Showing 21001 words to 24000 words out of 43291 words

Chapter 8 - RAMIN MUGUNTA Complete by Maman Hibba .txt

22 Nov 2024

4046

ba a kuma jefa ki cikin wani tashin hankalin ba daga ƙarahe dai ina miki fatan alkairi kuma insha Allahu daga yau na san kin dena wahala komai yazo ƙarshe bi ixinillahi”. daga haka SUNUSI ya tashi yayi musu se da safe hannu JAMAL ya zura a ajjihu ya ɗebo kuɗi da be san adadin su ba ya miƙa mai godiya yayi mai ya kuma yimusu seda safe.
“muma tafiya zamu yi na kaiki gidan ki kafin angwanki ya dawo ”dariya MANAL tayi dan JAMAL yabata dariya.
gida ne me kyau sosai wanda ya gaji da kyau ba babba bane sosai se dai daga gani kasan an kashe kuɗi ba kaɗan ba, hon yayi me gadi ya buɗe musu JAMAL ya cinna hancin motar ciki,
cikin gidan suka shiga dik da bawani tarkace bane acikin farlon amma yayi kyau matuƙa sosai ya tafi da MANAL ai ko ta ware ido tana kallon ko ina. " to MANAL wannan shi ne gidan ki a ciki zaki zauna har se SUHAIL ya dawo zan ringa xuwa ina duba ki fatan dai baza ki damu ba se yasa hannu a ajjihunsa ya zaro waya babba acikin kwalin ta ya miƙa mata gashi idab kin samu nutsuwa ki duba kiga tayi miki idan ba tayi ba se'a canza miki” karɓa tayi tara da yimai godiya sannan ya zaga da ita gidan ya nuna mata ko ina sannan sukayi sallama ya tafi ita kuma ta dawo ciki ta kulle ƙofa.
ɗakin da ya nuna mata a matsayin nata nan ta shiga kai tsaye wanka tayo wanda rabon da tayi irin shi har ta manta se da ta wanke lungu da saƙo na jikin ta har gashin kanta se data wanke bayan ta fito gaban mudubi ta zauna ta shafa mayukan data gani masu tsada ga ƙamashi sannan ta fesa ture cover ta buɗe taga kaya himili kuma dukka sababbi ne ɓan garan atamfofi da leshi da ban ɓan garan ƙana nun kaya daban wata rigar bacci me santsi da laushi ta saka tayi matuƙar yi mata kyau kamar dan ita akayi ta. alwala tayo ta gabatar da sallar magarib da isha'i. sannan ta haye luntsumeman gadon me laushi kamar burodi lumshe ido tayi tana jin wani sabon yanayi har ta manata raban data hau katifa wayar da JAMAL ,ya bata ta janyo ta fito da ita daga kwalin sosai wayan ya burge ta komai an sakawa wayar hatta da sim an saka mata kunnawa tayi kamar jira ake ta buɗe massage ya shigo wadda taga anyi sevin ɗin number da SUHAIL shiga cikin massege ɗin tayi ta buɗe ga abinda akace. "slm MANAL ya kike ya gida fatan kina ciki ƙoahin lfy? daga YARIMA SUHAIL.”
bata san sanda murmushi ya suɓuce mata ba se ta tsinci kanta da mayar mai da amsa kamar haka. "lafiya ƙalau fatan kai ma kana cikin ƙoshin lafiya” ta tura mai nan ta tsinnci kan ta da tina nin sa , lallai ta yarda komai lokaci ne bata taɓa tina nin zata kuma yin rayuwar jin daɗi ba bare ta kuma yin dariya da haka bacci me daɗi yayi awan gaba da ita....




MMN HIBBA✍️


RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)




WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)

07073193332


Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.


littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba


GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.


NA GODE.


SADAUKARWA
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA


ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)


AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.




19/20


Kiraye kirayen sallar asubah da ake yi ne ya farkar da MANAL, daga ni'imtaccan baccin data jima batayi irin shi ba banɗaki ta shiga ta dauro alawala ta gabatar da salla sannan tayi azkar kamar yanda ta saba bayan ta gama ne ta naɗe sallayar ta mai da ta ma'ajin ta ta kuma koma wa bacci se ƙarfe takwas ta tashi ta gyara gidan ko ina yayi fesss se ƙamshi da yake tashi kicin ta koma shima ta gyarashi sannan ta ɗora shayi ƙwai ta soya bayan ta kammala ɗakin ta ta koma wanka tayo ta sauya rigar baccin da take jikin ta zuwa doguwar riga wato A baya green color tayi mata kyau sosai, dik da ba wani kwalliya tayi ba man leɓe kawai ta shafa ta kalmi felet ta saka sannan ta fito farlo ta soma karya wa cikin nutsuwa take cin abincin cikin ranta tana gode wa Allah yanzu ne ta tabbatar da karin maganar gaskiya ne wadda bahaushe yake cewa mai haƙuri ya kan dafa dutse yasha har ma da roman sa sam bata taɓa tina nin zata fita daga ƙangin wahalar data shiga a gidan su se gashi Allah ya yi ikon sa a kanta, a fili tace. “alhamdulillah Allah na gode ma da ka haɗa ni da wa innan bayin naka ko ya su DADY suke? ko suna tinawa da ni? nama san ba zasu damu da ni ba tin da babu wanda ya rako ni gidan miji na ” ƙofar da ake ƙwan ƙwasawa ne ya katse ta daga tuna nin data lula miƙewa tayi taje ta buɗe JAMAL ne ta bashi hanya ya wuce . “Ina kwana Dr. ya kaje gida jiya?” ta faɗa tara da tsugunawa har kasa, murmushi, JAMAL yayi kana yace. “lafiya ƙalau amaryar mu ya baƙunta da Kaɗai ci ?”. murmushi kwai tayi gami da cewa. “Ina godiya a gare ka dakai da abokin ka Allah ya biya ku ya kai haske cikin rayuwar ku, daku da duk ahalinku Allah ya saka muku da gidan aljannar firdausi.” “Amin Amin ya Allah muma muna matuƙar godiya da wannan addu'a sannan daga yau bana so ki kuma yimin godiya Allah ne ya ƙaddara haɗuwar mu, kuma shine silar komai dan haka shi zamu gode wa ” “ haka ne Dr.” ”Zo ki ci-gaba da karyawar ki ko nine na tare miki guri?” A kunyace ta tashi ta koma kan dainin table ɗin tana shan shayin kamar me koyan sha, “SUHAIL ya kira ki kuwa?.” “A'ah be kira ba ya dai yi min massage” " “amma ya faɗa min yau da safe ya kira ki biki ɗaga ba” "da yake na bar wayar a ɗaki shi yasa daya kira banji ba” "okay idan kin gama abin da kike se ki kira shi ni zan wuce ko kina da buƙatar wani abun?" ''A'ah bana bukatar komai'' sallama yayi mata ya tafi .
yana fita kiran SUHAIL ya shigo tsayawa yayi a bakin motar sannan ya ɗaga wayar gami da karawa a kunnan sa, "wai dan Allah JAMAL me kake jira tin ɗazu baka tafi ba kabar ƴar mutane ba kaje ka duba lafiyar ta kaga a wana hali ta kwana haba meye hakan" SUHAIL ya faɗa cikin ɓacin rai, shi kuwa JAMAL be katse shi ba har se da ya dasa aya kana yace. "to ranka ya daɗe ko kuma nace baba na kagama faɗan naka ko kuma da saura?" JAMAL ya faɗi hakan cikin son ya ƙular da SUHAIL, ai kuwa ya kuma tunxura ta inda yake fita bata nan yake shiga ba, da JAMAL ya gaji faɗan nasa yace. "to tin da dik abinda nake yi maka ban birge kaba seka dawo ka kula da ita ya faɗa tarada gimtse kiran. ko kaɗan JAMAL beji haushin SUHAIL ba dan idan da sabo ya saba dariya ce ta kamashi, daya tuna abinda SUHAIL yace. "wai ya bar ƴar mutane ita kaɗai se kace wani abu ze kama ta ya lura SUHAIL ya kamu da son MANAL ba tun yau ba. “allah yasa ita ma tana son shi” JAMAL yaɗa lokacin da yayi fakin a harabar gidansu.


****


shi kuwa SUHAIL yana can abin duniya ya ishe shi shima ya san abinda yayiwa JAMAL be kyauta ba ko ba komai JAMAL abokin sa ne na haƙiƙa me ƙaunar shi tsakani da Allah amma ya iya da xuciyar sa ita ce ta axal xale shi dan yaji yanda MANAL ta kwana gashi ya kira wayan ta amma bata ɗauka ba faɗawa kan luntsume man gadon yayi wanda ya sha zanin gado na alfarma silin ɗin ɗakin ya ƙurawa ido yana tina nin mafita amma ya gaza samun mafita koɗaya dole dai ya koma wajan JAMAL ɗin iska mezafi ya furxar ya miƙa hannin sa kan allon gadon ya janyo wayarsa kira biyar yayi wa JAMAL be ɗaga ba shi kuwa JAMAL yana kallan kiran amma yaƙi ɗagawa se ana bakwai sannan ya ɗaga


babu Wanda yayi magana a cikinsu sun ɗauki kusan minti tala tin sannan SUHAIL yace. "sorry JAMAL na san ban kyauta ba amma kamin afuwa kai ma kasan ba halina bane" "ni babu abunda kamin SUHAIL kaima kasan ba zanyi fushi da kai ba kawai dai na baka lokaci ne idan ka huce kamin magana" JAMAL ya faɗa yana ƴar dariya daga nan fira ta ɓalle wanda firar tasu akan MANAL sukeyin ta cikin firar tasu ne SUHAIL ya cewa JAMAL. "wallahi ina tsoran ran da zan tunkari ME MARTABA da zan can MANAL wannan shi ne karon farko dana aika ta abu ba tara da sanin sa ba" "gaskiya ne SUHAIL ba kai bama ni kai na ina jin tsoro amma babu yanda muka iya dole mu gaya musu tunda baze yu mu ɓoye wannan maganar ba dole wataran asirin mu xe tonu in ban da abinka ai ME MARTABA yasan mahaifin ta ni A ganina baze ɗauki zafi damu ba " ajiyar xuciya SUHAIL yayi yace. "ba wannan xaka duba ba JAMAL auran da nayi batara da sanin su ba shine matsalar kasan halin me martaba idan ya ɗauki zafi" ƴar dariya JAMAL yayi kana yace. wallahi idan naga hukun cin da'ayi mana me tsauri ne zame wa zanyi in barka ko nace ban san anyi ba gaba ɗayan su suka sa dariya ƙarshe dai sukai sallama kan inya dawo zasu tunkari SARKI da maganar...


"Kwanciyar hankali da hutu yasa MANAL ta fara komawa MANAL ɗin asali kyawunta ya kuma fitowa fatar nan kamar ta jatirai dan laushi da santsi tayi ƙiba abinta ɓul ɓul kamar ba itava dirin ta da surar ta da baiwar da Allah yayi mata ta cikar ƙirji sun kuma fitowa kai hatta da gashin kan ta daya ƙuƙƙulle saboda wahala ya ware dik na mijin daya kalle ta se ya kuma kallanta kai bama na miji ba mace ma, seta kuma wai wayawa ta dube ta kullum se JAMAL yaxo ya duba MANAL tarada tambayar ta ko akwai abinda take so ga kuma wayar ta wacca take ɗebe mata kewa akai-akai SUHAIL yake kiran ta dik da bawani fira suke yi ba daga gaisuwa se ya kake,


Daga banɗaki ta fito jikin ta ɗaure da tawul ga kuma wani ahannunta tana goge jikin ta , da alama wanka tayo abinda bata taɓayi ba yau shi tayi wato kwalliya haka kurum ta tsinci kanta da tsarawa fuskar ta kwalliya ita kanta seda ta kuma duban kanta saboda kyan da tayi cover ta buɗe tana duba kalar kayan da xata sa ta jima tana xaro kayan dik wanda ta ɗakko se taga be mata ba a haka har hannun ta ya kai kan wani farin leshi me ratsin golden ajiki doguwar riga ce bubu sosai ɗin kin ya mata kyau sauran kayan data janyo ta mayar sannan ta saka kai tubarkallah masha allah kyau iya kyau gashi ɗin kin yayi mata ciff kamar dan ita akayi ɗaurin dan kwali tayi gamida feshe jikinta da turaruka masu ƙamshi wayar ta ɗauka ta koma farlo tana gemm lokaci lokaci takan ɗagowa ta kalli agogo kamar wacca take jiran wani.




Filin saukar jirage na malam aminu kano JAMAL ne tarada dogarawan masarautar zaki suna jiran fitowar SUHAIL sun jima sannan suka hango shi yana sakkowa daga sitef ɗin jirgin cike da takun ƙasaita kai daga gani sa kasan babu ƙarya ya haɗa iri da jinin sarauta yana ƙarasowa suka rungume juna shi da JAMAL sannan suka shiga mota tun a hanya SUHAIL yake tambayar JAMAL ya faɗawa MANAL yau xe dawo?" "a'ah ban gaya mata ba saboda ina so in shammace ta naga ya zata yi idan ta ganka" dariya suka sa gami da tafawa SUHAIL yace. "wallahi JAMAL baka da dama wato kaga yanda zata yi tome zata yi idan ta ganni bacin ba yau ta saba gani na ba," "dik da bayau ta taɓa ganin ka ba amma wannan shine karan farko da zaku kalli juna amtsayin miji da mataaaa" dai dai lokacin suka fito daga cikin mota bayi da ƙwarori se kwasar gaisuwa suke gami da yi mai sannu daxuwa gefe guda kuma algaita na tashi inda ake ta yimai kirari tara da yi mai barka da dawowa, kai tsaye ɗakin sa suka nufa wanka SUHAIL yayo ya sauya kayan jikin sa sannan suka tafi fada kamar yanda fadawan suka saba tashi sukayi suka basu guri JAMAL ne ya fara gaishe da me martaba sannan SUHAIL se sunne kai suke daga gani kasan basu da gaskiya, " lafiyar ku kuka zo kuka min gurfane anan naga tun ɗazu muka gama magana daku ko dai wata tsiyar kuka tafka ban sani ba ?" Cewar SARKI.
JAMAL ne ya ƙiftawa SUHAIL ido, dan kar ya ce komai, "kaga shaƙiyyan yara ina magana kunyi shiru kuna magana da ido to kutashi ku bani guri tunda yau shaƙiyan cin naku ne ya motsa" sarki ya faɗa tara da rarumo maficin da yake gefan sa . da gudu suka miƙe suna dariya gami da cewa. "allah ya huci zuciyar, sarkin sarakuna kabari in tayi tsami zamu gaya ma " " kai ku tafi cann ni kun ishe ni da iya shege dikkan su suka sa dariya,
Suna fita SUHAIL ya dubi JAMAL gami da cewa "me yasa ka hana na gaya mai?" "saboda ba yanxu ne lokacin wannan maganar ba kabari seda daddare semu gaya mai ko kuma xuwa gobe da safe yanxu dai muje in kai ka kaganta danna san ka matsu ka ganta" JAMAL ya faɗa tarada kashe mai ido ɗaya, duka SUHAIL ya kai mai yayi saurin gocewa, mota suka shiga suka kama hanaya da isar su magadi ya buɗe musu. MANAL dake kwance kan kujera two sita tana gem awayn ta sam bata ji tsayuwar motarsu ba sallamar su kurum taji da sauri, ta miƙe gamida cewa Dr. kai... bata ƙarasa abinda take son faɗa ba SUHAIL ya shigo ido suka haɗa tayi saurin sunkuyar da kanta jikin ta ya hau rawa kasa tsayuwa tayi da gudu tayi cikin ɗakin ta da ta saka keey tarada jingina bayanta a jikin ƙofar har yanxu ƙamshin tiraransa yana manne a hancin ta ga ƙirjin ta da yake dukan uku uku dama haka yake da kyau kamar shi yayi kansa wannan ai yama fita kyau kuma bama ajinta bane yafi ƙarfin ta gashi ɗan gidan sarauta" se da kallo ɗayan data yi mai taji ta kamu da son shi wannan shi ake kira da kallo ɗaya takk,




Can farlo kuwa JAMAL se ha tintsire da dariya se yi yake shi kuwa SUHAIL yanda kasa an dasa gunki yama kasa cewa komai seda JAMAL yayi me isarsa yace. "gaskiya SUHAIL ka firgita ƴar mutane gashi kasa ta shige ɗaki harda garƙama mukulli seya tsuguna ya ɗauki wayar MANAL data yarda aƙasa ya miƙawa SUHAIL karɓa yayi ya doshi ƙofar ɗakin nata cikin muryarsa me sanyi da daɗin sauraro yace. "MANAAL buɗe ƙofar ko nine baki son gani?" Ahankali ta buɗe ƙofar har yanxu kanta aƙasa yake miƙa mata wayar yayi yace. "wato guduna kikeoyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login