da hasken yanxu babu su yanxu ne ta san meye rayuwa ya akeyin ta gaba ɗaya ta fita a hayya cinta ta lalace, sakamakon baƙae wuyar data kesha A gurin ƙanin mahaifin ta dama matar sa da ƴaƴan su sun mai da tamkar baiwa MANAL da bata san sn shiga kicin ba yanxu ta sani wanki shara wanke wanke dik ita keyi inka ganta ba zaka taɓa cewa ta taɓa rayuwar jin daɗi ba wani. gigitaccan mari NABILA ta wanke ta da shi hagu da dama tace “ dan ubanki haka ake wanki? ji yanda kika bari kaya na suka ɓaci da ƙasa to wallahi se kin kuma wanke su kuma ki zauna anan har sesun bushe kinji Me nace ?” da suri MANAL tace “to” tsaki NABILA tayi, "shasha kawai dabba da bata san komai ba wallahi dama na tsane ki yanxu ba kida wani zaɓi daya wuce ki bimu in ba haka ba muna kasa ki, wannan kyan naki da kike taƙama da shi se na disa she shi kin zama mujiya acikin muatane.” tana gama faɗin haka tayi gaba. durƙushewa MANAL tayi ta saki kuka m ecin rai, mutuwa men min yan kan ƙauna kin raba ni da iyaye na tin ba aje ko ina ba na fara ganin sauyi wanda nake tina nin ze share min hawaye na shine A sahun gaba wajan ganin an kuntata min a yanzu ni MANAL ko suturar kirki bani da ita suna NABILA sun kwashe babu hutu kullum cikin aiki babu abinci me kyu babu gurin kwana me kyau ƙarshema aɗakin baƙi nake kwana wayo ni MANAL ya Allah ka kawo min ɗauki........”
MMN HIBBA CE
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER✍️
SUMAYYA ABDULLAH
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.✍️
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
3-4
Haka MANAL ta kuma wanke kayan dik da sanyin da ake su rawa , sannan ta zauna zaman jiran su bushe “kee kee kee MANAL” mamy ce take ƙwala mata kira, jiki na kyarma taje ta tsuguna “gani mamy" ta faɗa cikin rauna nan niyar murya dan tasan yau kashin ta ya bushe bata gama tina nin da take yi ba taji an rife ta da duka, ta ko ina ihuu take tana bata haƙuri amma kamar tana tunzura ta ƙafa tasa ta ringa haurin ta har se da taga ta galaɓai ta san nan ta ƙyale ta zuwa wannan lokacin MANAL ji take gwara mutuwa da wannan azabar da take ciki, ƙafa tasa ta taka mata hannu wata razananninyar ƙara ta saki se kuma ɗif babu alamar rai ajikin ta , “kuma wallahi ki tashi ki je ki ɗora abin cin rana ki gyara gidan nan dan baƙi na sun kusa ƙaraso wa ” se ta kuma harbin ta da ƙafa ta juya cikin gida abin ta, ahankali MANAL ta soma buɗe idon ta da suka mata nauyi tafi minti talatin da far faɗowa daga suman da tayi amma ta kasa motsa wa ji take kamar hannun ta ba'a jikin ta yake ba, tazo zata miƙe jiri ya kuma ɗibar ta, ta kuma
faɗuwa ta yi haka ya kusa sau uku kafin Allah ya bata sa'a ta miƙe tana ɗingisa ƙafa haka ta shiga kicin ɗin dik da ba gani take sosai ba ta jima tana girki ita ce ɗora wannan sauke wannan se la'asar sakaliya ta gama,
sa shin msmy ta nufa wanda ada yake mazaunin na MOMYN ta da sallama ta shiga amma ba'a amsa ba hakan yasa ta kuma yi wata sallamar ZAINAB ce ta fito daga ɗakin ba tara da ta kalli inda take ba tayi gaba ganin haka yasa ita ma MANAL ta fito daga ɗakin A hanya sukai karo da mamy tayi saurin durƙusawa ƙasa baki na rawa tace “momy na gama girkin ko da abin da za'ayi miki ?" wani matsiyacin kallo ta bita da shi kana tace, “au so kike in kuma mai mai ta miki to cewa na yi ki gyara ko ina na gidan nan”, sunkuyar da kai MANAL tayi hawaye na bin kun cin ta cikin tsoro da gudin abinda zeje ya dawo tace “ dan Allah mamy ki bani abinci yinwa nake ji yau kwana na biyu banci komai ba ”
“ehhh lallai yarin ya kin giga ina magana kina cewa abinci zaki ci shegiya acici to ka zakici ba maza maza ki tashi kiyi abinda nace miki” ta faɗa cikin tsawa jiki na ɓari, MANAL ta tashi har tana neman faɗowa daga matattakalar benan haka ta gyara gidan tana yi tana faɗuwa sabida yinwar da taci ƙarfin ta, tana gamawa taja jiki da kyar ta shige ɗakin ta , sallah ma a zaune tayi ta, tana idar wa ta ɗan kishin giɗa. nan take wani azababben bacci me haɗe da yinwa yayi gaba da ita tara da