Showing 30001 words to 33000 words out of 43291 words
ta ya zagaya ya ruƙo kugun ta ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yace ''ni gaskiya ina buƙatar mata ta a kusa dani plsss ki ajiye wannan girkin kiji dani'' ya faɗa yana turo hannunsa cikin rigar ta. Juyowa tayi suka fuskanci juna tace ''wallahi kafiya ta kura fa baka barina na huta ko kaɗan tunda garin Allah ya waye kake abu ɗaya kaƙi bari in ɗora mana abinci rana ko sokake ka maida ni, fanko ne''? ta ƙarasa maganar tana jan hancinsa taɓe baki yayi kamar ƙaramin yaro yace. '' koma me zaki ce se dai kice Ni na san ba daga ni bane daga ke ne ke ɗin ta musamman ce'' hannu ya kai ya kashe gass ɗin data kunna batai aune ba taji yayi sama da ita wutsil-wutsil ta soma yi ''da Allah ka sauke ni babu inda zani mutum se kace doki kai baka gajiya da abu ɗaya'' be ajiye ta ko ina ba se kan gado hararar wasa ta sakar mai shi kuwa dariya ya mai da mata. a haka ya soma sarrafa ta har samu gamsuwa
kwanciya ta yi ajikin sa tana ta zuba mai shagwaɓa shi kuma yana aikin rarrashi har suka yi wanka MANAL bata dena kuka ba daya gaji se cewa yayi ''wallahi in biki yi min shiru ba sena ƙara'' wata uwar harara ta banka masa tace ''aikuwa da ni da kai har abada kona gudu wajan Gwaggo'' ta faɗa tana murgu ɗa ɗan ƙaramin bakin ta, hannu ya kawo xye buge bakin ta goce tana turo baki shi ''wallahi yau se nayi maganin bakin nan mara kunya sena hukunta shi ya faɗa tarada miƙewa yana binta da gudu, MANAL tayi farlo aikuwa ya biyo ta suka ringa zagaye ɗakin ganin da gaske so yake ya kamata seta fita waje tayi sashin KILISHI wato mahaifiyar sa, shima kuwa ya bita duk inda sukai se an bisu da kallo kowa yana sha'awar su, wasu ma dariya sukeyi wai yau SUHAIL ne yake gudu yana bin matar sa ?.kamar anjefo ta ta faɗa dakin bayan ANNAH ta ɓuya se haki take '' a'ah MANAL Lafiya kike wannan uban gudu haka ke dawa ?" Kafin MANAL tayi magana SUHAIL ya shigo ɗakin shima yana haki, ''wayyoooooo Allah ANNAH kiyi mai magana don Allah karya duke ni,'' se ta ƙanƙame ANNAH. yarinya gwara ma ki fito dan babu abinda ze hanani dukan ki ba dai junin ki rashin kunya ba to daga yau baza ki kuma murguɗa wa kowa wannan bakin ba'' ya faɗa yana ƙoƙarin zagayawa bayan ANNAH ''kai SUHAIL kafita idona na rufe kai Yanzu ko kunya bakaji ba ka biyo ta kuka keto gidannan kuna gudu to naga ka taɓa ta ɗin'' ''haba ANNAH ya zaki goyi da bayan ta bacin itace bata da gaskiya'' ya faɗa kamar xeyi kuka ita kuwa MANAL se xuro kai take tana masa gwalo. tsaki yayi sannan ya fita yana gun guni bayan fitarsa ANNAH ta dubi MANAL kana tace '' Idan kika kuma tsokano shi bazan hana shi dukan ki, ba dan SUHAIL baya kunyar dukan ki ze yi ba, shi kamar ƙaramin yaro haka yake'' baki MANAL ta turo gaba tace ''ni wallahi babu abinda nayi mai kawai dai muguntar sa, ce ta motsa'' na dai gaya miki dan haka fito min daga baya duk kinbi kin yamutsa min kaya. MANAL bata bi takan ANNAH ba ta ɗauki furar data gani kusa da ita tasha nono se ƙamshi take nan MANAL ta gyra zama ta fara antawa Cikin ta tana yi tana lumshe ido, ''hummmmmm wannan yarinya da fi'ili kike naga ca kika yi baki shan fura yanzu kuma me ya haɗa ki,da ita har kike zalama haka?'' "uhum uhum ''nima ban san ya aka yi ba naji ina son sha kuma in ban sha ba ba zan iya sukuni ba'' taɓe baki ANNAH tayi tace ''kya ji da shi uwar tsugudidi''
To, rayuwar MANAL acikin gidan mijin ta rayuwa ce me tsaf ta gaskiya da ruƙon amana duk abinda take so se an mata tayi kyau tayi ɓul-ɓul da ita tayi ƙiba tayi fari fatar nan kamar ta jarirai SUHAIL na iya ƙoƙarin sa Wajan faranta mata yanda ya kamata. Cikin dare MANAL zazzaɓi me zafi ya rufe ta wanda dama tun jiya yake nuƙur ƙasar ta daurewa kawai take yi can Kuma ta ringa kyalaya amai hankalin SUAHAIL ya tashi kan kace me har ta gala ɓaita bata ma san wanda yake kanta gashi duk ta ɓata ɗakin da amai SUAHAIL ya
rasa ya zeyi fita yayi harya doshi ɗkin Gwaggo seya tuna yau itace da girki ɗakin ANNAH ya shiga ya tarar tana bacci tashin ta yayi ya gaya mata abinda yake faruwa tara suka taho suka tarar da MANAL kwance kamar gawa bata ko motsi ''innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL MANAL me ya sameki dan Allah ki tashi karki tafi kibar ni wallahi bazan iya rayuwa da wata mace ba idan ba ke ba'' cewar SUHAIL yana share ƙwalla ruwa ANNAH ta ɗakko a firixa ta juye mata shi ajikin ta, ajiyar zuciya, tayi wata robar ruwan ta ɗakko ta miƙawa SUHAIL tace "ungo wannan idan kaga tayi irin haka ka zuba mata ni zan koma na ɗakko ta kalmi se mutafi asibiti'' karɓar robar ruwan yayi ita kuma ta fita ƙura mata ido yayi baya ko ɗif tawa gani yake idan ya ɗauke idonsa ze iya rasa MANAL ɗin sa, Kafin ANNAH ta dawo ai harya cicciɓo MANAL a bakin ƙofa suka ci karo kawai se ta juya suka shiga mota da kanshi yake tuƙin ga masu gadinsa na biye dasu awata motar Lokaci-lokaci ya kan waigo yaga yana yin jikinta sosai yake gudu kafin su isa ya kira JAMAL awaya kuma akayi Sa'a yau aikin dare JAMAL yake yi suna zuwa aka kaita Emergency aka fara bata agajin gaggawa dirip a kasa mata domin ta jigata sosai gashi tayi amai yafi a'irga wajan rabin awa JAMAL da sauran Dr. cin suke kanta bayan gwaje-gwaje da akayi aka tabbatar da MANAL tana ɗauke da juna biyu na tsahon sati huɗu wanda hakan yayi dai-dai cikar satin bikin su huɗu a ranar da aka kaita tasamu Cikin.
Bayan sun gama komai kuma har ta dawo hayya cinta suka fito inda suka tarar da ANNAH da SUAHAIL a inda aka ta nada cikin hanzari SUAHAIL ya nufo inda JAMAL yake itama ANNAH ta biyo bayan shi dan san sanin awana hali MANAL take ciki '' JAMAL me ya ke damun ta? ina fatan dai yanzu ta dawo hayya cinta?'' cewar SUHAIL yana kallon JAMAL dan jin mexe ce ''ka kwantar da hankali ka, SUAHAIL babu abinda yasa meta kuma taji sauƙi sosai yanzu ANNAH ki shiga ki zauna agurin ta kai, kuma ka biyo ni Office zamu yi magana ɗakin ANNAH ta shiga su, kuma suka tafi Office ''zauna mana SUHAIL muyi magana seka ce wanda ake min tsini'' ''kaga JAMAL ba zama bane ya kawo ni ka gaya min abinda yake damun mata ta'' dariya JAMAL yayi, kana yace ''idan kuma naƙi faɗa maka fa me zaka yi kaga SUHAIL in zaka zauna muyi magana ka zauna dan wallahi bazan gaya maka ba kana tsaye se kace wanda ya haɗiyi muciya'' tsaki SUHAIL yayi sannan ya zauna shi kuwa JAMAL zama ya gyra kana yace ''albishirin ka, ''goro'' ya bashi amsa ata kai ce. JAMAL ya kuma cewa ''fari ko jah'' wayyo Allah SUHAIL ji yayi kamar ya rufe JAMAL da duka amma ya daure dan yasan halin JAMAL idan zasu shekara to seya amsa masa tambayoyi Sannan ze gaya mai abinda ke damun MANAL dan haka yace ''fari kal-kal'' murmushi JAMAL ya kuma yi kana yace ''MANAL ɗinka tana da juna biyu'' kamar wani dolo haka SUAHAIL ya ringa bin Jamal da kallo bakin sa har rawa yake wajan faɗin ''da da dan Allah JAMAL da gaske kake MANAL na da ciki'' ''ƙwarai ma kuwa SUHAIL matar ka nada juna biyu na tsahon sati huɗu ina taya ka, murna aboki na Allah yara bata da shi lafiya''
SUHAIL sauka yayi Daga kan kujerar da yake ya kai goshin sa , ƙasa yanawa Allah godiya sannan ya tashi ko sallama be yiwa JAMAL ba ya fita ɗakin da aka kwantar da MANAL ya shiga lokacin tana zaune tana shan furar da ANNAH tasa aka kawo mata sabida bata son komai idab ba fura ba. tunda ya shigo ya kafe ta da ido baya ko ƙif tawa ƙarasawa yayi ya zauna akan gadon yana kallon furar data kesha kanta ya shafa kana, yace ''beby na ina godiya agare ki, da irin wannan kyautar da ki ka min naji daɗin haɗuwa dake seya shafa fuskar ta zuwa wuyanta. Ture hannun sa tayi, ta nuna namai inda ANNAH take tana sallar asubah. ANNAH na idarwa take tambayar SUHAIL me yake damun. MANAL sosa kai, yayi yace ''dama ba Wani abu bane yake damun ta ba illah ƙaruwar da muka samu MANAL na da ciki'' ya faɗa tara da saurin barin ɗakin saboda kunya dama kuma beyi sallar asubah ba. itama MANAL ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige don kunya furar data ke, sha ta ajiye ta koma ta kwanta tana mai jin kunyar ANNAH ita kuwa ANNAH ko a jikinta , se godiya da tayiwa Allah dama tana so taga ƴaƴan SUAHAIL se gashi Allah ya amsa mata.
Gari na waye.wa asibitin ya cika da muta ne hatta dasu LUBABATU da ZAINABA sunxo kowa se nan nan yake da MANAL, se azahar aka sallame su suka dawo gida nan fa aka ɗora daga inda aka tsaya kowa burin sa ya faran tawa MANAL sarki da kansa yazo yayi mata ya jiki kai MANAL taga gata iya gata ko wasshhh, tace se an tambaye ta inane yake mata ciwo ko Akwai abinda ta ke so,
Se dare SUHAIL ya shigo ya same ta Ita da MEENA suna fira gaisawa sukayi da MEENA ta tashi ta basu wuri zama yayi ya kamo hannunta yana kallon idon ta Sannan yace ''ya jikin naki ina fata dai kinci abinci?'' ''eh naci sosai ma kaima kaci ko''? ta faɗa tarada shigewa jikinsa, ''hannu yasa ya ɗaga
ƴar yo loluwar rigar baccin data saka yana shafa cikin ta yace '' in dai mata ta da beby na sunci bani da matsala domin sune farin ciki na'' hannu tasa ta saƙalo wuyansa tace '' indai baka ci abinci ba to muma baxa mu iya ciba kai ɗin katanga ne agare mu taya kake tunanin in baka da wal-wala muma zamuyi" ira Iran wa'inna kalaman suka ringa wa junan su ɗaukar ta yayi suka shige beed room....
Nima dai nace Bara inyi ta kaina domin wannan kalaman soyayya da suke, zayya nowa juna haka kamar ba gobe
MMN HIBBA CE.
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER✍️
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN MMN HIBBA
07073193332
SADAUKARWA
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA
ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)
AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.
25 -26
Tin da aka ɗauki amare a motocin da angwaye suka turo domin kai su gidan su, na aure ana cikin tafiya duka motocin da mijin NABILA ya turo suka lalace A hanya gashi kuma babu mutane sosai agurin dan haka yace Bara ya turo wasu motocin a mai da su gida idan yaso ' daga baya sa zo suga gidan hakan kuwa akayi aka kawo wasu motocin aka juya dasu shi kuma ya ɗauki matar sa , awata mota suka tafi seda aka wuce wani ƙungurmin daji sannan akazo gidan shi kaɗai ne agurin babu gida ko ɗaya agurin tunda NABILA take bata taɓa ganin gida me kyan wannan ba kai amma Allah ya kashe ya ba ni irin wannan gida haka se kace wanda aka gina da zinare malam ko ina se walainiya yake ta faɗi hakan cikin ranta, koda suka shiga gidan se taga ashe ɓangare biyu ne ko wanne dana sa kalar fentin wanda yafi tsaruwa suka shiga faɗar dukiyar da aka kashe wa gidan ɓata baki ne kai kace aƙasar waje kake idan ba fitowa kayi ba ba zaka taɓa cewa a Najeriya kake ba, sallah sukayi Sannan ya baje mata nama kala-kala na kaji da na rago da na shanu har da na Raƙumi bayan sun gama yaja ta suka shige ɗaki tun ƙarfe sha biyu na dare ALAJI yake abu ɗaya har seda aka kira sallar asuba sannan ya saurarawa NABILA ta jigata ba kaɗan ba tunda take yawan barikin ta bata taɓa haɗuwa da namiji irin Alhaji daze kwana yana gurzar ta abin mamaki shine tunda tazo gidan sau ɗaya taga yayi Sallah idan tace beyi Sallah ba se yace yayi awaje kafin ya shigo, a haka har aka shafe wata biyu idan aka kai amarya ɗakin miji ƙiba take yi tayi kyau amma banda NABILA Gashi dai zata ci me kyau tasha me kyau ta kwanta ame kyau kai hatta da aikin gidan ba tayi saboda Akwai ƴan aiki agidan amma hakan be sa NABILA ta samu kwanciyar hankali ba saboda jaraba irin ta Alhaji kullum cikin abu ɗaya yake baya taɓa barin ta ta huta wani zubin ma yana gama saduwa da ita idan yaje ya dawo ze kuma komawa ruwa tun abun baya damun ta har ya soma damun ta ga ramar da tayi dik ta koɗe se wasu iyayan ƙasusuwa da sukayi mata sarƙa awuya watan ta biyu agidan tasa mu ciki nan fa abun ya kuma rin caɓe mata gashi ya amshe mata duk wayoyin ta bare ta kirawo wani nata ta gaya mai halinda take ciki, ita ba abokin fira gare ta ba, su, kansu masu aikin gidan basa wani yin doguwar fira da ita, saboda Alhaji yaja musu kunne gashi Allah ya haɗa ta da ciki me laulayi na masifa amma duk da haka ALAJI baya raga mata ka ida ne idan ya fara se asuba kuma yana gama wa ze fice daga gidan bashi ze dawo ba se magrib ta ƙwanja me ta bushe ta. tayi baƙi ta Lalace kamar ƙwaran gwal se uban ciki daya yo mata gaba kamar ba NABILA ba
yau dai NABILA ta shirya tsaf domin zagaye ko ina na gidan sannu a hankali take tafiya har takai ɗaya ɓan garan shiga tayi cikin farlon shi ma dai kamar wancan yake har ma ya fishi tsaruwa zama tayi a ɗaya daga cikin farlon tana hutawa ta kai kusan awa biyu a ɗakin sannan ta tashi zata tafi magan ganun mutane ta juyo ƙasa ƙasa Dama da akwai mutane Acikin gidan nan to amma ai alaji yace min babu kowa aciki mu kaɗai ne ta faɗi hakan cikin ranta tsintar kanta tayi da son shiga ɗakin dan taga suwaye.
Innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn, abinda kunnan ta ya jiye mata ne yasa tayi suman tsaye dama ALAJI ɗan mafiya ne?'' tayiwa kanta tambayar da bata dame bata amsar ta. ''yawwa Gali zuwa yanzu na san cikin matar ka, ya kai wata biyar kuma kasan alƙawarin da aka yiwa dodo idan kayi aure matar ka, ta samu ciki zaka bashi jinin matar da kuma abinda ke cikin ta dan haka lokaci yayi da zaka yi hakan gobe ka kawo mana ita dan DODO yana ƙishiruwar jinin su," buɗar bakin ALAJI se cewa yayi "angama ya. shugaba na ai, dama na gaya maka zan kawo wa DODO Kalar jinin daya ke so shi yasa da naga wannan yarinyar na kuma sa akayi min bincike akan iyayan ta se faɗuwa tazo dai-dai da zama naji labarin suna da san kuɗi se na siye su da kuɗi banza ye wawaye ko bin ciken asalina basu yi ba suka bani auran kai in taƙai ce maka ko sunan basu sani ba, dama ni,ba sonta nake ba na auro tane kawai danna bawa DODO jinin ta Ni kuma na samu dukiya na zarce kowa'' ALAJI ya faɗa cikin ƙwarin guywa da karsashi. Sulalewa NABILA tayi a ƙasa ta ɗora hannu aka zata fasa ihu ta tuna idan tai zasu ji ta dan haka ta toshe bakin ta tana rizgar kuka jin motsin za'a fito yasa tayi saurin barin sashin ta koma nata sashin hankali tashe shi kenan ta mutu ta lalace yanzu bata da wani maceci se Allah gashi babu wanda ya taɓa zuwa inda take, agefe guda kuma ALAJI duk sati seya aika da kayan abinci gidan su NABILA da kuɗaɗe masu tarin yawa Sannan yace NABILA tana gaishe su, in suka samu lokaci zasu zo shi da ita basu samu zama bane saboda suna