Showing 27001 words to 30000 words out of 43291 words

Chapter 10 - RAMIN MUGUNTA Complete by Maman Hibba .txt

22 Nov 2024

4047

be bayar ba sannan bana so kowa yaji wannan maganar abar ta iya nan ni, zanji da komai Allah ya shige mana gaba" gaba ɗaya suka amsa da Amin. "To MANAL ga baban nin ki, nan duk abinda kike so ki tambaye su nan gidan ku ne ki yi komai kanki tsaye India be saɓa faɗar Allah ba duk Kuma wanda kika ga ze miki ba dai-dai ba to kizo ki gaya min in ɗau mataki kinji ko"? ''insha Allahu ranka ya daɗe nima kuma zaka same ni ame yi muku biyayya har ƙarshen rayuwa ta Na gode sosai Allah ya ƙara maka lafiya'' suka amsa da ameen ameen. "Ni dai ranka ya daɗe ina so a bani ita danna kula da ita'' cewar Gwaggo. Murmushi, me martaba yayi yace. ''an baki ita uwar yara na san zaki kula da ita dan bani da shakku akan ki,''. ''godiya nake ranka ya daɗe Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana'' ''Shike nan nima na samu abokiyar fira kuma a ɗaki na zamu ringa kwana'' cewar MEENA tana dariyar farin ciki, Harara SUHAIL ya banka mata dan haka tayi tsit ne san me martaba yana kallon sa ba seji yayi yace ''sannu baba na da wannan kallon da kake mata me tayi maka? dan kawai tace zasu kwana guri guda shi ne kake hararar ta wato kai me mata ko'' da sauri SUHAIL da JAMAL suka fice daga farlon suna dariya. To rayuwar MANAL a cikin gidan sarauta ta zama tamkar ƴar gold kowa ririta ta yake babu wanda ya taɓa yi mata koda kallon banza duk inda take so zata shiga ko tayi abinda take so duk inda kaga MEENA to zaka ga MANAL sun zama tamkar ƴan biyu.
yau da daddare bayan sallar isha MANAL ce kwance akan gado tana danna waya kiran SUHAIL ya shigo ta ɗauka tara da karawa akunnan ta tayi sallama amsawa yayi ciki ciki ya ɗora da cewa ''wato MANAL dana ce kizo shine kika ƙi zuwa se kace zan cinye ki ko, shikenan Nagode'' ɗifff ya katse kiran da kallo tabi wayar ita ma ta san bata kyauta ba jikin ta ne yayi sanyi ace tun daga yanzu ta fara ɓatawa mijin ta rai amma ai ba lefinta bane gwaggo ce ta hana ta zuwa sakkowa tayi daga kan gadon ta ɗaura hijab akan rigar baccin da take jikin ta, ta ƙofar baya tabi dan kar Gwaggo ta ganta tana zuwa masu gadin shi suka bata hanya ta shiga bata same shi a farlo ba dan haka ta wuce cikin ɗakin kwance ta same shi ya ƙurawa silin ido yana kallo kamar me naza rin wani abu ''YAYA gani'' ko kallan inda take be yi ba bare tasa ran xe bata amsa. Zama tayi abakin gadon ta kamo hannin sa ta haɗa da nata tace ''plsss YAYA SUHAIL dan Allah kayi haƙuri wallahi Gwaggo ce ta hanani zuwa yanzu ma bata san na fito ba.


Zaga yawa tayi inda ya maida fuskar sa ta marai rai ce tana bashi haƙuri ''yanzu kina nufin ban isa ince kiyi abu kiyi na san kinyi karatun addini kin san hukuncin macen da bata bin Umar nin mijinta amma shine har kike gayamin cewa wai Gwaggo ce ta hanaki zuwa kenan ita take auran ki ?'' "a'ah amma naga ita uwace a guri na idan nayi haka ba-zata ji daɗi ba seta ga kamar dan ba ita ta haife ni ba shi yasa banji maganar ta amma kayi haƙuri'' hannun ta ya kuma riƙe wa yace ''ya na iya tunda ina son ki'' bata san sanda tace ''nima ina sonka''. da sauri ta rufe fuskantar da tafin hannun ta dariya yayi yace ''me kika ce ɗan mai mai ta banji ba'' baki ta turo gaba, kana tace ''wallahi kaji kawai dai kana so na kuma faɗa ne'' ''eh naji amma sekin kuma mai mai tawa'' Ina son ka Ina son ka YAYA SUHAIL har Cikin, zuciya ta tun randa ka dawo daga na ganka naji zuciya ta ta Amin ta da kai,'' '' da gaske MANAL kina so na amma naji daɗi sosai da kema kina ƙauna ta atina nina ni kaɗai nake sonki'' murmushi ta sakar masa wanda ya bayyanar da farin ciki, hancin ta yaja yace ''yanxu ki koma kar Gwaggo ta gane ba kya nan'' miƙe wa tayi ya raka ta har bakin ƙofar yana jin wani son ta na Kuma shigar sa , tana komawa ta ta tarar da MEENA tayi shirin kwanciya ga waya akunnan ta da alama waya take yi itama kwanciyar tayi MEENA ce ta juyo ta kalle ta se wani murmushi take ita kaɗai ''Anty MANAL ina kika je tun ɗazu nake neman ki yanzu kuma kin shigo kina ta murmushi ko dai gurin yaya SUHAIL kika je ?'' harara ta jefa wa MEENA tace ''idan ma gurin sa naje ina ruwan ki naga miji na ne''''' ''iyeeeeeee lallai kema kin zama irin yaya SUHAIL yanzu babu kunya kike cewa mijin ki ne nifa ƙanwar mijin kice tamkar suruka nake awajan ki'' duka MANAL ta kaiwa MEENA ta goce tana mata dariya, kwanciya ta yi tana cewa zaki gane kuran ki.”
WASHE GARI
ya kama juma'a aranar ne aka kawo lefan MANAL wanda daga ƙasar India aka siyo su
zo kuga kaya kamar an buɗe kantin kwari aka kira MANAL tazo taga kayan lefan ta kuka MANAL ta saka wannan kayan ko iyayan ta ne iya kacin abinda su suyi mata ke nan da kyar aka samu tayi shiru se godiya take musu. SARKI yasa aka kirawo ta yayi mata nasiha Sannan yace kar ta kuma yimai godiya in kuwa tayi yasan bata ɗauke shi a matsayin mahaifin ta ba sannan yace idan akwai abinda be mata ba ta faɗa A canza mata Kuma ta zaɓi kalar kayan ɗakin data ke so seta gayawa su Gwaggo Asiya mata ya danƙa mata sadakin ta Wanda bata san iya adadin su ba sannan ga mulkin mota ɗaya SUHAIL ne ya bata ɗaya kuma shi ya bata sannan Kilishi ita ma ta bata Sai kuma Gwaggo wacce ta zama babar amarya MANAL ita kuma ta bata kyautar GIDA dan ƙarere.




Yau ne ya kama asabar kuma yau ne ran da aka shirya taron bikin, kowa mamaki yake a ina SUAHAIL ya samo matar aure A'lna ma aka ɗaura auran? dik iyakar me gulma an kasa gane kan zaran duk wanda ya tambayi me martaba se yace ƴar ɗan uwan sa ce daga haka kowa yaja bakin sa ya zuge . Biki yayi biki, bikin da ya haɗa manya manyan sarakuna da ƴan siyasa da masu kuɗi kaɗe kaɗe da bushe-bushe kawai ke tashi faɗar kyan da MANAL tayi ɓata lokacine tayi kyau iya kayu ga alkyabba da akasa mata ta fito a matar a saki seta juye ta zama jinin sarauta daloli aka ringa watsawa kai kace shara ce ko takardu ne Se yamma likisss biki ya tashi
wajan ƙarfe tara na dare aka raka amarya ɗakin ta wato ɓan garan SUHAIL ƙarfe sha ɗaya abokan ango suka rako shi bayan anyi siyan baki aka ɗora da nasiha Sannan akayi addu'a kowa ya kama gaban sa aka bar amarya da ango sallah sukayi bayan sun idar ya kama goshin ta yayi mata addu'a sannan yayi mata wasu ƴan tambayoyi Game da addinin ta, ta kuma bashi amsa yanda ya kamata kajin da ya shigo dasu ya ɗakko sukaci suka kora da madara kamar kowa na angon da aka kai mai amarya ɗakin sa kuma suke raya sunnar ma aiki (s.a.w) haka suma daran ya kasance a gare su sun nunawa juna kulawa sosai SUHAIL kuwa ya godewa Allah daya mallaka mai MANAL a matsayin mata kuma ya same ta abudurwa.
WASHE GARI
da safe kamar yanda al-adar masarautar take farin ƙyallan da aka basu aka fito dashi kowa ya gani wannan shine shedar MANAL ta kawo budur cinta gidan miji


''MANAL MANAL MANAAL ki tashi mana gari fa ya waye ki tashi kiyi sallah'' SUHAIL ya faɗa yana yaye bargon data lulluɓa da shi shashsheƙar kukan ta yaji, dafe kansa yayi kana yace '' me kuma aka yi miki MANAL? na ce bazan ƙara ba kiyi haƙuri mana ki tashi kiyi sallah lokaci na ƙurewa '' ''bazan iya tashi ba yaya SUHAIL don Allah ka kiramin Gwaggo wayoo Allah na zan mutu'' se ta fashe da kuka me ɗaga hankali gaba ɗaya tabi ta ruɗa SUHAIL shima ji yake kamar yayi kukan fita yayi cikin hanzari ya nufi sashin Gwaggo kamar an wurgo shi Gwaggo kizo dan Allah MANAL ce bata da lafiya se kuka take kuma ke take kira hankali tashe, Gwaggo tabi bayan shi yanda yabar ta haka suka zo suka sameta se yanzu hankalin Gwaggo ya kwanta dan ita atuna nin ta MANAL ɗin bata lafiya ne ashe ciwon da kowace mace take ji ranr daran ta na farko dan haka Gwaggo tace ya fita ya basu guri da kyar ya fita bayan fitar sa Gwaggo ta shiga bayi ta cika baf ɗin ruwan zafi Sannan tace ta shiga ƙara ta saka tana yarfe hannu ahaka har seda ta sauya mata sau uku sannan ta haɗa mata me tirarakan jiki tawshiga bayan ta gama mata wannan tasa aka kawo mata madara ta haɗa mata da wani magani wanda ze sassauta mata zafin da takeji tace ta kwanta ta huta bayan fitar Gwaggo SUHAIL ya shigo kan gadon ya hau tara da kamo hannun ta yana kallon fuskan ta ''sannu ko ya jikin naki'' tashi tayi zaune ta ɗora kanta a, kafaɗar sa ''da sauƙi'' shafa kanta yayi gamida ''to Allah ya ƙara sauƙi dana san haka zata faru da ban zo inda kike ba ji nake kamar ban kyauta ba” Cikin shagwaɓa tace. ''habaaa yaya SUHAIL kai ɗin fa miji na ne kuma Allah shiya halasta yin hakan tome zesa kace haka wannan ai ba abun damuwa bane kuma haka kowace mace take tsintar kanta ran daranta na farko idan har ta riƙe Mutun cinta ni dai ina alfahari da kai kai ɗin jarumi ne ta ko ina'' ta faɗa tarada rungume shi shima rungume ta yayi nan suka lula duniyar masoya.






MMN HIBBA✍️


RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)




WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)

07073193332


Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.


littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba_


GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.


NA GODE




23/24


GIDAN ALHAJI BUKAR.


Tin bayan barin MANAL daga gidan suka buɗe, sabon shafin rayuwa sun manta da wata MANAL karan su suke ci babu babbaka kuɗi kuwa kamar yayi mosu suke yi an samu dukiyar marainiyar Allah anata ci, NABILA ce ta fito daga cikin gidan tara da wani mutum babba kuma baƙiƙƙirin yake kamar gawayi amma me kuɗi ne na gasken gaske idan ba kuɗi ba babu abinda ze sa NABILA ta bashi fuska wajan da yayi fakin ɗin motar sa suka, nufa wata jib gegiyar mota cd mai numfashi ita kanta NABILA bata taɓa ganin Irin ta ba. Cikin kwar kwasa da yauƙi gami da yin fari da ido tace'' yanzu beby se yaushe zaka dawo kasan bana son kayi nesa dani ji nake kamar bani da lafiya'' ta ƙarasa faɗa cikin shagwaɓa. ''haba swet ki kwantar da hankalin ki, mana sati biyu fa kawai zanyi sannan inna dawo za'ayi maganar auren mu, danna gaji da zama babu aure ''to Shi kenan seka dawo ɗin pls ka kula min da kanka kaji beby'' mota ya shiga ya ɗakko wata ƴar ƙaramar akwati ya miƙa mata yace ''ga wannan kiyi mane ji dasu kafin na dawo'' karɓa tayi ta sunkuyo kanta dai-dai kuma tunsa tayi mai kisss wani jaɓarrrrr yayi a motar yana lumshe ido, wai shi yaji daɗi ''shi yasa nake so ayi maza-maza a bani ke dan kin haɗa komai da nake buƙata ta fannin ƴa mace'' dariya tayi mai shi kuma ya tada motar ya fita suna ɗagawa juna hannu.
''mommy mommy zo kuga Abin arziƙin'' da sauri mommy ta fito tana cewa ''kar dai kice harya tafi Allah yasa dai ya baki kuɗi masu yawa'' ta faɗa sa'ilin data zauna akan kujera buɗe akwatin tayi sega kuɗi fal akwatin kuma ba nera bace daloli ne jikin mommy har rawa yake, saboda murna bandir ɗaya ta dauka tana wul wulasu kana tace ''NABILA yanzu ne kika samu mijin da ya kamata ki aura dama wannan ranar nake jira kuma gashi tazo dan haka ki ce mai ya turo da maga batansa kawai ayi magana babu ruwan mu da koshi waye mu dai kuɗi k muke so kinga se a haɗa dana ZAINAB a yi mun huta dukiyar mu zata kuma haɓaka kina auran me kuɗi ita ma ZAINAB tana auren me kuɗi kai Allah Nagode maka, ƴaƴa na masu farin jini ga ƙashin arziƙi''' hhhhhh suka sa dariya NABILA tace '' mommy shi ma seda yayi min maganar yanzu yace shi baya so aja lokaci'' to mu meya ruwan mu ko yanzu ya fito bashi ke, zamuyi India da wannan ai bamu da matsala ta faɗa tana karkaɗa bandir ɗin dalolin dake hannun ta. Daddare ALAJI BUKAR ya dawo Bayan ya gama cin abinci mommy ta kawo mai kuɗin da saurayin NABILA ya bata ta ɗora da faɗin "kuma yace inya dawo ze aiko da manyan sa ayi maganar bikin su ," washe baki Dady yayi yana ɗaga kuɗin yace '' ko yau yace a ɗau musu aure da ita ai bashi ita zanyi me za mu, tsaya jira muga samu muga rashi" '' nima haka nace kaga faɗuwa tazo dai-dai da zama se ahaɗa dana ZAINAB'' cewar mommy. jin jina, kai Dady yayi alamar gamsuwa da maganar ta, "kaga tunda wannan shegiyar yarinya ta bar gidanna muke, ta samun alkari dama na gaya maka kasan yanda kayi da ita idan ba haka ba wallahi muda ci-gaba se dai muga ana yi yanzu gashi duk yaran mu, sun samu mazajan aure masu kuɗi na kere sa'a''. taɓe baki ALHAJI BUKAR ya yi kana yace ''ni fa wallahi na manta da wannan ƴar iskar yarinyar kuma banaso a dinga tuna min da ita taje can ta ƙaraci Iskan cin ta,'' kamar yanda saurayin BABILA ya faɗa in ya dawo ze aiko iyayan sa hakance ta kasance suka zo akayi magana saboda tsabar idon su ya rufe basu tsaya binciken ko shi waye ba, daga ina yake suwaye iyayansa. sati biyu aka saka Kuma yace karsuyi komai na kayan ɗaki shi zeyi NABILA kawai yake so akawo masa ko tsinke kar akawo ta dashi murna da farin ciki suka mamaye su, ita ma ZAINAB haka nata saurayin yace shi ze mata komai su ZAINAB da NABILA se gyaran jiki akeyi inka gansu kamar ka sace su, dan kyau tun ranar Laraba aka fara biki kuma duk fita akeyi tunda aka fara bikin ba'a liƙa nera ba Daloli kawai ake amfani dasu mommy kuwa se fan kama take cikin ƙawayan ta tana homa yaran ta sunyi dacen mazaje masu kuɗi se bisha sha akeyi da kuɗi kamar ba'a so Raƙuma da shanu aka yanka na girkin biki Banda naman kaji wanda akakai aikin su wajan masu girkin abincin biki ko suna Yau Lahadi kuma yaune aka ɗaurawa su ZAINAB aure akan sadaki masu tsoka NABILA akan sadaki million hamsin ZAINAB kuma million tala tin bayan ɗaurin aure duk wanda ze tafi se anbashi jaka wanda aka manna hotan amare da angwaye ajiki kayan ƙwalma da ma kulashe ne aciki se kuma tsabar kuɗi nera duba ashirin haka aka ringa rabawa duk wanda suka halarci bikin maza da mata shaɗaya na dare angwaye suka turo moto cin ɗaukar amare domin kai su gida jansu dik cikin motocin babu motar ƙasa da million ashirin se walainiya suke da ɗaukar ido haka akasa kowacce amota domin kaisu gidan jansu...


MASARAUTAR ZAKI




A ɓan garan amarya MANAL soyayya kawai suke sha ita da mijin ta SUHAIL gaba ɗaya ta miƙa masa kanta se yanda yayi da ita kulawa da soyayya kawai suka sani basu san wani abuba waishi ɓacin rai. MANAL ce a kicin tana ƙoƙarin ɗora grlirki SUHAIL ne ya shigo kicin ɗin bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login