Showing 3001 words to 6000 words out of 43291 words
wasu muna nan mafarkai, tayi nisa cikin baccin da bawani daɗinsa take ji ba cikin taji ankwara mata ruwa me sanyi kamar daga cijin fireza aka ciro shi .
tini jikin ta ya hau tsuma ta koma gefe ta kure kamar tsumma., wata wulaƙan tacciyar dariya ZAINAB tayi tana kallon yanda haƙoran MANAL suke gwaruwa kamar mazari “shigiya me suffar aljanu se kizo DADY na kiran ki yau kam se kin ƙwammace ƴan fashin da suka kashe iya yanki kema sun haɗa dake mayya” daga haka ZAINAB ta juya tana sakin wani shu'umin murmushi kayan da suka jiƙe ta canza dik da suma wa'inda tasa ba wankakku bane raban da tasa kaya masu kyau wankakku har ta matan shekarun gashin kanta kuwa ba'a magana yayi dauɗa ya cukur kuɗe shima se tashin wari da hamami da yake yi ko ɗan kunne babu a kunnan ta ta koma tamkar namiji se idanu da suka yo waje sabida baƙar azaba da kuma yinwa,.
Ras rasssss gaban ta ya yanke ya faɗi yanda taga fuskokinsu ya tabbatar mata da akwai abinda yake faruwa, can nesa da su ta samu guri ta ta kure
“Keeeeeeeeee MANAL ina sarƙar gold ɗin da kika ɗauka?” cikin firgici gamida razana bakin ta har harɗewa yake wajan faɗin “sassa sarƙa kuma DADY wallahi ban ɗauka ba bamma san a'ina aka ajiye ta ba,” “Kam bala'i, to idan bake kika ɗauka ba uban waye ze ɗauka ko kina nufin su NABILA ne suka ɗauka to wallahi fito min da sarƙa ta kona kashe ki” cewar MAMY
“wallahi wallahi MAMY ba ni na ɗauka ba.”
ZAINAB ce ta ce . “ amma naga kin shiga ɗakin MAMY ɗazu kuma naga kin ɓoye wani abu a zanin ki dana tambaye ki me kika ɗauka kika ce babu komai kona miki ƙarya?”girgiza kai MANAL tayi dan in tace ba haka bane ba zasu yarda ba “DADY aje a duba ɗakin ta”cewar NABILA, meze faru ana xuwa ɗakin aka ga sarƙar aƙar ƙashin tsummo karanta kuka MANAL take iya ƙarfin ta tana gaya musu ba ita ta ɗauka ba DADY ne ya dunƙule hannun sa ya sakar mata abaki tini haƙoran ta biyu suka yo waje be tsaya anan ba falo ya jata yace ta kwanta aƙasa ta kuma ɗaga rigar ta wata mirtikekiyar dorina ya ɗakko wacca da ita ake dukan dokuna, dokunan ma na gidan sarauta wa inda suka giga. babu imani babu tausayi DADY ya shiga sauke mata wannan dorinar agadan bayan ta , tin MANAL na ƙara har ta dena ne man ɗauki NABILA da ZAINAB se ihuuu suke suna cewa ƙara mata DADY karka ƙyale ta har se ta mutu se da yaga ta de na motsi sannan ya bar ta.
haka suka tsallake ta suka wuce ko a jikinsu hasali ma daɗi suke ji Dady kuwa cewa yake “Allah yasa ta mutu kowa ma ya huta dan so yake yayi wadaƙa da dukiyar ta, MANAL kuwa bata far faɗo ba kuma babu alamun zata farka ɗin inda sukabar ta nan suka dawo suka same ta kamar gawa kanta ya kumbura kamar ze fashe haka ma idanun ta suka koma kamar lemon zaƙi dan kumburi, bayan sun gama karyawa NABILA taje inda MANAL ke kwance tasa ƙafa ta harbe ta amma kamar ta taɓa dutse shewa ta saki gamida ƙwallawa su Dady da mamy kira suzo su ga MANAL ta mutu burin su ya cika , zasu ci karan su babu babbakaaaaa suma ihuuuuu su kasa suna murna Allah ya rabasu da alaƙakai, dariya ZAINAB tayi gamida cewa "shi kenan Dady dukiya ta zama tamu dik wanda ya tambaya me yasa Meta se muce karuwan ci ta shiga har ta kwaso cutar , H.I.V wato ƙanjamau ita ce ta kashe ta kaga babu wanda ze zarge mu ” “haka za'ayi zee kin kawo shawara me kyau, nan suka bar ta kowa ya shige ɗakin sa acewar su se sunyi wanka sun gama abinda suke sannan zasu gayawa mutane mutuwar MANAL,
MANAL kuwa wacca ta mance a'ina take aduniya ko alahira ta dai fi zoton alahira take, cikin azaba da radaɗi ta fara motsawa dishi dishi ta soma gani hakan yasa ta maida idon ta ta rufe , bayan minti tala tin ta sake yin ƙurin sake buɗewa dik hazo hazo take ganin komai ga bakin ta da yake shatatar da jini sakamakon haƙoran ta da suka fita cikin ranta tace “shi kenan na zama me wawulo sun raba ni da haƙora na, Hannun ta da ƙafar ta wa inda suka zama kamar tirmi dan kumburi suma ta kasa motsasu se yanxu ne ta sake tabbatar da rashin iyaye ba ƙaramin musiba bane ashe haka rayuwa take? Ashe dama mutane kowa da kalar zuciyar sa dama in kuka fito ciki ɗaya da mutum halinku ba iri ɗaya bane kowa da nasa ? Allah sarki ABBANA ashe yanda ka. ɗauki ɗan uwanka shi ba haka ya ɗauke ka ba ashe ba sonka yake ba afili yake nuna ma yana sonka a Zuciyarsa kuɗin ka yake so Allah Sarki iyaye na kun tafi kun bar ni alokacin da nake matuƙar buƙatar ku Allah sarki ABBA na kullum kana gaya min cewa ko bayan ranka ƙanin ka shine wanda ze riƙe ni ze bani kulawa kamar kai, se gashi shine yake neman makasa ta baya so ya buɗe ido yaga ina numfashi sabida abin duniya wanda kaima daka tara su kuma kake alkairi dasu ka tafi ka barsu ina ma mutuwa tazo ta ɗauke ni, na huta da wannan uƙubar hawayen azaba ne suka ringa xubo mata kanta ya kuma yi mata nauyi, tamkar dutse
Wata ƙara taji an saki wan da ta san NABILA ce nan ta shiga ƙwalwa su mamy kira “Dady mamy kuzo ku ga wannan baƙar mayyar ashe bata mutu ba”
sabida sauri dady har neman sulewa yake nan suka tsaya akan ta . wani ƙululun baƙin ciki ne ya kama DADY wannan waca iriyar yarinya ce me baƙin naci dik wannan wahalar da ya bata be sa ta mutu ba tsabar takai ci daya cika shi cewa yayi “ kar wanda ya kuma sauraran ta kuma kar a kuma bata abinci har se yinawa da ƙishiriwa sun kashe ta yana gama faɗar haka ya haye saman be ne yana ta masifa ɗakin sa ya shiga yana ta faman huci se zagaye ɗakin yake ya riga da ya gama tsara komai game da yanda ze yi da dukiyar MANAL idan ta mutu se gashi ta far faɗo tsaki ya kuma yi a fili ya ce“ dole ne ki mutu bazan ci gaba da zama a haka ba tin da mahaifin ki baya doran duniya kuma ke kaɗai ya bari aka mallaka miki dukiyar sa dole ke ma ki mutu ko ta halin ƙaƙa se kin bar dunyar nan ni ma na fanta ma da dukiyar ɗan uwa na! na yi facaka da ita zaki mutu zaki mutu zaki mutu MANAL” ya faɗa yana jefar da hular kansa.
KEEEEE DUNIYA INA ZAKI DAMU NE ANYA WA INNAN MUTANAN SUNA JIN TSORAN ALLAH YA ALLAH KASA MU FI ƘARFIN ZUCIYAR MU ALLAHUMMA AMEN
IDAN HAR KE MASOYIYA TA TA TSAKANI DA ALLAH KUMA KINA JIN DAƊIN LITTAFIN NAN TO KI TAYA NI TURAWA CIKIN WASU GRP MMN HIBBA TANA GODIYA DA TARIN MASOYA DA ADDU'AR DA KUKE MATA
SHAWARA D'AYA ZAN BAWA MASU KARATUN LITTAFIN RAMIN MUGUNTA SISTER BAN CE KARKI KARANTA LITTAFIN NAN BA AMMA IDAN KIN SAN KINA DA RAUNIN ZUCIYA TO KARKI KARANTA DOMIN BA'A FARA KOMAI BA YANZU MANAL ZATA FARA SHAN WUYA WANNAN SHARAR FAGE NE.
ƙalamin mmn hibba ne✍️
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER✍
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi Shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
5-6
Kamar yanda DADY ya faɗa hakan ce ta kasance yau kwanan MANAL huɗu ba tara da tasa komai acikin ta ba se dai ta sha ruwa nan da nan ta kuma tsotsewa ta koma kamar ƴar tsana kana iya ganin ƙasusuwan jikin ta , ƙafar ta ta kumbura har ta soma xubar da ruwa amma babu wanda yaji tausayin ta sema abinda ya kuma yin gaba yau ta kama litinin NABILA da ƙawayan ta sun cika gidan se shaye shaye suke abin babu kyan gani maza da mata, ne sunyi wata iriyar shiga wacca da ita gawamma babu kowacce da saurayin ta suna holewar su, gefe guda hakimar tasu uwar gayyar ce jikin wani saurayin ta babu kunya babu tsoran Allah gaba ɗaya gidan ya kauraye da warin wuy wuy da sigari se guntsa suke suna fesarwa. MANAL, ce ta fito tana bin bango dan ko tsayuwar kirki bata iyayi sabida yinwa gaba ɗayan su suka bushe da dariya, kamar mahaukata sabbin kamu MANAL kuwa ko ajikin ta ita bata damu ba dik da tasan da ita suke. ɗaya daga cikin samarin ne yace.
“BEBY NABEE ina kuka samo wannan ƙasusuwan jifa ƙashin ta ina iya irgasu zama da irin wannan matsala ne se su goga muku talauci”
hhhhhhhhhhhhh, suka kuma sa dariya irin ta gogaggun ƴan duniya tsaki NABILA tayi gami da cewa “kai dai bari Beby wallahi daga ƙauye aka kawo mana ita take mana shara da wanke wanke baku ga yana yin ta kalar na ƴan ƙauye ne ba ?” suka kuma bushewa da wata wula ƙantacciyar dariya, “keeeeee, MANAL baki ga mutane bane zaki wuce baki gaida su ba ?” a san yaye tace “kiyi haƙuri aunty NABILA” se ta juya gurin ƙawayan nata har ƙasa ta tsuguna tace “sannun ku” babu wanda ya amsa a cikin su se ma wani ƙas-ƙantaccan kallo da suka bita da shi.
“da halla ni jeki dafa mana shayi ki kawo mana kuma wallahi kika daɗe sena miki bille afuskar ki” ta faɗa cikin ɗaga murya,
kicin ɗin ta shiga dafe da cikin ta da yake ƙugin yinwa tana addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki da gaggawa. wani ragowar abinci ta gani an ajiye da alama bana yau ba ne dan har ya fara yami ALLAHU akubar, haka MANAL tayi zaman dir shan tana ci kwa nan nan abinci da ko dabba baza'a bawa ba ita kuwa murna, take yi ta samu abin da zata sawa cikin ta.
ta manta da wani dafa shayi se da taji NABILA na ƙwala mata kira bashiri ta miƙe jiki na ɓari, kamar mazari gass ɗin ta kunna ta haɗa komai da ake buƙata na shayi kan kaceme har ta gama ta juye musu a' filas ɗin shayi ta ɗauki ƙana nun kofuna na shan shayi ta fita kanta aƙasa dan bata son haɗa ido da wa innan ƙartin. gaban NABILA ta kai filet ɗin ta ajiye ta juya zata tafi “ uban waye ze zuba mana shayin da kike ƙoƙarin tafiya ko kinji na ce ki tafi ne?” girgiza kai ta yi gami da dawo wa ta zuba wa kowannen su sannan ta bisu ɗaya bayan ɗaya tana miƙa musu “NABEE dama haka kuke dafa shayi agidan ku?” NANSY ta faɗa gami da furzo, shayin daga bakin ta . nan suma sauran suka kai cup ɗin shayin bakin su ai kuwa suma suka furxo da shi suna ya mutsa fuska, haushi ne ya kama NABILA ta ɗauki cup ɗin shayin ta kai bakin ta ai kwa ita ma ta furzo shi ashe ba siga MANAL tasa acikin shayin ba gishiri ta saka a madadin siga haushi ne , ya kama NABILA yanda MANAL ta kunya ta ta agaban ƙawayanta MANAL kuwa ta rakuɓe jikin ta se kyarma, yake cikin ɓacin rai, NABILA ta cika cup ɗin da yake gaban ta da shayi bata ɓata lokaci ba ta sheƙawa MANAL afuska wata gigitacciyar kara, MANAL ta saki sabida azaba da raɗaɗi NABILA kuwa ko ajikin ta wani cup ɗin ta kuma cika wa ta kuma sheƙa mata, azaba tai azaba Uƙu ba tai Uƙu ba gaba ɗaya fuskar MANAL babu kyan gani domin kuwa ƙunar ta shige ta fatar fuskar ta ta saɓule tin daga wuyan ta da sauran sassan jikin ta
hakan bai ishi NABILA ba seda ta haɗa mata da duka tana zagin ta dama iyayan ta da suka rigamu gidan gaskiya.
se da aboka nan sha shancin nata suka riƙe ta wai ta bar ta haka Ahakan ma taji jiki . “ NABEE wannan ƙunar da kika yi mata be dace ba idan aka bar ta ahaka fuskar ta ze iya samun matsala kamata yayi mu kaita asibiti tin da wuri” cewar JAMSY. wata uwar harara NABILA ta jefi JAMSY da ita kana tace. “wallahi babu inda zani se dai ta mutu idan ma ta mutu waya damu da ita. fuuuuu, ta wuce kamar zata tashi sama.
suma sauran suka fice daga gidan suka kama gaban su akabar JAMSY kaɗai ita kuwa tausayin MANAL ne ya cika ta dan haka ta ƙudiri aniyar ce to rayuwar ta ɗaukar MANAL tayi kamar gawa babu alamar rai atare da ita bayan mota ta saka ta sosai take gudu, tamkar zata tashi sama tin kanta isa asibitin ta yiwa Dr. ɗin waya abinka da ƴaƴan masu kuɗi babu wani bincike ko ace se tazo da ƴan sanda aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta jim kaɗan Dr ɗin ya fito yace.
"JAMSY ta same shi a office ɗin sa baya nin da Dr JAMAL yayi wa JAMSY ya ɗaga mata hankali, ya tabbatar da cewa. fuskar MANAL tayi dameji In kuwa ana so ta dawo dai-dai to fa se an kashe maƙudan kuɗi wanda aƙallah sun kai million goma da dubu ɗari bakwai da hamsin
sosai hankalin, JAMSY ya tashi ta san Ko ta gayawa su NABILA ba zasu biya kuɗin ba, dan haka tayi alƙawarin zata ɗauki nauyin aikin tinda tana da kuɗin da suka fi haka a Account ɗin ta nan ta cewa Dr. su fara aikin zata biya na dai ta cike komai da komai aka shiga da MANAL ɗakin tiya ta....
Can gidan kuwa babu wanda ya tambayi inda MANAL take har kokin gaban su kawai suke likafa taci gaba DADY ya mallakawa su ZAINAB da BABILA motoci kowacce uku tara da dan ƙara musu maƙudan kuɗaɗe a account ɗin su haka ita ma MAMY ya ɗauki gida sukutum guda ya bata wanda aƙalla ze kai million hamsin bayan haka ya biya musu kuɗin tafiya ƙasar India dama sauran ƙasashe wai suje su huta duniya sabuwa DADY se wadaƙa yake da dukiyar ƴar ɗan uwan sa ba tara da yasan abinda zeje ya dawo ba. su NABILA da ZAINAB sun samu yanda suke so mahaifinsu ya basu damar su zagi kowa su daki uban kowa kuma su zauna lpy hakan ya ƙara musu girman kai da jin cewa suma ƴaƴan masu kuɗi ne hakan yasa suka kuma dulmiya cikin ƴaƴan masu kuɗi abin dai ba kyan gani sune shaye shaye Kwan a hotel dik wani gidan fati in dai a kano yake to fa sun san shi samari ta ko ina se ɓullu musu suke suna kashe musu kuɗi kamar basa so musamman ma NABILA dan tafi ZAINAB mutane kai in kaga manya manyan masu kuɗin da suke zuwa gurin ta abin se ya baka mamaki hakan be taɓa damun iyayen su ba hasali ma daɗi suke ji ƴaƴan su sun zama man yan yara yau kwanan NABILA huɗu bata gidan abige ta shigo gidan tana tangaɗi gamida layi da surutai bar katai irin na ƴan