Showing 42001 words to 43291 words out of 43291 words
ce tasa Meta muna roƙon ki da ki yafe mana mun san da wuya ki manta da irin abubuwan da muka yi miki'' cewar NABILA tana kuka kamar ranta ze fita Allah sarki MANAL me zuciyar imani '' Shi kenan na yafe maku Allah ya yafe mana baki ɗaya yasa hakan ya zama IZINA ga yan baya''' gaba ɗaya suka amsa da ameen
ZAINAB ce tace ''muna godiya MANAL kuma ina ƙara roƙon ki dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri ki yafe wa DADY'' share hawaye MANAL tayi kana tace '' na yafe masa seya nemi yafiya gurin Allah, Allah ya tsare gaba'' ''na na nagode sosai MANAL tabbasss ke jinin SA'AD ce na gode Allah yayi miki albarka dake da xuriyan ki, ya kare ku daga mugun ji mugun gani na gode ƙwarai da gaske'' cewar DADY yana kuka ga wani numfashi da yake fitarwa sama-sama me martaba yasa aka kaishi asibiti sannan ya basu abinci da kuɗi masu yawan gaske sannan yace idan wata matsalar ta taso suxo su gaya mai Godiya suka yi mai. Kwanan DADY biyu a asibiti Allah yayi mai rasuwa saka makon tarin daya ci ƙarfin sa wanda likitocin sukayi iya ƙoƙarinsu amma ina rai yayi halin sa . Lokacin da labari ya riski MANAL tayi kuka sosai koba komai shi ma ubane awajan ta rayuwa taci gaba da juyawa yau daɗi gobe akasin haka an samu ci gaba sannan kuma anyi rashe rashe ciki kuwa harda Mutuwar SARKI wato mahaifin SUHAIL mutuwar da tadaki kowa bayan arba'in aka naɗa SUHAIL amatsyin sarki, Wanda kowa yayi na'am da haka kwanciyar hankali ta wanzu ɓangaran su MEENA da JAMAL suma ba'a cewa komai dan kuwa itama MEENA ta haihu ƴa mace wadda taci sunan mahaifiyar JAMAL suna kiran ta da KAISAR NABILA ma tayi aure inda ta sami me irin cutar ta ta amince masa suna zaune cikin rufin asiri ZAINAB ma ta koma gidan tsohon mijin ta MUKUTAR wanda tun bayan tafiyar ZAINAB asirin da HAULE tayi mai ya karye ya danƙara mata saki suna zaman su cikin so da ƙauna ita da yaran HAULE wanda ta fita ta bari MOMMY kuma SUHAIL ya siya mata gida sannan lokaci-lokaci suna xuwa su gaishe ta, MIJIN NABILA da ta aura ƴan sanda sunyi nasarar danƙe su gaba ɗaya su Wanda dama tun lokacin da aka kaisu NABILA wajan su suka sa musu ido yana dirowa garin ƴan sanda sukayi ramm da shi. aka kuma ka masu Gaba ɗaya.
BAYAN SHEKARA TAKWAS.
Wasu kyawawan yara na hanga cikin wani ƙaya taccan farlon suna wasa wasu kuma suna karatu. wata mata ce ta fito cikin shiga ta alfarma gefanta kuyangu ne guda uku hannayen su riƙe da kwani ka, ɗaya kuma tana ɗauke da jariri da alama dai ɗan matar ne lokacin da suka ƙaraso seda na murza ido na danna ƙara tabbatarwa da gaske ne Abinda ido na yake gane min ko kuma gizo ne. Murzawa nayi da kyau na kuma buɗe su fesss akan. Matar da gaske ne MANAL ce agaba na ta zama big Madam komai nata ya sauya ta zama. Babbar mace. Gaba ɗaya yaran suka taso suna mata magana kowa da abinda yake cewa bata saurare su, har seda ta sallami Kunyan gun ta karɓi jaririn gaba ɗaya sun. Cika mata kunne tama rasa yanda zata yi dasu tsawa ta daka musu tsittt suka yi kamar ruwa yaci su '' haba gaba ɗaya kun dame Ni, dame zanji se kace ku kaɗai ne ƴaƴa wallahi duk wanda na sake jin bakin sa sena zane shi'' ta faɗa cikin zare musu ido, USAINI dake zaune kan kujera yana danna computer yace '' kema mommy idan da sabo yaci ace kin saba da hayaniyar wa'inna ɓerayan na ki'' '' ƙyale su, baba na sena ringa zane su tunda basa jin magana musamman kai NAUFAL me taurin kan tsiya irinna baban,ku'' dai-dai lokacin SUAHAIL ya shigo farlon ''naji duk abinda ake cewa ƴaƴa na masu tauri kai irin nawa'' ya faɗa tarada Zama akan kujera gaba ɗaya sukayo kansa kowa yana so ya hau cinyar sa, ɗaukar su yayi ya ɗora su, yana musu wasa cikin so da ƙauna NIHAL da baza ta wuce shekara huɗu ba tace '' DADY gobe ina son ka Kai ni gurin wasa nayi wasa'' '' shi kenan mama na zan kai ki , shi kuwa NAUFAL cewa yayi '' DADY Ni kuma so nake ka saya min kayan wasa mota da jirgi'' an gama kaima Allah ya kai mu duk zan siya muku'' kallan MANAL yayi wadda take bawa SUHAILA nono yace '' shi kenan abinda kuke so?'' Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin '' yesss DADY'' murmushi yayi kana yace '' to maza ku tashi kuje ku kwanata kuce yaya HASSAN yayi muku addu'ar kwanciya kunji '' to DADY seda safe Mommy seda safe suka faɗa suna barin ɗakin. Tashi SUHAIL yayi ya matsa kusa da MANAL da take ta yamutsa fuska a ranshi yace '' me hali baxe taɓa de nawa ba har yanzu MANAL bata son bawa yaro Nono'' afili kuwa cewa yayi '' maman yara dare fa yayi ya kamata muje ki kwanta nima kuma aji dani'' ya faɗa yana kashe mata ido ɗaya '' wai dan Allah kai ABBEN WTO YINS baka girma da wannan abun '' ta faɗa kamar zatayi kuka '' kin taɓa ganin wanda ya gaji da raya sunnar ma'aiki nifa so nake yau ɗin nan na baki ajiyar wani BEBYN'' yasa hannu ya ɗauki SUHAILA wadda ta jima da yin Bacci ɗaki ya kaita sannan ya dawo ya ɗauki MANAL da take ta turo baki be dire ta ko ina ba se kan gado yaje ya rufe musu ƙofar sannan ya dawo kan gadon ya hau ya janyo MANAL jikin sa yana shafar bayan,ta cikin tattausar Muryar yake gaya mata kalamai masu sanyaya zuciya daga haka suka lula duniyar ma'aurata bayan komai ya lafa MANAL ta riƙo hannu sa kana tace "alhamdullih Allah Nagode maka da ka bani mijin marainiya me share min hawaye na dama ance me HAƘURI shi ke dafa dutse yasha har da roman ,sa ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH ALHAMDULLILAH. INA ALFAHARI DA ZAMO WAR KA UBAN YAYA NA.
LEFIN DAƊI ƘARE WA.
Duka duka anan na kawo ƙarshen wannan littafin na RAMIN MUGUNTA ina fatan wannan yazama darasi ga ƴan baya kunga dai yanda ƙarshen Dady ya kasance sanadiyyar biyewa san zuciya da yayi da son Abin duniya harya kaisa ga aurawa ƴaƴan sa wa'inda besan ko suwaye ba bema san asalin su, ba wanda hakan yasa ya kamu da Cutar shanyewar ɓarin jiki NABILA kuma ta gamu da Cutar H.I.V, ZAINAB kuma yoyan fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya wannan kaɗai ya isa yasa mutum yasan cewa duniya ba mattabba bace ALLAH YA TSARE MU DA AIKATA IRIN WANNAN ZALUNCI YASA MUFU ƘARFIN ZUCIYAR MU, YASA DUNIYA TA ZAMO A HANNUN MU, BA'A ZUƘA TANMU BA
GODIYA TA MUSAMMAN A GAREKI KHADIJAH ABDULLAHI UMAR (OUM SHARIFAT) GARKUWA JARUMAI KUMA (BESTY NA🥰🥰) ALLAH UBANGIJI YA BIYA MIKI BUƘATUN KI, NA YAU DA KULLUM
DAGA
MARUBUCIYAR
1 - MATAR YARO
2 - NI DA YAYA OMAR
3 - IZINAH
4 - GANI GA WANE
5 - RAMIN MUGUNTA
6 - ƳAR SHAYE SHAYE
8 - MIJIN BERA
9 - KISHIYAR UWA CE SANADI
️ SUMAYYA ABDULLAHI ALHUSEEN (MAMAN HIBBA)
SHA RUBUTU..
nake cewa bissalama
ASSALAMU ALAIKUMA BAYIN ALLAH
SE MUN SAKE KASANCE WA DAKU A CIKIN WANI SABON LITTAFIN NAWA ALLAH YA ƘADDARA SADUWAR MU AMEN.