Showing 9001 words to 12000 words out of 43291 words

Chapter 4 - RAMIN MUGUNTA Complete by Maman Hibba .txt

22 Nov 2024

4043

baze ba da tasa ƴar ba Haka aka biya wa MANAL kuɗin komai na karatu ta tafi ita kuma ZAINAB aka sama mata wata anan garin Kano kamin wannan lokacin BILKISU ta kuma haihuwar ƴar ta mace wanda ba haka taso ba so tai ta haifi namiji kamar dai ko yaushe Alhaji SA'AD ne yayi komai na suna a lokacin MANAL ta kammala karatun ta ta dawo da sakamako me kyau hakan yasa mahaifinta ya shirya mata walima da kuma yi mata Al-ƙawarin kaita gurin shaƙatawa gefe guda kuma BILKISU ta saka alhaji bukarr tana yi mai huɗubar sheɗan wai ɗan uwansa ya asir ce shi dan kar yayi kuɗi kamarsa ga kuma wulaƙanci da yake musu baya jansu ajiki so sai ALAJI BUKAR ya hau ya zauna kan zugar da matar sa BILKISU take yi mai dan haka ALAJI BUKAR ya wanke ƙafar sa yaje gidan ALAJI SA'AD ME DALAH kan ya bashi kuɗi zeja jari shagunan sa sunyi ƙasa babu kaya aciki gashi kuma bashi da kuɗi sannan million goma yake so ya bashi tunda yake zuwa karɓar kuɗi gurin ALAJI SA'AD be taɓa yi mai musu ba amma wannan karon yace. yayi haƙuri ze bashi amma se an da sati ɗaya dan shima babu wasu isassun kuɗi agurin sa saboda yayi odar kaya daga ƙasashen da yake odar amma in sha Allahu nan da sati ze ba shi nan fa Alhaji bukarr ya soma wasu munanan magan ganu yana cewa dama be damu da shi ba baya te maka mai daga shi se ƴar sa da matar sa magan ganu dai marasa tushe shi kuwa ALAJI SA'AD yaji zafin abinda ɗan uwan nasa yayi mai har ya kai su gayin sa'in sa Abin da busu taɓa yi ba haka ALAJI BUKAR ya bar gidan cikin fushi da ɓacin rai yana zuwa BILKISU ta kuma ɗora shi akan network ya kuma fusata. washegari misalin ƙarfe huɗu na yamma aka gudanar da gagarumar walima da aka shir yawa MANAL walimar data haɗa manya manyan ƴan kasuwa da masu kuɗi kai harda ɗan sarkin marautar *ZAKI* daya halarci taron a madadin *SARKI* kyaututtuka kam tashasu daga me bata mota seme bata gida sema bata fili dame bada cek ɗin kuɗi har da wanda ya biya mata aikin hajji. Shima ALAJI BUKAR yaje gurin walimar shima ya bata kyauta fuskar nan tashi wasai kamar babu abinda ya faru.an sha hotuna sosai kowa ka gani yana cikin farin ciki ba dan komai ba se dan karamci da mutunci irinna alaji sa'ad me dalah.
*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJU'UN*
A daran ranar ƴan fashi suka haura gidan ALAJI SA'AD ME DALAH suka kashe shi shi da matar sa Wanda awashe garin Ranar da akayi walimar MANAL suka yi mata Al-ƙawarin kaita gurin shaƙatawa gurin shaƙatawar da basu je ba kenan Abin da yafi ɗaurewa mutane kai shine yanda ALAJI BUKAR be wani nuna damuwa akan mutuwar ɗan uwan nasa ba kamar ma ba ɗan uwan sa ba ne ya rasu.




WANNAN SHINE LABARIN MANAL DANA IYAYANTA WANDA IDAN ME KARATU BE MANTA BA KISAN DA AKAYIWA ALAJAI SA'AD ME DALAH SHINE FARKON FEGE ƊIN MU TO KUNJI DAI ALAJI BUKAR KANINE AWAJAN MAHAIFIN MANAL BARA KUMA MU KOMA CIKIN LABARIN DAN MUJI KALAR RAYUWAR DA MANAL ZATA CIGABA DAYI BAYAN DAWOWAR TA DAGA ACIBITI....


Cigaban labari


Sosai magan ganin Dady suka yiwa MANAL zafi, tin da suke zagin ta ko ai bata ta taɓa jin zafi irin na yau ba ace dik irin halaccin da ABBAN ta yayi musu basu gani ba sema zagi da tozarci daya biyo baya kuma wani babban abin takaicin ma ɗan uwansa shine yake yi mai haka dama masu iya magana sunce Naka shi yake bada kai NABILA ce ta taso dan har yanzu bata gama yar da cewa fuskar MANAL ce ba wasu ƴan iskan kayane A jikin ta wanda dasu ƙwamma babu se da ta gama ƙarewa MANAL kallo tana wani yamutsa fuska tamkar taga kashi tace. “Sannu da dawowa karuwar waje ina fatan dai su ƴan iskan naki sun sallameki dan naga kinyi kyau ba lefi gaskiya kin shiga bariki da ƙafar dama" se ta finciko ledar dake hannun MANAL kayan da jamsy ta siya mata ne aciki se magun guna da aka bata da wanda zata sha da wanda kuma zata shafa se kuma kuɗin da Dr. JAMAL ya bata waro ido, NABILA tayi gamida cewa. “Ehhhhy lallai yarinya ki ce da gaske ƙanjamau gareki" ta faɗa tana ɗaga wani kwalin magani wanda maganin goge tabo ne wato (NIYO SIKIN) aka bata saboda sauran ragowar tabon dabe goge ba ya goge, amma shine NABILA take kira da maganin ƙanjamau saboda toshewar basira.
Juya wa tayi gurin su Dady tana nuna musu kuɗin “ kun gani ko? Dady kalli wannan kuɗin ku gani” nan da nan Dady ya kuma hassala yace NABILA ta ba shi kuɗin karɓa yayi yazura a ajjihu sa ya cika rigarsa da iska. MOMY kuwa cewa tayi yo “allah na tuba idan bata yi bariki ba se allah ya tambaye tako kun manta labarin babart a dana baku ita ma ai ƴar barikin ce" Da sauri MANAL ta bar gurin dan ba zata iya jiyewa kanta wannan ɓacin ran ba dan haka taja ƙafafunta ta shiga ɗakin ta wanda babu komai aciki se tsummo karan ta zama tayi tana sauke numfashi kamar wadda tayi tseran gudu fuskar ta ta taɓa taji sumul afili tace. “Allah na gode ma daka haɗa ni da su JAMSY da DR JAMAL da dan su ba da tini na zama makauniya ko kuma kuturwa eh mana kuturwa yo fuska ta ƙone kuma ba ni da wanda ze te maka min da se abinda Allah yayi karshe ma na dinga ɗoyi mutane su dunga gudu na kiran da NABILA take ƙwala mata ne ya katse mata dogon tina nin data lula a sanyaye ta fito tsuguna wa tayi gamida cewa. "gani" wani mitsiya cin kallo ta bita da shi kana tace “ Idan kin gama tina nin ƴan iskan naki kije ga wanki na kimin idan kin gama ki dafa min abinci merai da lpy zanyi baƙo kuma kwana zee yi” daga haka ta juya ta fara tafiya haj tayi taku biyu se ta dawo . “Au na manta idan kin gama kije gurin ajiye motoci akwai farar mota ta ki wanke min da wanki zan kai se naga keee ya kamata ki wanke ta saboda baki da wani kima da daraja dan haka kiwanke min ita tassss ke ba komai bace face baiwar mu shi yasa da Dady ya ce ze koreki na hana ko dan mu na kasa ki” ta faɗa tarada kama kunnan MANAL ta murɗe da iya ƙarfin ta har seda MANAL tayi ƙara ƙafa tasa ta harbe ta sega MANAL aƙasa kanta ya bugu da ƙasa, tashi tayi tana shafa kanta taji koya fashe se taji be fashe ba lokacin da taga kayan se da gaban ta ya faɗi ta tuna dokar Dr. JAMAL da ya kafa mata na kar ta yawai ta sunkuyo da aikin ƙarfi saboda har yanzu fuskarta da saura kuka ne ya ƙwace mata ya Allah ka kawo min ɗauki cikin gaggawa ka raba ni da Rayuwar cikin gidannan wallahi gwara zaman gidan yari da zaman gidan nan sosai take kuka me tsuma zuciya
dakyar ta samu ta gama wankin sannan ta shiga kicin ta ɗora girkin rana bayan ta gama ta ɗora wanda NABILA tasa ta nan da nan gidan ya kaure da ƙamshi ta ko ina. ƙarfe biyar ta gama komai dan haka tayi sallar la'asar sannan ta fito wajan ajiye motocin kai daga ganin motar kasan babu wani datti ajikin ta amma saboda tsabar zalunci tasa ta wanke mota. Ruwa ta ɗebo A botiki ta zuba kilin sannan ta soma wanke motar nan da nan motar tayi fesss kamar masu wankin mota ne suka wanke agajiye ta shiga gidan tana jan ƙafafu se dai mee tana shiga taji an ɗauke ta dawasu gigittun maruka kuma lafiyyayu har seda ta kifa ta dungura ta kuma dungurawa......






Muje zuwa fan




MMN HIBBA✍️


RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)




WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)

07073193332


Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.


littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba.


GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.


NA GODE


9-10
A gigice, MANAL ta ɗago hawaye fal fuskar ta“ke waca iri yar mahaukaciya ce da bakya kallan gaban ki jibi yan da kika taka ni” "ki yi haƙuri momy wallahi ban gani ba” to dama ina zaki gani kina tafiya bagazar bagazar da halla matsa ki bani guri” jiki na kyarma MANAL ta matsa kai tsaye ɗakin ta ta nufa ɗauro alwala ta gabatar da sallar magrib ta tana kaiwa allah kukan ta da nema wa iyayan ta gafara wajan ubangiji sosai taji xuciyar ta tayi sanyi dik wata damuwa da take ciki ta gushe lallai dik wanda ya miƙa lamuran sa ga ubangiji subhanahu watala ala baze taɓa dana sani ba tana nan zaune har aka kira sallar isha'i tayi kwanciya tayi bacci ɓarawo yayi awan gabada ita.
innalillahi wa'inna ilaihi raju'unnn, abin da nake ta maimaita wa kenan lokacin da idona ya sauka a kansu NABILA ita da saurayin ta keeee duniya ina zaki da mu abin babu kyan gani bayan sun gama ai kata masha'arau suka shiga banɗaki tara sukayo wanka suka haye gado suka kwanta babu abinda ya same su cikin dare kwar-tan NABILA ya tashi ita kuwa se sharara bacci take saɗaf saɗaf ya fice daga ɗakin yana tafe yana waige waige ɗakin MANAL️ ya nufa ahankali ya tura ƙofar ya maida ya rufe MANAL dake bacci sama sama taji ana shafa ta juyi tayi bata ra da ta kawo komai aranta jin an ci-gaba dayi harma anxarce yafi na da yasa tayi xumbur ta miƙe “waye” abinda bakin ta iya faɗa kenan jikin ta na ɓari tsoro ya kama ta ko ƴan fashi ne suka dawo ita ma su kashe ta aiko da tafi kowa jin daɗi kawai se taji bakin ta yana faɗin. “ kune kuka dawo nima Ku kashe ni dan Allah kuyi saurin kashe ni ni ma na gaji da rayuwar nan gwarama na mutu ko na huta” "ke basu bane ni ne saurayin NABILA kuma nazo gare ki ne dan ki temaka min ko ince mu temaki juna tin da na ganki naji sha'awar ki ta kama ni naji ina son kasance wa dake dan haka kawai ki amin ce muji daɗi tare ke ma kifi ta daga cikin wannan gidan kisiyi naki ki samu kuɗaɗe ki se mota ke ma ki koma babbar yarinya irinsu NABILAA in dai kika bani kanki to zaki samu dik waɗan nan abubuwan dana lissafo miko” ya faɗa yana shafa jikinta tsoro ne ya kuma kamata ta cure guri guda jikin ta se rawa yake kamar maxari ta tina nasihar da momyn ta take mata cikin mafarkin ta “dan Allah ka rabu dani ni ba ƴar iska bace in dai se nabi maza sun samu kuɗi na ƙwammace talauci ya kashe ni, kuɗi basu dame ni ba domin ina da zuciya me kyau” “haba beby ki gwada mana kiji wallahi da kanki se kin neme ni” ya faɗa yana kai hanninsa kan fuskar ta da sauri ta bige hannin ta ƙwallla ƙara me raxanar wa gaba ɗaya ƴan gidan suka fito suna ta zagin ta ta tashe su daga bacci. “ wai me yasa meki da kike mana ƙara acikin gida?” cewar ZAINAB “wa wa wani ne ya shigo ɗaki na wai yana so na bashi kai..” se kuma tayi shiru jikin ta na kar-kar wa tsaki ZAINAB tayi gami da cewa “ yo Allah na tuba ko kwarto ne ya shigo gidan nan me zeyi dake abu A ko maɗe dahallah rufewa mutane baki” NABILA dai kasa magana tayi domin tana zargin wani abu game da saurayin ta lokacin da MANAL tayi ƙara data tashi bata gansa aɗakin ba afusace ta nufi ɗakin nata, tana hura hanci tana xuwa ta ganshi akwance kuma idon sa biyu cikin masifa, ta soma magana “wannan wan irin wulaƙanci ne zaka kama kashiga ɗakin ƴar aikin gidan mu ai seka jamin raini sannan daka fita idan wani ya ganka fa ?” dariya yayi irin tasu ta ƴan bariki yace. “ haba beby ke ma kin san babu abin da zanyi da waccan kucakar yarinyar koda kuwa mata sun ƙare A duniya ke kaɗai kin ishe ni kawai naje wuce wa ne naga Ƙofar ta a buɗe shine na janyo mata ƙofar shi ne ta tsorata da kike cewa idan wani ya ganni ba kin ce min sun san da zuwa na ba?” “eh sun sani amma basu san kwana zakayi ba” daga haka suka ɗora daga in da suka tsaya.




*MASARAUTAR ZAKI*


“wai daga ina kake naga ka jima baka ƙara so ba?" cewar SUHAIL. “wallahi naje wata anguwa ne shi yasa kaga na jima” JAMAL ya faɗa lokacin daya zauna. “ ya ake ciki na san maganar bata wuce ɗaya maganar buɗe asibiti ya faɗa yana ƴar dariya" "eh wallahi ita ce sabida Me martaba yayi min magana kan yaushe ne xan buɗe nace mai se na zauna da kai munyi shawara” taɓe baki JAMAL yayi “wai shawara se kace wani ƙaramin yaro” gaba ɗaya suka sa dariya, nan dai suka tattauna kan yanda za su gudanar da komai. MEENA ce ta shigo ɗakin tana ƙwalawa SUHAIL kira, “YAYA YAYA SUHA....” se kuma tayi shiru sakamakon ganin JAMAL da tayi shi kuwa JAMAL dariya yayi yace." a'ah matar ya kika tsaya ƙaraso mana ko dan kin ganni ne?” a'ah wallahi ni ba matar ka bace dube ka fa tsoho da kai fuskan ka dik gemu wallahi da zan auri tsoho ba” ta ƙarasa faɗa tana turo baki, ga baki ɗaya su suka sa dariya harda riƙe ciki. haba MEENA ta ya zaki min haka so kike a yi mana dariya in dai gemu ne zan aske se ki dena ganin tsufa na ko?” kai ta gyaɗa mai alamar eh “yawwa mata ta ƙaraso kusa da mijin ki” ƙarasawa tayi ta zauna shi dai SUHAIL ido ya zura musu a ransa yace. “Oh ko yaushe MEENA zata yi hankali? yarinya kusan shekara shabiyar amma tana abu irin na ƴan shekara biyar shi kuma ƙaton banza ya zauna se biye yarinya ƙarama da bata san me ne ne so ba bare ta soka SUHAIL ya faɗa cikin ransa be san maganr ta fito fili ba se ji yayi JAMAL yace. “ehh gwara/ni ina da wacca nake so dik da ƙaramace kai kuwa fa ko budurwa baka da ita” tsaki SUHAIL yayi gami da cewa. “to ai seka ci gaba da zaman jiran randa zata yi hankali se ka aure ta ai kin banza kawai ” dariya JAMAL yayi yace. “ ni da yarin tar ta nake son ta babu ruwa na da rashin wayon ta” SUHAIL kuwa ya faɗa duniyar tinani kan mafarkin yarinyar daya keyi wanda harya zame mai jiki shi dai fatan sa Allah ya bayyana masa ita ta ko ina. “SUHAIL ya dai tina nin me kake yi se magana nake kayi shiru?” fir gigigit ya dawo daga duniyar tina nin daya lula “babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login