Showing 6001 words to 9000 words out of 43291 words
maye,
SUNA WANI LITTAFINA DANA KESON RUBUTAWA MAI SUNA
(ƳAR SHAYE SHAYE )
Yaune ake saran kwance tiya tar da aka yiwa MANAL wanda rabin jin yar tata ya ta'allaƙa akan Dr. JAMAL wanda JAMSY ta bashi amana da kuma gayamai irin halinda MANAL ke ciki sabida ita tayi tafiya ƙasar KAMBIRIC dan iyayen ta acan suke da zama shi ne suka bugo mata waya lallai tazo suna son ganin ta hakan yasa ta damƙa amanar MANAL a hannun sa masha Allah aiki yayi kyau sosai su kansu likitocin da suka mata aikin sunyi mamakin aikin basu taɓa tsammanin zeyi kyan haka ba. sosai MANAL ta saba da Dr. JAMAL dan mutum ne me sakin fuska ga kuma faran faran, da mutane ai kuwa MANAL tayi kayu jikin ta da kyan ta da hasken ta suka soma dawowa dik wannan kasusuwan yanzu sun koma. kullum idan MANAL tayi sallah bayan ta yiwa iya yanta addu'a se ta yiwa JAMSY da Dr. JAMAL yau watan ta uku cifff a asibitin Kuma yau ne za'a bata sallama se dai abinda yafi bawa Dr. JAMAL mamaki ya kuma ɗaure mai kai yanda MANAL ta shafe wata uku s asibitin amma babu wanda yazo yace shi ɗan uwan MANAL ne sosai yake mamaki yana so ya tambaye ta se dai baya son shiga hurimin da ba na sa ba dan haka yaja bakinsa ya zuge.
MASARAUTAR ZAKI
Yau ma kamar kullum yarima SUHAIL ne kwance akan taf keken gadon sa wanda ya sha zanin gado na al-farma. bacci yake sosai amma se juyi yake yi kamar wanda yake ganin wani abu cikin baccin nasa frigigit ya tashi yana salati se gumi yake kamar wanda yayiwa sarki ƙarya ƙafafunsa ya xuro ƙasa yasa wani tattausan ta kalmi mafarki da ya saba yi kullum yau ma shi yayi se dai be taɓa ganin fuskar ta ba kawai abinda ya sani shine tana yawan zuwar mai a mafarki tana kuka tana neman tema konsa kuma wai acikin wata rijiya me zurfi da duhu take ga macizai da kunamu suna ta saranta shi kuma yazo wuce wa ta gurin ya ganta cikin wannan halin da zarar yaje gurin domin ya temaka mata se rijiyar ta dinga matsawa ahaka ahaka har ta yi mai nisa “wace ce ke a ina kike wana irin temako kike so na yi miki” me yasa ba zaki bayyana min kanki ba?” yayi wa kansa tamabayar da bashi da me ba shi amsar ta.
tashi yayi jikin sa babu ƙwari kamar anyi mai duka toilet ya shiga yayi wanka gaban mudubi ya wuce wasu tsadaddun mayuka masu ƙamshi kamar tirare ya shafa a jikinsa wasu kaya masu taushi da santsi kamar Auduga kuma farare yasa sosai suka yi mai kyau jikinsa ya feshe da turare me ƙamshi da daɗin ji al-kyabba ya ya ɗora akai sosai ta ƙara mai kyau waje ya nufa cikin takun sa na ƙasai ta irin na sarakuna gaba ɗaya bodi gad ɗin sa da dogarawa da suke bakin ƙofar suka zube suna kwasar gaisuwa kai kawai ya gyaɗa musu. Bodi gahd ɗin suka take mai baya su kuma dogarawan suka zauna gadin sashin nasa dik inda ya gifta bayi da ƙwarori sai sun tsugunna sun kwashi gaisuwa kai kawai yake gyaɗa musu kun san masu mulki busu fiya son magana ba domin tana yi musu wuya. Kai tsaye FADA suka nufa. “An gaishe ka yarima ɗan sarki jikan sarki wanda yagaji sarauta gaba da baya taka lafiya yarima mejiran gado kaga ɗan Sarkin sarakuna kaga ɗan Sarkin daya san sarauta gaba SALAMUN baya SALAMUN ɗan sarki jikan sarki wanda suka gaji sarauta kaga masu abu da abun gado ba taka haye ba”.
Abin da dogarawan suke ta faɗa kenan har yarima ya shiga fada yayin da mutanan dake ciki suka fito suka basu guri wannan Umar nine daga sarki muddin yarima zezo fada dik wanda yake cikin fadar ya fito ya basu guri sun gana in yaso bayan ya tafi se su dawo yana shiga ya rungume Mahaifin nasa yana dariya kamar wani ƙaramin yaro bayan sun gaisa memartaba yake tambayar sa yau she ne ze gudanar da bikin buɗe asibitin sa da ya gina Sosa kai yayi yace, “ehh to ranaka ya daɗe ban tsaida rana ba amma zan kira JAMAL se mu tsaida rana” "to toto shike nan yarima Allah ya bada Sa'a nima in an tashi taron asanar da ni da wuri dan ina so in halarci taron kuma nima ina son na bada tawa gudummawar” “to memartaba” In sha Allahu muna godiya Allah ya ƙara girma da buɗi ya baka lafiya me ɗorewa gaba ɗayan su suka amsa da Amin.
ɗakin mahaifiyar sa ya shiga wato uwar gidan sarki bayan sun gaisa ya shiga sashin kilishi itama suka gaisa sannan ya shiga sashin gwaggo wato ƙaramar matar sarki acan yayi karin kumallo dan dama yafi sabawa da ita kome zeyi in dai yana neman shawara to ita yake gayawa in dai bata gidan bace. ko Sarki da suka fi shaƙuwa da shi fiya da kowa be fiya gaya mai wasu matsalolin nasa ba A cewarsa girma ya kamashi be kamata yaringa ɗaga mai hankali da nasa matsalolin ba ya maji da mulkin da yake kai, jefi jefi suna taɓa fira da gwaggo damma yarima be fiya son magana ba.
(Kunji fa masu karatu ya tsallake ɗakin mahaifiyar sa yazo yana ci aɗakin kishiyar ta shin me yakawo hakan??????)
miƙewa yayi yace. “Gwaggo se anjima” “to se ka dawo Allah ya tsare ” “amen gwaggo se na dawo har
ya kai bakin ƙofa yaji ankira suna shi . “YAYA SUHAIL,” ta faɗa lokacin da take ƙoƙarin sakkowa daga saman be ne tana zuwa ta ware hannunta alamar ya ɗauke ta ɗaukar ta yayi ya shiga jijjuya ta kamar wata ƴar tsana ita kuwa se dariya take. Sauke ta yayi ya lakace kumatun ta yace. “ ƴar lukutar gwaggo ya akayi ne na san wannan kiran da akamin Akwai magana” baki taturo tace. “ba kai bane jiya kace inka fita zaka sayomin dogayan riguna kuma baka siyamin ba” ta faɗa cikin muryar shagwaɓa “sorry MEENA mantawa nayi ungo ATM ɗina kisa Direba ya kaiki kuma kice sikiruti suraka ku kinji” tsalle tayi,
gamida cewa “yawwa YAYA na nagode amma fa se wani satin zani sabida akwai abinda zanyi” “wannan kuma ya rage naki ga dai A.T.M nan na baki” Gwaggo na zaune tana kallansu se yanxu tasa musu baki da cewa. “A'A tin da ba yau zata je ba karɓi A.T.M ɗinka kar ta wullar maka ka san ta da shirirta” “a'ah gwaggo kibar mata kawai idan ma ta ɓatar se na sake yin wani ko autr mu?")” “Eh yaya na” “to Shi kenan ni zan wuce” “to seka dawo Allah ya tsare” da “Amin” ya amsa
“kai tsaye sashin sa ya koma wayarsa ya ɗauka ya kunna wadda tin jiya ya kashe saƙwani nine suke ta shigowa cikin wayar na abokansa dama na ƴan matan da suke son sa shi kuma baya son su , saƙwan JAMAL kawai ya duba dariya yayi afili yace. “kai JAMAL se abarka ba dai tsokana ba” number sa ya kira . dai-dai lokacin da JAMAL yayi fakin a'kofar gidansu MANAL Wanda ya koma na su Dady ɗaukar wayar yayi yana dariya yace. “Se yanxu ka ga damar kira na wallahi SUHAIL idan kayi aure se dai mu dinga zuwa inda kake danna san mantawa zaka yi damu” kome yace mai Seya kwashe da dariya yace. “Ina xuwa zan kiraka naje wata unguwa ne oky sena kira ɗin” ya faɗa tara da sauke wayar daga kunnen sa
ya dawo da duban sa gurin MANAL wacca dik tabi ta fiegice ta gigice. Maganar sa ce ta dawo da ita daga tina nin da take . “kiyi haƙuri MANAL dik da ban sanki ba amma na fuskanci kina cikin damuwa da alama ke marainiya ce ki cigaba da haƙuri da kai wa Allah kukan ki haƙiƙa Allah maji roƙon bayinsa ne ba zaki taɓa dana sani ba muddin kika riƙe sallah da addu'a zaman wannan gidan yafi miki alkairi idan kika ce zaki bar gidan nan zaki tsinci kanki a yana yinda ba aso addu'a itace makamin mumini zaki ga ribar haƙuri ga wannan kuɗin ni ne na baki kisiyi kayan sawa dana kwalliya” girgiza mai kai tayi tace “A'ah kabar su Na gode da temakon da kukayimin Allah ya saka da alkairi” “Amin amma ki karɓi kuɗin nan” ganin ya dage yasa ta karɓa yasa ta amsa tara da ƙara yimai godiya fitowa yayi ya buɗe butt ɗin motar ya fito mata da sauran kayan ta da magun gunan ta sannan suka yi sallama ta jima a tsaye tana bin motar da kallo harta ƙulewa ganin ta .
Dam dam gaban ta yashiga bugun tara, tara lokacin data kalli makeken git ɗin gidan ƙwan ƙwasawa tayi me gadi ya buɗe mata tafiya take kamar wadda ƙwai ya fashewa aciki afarlo tayi arba dasu suna karyawa sabida safiya ce gaba ɗayan su suka xubo mata ido kamar zasu cinye ta musamman BABILA da taga babu abinda fuskar ta yi “ To ƴar iska kin gama yawon barikin naki kin dawo?” cewar Dady rintse ido, MANAL tayi sosai taji zafin maganar, “kayi haƙuri Dady wallahi ba yawo bariki naje ba ”
Cikin ƙaraji, DADY yace. “Karki kuma ce min Dady ni ban haifi mazinaciya ba kin ga ƴaƴa na nan ƴan albarka akusa dani kije can ki nemi mataccan ubanki wanda mugun abinsa yaja masa har ƴan fashi suka kasheshi yanzu yana inaaa? dukiyar da take sawa yana min wulaƙanci ya tafi ya barta ni ɗin da bayaso nine akan dukiyar nake yanda na gadama da ita da gani se ƴaƴana kema da suka barki don ki gaji dukiyar wahalace zata kashe ki abanzaaaaaa”..
ALLAH KAI MANA DA KYAU KA RABA MU DA SON ZUCIYA
MMN HIBBA CE
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
7-8
TUSHAN LABARIN.
ALHAJI Sa'ad mai dalah wato mahaifin MANAL da alhaji bukarr uwassu ɗaya ubansu ɗaya tun suna yara mahaifin su yara su ya barsu hakan yasa ɗawainiyar su ta dawo kan mahaifiyar su ita ce cin su ita ce shan su , haka suka taso cikin yana yin rayuwa yau daɗi gobe akasin haka ga rashin kuɗi ga karatun su uwa uba cida sha, koda ta samu dangin mahaifin su da maganar gona kinsu na gado suka ce ba zasu bayar ba ƙarshe ma se suka kulle mata baki ta hanyar bin malamai tin daga nan bata Kuma yin maganar gadon ƴaƴan ta haka suka ci gaba da faɗi tashi ita da yaran ta SA'AD tun yana ƙarami Allah yayi mai baiwa dik abin da ya taɓa to in sha Allahu se Abin yayi albarka da haka ya fara ƴan seda sede na kayan kanti cikin ikon Allah Allah yasa musu albarka da wannan kayan da yake siyar wa da su suke ci da su suke sha, suke biyan kuɗin makaranta. ABUBAKAR wato ALAJI BUKAR tun yana ƙarami yake da wani irin bauɗaɗɗan hali ga baƙar zuciya kamar kuturu. saɓanin ɗan uwansa SA'AD wato ALAJI SA'AD ME DALAH babu ruwanshi da kowa harkar kasuwanci sa da karatun sa kawai yake Sannu ahankali shagon sa ya bunƙasa ya zama babban ɗan kasuwa Wanda duniya tasan da zaman sa har ƙasashe yake fita domin sarin kayayyaki lokacin da suka isa aure mahaifiyarsu tace ya kamata suyi aure dama shi ALAJI SA'AD ME DALAH bame kula kulan mata bane mace ko ƴar uwassu ce iya kacin su da shi gaisuwa daga haka baya wani fira da mace saɓanin BUKAR da yake biye biyen mata shi yasa da aka ce su fito da matan Aure yace yanada wacca yake so me suna BILKISU BILKISU dai irin mutan nan ne wa inda ba kwaɓa ba harara gabin malamai da bokaye gaba ɗaya gidan su haka suke . shi kuwa SA'AD cewa yayi ake komai mace me hankali da nutsuwa ze aura. haka kuwa akayi mahaifiyar su ta nemo mai wata yarinya wacca suke maƙota dasu mai suna, ZARAH Marainiya ce ba uwa ba uba tana zaun ne agurin kakar ta ta gurin uwa haka akasha biki bayan bikin su da sati biyu Allah ya yiwa mahaifiyar su ALAJI SA'AD rasuwa sunyi kuka sosai musamman SA'AD.. A kwana a tashi ba wuya gurin Allah ALAJI SA'AD ME DALAH ya zama shahararren ɗan kasuwa Wanda sunan sa ya zaga duniya Mutum me mutumci da karamci ga temakon talakawa kullum gidan sa cike yake da mutane saboda kullum se yayi sadaka abinci da kuɗi da Kayan sawa hakan yasa dukiyar sa kullum daɗa bunƙasa take rumfar kasuwa uku ya sewa ƙaninsa da motoci nahawa guda uku da danƙareran gida na gani na bugawa a jarida dik Kwana biyu yake aika mai da kayan abinci da kaji da kayan marmari sannan ya tura mai kuɗi ta account ɗinsa sannan idan lokacin aikin hajji yazo tare suke tafiya da mata yan su . Amma duk da haka ALAJI BUKAR baya gani kullum cikin yi mai ƙorafi yake kuɗin da yake ba shi basa isar sa hakan be dame sa ba sema ƙara masa daya ke yi haka rayuwa taci gaba da juyawa har Allah ya bawa BILKISU ciki wato matar ALAJI BUKAR ta haifi ƴar ta mace ALAJI SA'AD ya nemi ɗan uwan nasa da yasa sunan mahaifiyar su amma yace baze sa ba koda ya koma gida ya gayawa BILKISU uban ashar ta ƙunduma tace. "wllh baza'a sawa ƴar ta AMINA ba ƙarshe dai a kasa sunan mahaifiyar ta wato ZAINAB. ranar suna Alaji Sa'ad ne yayi komai raguna biyar aka yanka banda shanu da raƙuma kyautar mota ya bawa BILKISU tara da kuɗi shi kuwa uban gayyar ba,a magana. BILKISU se hura hanci take tana homa ta haihu hada yiwa ZARAH habaici bata haihuwa hakan bedamu ZARAH ba Kuma bata taɓa gayawa mijin ta ba tasan haihuwa nufine na Allah idan Allah yayi zata haihu zata haihu. Se da ZARAH ta shekara goma sannan ta samu ciki lokacin ZAINAB ƴar gidan ALAJI BUKAR na da shekara huɗu aduniya lokacin haihuwa yayi ta haifi ƴar ta mace kyakkyawa fara sool mai kama da mahaifinta ranar suna yarinya taci suna AMINA amma ana kiranta da MANAL
MANAL yarinya ce mai hankali da nutsuwa kuɗin mahaifin ta be rufe mata idoba babu ruwan ta da duniya kamar dai iyayen ta tin MANAL na ƙarama take fuskantar ƙalubale daga wajan ƙanin mahaifin da matarsa in dai taje gidan da ɓacin rai zata dawo gida tun abin baya damunta har ya soma damun ta ko da ta gayawa iyayen ta basu bata goyan baya ba se cewa su kai tayi haƙuri wataƙila dik sanda zata je ransu aɓace yake MANAL da ZAINAB makaranta ɗaya Alaji Sa'ad ya saka su dik abinda ze yiwa MANAL to se yayi wa ZAINAB da suka kammala secondary school Alaji Sa'ad yace su zaɓi ƙasar da suke so su ƙarasa karatun su MANAL tace ita India take so ZAINAB ma tace nan take so da maganar taje kunnan Alaji bukar se cewa yayi ƴar sa ba zata je wata ƙasa karatu ba haka kurum ta lalace se dai shi ya kai ƴar sa amma