Showing 39001 words to 42000 words out of 43291 words

Chapter 14 - RAMIN MUGUNTA Complete by Maman Hibba .txt

22 Nov 2024

4053

cikin ƙaraji hankalin mutanen gurin ya dawo kansu anyi anyi SUHAIL ya sake shi amma yaƙi dukan sa kawai yake sarki da kansa yazo amma ina SUHAIL yayi nisa baya jin kira jibagar sa, kawai yake kamar Allah ya aiko sa duk wanda yaxo da nufin ceton sa SUHAIL seya haɗa da shi nan akayi carko carko ganin abin bana ƙarau bane yasa MANAL kutsawa cikin mutanan da turtsetsan cikin ta tana zuwa ta riƙe SUHAIL cikin kuka tace "ya isa haka dan Allah na roƙeka kabar shi, haka in dai danni kake yi to naya fe masa, cakkk, SUHAIL ya tsaya da dukannasa ta kama hannunsa suka bar gurin tini gayan ya arce, ɓangaran su ta nufa riƙe da hannun SUHAIL wanda yake ta huci kamar kububuwa zaunar dashi tayi akan kujera ta buɗe firij ta ɗakko ruwa me sanyi ta xuba a Cup ta kafa mai abaki shanye wa yayi ta kuma ƙara mai sannan tasa mu guri ta zauna tarada kamo hannunsa tana jamai yatsun sa wanda take ja tasaki ta kama ɗayan shima ta jima tana mai har seda taga jijiyoyin sa sun saki sannan ta soma magana cikin sanyin murya tace '' Allah ya huci zuciyar yarima na, fatan dai ze manta da dik abinda ya faru'' ta faɗa tana shafa sajan sa, ɗauke kansa yayi alamar har yanzu be huce ba, '' haba nawan ni kaɗai har abada, Kisss ta manna mai agoshi To ance tsakanin mata da miji sai Allah cikin hikima da Bara MANAL ta shawo kan mijin nata ta hanyar gaya mai kalamai masu kwantar da hankali, daga haka ta miƙa masa kanta dan tasan shine abu, na biyu da yake ƙara kawantar wa, da SUHAIL hankali adik sanda ranshi ya ɓaci washe gari aká ɗaura auran MEENA da JAMAL akan sadaki mafi inganci daddare aka kai amarya gidan ta SUHAIL ne ya kai MANAL dan yace baya so, tasha wahala tunda ba ita kadai bace an kai amarya gidan ta me kyau da tsari Kowa ya kama gaban sa akabar amarya da ango, agajiye liƙisss MANAL ta kwanta salla ma, da kyar tayi ta bata tsaya jiran SUHAIL ba tayi kwanciyar ta ga zazzaɓi da ya rufe ta, cikin dare MANAL taji wani axababban ciwo wanda tunda take bata taɓa jin Irinshi ba, tun tana daurewa har ta, kasa cikin azabar ciwo ta tashi SUHAIL da yake ta rafsa baccin,sa fita yayi ya kira Gwaggo tana zuwa taga naƙuda MANAL take ba tara da ɓata lokaci suka tafi asibiti ɗakin haihuwa aka shiga da ita minti biyar Nos ta fito ta samu SUHAIL tace abasu kayan haihuwa su sun manta da wani Kayan haihuwa saboda ruɗewa dole se siya akai acikin asibitin minti biyu Nos ɗin ta sake fitowa ta kalli SUAHAIL tace ''ranka ya daɗe albashirin,ka'' cikin zaƙuwa SUHAIL yace ''goro'' yanda yayi maganar seda yasa Nos ɗin tayi dariya kana tace ''MADAM ta sauka lafiya kuma an samu 'yan biyu duka maza'' dan farin ciki SUAHAIL kasa yin magana yayi se motsa bakin sa yake goshin sa ya kai ƙasa yayi wa Allah godiya '' ''Alhamdullih Allah abin godiya SUHAIL ya zama uba cewar Gwaggo sosa kai SUHAIL yayi yana sunne kai wai kunya yake ji bayan an kai MANAL ɗakin hutu suka shiga ga gadanta gana yaran ta wanda aka naɗe su cikin kayan jarirai masu kyau da tsada tunda SUHAIL ya shigo idon sa na kan yaransa inya ɗauki wannan seya ajiye wannan ya kuma ɗaukar dayan har ya bawa MANAL haushi wato ba ta ita yake ba ta ƴaƴan sa yake nan ta cika tayi fammmm, ya kusa 30 minit yana kallon yaran sa, sannan yazo gurin MANAL maganar duniya yayiwa MANAL amma tayi burusss da shi, se cika take tana batsewa Ita dai Gwaggo tana kallan su bata ce ta tafas ba, bare a sauke ''kuka MANAL tasa mai tana cewa shi kenan yanxu ta san baya son ta ƴaƴan sa yake so, shi,kuwa SUHAIL dariya ma, ta bashi, nan dai ya lallaɓa ta suka rabu lafi, kangari ya waye SUHAIL ya ɗora photo yaran a MIDIA anyi masa haihuwa
Kan kace me, ƴan uwa da abokanan arziƙi sun sani kankace kwabo ƴan barka sum a cika acibitin ba masaka tsinke ƙarfe goma na safe aka basu sallama sabida basu da wata matsala daga me jegon har yaran ta kai tsaye sashin Gwaggo aka kai MANAL dan akula da ita da kuma yaran ta, zo kuga yanda ake nannan da MANAL kai ba zaka taɓa cewa bata da iyaye ba, shima SUHAIL yana can gurin abokanan sa sunata yimai tsiya se dare ya samu shigowa cikin gidan ɓangaran su, ya nufa cike da ɗaukin sake ganin yaran sa amma me babu kowa fitowa yayi yanufi sashin Gwaggo dan yafi zaton tana can ilaikuwa ya sameta tana cin tuwan dawa miyar ɗanyar kuɓewa data sha manshanu da yajin daddawa wanda Gwaggo da ta,shiga kicin ta dafa mata shi .
ƙarasa wa inda take yayi se faman Binta da kallo yake kamar ze cinye ta, huremai ido tayi ''kallon fa haka'' dariya yayi yace "gani nai kinyi kyau kuma kin manta dani tunda gashi har kina iya cin abinci batara dani ba, sunkuyar da kanta tayi kana tace ''kayi haƙuri nima dan babu yanda zanyi ne duk duniya na fiso na ganka kusa dani bana so, naga kayi nesa dani dan Allah kada kaga na haihu kace zaka min kishiya wallahi bazan iya sheres ɗin ka da wata na fiso ka zauna dani ni ɗaya takkkk kayimin wannan alƙawarin'' ta faɗa fuskar,ta cike da kishi'' shiru SUHAIL yayi yana mamakin dama MANAL nada irin wannan baƙin kishin haka? tambayar da bashi dame bashi amsar ta ''kayi shiru ko Kanada wata budurwa awaje baka gaya min ba?''' ta tambaye shi idonta fal hawaye da sauri SUHAIL ya girgiza kansa yace ''wallahi kiyar da dani tunda nake ban taɓa ssuraran wata ƴa mace ba hasali ma su, suke cewa suna sona,'' ajiyar zuciya MANAL tayi tace shi kenan na yarda da kai, danna san baza kamin ƙarya ba, dai-dai lokacin yaran suka tashi suna kuka da alama yinwa sukeji ɗakko su, yayi, ya bata HASSAN shi kuma yana jijjiga USAINI bayan tagama bawa Hassan ya miƙa mata usaini ya mutsa fuska tayi ''wallahi na gaji plssssssssssss ka siyo madara a dinga basu ta faɗa tana turo baki'''




Kallan da SUHAIL ya bita da shi ne yasa ta karɓi Usaini tana bashi nono tana gama bashi ta miƙa masa ɗansa ta juya musu baya ya jima a zaune yana yiwa yaran addu'a ya kuma yi musu huɗu ba kwantar da su, yayi yasa hannu ya juyo da MANAL yana kallan cikin ƙwayar idon ta, '' ko bayan raina kika bawa yara na madara ba zan yafe miki ba saboda lafiyar ki ƙalau ki faɗi duk abinda kike so zanyi miki amma kada ki, kuskura ki bawa ƴaƴa na madara'' ya faɗa cikin faɗa da ɗaga murya idanun sa sunyi ja kamar garwashi fita yayi daga ɗakin zuciyar sa, na suya. tun daga nan SUHAIL ya dena shigowa ɗakin idan ma yaxo iya kacin sa farlo yace amiƙo masa yaran sa idan ya gama ganin su ya bada abinda ze bada ya tafi hakan ya ɗagawa MANAL hankali tana ji ze ringa waya da ƴan mata yana dariya kullum cikin kuka take ga kishin mijin ta da yake damun ta ga watsin da yayi da ita.




Gida ne ginin jar ƙasa Irin na da ko albarkacin ƙofa babu se buhun siminti da akasa aka rufe gidan shima duk ya yayyage kana iya ganin wanda yake ciki Ahankali yake magana cikin sarƙewar numfashi yace '' kaico na ni, ABUBAKAR ban riƙe amanar yar ɗan uwana ba gashi yanzu nayi biyu babu ba dukiyar ba lafiya tari ne ya kamashi ya kusa minti 30 yana yi kafin ya lafa masa yaci gaba da cewa '' tabbasss Allah ba azzalumi bane tun aduniya yake hukunci base anje lahira ba BILKISU ZAINAB BABILA ya kira sunan,su. Suka amsa cikin kuka yace '' hakiƙa na kasan ce me son kaina a koda yaushe saɓa nin ɗan uwana da ba haka yake ba, baya taɓa nuna ban-banci duk abinda nake so yana min baya taɓa gajiwa dani amma bana duban haka wata rana naje gidan sa nace ya bani kuɗi zan yi jari yace to amma in yi haƙuri babu kuɗi agurin sa saboda shima yayi odar kaya amma nan da sati inzo in karɓa, alokacin na rufe ido na, nayi mai rashin mutunci wanda shima hakan ya fusata shi, har mukayi musayar yawu na dawo gida na gayawa mahaifiyar ku, itama ta zuga ni nan dai na kuma hawa dokin zuciya cikin daran na fita na haɗa kai da ƴan fashi na basu kuɗi nace su kashe ɗan uwana ALAJI SA'AD ME DALAH nace kar su kashe MANAL saboda idan ba ita bazan samu duka kadarorin dana keso ba Lokacin zuciya ta ƙeƙashe bana ganin komai, cikin dare kuwa ƴan fashin nan suka kashe shi, shi da matar sa wanda daga nan ne MANAL ta dawo gurina da Zama itama ba'aje ko ina ba na amshe dukiyar ta nasa agaba mukai taci ita kuma muka barta cikin wahala da azaba. Wannan shine babban zunubin dana ai kata wanda ban taɓa gayawa kowa ba, wanda na san alhakin ɗan uwana ne yake ta bibiya ta dani daku, babu kuɗi babu gidaje ba motoci ba shaguna komai ya ƙare munsiyar da komai abincin da zamuci ma gagarar mu, yake ƙarshe ga inda muka dawo gidan da bashi da maraba da titi wayyoooooooooo Allah na ina zanga MANAL na roƙe ta gafara ta yafe min ko naji sanyi ta wani ɓangaren na san tawa tazo ƙarshe ba lallai na tashi ba dan haka nake jan hankalin ku, da kuguji duniya domin babu komai Acikin ta se ɓata. NABILA wacce itama ta haihu sedai ɗan nakasashhe ne bashi da ƙafa gashi ita kuma ta gamu da cutar H.I.V wanda mijin da ta aura yasa mata har taci ƙarfin ta tace '' in sha Allahu DADY zamu nemo duk inda MANAL take mune mi, yafiyar ta dan mun azabtar da ita ga mugayan kalamai da muke faɗa akanta wanda kan mu, suka dawo'' ta faɗa cikin kuka me nuna tsantsar nadama Mommy da ZAINAB ma kukan suke "yanxu idan mukace zamu nemo MANAL ina zamu, bamu san inda take ba sannan bamu san gidan wanda aka aura mata ba cewar mommy gaskiya ne mommy amma Ni, aganina mu nemi, RABE me gadi ina ganin ze san gidan tunda shi ne wanda ya nemo mijin da aka aura mata cewar ZAINAB gaba ɗaya sukai na'am da zancanta. Kwana biyu suna neman Rabe wanda da kyar suka Ganshi suka taho dashi,. Shi kanshi RABE seda ya tausaya musu amma daya tuna rashin imanin da sukayi wa MANAL se yaga be Kama tama yaji tausayin su ba,
Nan Dady ya kuma faɗawa RABE me gadi Irin aika aikar da yayiwa ɗan uwan sa ya ƙara da cewa ''Rabe ina roƙon ka, daka kai ni gurin MANAL na roƙi gafarar ta kona samu sauƙin ciwon dana keji a jiki na kai kaɗai kasan inda take shi yasa nasa aka nemo min kai kate maka RABE,'' DADY ya faɗa cikin sarƙewar tarin daya kamashi wanda har da jini seda ya lafa sannan Rabe yace '' gaskiya ALAJI bazan ɓoye maka ba wanda na kawo maka bashi MANAL ta aura'' ''wata aura?'' cewar mommy nan RABE ya kwashe duk yanda akayi gurin ɗaurin auren ya gaya musu yaci gaba da cewa ''yanxu haka shekaran jiya na sami labarin MANAL ta haihu kuma ƴan biyu zancan nan da nake muku MANAL matar ɗan Sarkin masarautar ZAKI ce, Gaba ɗaya ɗakin yayi tsittt kamar ruwa ya cinye su, '' DADY kuwa cewa yayi "alhamdullih Allah Nagode maka daka juya wannan lamari RABE na gode da baka aurawa MANAL wanda ka kawo ba ina fata zaka mana, jagora don muje mu nemi yafiyar MANAL” insha Allahu ALAJI duk sanda kuka shirya kuyi min magana zan kai ku Allah ya tsare gaba yasa mufi ƙarfin zuƙatan mu, suka amsa da Amin kowannan su, yana mamakin yadda akayi haka lallai ikon Allah da girma yake,








MASARAUTAR ZAKI


SUHAIL ne zaune a farlon Gwaggo yazo ganin yaran sa Bayan an kawo masa su, ya zauna yana ta ɗaukar su, a photo se zabga murmushi yake MANAL ce ta shigo farlon cikin shiga ta alfarma tayi kyau sosai sallama tayi ya amsa ciki-ciki dan har yanzu fushi yake da ita. Guri ta samu akan kujerar da yake kai ta zauna tara da yi mai sannu da zuwa banza yayi mata duk da haka bata haƙuri ba tace '' kayi haƙuri YAYA wallahi b...'' da sauri ya ɗaga mata hannu yace "ya isa haka MANAL bana son jin komai daga gare ki kin riga da kin nuna min koke wace ban taɓa tina nin zaki yiwa yara na wannan horon ba mena rage ki, da shi me kika nema kika rasa da har zaki ce ba zaki shayar da su ba shi kenan ai bake kaɗai ce mace aduniya ga mata nan birjik aduniya ko nawa nake so zan aura da har zan zauna ina kallo ki ringa yiwa ƴaƴana horan madara '' kuka MANAL ta saka mai har cikin ran sa yake jin kukan nata Amma ya maze dan baya so ko kaɗa nan gaba idan ta kuma haihuwa tace zata bawa ɗan sa madara dan haka yayi banza da ita taƙaraci kukan ta, miƙewa yayi ze tafi ta riƙe rigar sa cikin kuka tace '' saboda bani,da kowa shine kake min duk abinda ka gadama har kake iƙirarin zaka ƙara aure shi kenan SUHAIL ina so ka sani kafin na bar gidan ka seka bani yara na dan sba naka bane da abina ka ganni ko yanzu kace in tafi tafiya zanyi amma da yara na zan tafi" Jikin sa ne yayi sanyi da yaji ta amci bata da kowa se kuma ta basa dariya da tace yaran ta ne cikin son ya ƙular da ita yace '' bazan bayar da yaran ba duk inda zaki kije amma bada yara na ba sannan da kike cewa yaran ki, ai duk wanda yaga yaran nan yasan ƴaƴa na ne saboda kamar da muke yi dasu'' dan takai ci MANAL magana tayi Fuuuuuuuuuuuuu ta bar farlon ranta aɓace shi kuwa SUHAIL dariya yayi yace yarinya se rigimar tsiya wai kaji yaran ta Saboda tsabar rigima Irin Tata,
ranar suna yara suka ci sunaye HASSAN akasamai sunan me martaba USAINI kuma akasamai sunan mahaifin MANAL wato SA'AD, anyi taron suna me jego da yaran ta suka samu kyautittika da dama har da wani abokin. SUHAIL daya biya mata kujerar maka idan tayi arba'in zata tafi. cikin ikon Allah MANAL tagama wanka yaran ta sunyi kyau sunyi ɓul-ɓul kamar ba haihuwar fari ba randa zata koma sashin su, Gwaggo tasa aka gyara ta da magun gunan mata ga Gara da akayi mata daddare aka rakata ɓangaran ta, washe gari da yamma me martaba yasa aka kira masa SUHAIL da MANAL basu ɓata lokaci ba suka je Gaban MANAL ne ya yanke faɗi lokacin da tayi tozali da su DADY wanda daga ganin sa kasan ba shi da lafiya sabida akwance yake, kasa zama tayi har seda me martaba yace ta zauna sannan ta zauna nasiha me ratsa zuciya SARKI yayi musu sannan yace '' MANAL duk abinda kika ga ya sami mutum to daga Allah ne dama ya riga da ya ƙadar maka haka tun kan kazo duniya na san baki manta da wa'innan mutanen ba to dan haka kiyi haƙuri kiya fe musu duk abinda suka miki saboda manzon Allah (s.a.w) yana son me yafiya'' '' Hakiƙa MANAL munzalin ce ki, ina me roƙon gafara agurin ki, da ki yafe min kona samu Salama a rayuwa ta haƙiƙa ban riƙe zumunci ba na biyewa duniya ina ganin kamar bazan mutuba se gashi tun aduniya Allah ya nuna min iya kata ki yafe min MANAL nina san tawa ta ƙare Allah baxe bar ni ba kodan Abinda nayiwa ɗan uwana Nana ya gaya musu cewa shine yasa aka kashe mahaifin MANAL innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn MANAL ta faɗa tarada miƙewa tsaye cikin kuka tace “ dad da da dama kai ne kasa aka kashe min Abba na momy na?'' ta faɗa cikin kuka se Kuma gani su kai ta sulale ƙasa sumammiya da sauri SUHAIL yayi kanta yana kiran sunan ta ruwa ya ɗakko ya fesa mata ajiyar zuciya tayi kuka take me tsuma zuciya rungume ta SUHAIL yayi ajikin sa yana rarrashin ta, '' bazan taɓa yafe maka ba tunda ka raba ni da iyaye na kuka saka rayuwa ta cikin wahala'' Mommy da ZAINAB da NABILA suka durƙusa gaban MANAL suna neman afuwar ta. ''kinga yanda na koma ko MANAL jibi yanda rayuwa ta juya min baya yanzu haka na kamu da cuta me karya garkuwar jiki ZAINAB Kuma ta gamu da yoyon fitsari mommy kuma Cutar farfaɗiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login