Showing 12001 words to 15000 words out of 43291 words

Chapter 5 - RAMIN MUGUNTA Complete by Maman Hibba .txt

22 Nov 2024

4045

komai kawai dai ina tina nin wani abu ne amma karka damu ba wani abun damuwa bane” “okay allah ya shige magana gaba” dikkan su suka amsa da ameeeeeeen.
daga haka JAMAL ya tashi da nufin tafiya gida har mota suka rakashi MEENA na ɗaga mai hannu...




kamar yan da Alhaji bukar ya tsara zasu je yawon buɗe ido shi da iyalan sa hakan ce ta kasan ce aƙalla zaswuje ƙasashe kusan biyar daddare yasa aka kira masa MANAL guri ta samu ta zauna ne sa da su ta ta kure kamar tsumma. wani kallan tsana DADY ya bita da shi “ to ƴar iska ragowar kantiti mu dai ta fiya zamu yi ba zamu dawo ba zuri ba amma ki sani ba wai bamu tafi mubar ki agidan nan bane dan kiyi yanda ranki yake so se mun kulle ko ina na gidan nan ko ruwan sha ba zmu bar miki ba bare abinci dan haka ya rage ya naki ko ki nema wa kanki abinci da zaki ci koki zauna da yinwar ki wannan matsalar kice kinji abinda nace miki?” ya faɗa cikin tsawa., “ehhh naji in sha Allahu zaka same ni a me bin umar nin ka” tsaki NABILA tayi gamida cewa. “kai ma dai DADY ina ita ina zama da yinwa tana da ƴan iskan kwaratan samari ai babu zan can yinwa tare da ita bare tana ganin bama nan ai se abin da ta gada ma zata yi waƙila ma ta kawo mana kwarye cikin gida”
“taɓ ɗi wallahi da tayi dana sanin haihuwar ta da akayi ta shigo mana da kwartaye cikin gidan mu na sunna” cewar MOMY. ZAINAB kuwa cewa tayi. “ caɓ da ta gane shayi ruwa ne wallahi kinji na ranste dik randa kika kawo mana kwato cikin gida haɗuwa zamu yi mi miki dukan kawo wuƙa banza ballagaza ƴar isaka wacca tayo gadon uwarta Anzo a ban za za'a koma a iska” ira iran waɗan nan magan ganun suka dinga faɗawa MANAL ita dai jinsu kawai take a ranta tana addu'ar Allah ya tsare ta daga aika ta zina masuyi yi ma allah ya shirye Su. washegari kamar yanda DADY ya faɗa seda suka kulle ko ina na gidan sannan yasa aka raba wutar gidan da fam-funan ruwan gidan ƙarfe bakwai jirgin su ya ɗaga. MANAL na ɗakin ta tsoro ya kama ta yanxu ita kaɗai zata kwana A wannan tanƙa meman gidan wanda zeci mutane sama da dubu gashi babu fitila babu ruwa lallai akwai matsala gagaruma..








YANXU AKASOMA KUDAI KUBIYO NI DAN JIN KALAR RAYUWAR DA MANAL ZATAYI ITA KAƊAI ACIKIN GIDAN BABU ABINCI BABU RUWA GASHI BABU FITILA WOHOHOOOOOOOOOOO WATA MIYAR SE'A MAƘOTA








MMN HIBBA CE




RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)




WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)

07073193332


Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.


littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba


GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.


NA GODE




11/12




A yau ne yarima SUHAIL yake gudanar da bikin ƙaddamar da buɗe katafaran asibintin da ya gina shi domin talakawa komai kyauta ne kama daga duba mara lafiya magun guna kai hatta katin daza'a rubuta maka magani kyauta ne sosai gurin ya cika da al'uma manya manyan mutane masu ji da kan su , ƴaƴan sarakuna maza da mata suma sun zo kai hatta da wasu sarakan na garuruwa sun halar ta shi kan shi memartaba ya halar ci taron SUHAIL ne tara da babban aminin sa wato JAMAL sune akan gaba al'makashi aka bawa SUHAIL ya yanka farinn ƙyallan da aka saka agurin ai ko gurun ya kaure da tafi, nan aka gama komai taro ya tashi lafiya tara da sanar da mutane sati mai zuwa za'a fara aiki a asibitin tara da manya manyan ƙwararrin likitoci daga haka taro ya tashi.


MANAL ta koma tamkar ƙwarangwal sabida yinwa ashe da ba rama tayi ba yanxu ne tayi rama tayi baƙi ta rame ta lalace ta ƙwanjame kamar mai curar H.I.V sabida yinwa har ta kai ta kawo bata gani sosai ganin yinwa na neman halaka ta yasa ta yanke shawarar fita tayi bara ko zata samu abinda zata bawa ƴan hanjin ta wanda suka dunƙule guri guda kamar an sa mata dutse a cikin ta., kome gadi bata tsaya saurara ba domin shi ma DADY yayi mai wonin idan ya sake ya bata abinci to A bakin aikin sa shi yasa ko da wasa bata tin kari inda yake ba, bakin titi ta fito tana tafiya tamkar mara hankali dik inda ta gifta se an kalle ta wasu ma sun ɗauka mahaukaciya ce.saboda kayan dake jikin ta basu da maraba dana mahaukata ita dai tafiya kawai take har ta shiga cikin kasuwa shago shago ta ringa bi tana a temaka mata da abin da zata ci yinwa take ji har tsugunawa ƙasa take yi tana roƙon mutane amma babu wanda ya saurare ta se data zagaye kasuwar amma bata samu ko sisi ba tink ƙarfin ta ya ƙare juwa ta soma ɗibar ta ganin ta ya ɗauke kawai se gani akai ta faɗi nan da nan mutane suka yo kanta ruwa me sanyi aka fesa mata ta farfaɗo tana bin mutanen da suka yi cirko cirko akan ta “ ke yarinya me ke damun ki” cewar wani dattijo da kyar ta buɗe baki tace. “yinwa nake ji yau satina ɗaya banci komai ba dan Allah ku bani abinci kar yinwa ta kashe ni ku temaka min ba ni da kowa ba uwa ba uba,” se data bawa dik wanda yake gurin tausayi har da masu kuka wani mutumi ne yasa aka kamo ta aka kawo ta shagon wata me siyar da abinci ya bada dubu biyu yace azuba mata taci ta ƙoshi a zuba mata wani ta tafi da shi godiya ta shiga yi mai tara da yimai addu'a har mutumin ya bar gurin ba ta de na yi mai addu'a shinkafa da miya da nama aka zuba mata ci take tamakar zaki yaga nama hannu baka hannu ƙwarya kan takai wata lomar ta ɗebo wata mutanan gurin se kallan ta suke tana gama ci ta kora da ruwa me sanyi a take a nan bacci ya ɗauke ta se ƙarfe biyu ta farka salati tayi tara da miƙe wa, ta saka siɗaɗɗun takalman ta zata tafi me abinci tace. “ga sauran abinci ki ” karɓa tayi tara da yin godiya ta cewa me abincin idan mutumin ya dawo ta yi mai godiya sannan ta kama hanyar gida Hannun ta ɗauke da kwalin tec'awaye. tana zuwa ta ƙwanƙwasa me gadi ya bude mata ta shi fiyo watan da aka bata da shi ta yi alwala ta jero sallolin da ake binta sannan ta janyo abinci ta soma ci tare da yiwa Allah godiya tana gamaci tayi sallar isha'i sannan ta kwanta bacci me daɗi yayi awangaba da ita wanda ta manta rabon d atayi irin shi . tin daga wannan ranar MANAL seta fita bara shago shago wani xubin ta samo kuɗi wani zubin abinci ko garin kwaki da haka take samun abinda zata sawa ƴan cikin ta


MASARAUTAR ZAKI


“SUHAIL SUHAIL SUHAIL me yasa baza ka te maka min ba? me yasa ka kasa ƙaraso wa gare ni? ko ba zaka temaka min ba duba kaga yanda macizai suke sarana kuna mu na harbi na ka dubi maraice na ka cecen i daga wannan baƙin ramin me duhu da ƙunci da azaba babu komai acikin sa se uƙuba nice nice MANAAAAL”
A matuƙar razane, ya tashi gaba ɗaya ya jiƙe kamar an yi mai wanka da ruwa durowa yayi daga kan gadon kamar zararrre jikin sa se ɓari yake bakin sa, na faɗin “MANAL MANAL MANAL a ina zan ganki a ina kike?” se kuma ya soma hamdala ga Allah buwayi gagara misali gagara kwai kwayo. “Allah na gode ma daka nuna min wannan baiwar taka zan temaka mata zan kutsa lungu da saƙo in ne mota adik inda take”
wayar sa ya janyo lambar JAMAL ya lalubo ya danna kira gami da karawa akun nan sa bugu biyu JAMAL ya ɗauka be bari sun gaisa ba “JAMAL dik abin da kake ka bari kazo Ina son ganin ka yanxu dan Allah ” “ lafiyarka ka kuwa ka duba a gogo ƙarfe bakwai na safe meke faruwa ne ko baka da lafiya ?” tsaki SUAHIL yayi tara da cewa. "kaga malam idan ba zaka zoba kace ba zaka zoba ” daga haka ya katse kiran. murmushi JAMAL yayi yace.
“kaji da shi ciwon ajali a ɗan yatsa haka kurum zaka kira ni da wannan uwar safiyar kamar wani zararre wallahi se na gama abin da nake zanje in yaso ma shawota ”
SUHAIL bayan ya katse wayar ta gumi ya rafka ya tsurawa guri ɗaya ido idanuwan sa suna ƙara hasko mishi fuskar MANAL ji yake kamar a zahiri ya gan ta. ji yayi an da fashi yayi saurin ɗagowa “MANAL ke ce?”sororo JAMAL ya tsaya yana kallan abokin nasa ya kuma maimaita. “MANAL kuma” ji yake kamar ya taɓa jin sunan. "SUHAIIL wai meke faruwa ne tin da safe ka kira ni kace nazo yanxu kuma naji kana kiran sunan wata MANAL plsssss me ya faruwa ?”
"ban sani ba JAMAL ban santa ba ban san wacece ita ba A mafarki take zuwar min tana neman temako na amma ban taɓa ganin fuskar ta ba se yau ta bayyana min kanta ta kuma gayamin sunan ta MANAL”
shuru JAMAL yayi yana bin abokin nasa da kallo lallai ya tausaya mishi kuma ga dikkan alamu ya faɗa soyayya da yarinyar da take xuwar mai a mafarki caɓɗi akwai cakwakiya “ JAMAL a ina zamu nemo ta ba zan iya cin komai ba idan ban nemo ta ba kuma A yau ɗin nan”
wata uwar harara JAMAL ya watsa mai yace. “sannu shugaban mahaukata na didduniya ta ina zamu nemo ta yarinyar da bamu santa ba hasalima amafarki ka ganta wai waya gaya ma ana yin haka? kawai daga kaga mace amafarki seka dage seka nemo ta to idan kai ka haukace ni da hankali na wallahi wama ya sani ko aljanu ne suke xuwar maka amafarki da yake kasha giyar wake seka tafi neman ta Allah ya bada sa'a seka dawo amma ba dani ba danni ban shirya wahalar da kai na ba kai da kaga zaka iya ga hanya nan Allah ya tsare ”
"haba JAMAL ya zaka yimin haka a tina nina abokin kuka shi ake gayawa mutuwa amma se gashi kana neman juya min baya” “ dole in juya maka baya badan komai ba se dan lafiyarka baka san wacece ita ba kawai tana xuwar maka a bacci se ka dage seka nemo ta gaskiya ba zan goyi da bayan ka ba”
A fusace, SUHAIL ya miƙe ya ɗauki mukullin motar sa yayi hanyar waje motar sa ya shiga tarada bata wuta ya buga wani uban ham da gudu ya fice daga gidan har yana ƙoƙarin taka masu gadin gidan kowa mamaki yake tunda suke basu taɓa ganin yarima SUHAIL a irin wannan yana yin ba shima JAMAL motar sa ya shiga ya bi bayan sa ganin gudin da SUHAIL yake shararawa ya ɗagawa JAMAL hankali,,, tsoran sa ɗaya kar yaje suyi karo da wani da kyar ya samu yasyha gaban sa saura ƙirissss su yi karo gaban sa yaje ya tsaida motar dole SUHAIL yaja birki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiiiiiii. fitowa JAMAL yayi daga tasa motar ya buɗe ta SUHAIL ya shiga “yanxu SUHAIL da kake wannan gudin baka gudin wani abun ya same ka?”
SUHAIL daya kifa kan sa A kan sitiyarin ɗin motar ya ɗago tini ida nin sa, suka sauya launi daga fari zuwa ja “dik abin da ya same ni ba matsalarka ba ne ka fitar min a mota zanje in nemo ta dik inda take ba zan kuma ne man temakon kowa ba”
“Shi kenan SUHAIL zan taya ka neman ta dik inda take ka kwantar da hankalin ka” bara na kira azo a ɗauki mota ta se mu tafi a taka haka kuwa akayi JAMAL ya kira Direban sa ya ɗauka suka tafi a tasa lungu da saƙo suka shiga su kutsa nan su kutsa can amma babu me kama da ita har wajan da almajirai mata suke zama se da suka je amma ba su ganta ba ko mace suka gani ahanya se SUHAIL yace su tsaya su ga fuskar ta ko ita ce A hanya magariba tayi musu sunyi laushi kamar fulawa musamman JAMAL dole suka koma gida tin daga wannan rana se sun fita neman ta se dai har yau ba A dace ba sosai jikin SUHAIL yayi sanyi gashi kullum se yayi mugayan mafarkai da ita tana neman temakon sa hakan yasa hankalinsa ya kuma tashi,,,, dik ya rame yau kima nin sati uku suna fita neman ta Allah be sa sun ganta ba yau ma kamar kullum JAMAL ya shiryo tsaf se dai me ganin mutumin nasa yayi a kwance babu alamun shirin fita a tara da shi a bakin gadon JAMAL yayi wa kansa masauki gamida cewa. “yau baza mu fita ba ne?” “eh mubari se gobe kai na ne yake ciwo” “to Allah ya sawaƙe kasha magani ?” kai ya ɗaga mai alamar eh "“yawwa SUHAIL bara na nuna maka Hotunan wasu takalma da naga anyo odar su JAMAL ya faɗa tarada fito da wayar sa daga ajjihun sa ya shiga gurin hotina “ka gansu wallahi sunyi kyau sosai kuma nasan zaka so su ” ya miƙa mai wayar karɓa yayi yana dubawa “eh gaskiya sunyi kyau ”seya cigaba da dubawa kamar wanda akasa ya cigaba da dubawa hotina har ya wuce hotunan ta kalman Zumbur ya miƙe hannunsa dafe da ƙirjin sa jikin sa na ɓari,,,,, kamar mazari shi kuwa JAMAL firgita yayi yace. "SUHAIL lafiya kake wannan zaburar ” “ita ce ita ce ita ce wallahi JAMAL ita ce MANAL ce JAMAL dama kasan ta ? me hotan ta yake yi a wayarka ? ko ƴar uwarku ce ?”
"wai wace ce kake magana akanta ni ban fahimci komai ba” “baka santa ba me ya kawo hotan ta cikin wayar ka?” SUAHIL ya faɗa tarada nunawa JAMAL hotan MANAL wanda ya ɗauka lokacin da aka yi mata tiyata JAMSY ce tace ya ɗauki MANAL a hoto ya tura mata dan taga yanda fuskar ta tayi shi ya ma manta daya ɗauki wata MANAL a hoto dama ita ce SUHAIL yake gani cikin mafarkin sa ohhhh Allah me iko tabbasa koda ba ita bace to sunan yaxo iri ɗaya.














MMN HIBBA
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)




WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)

07073193332


Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.


littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi sho dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba


GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.


NA GODE


SADAUKARWA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login