Showing 18001 words to 21000 words out of 43291 words
yayi. “komai yazo ƙarshe insha Allahu za'a yita ta ƙare ba dai maza take biba to zan aura mata wanda ya dace da ita kuma kyauta zan bayar da ita ko in ce sadaka” daga haka DADY ya shige ciki suma suka mara mai baya suka bar MANAL tsaye jikin ta dik ya mutu, yanxu ƙiyayyar da suke mata har ta kai a bayar da ita sadaka?.
kururuwar, da NABILA take yi ne ya dawo da ita daga duniyar tina nin data lula a ƙofar ɗakin ta, ta gansu NABILA na cikin ɗakin tana fir fito da kayan dasu SUHAIL suka kawo mata se da ta fito da komai hatta da kayan sawa seda NABILA tayi musu filla filla. “magana ta ƙare kuna gani har da kayan abinci hummm ƴar gata wato ruwan roba ma take sha gaskiya ne kin samu sake to wallahi ba zaki kuma amfani da su ba mu zamu ɗauka” gaba ɗaya NABILA ta kwashe kayan bata bar mata ko tsinke ba se kayan jikin ta ɗakin ta ta kai kayan na abinci kuma ta kai su kicin tofa rayuwar MANAL ta kuma koma ruwa tinda suka dawo bata samu zama aiki kawai take kanta gama wannan ance tayi wannan nan da nan ta koma gidan jiya. yau da daddare DADY yasa aka kira mai MANAL gyaran murya yayi yace. “to ƙaramar karuwa tin da kin nuna auare kike so zanyi miki aure zan sa a nemo min faƙiri matsiyaci matalauci wanda bashi da cin yau bare na gobe na aura masa keee, kije can ki ƙawata da iskancin ki zan sa me gadi ya nemo min koma waye dik tsufan sa koda sadaki ko babu haka zan bashi ke tin da baki da galibu” kuka ne ya ƙwace wa MANAL me tsuma zuciya yi take kamar ran ta ze fita dariya su NABILA suka sa gamida tafawa ZAINAB tace. “gaskiya DADY kayi abinda ya dace dama auaran take so magana ta ƙare seta tafi Allah ya raka taki gonaaaaaa.NABILA ta amshe da cewa “ni kam DADY wata alfarma nake so kamin” “faɗi dik abin da kike so ni kuma zan miki shi” “ dama ba wani abu bane face ina so ayi auran cikin satin nan bana so aja lokaci sannan kasa afara yi maka bin ciken wanda ya dace da ita” “an gama ƴar lele ai ko yau kika ce a ɗaura auran yau za'a ɗaura shi” dikkan su suka sa dariya ”kukan MANAL ya kuma tsanan ta yi take kamar zata shiɗe, tsawa DADY, ya daka mata yace. “tashi ki bani guri ƴar iska kawai kukan ubanki kikeyi” Murmushi mugunta NABILA ta yi kana tace “ƙyale ta DADY wai ita muna fuka."
Washegari
da safe Dady ya samu me gadi ya faɗa mai abin da yake so kan cewa ya nemo mai mutumin da yasan matalauci ne bashi da cinyau bare na gobe. “to Alhaji insha Allahu Zan nemo maka Amma ranka ya daɗe idan an nemo mutumin me zaka yi mai Idan wani aikin ne nima zan iya” "ba aiki bane ba Malam rabe ina so in yiwa MANAL aure ne shi yasa kaji nace ka nemo min matsiya ci faƙiri irin ta sabida ta da cewa da shi ” shiru mai gadi yayi can kuma yace. “kuma fa ALAJI kayi gaskiya dan wallahi auran yafi da cewa da ita ina gaya ma yarinyar nan bata jin magana kaga yanda take kawo ƙartai cikin gidan nan da nayi mata magana seta nemi zagi na shi yasa naja baki na na zuge kuma insha Allahu zan kawo maka irin mutumin da kake so koma wanda ya fishi talauci” “ ai kuwa Malam rabe da nayi maka kayuta me tsoka” baki Rabe ya washe
“An gama ranka ya daɗe " ƙofa ya buɗe mai bayan fitar alaji BUKAR me gadi ya koma ɗakin sa gamida turo ƙofa wayar sa ya ɗakko wacca tasha ɗaurin ƙirji da kyauro number JAMAL daya bashi yace idan yaga wata matsala data shafi MANAL yayi gaggawar sanar dashi, “hello ranka ya daɗe malam Rabe ne me gadi ne na gidan su MANAL” daga ɗaya ɓan garan JAMAL yace.“ okay ya kake ya MANAL ɗin tana lafiya dai ko?” cikin rawar baki RABE me gadi yace. “eh tana lafiya se dai akwai abin da yake faruwa wato yanxun nan ALAJI BUKAR ya same ni da wata magana wai na samo mai mutumin da bashi da cin yau bare na gobe nan ya kwashe dik yanda suka yi da ALHAJI BUKAR ya faɗa mai ya ƙara da cewa “ ya bani nan da kwana biyu in nemo mai mutumin shi yasa nace bara na gaya maka .” “to ranka ya daɗe an gama se naji ka, daga haka ya kashe wayar. Afili yace. “ ƙarshan ku yazo mugaye azzalumai marasa imani.”
MASARAUTAR ZAKI
SUHAIL ne, zaune gaban memartaba gyaran murya yayi yace. “SUHAIL jibi in Allah ya kai mu kan tura Ka London gurin MUHAMMAD zaku tattauna kan yanda za'ayi game da harkar kasuwanci daga nan kuma zaka wuce Amerika ka amso min sako gurin aminina LAWAN” cikin girmamawa SAUHAIL yace “ an gama RANKA YADAƊE na barka lafiya .” ɗakin sa ya koma wayar sa ya ɗauka ya kira JAMAL kan yazo suje gidans u MANAL saboda jibi ze bar garin “okay Shi kenan seka zo ɗin” mintina ƙalilan JAMAL ya ƙaraso.
“yawa ka ƙara so ai ba seka zauna ba muje kawai” kallansa JAMAL yayi ya kawar da kansa kana yace. “so kake mu janyo mata wata masifar to masu gidan sun dawo dan haka ka saurara min da wannan soki burutsun naka" cikin tashin hankali SAUHAIL ya ce “ kana nufin s ta koma wannan wahalalliyar rayuwar?” ƙwarai ma kuwa amma na samu hanyar da zamu te maka mata nan JAMAL ya kwashe yanda su kayi da RABE me gadi ya gaya mai sosai hankalin SUHAIL ya tashi ,. ganin haka yasa JAMAL cewa. “ka kwantar da hankalin ka a wannan lokacin ne ya kamata ka temaka mata” “ ta waca hanya zan temaka mata ?” “ta hanyar auran ta ” zaro ido SUHAIL yayi yace. "auran ta fa kace kai ma kasan hakan beme yuwa bane memartaba baxe taɓa amince ba” gyara zama JAMAL yayi yaci gaba dacewa. “in dai da gaske kana son ka t temaka mata to ka aure se dai idan ba tausayin ta kake ji ba” shiru SUHAIL yayi tarada furxar da zaxxafar iska kana yace. “shi kenan JAMAL ya kake ganin za'ayi?” " tun da ka amince ka bar min komai a hannu na san yanda zanyi”
kamar yanda ALAJI BUKAR ya bawa malam RABE me gadi umarni ya kawo mai mutumin da bashi da cinyau bare na gobe hakance ta kasance wani tsoho ne tukuf har ya ranƙwafa saboda tsufa ƙafafunsa dik gidan memery wato faso takalmin ƙafarsa kuwa silifa ne lamba gomasha ɗaya yadin jikin sa kuwa irin ya din nan ne da ake cewa ishirinka maraya shima dik ya fefe har ya fara fashewa cikin gidan suka shiga inda suka iske dika mutanan gidan har MANAL bayan sun gaisa RABE yayi wa alaji bukar baya nin mutumin da yace a samo mai. washe baki DADY yayi gamida cewa. “ƙwarai kuwa yayi yanda nake so ”MOMY ma cewa tayi “gaskiya kam yayi ga dikkan alamu talauci yayi mai kanta kuma ya dace da ita se dai bamu san kenan shi ba?” “suna na SUNUSI kuma ni almajiri ne ina da mata uku ƴaƴa na sha takwass sannan banida sana'a ruwa nake siyar wato garuwa” “masha Allah haka ake so”cewar ZAINAB. “gaskiya kam dady yayi se taje ta riga tuƙa tuwo a lamaba talatin ina ga shima ba kullum ake cin tuwon ba” inji NABILA kenan. “kin faɗi gaskiya yarinya se muyi sati bamu ɗora tukunya ba se dai na basu ashirin ashirin su se garin kwaki su jiƙa su sha” inji SUNUSI kenan, “shi kenan malam SUNUSI dama wannan yarinyar zan aura maka kuma kyauta na baka da idan har ka amince to gobe ka turo magaba tanka a ɗaura kuma na gaya maka bana son komai daga gare ka ko sadaki bance ka kawo ba” “haba ALAJI wa za'a yiwa wannan kyautar yace baya so ai se dai in bashi da hankali wannan kykkyawar yarinya san kowa ƙin wanda ya rasa in sha allahu gobe zan turo” SUNUSI ya faɗa yana washe bakin sa me ɗan karan wari haƙoran nan kamar jar dawa dan dauɗa “to shi kenan idan kazo da ƴan uwan naka ka samu malam RABE shi na wakilta a matsayin wanda ze aurar da ita️”
Jama'a muji tsoron ubanguiji mu ku sani akwai mutuwa akwai kwanciyar kabari akwai hisabi
WANNAN AL-ƘALAMIN MMN HIBBA NE
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba.
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
17/18
Washe gari misalin sha ɗaya na safe SUNUSI da ƴan uwan sa suka bayyana a gidan su MANAL sun sha yadin su mamar dik ya ya muste kamar an ƙwato su daga bakin kura fuskar nan komai ba su shafa ba takalmin nan dai na jiya shi ne be canza wani ba haka aka ɗaura auran ko sadaki babu, MANAL kuwa tana ɗaki taji anɗaura mata aure da sa'an kakan ta taci kukan ta, ta ƙoshi zazzaɓi me zafi ya rufe ta daddare SUNUSI ya turo wasu dattawa sune ƴan ɗaukar amarya a cikin A daidaita suka zo jakar tsummo karanta ta ɗauka ta fito har lokacin kuka take yi , A farlo ta same su babu nasiha babu komai DADY yace. “gata nan ku tafi da ita ni dai na gama nawa na fita haƙƙin ta tin da na aurar da ita ga wanda ya fi dace wa da ita" se a sannan kukan MANAL ya ƙaru , taje gaban DADY tana roƙon sa da ya yafe mata dik laifin da tayi mai sannan taje gurin MOMY da su NABILA amma babu wanda ya tanka mata illah wani mugun kallo da suke bin ta da shi . tana kuka tana komai dattawan nan suka sata a ɗan sahun da suka zo da shi suka ɗau hanya sun jima suna tafiya sannan taga an ɗauke hanyar cikin gari an shiga cikin wani sur ƙuƙin daji doguwar tafiya kafin suka isa wani gidan jar ƙasa dik da a duhu ne hakan be hana MANAL ta ƙare mai kallo ba irin ginin nan ne na da wanda akeyi da jar ƙasa shi ma ya mutu kana iya hango na cikin gidan ɗaku nan ma ana hango su A taƙaice dai ba shi da maraba da wanda yake waje shiga cikin gidan suka yi caɓal MANAL taji ta tsoma ƙafar ta cikin ruwa wasu zafafan hawaye ne suka sirnano daga idan ta zuwa kuncin ta cikin ranta tace “ inna ilaihi wa inna ilaihi raju'un na shiga uku ni MANAL nan kuma ƙaddara ta jefo ni Allah ya sa nan ɗin ya zame min Alheri ya sa ƙarshen wahala ta ce tazo ya Allah ka ba ni ikon cinye wannan jarabawar ” ɗakin da dattawan suka shiga nan ta nufa taxo shiga ta ƙume ji kake gummm, ashe irin ƙofar nan ce ta ƙauye da seka tsuguna zaka shiga sosai ta bugu sukuwa dattawan se sannu suke rattabo mata kai kawai ta ɗaga musu.
Ƙarfe goma na dare SUNUSI ya shigo da abokanan sa se washe wargajejan bakin sa yake hakan yasa dattawan miƙewa suka yi mata se da safe. nanfa MANAL ta kuma takure wa sabon kuka ya ɓalle mata, kamar famfo yau ne ta ƙara tabbatar da maraice babu daɗi idan iyayan ta suna raye ko rasa mijin aure tayi baza su aura mata wannan tsohon ba sallamar da aka yi ne ta dawo da ita daga tinanin da take kasa amsa sallamar tayi illah miƙewa tsaye da tayi bakin ta na rawa tace. "Dr. JAMAL kai ne? ya akayi kazo nan? waya gaya ma a ɗaura min aure? ya aka yi kasan ina nan?” dariya JAMAL yayi kana yace. “ai nine na ɗaura miki auran.”
“kai ne ka ɗaura min aure ? ta yaya hakan zata faru bacin dazu aka daura min aure da Wannnan bawan Allah kuma kace kai ne ka daura min Aure plsss JAMAL me ke faruwa da ni ne ka gaya min gaskiya ina cikin Rudani ko kai ma cutar da ni zaka yi dan Allah karka min wani abu ka bar ni da tashin hankalin da nake ciki na yi ƙanƙanta da Wannan tashin hankalin.” ta karasa fada tara da zubewa ƙasa tana kuka me tsuma zuciya.
tausayin ta ya kama JAMAL tabbas ba tai ƙarya ba ta yi ƙanƙanta da kalar rayuwar da take ciki ba ko wace mace ce zata iya fuskantar haka ba tare da ta sama wa kanta mafita ba.
“ ki yi shiru MANAL ba ni da nufin cutar dake ina me miki albishir da cewa daga yau kin de na hawayen baƙin ciki se dai na farin ciki ki tsaya ki saurari abin da zan gaya miki”.
“ a hankali ta ɗago tana kallan sa kallo me cike da tambayoyi.
ME KARATU BARA KOMA BAYA DON JIN YA AKAI HAKAN TA FARU INYASO SEMU CIGABA
JAMAL yaci gaba dacewa. "malam RABE me gadi ya sanar dani cewa ƙanin mahaifin ki yana shirin aurar dake ga mutumin da yaso kuma wanda bashi da sana'a hakan yasa na samu SUHAIL da maganr bayan mun gama tattauna wa nace mai shiya kamata ya aure ki dan ya ceto ki daga wannan masifar da ake neman jefa ki cikin ta na samu malam RABE na gaya mai halin da ake ciki na kawo mai SUNUSI a matsayin shine wanda ze aure ki in da allah ya temake mu ALAJI BUKAR ya danƙawa malam RABE me gadi ragamar ɗauri auren ki hakan yasa muka yi amfani da wannan damar muka ɗaura auran wanda A zahiri muka cewa alaji BUKAR da SUNUSI aka ɗaura a baɗini kuma da YARIMA SUHAIL aka ɗaura miki aure kinji yanda abin ya kasance ”. “ƙwarai ma kuwa yarinya gaskiya ya gaya miki hatta da wa in nan tsofaffin da kika gani sun taho dake suma haya muka ɗakko su kuma wannan gidan ba gida na bane hayar shi muka yi ko da su alhaji bukarr zasu biyo mu shi yasa kika ga an kawo ki gidan nan wannan shine gaskiyar lamari kuma ba da ni aka ɗaura miki aure wannan kayan da kika gani a jiki na suma aro shi mukayi ba wai kaya na ba ne” cewar SUNUSI, cikin rawar murya MANAL tace.
“yanxu kuna nufin ni matar yarima ce? kuma ɗan sark? ko dai tsokana ta kuke yi don allah ku gaya min gaskiya karku yaudare ni idan da shi aka ɗaura min aure wannan ba damuwa bane danni bana buƙatar wasu kayan more rayuwa na san zan ƙare rayuwa ta acikin baƙin ciki mutuwa ta nake jira danna fison mutuwa akan komai”.
“haba MANAL se kace ba musulma ba biki yarda da ƙaddara bane kiyi gaggawar yin istigifari”cewar JAMAL.
" astagafirillah astagafirillah astagafirillah astagafirillah MANAL ta shiga nanatawa “SUNUSI yace "ƙwarai MANAL kuma ki gode wa allah kina da xuciyar imani da yarda da ƙaddara wallahi da wasune da tuni sun fantsama duniya Allah yana gani ba kowa ba ne ze iya jure wannan uƙubar da kika sha, dan haka ki gode wa Allah ki kuma gode wa, wa innan bayin Allah da suka tsaya kai da fata wajan ganin