Showing 15001 words to 18000 words out of 43291 words
NA
SUDAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA UBAN GIDA NA JAGORA NA A CIKIN DUNIYAR MARUBUTA
ISHAQ NASIR ABDULLAHI (NASSURILLAH)
AL-KAIRIN ALLAH YA ISAR MAKA A DIK INDA KAKE YA KARE GABAN KA DA BAYAN KA YA RABA KA DA SHARRIN MASU SHARRI YA KIYAYE KA DAGA MUGUN JI MUGUN GANI ALLAH YA BAKA ABIN DA KAKE NEMA DUNIYA DA LAHIRA YA RABA KA DA IYAYAN KA LAFIYA.
13-14
“Dan Allah JAMAL ina zan ganta? wallahi ita ce nake gani cikin mafarki na dan Allah aboki na ka temaka min na san kana da masaniya akan ta tin da ga hotan ta awayar ka plsssss JAMAAL” ajiyar xuciya JAMAL ya sauke gami da cewa. “tabbasss na santa amma ban san komai game da ita ba hasali ma wata ce ta kawo ta asibiti na lokacin da aka ƙona mata fuska har ma seda akayi mata aiki wato tiya ta domin gaba ɗaya fatar ta ya saɓule kuma gaskiya ina ganin yarinyar nan marainiya ce don gaskiya babu iyayan da zasu bar ƴar su ta shafe watanni ba suzo inda take ba kai bakaga wani abun mamaki bama seda na rakata gidanna su wallahi gidane na masu kuɗi kuma shahararrru dan wannan gidan daka ganin wanda ya gina shi ba ƙaramin me kuɗi bane kai wallahi yafi gidanmu tsaruwa da komai wannan shine abinda na sani akan ta gaskiya kuma na faɗa maka
zazzafar iska SUHAIL ya furzar daga bakinsa, yace. “ka gani ko abin da nake gaya maka ai ni na san wannan mafarkin dana keyi da ita da akwai magana gashi kai da kanka ka faɗa tana cikin wani yana yi ya zama dole yau ɗin nan muje gidan su” be jira abin da JAMAL zece ba ya faɗa ban ɗaki agurguje yayo wanka ya fito mai kawai ya shafa ya zura kaya gamida fesa turare yace. “ ma iya tafiya” ba musu JAMAL ya tashi suka shiga mota se gidan su MANAL....
kamar kullum yauma MANAL ta fita bara wannan karon harda robar ta shagunan kasuwar ta ringa shiga tana bara se dai yau se ahankali babu sa'a gashi jiya bata samo na kirki ba dan data gaji da yawo se ta samu wata rumfa inda bakowa bane yake xuwa gurin ta zauna tarafka tagumi har aka kira la'asar amma MANAL bata samu ko ƙanzo ba dan haka ta kamo hanyar gida a hanyar ta ta dawowa ne ta gamu da wani mes eda lemo da ayaba da kankana tsayawa tayi agurin ta dubawa baron lemon ido bata ko ƙiftawa se zare idanu, take kamar wacca taga nama shi kuwa me lemon kallan mahaukaciya yake mata don haka ya ɗauki guda ɗaya ya bata saboda murna har haɗawa take da hannin sa tayi mai godiya shi kuwa me lemo mamaki ne ya kashe shi wai dama tana da hankali?
tafiya take tana shan lemon ta kamar mahaukaciya sabon kamu se jan lemon take tana tura wa cikin bakin ta
dai-dai ƙofar gidan su JAMAL yayi fakin ɗin motar dikkan su suka fito daga motar SUHAIL se kallon gidan yake ji yake kamar ya taɓa shiga gidan “INNALILLAHI WA,INNA ILAIHI RAJUN” abin da SUHAIL yake ta nana tawa ke nan afili yace. “wannan ai gidan ALAJI SA'AD ME DALAH ne wanda a shekarun baya ƴan fashi suka shiga suka kashe shi shida matar sa” cikin mamaki JAMAL yace... “ kar dai kace min wanda she karun baya memartaba ya wakilta mu muzo gidan sa saboda walimar da yayiwa ƴar sa lokacin data kammala karatun ta?” “ ƙwarai ma kuwa JAMAL ita ce to amma abin tambayar shine waye yake ruƙon ƴar tasa? kuma su waye a cikin gidan?” “ ba wannan zamu tsaya yi ba gidan ya kamata mu shiga koma me nene zamu gani” cewar JAMAL ƙarasawa suka yi tara da ƙwanƙwasa ƙofar gidan me gadi ne ya buɗe ƙaramar ƙofar suka shiga bayan sun gaisa JAMAL yayi saurin amshe zan can dan baya so SUHAIL yayo musu katoɓara yana so yaji komai abakin me gadin .
“dan Allah malam me gidan nan alaji sa,ad muke nema” “Ayya ai ALAJI ya jima da rasuwa hala dai kuba ƴan garin nan bane ko?” “eh gaskiya mu ba mazauna nan bane” me gadi “shi yasa baka samu labarin kisan da aka yiwa alaji ba” JAMAL yace. “wallahi ban sani ba to ina matar sa da ƴar sa suke?” "kayya ai shida matar tasa aka kashe yanzu ƴar sa ce kaɗai ta rage” “ Ko zamu iya sanin inda take kuma su waye acikin gidan?" shiru me gadi yayi yana Nazarin abinda ze ce can ya nisa kana yace “ ai tin ran sadakar uku ƙanin sa ALAJI BUKAR ya dawo gidan da zama ƴar sa kuma tana nan gidan wato MANAL bata jima da fita bara ba yanxu zakuga ta dawo ”
“BARAH!!.” SUHAIL da JAMAL suka haɗa baki gurin faɗa “ƙwarai ma kuwa ta tafi bara saboda ƙanin mahaifin nata basa nan shi da iyalan sa sun tafi yawon mema kuke cewa ko yawon zaga gari na dai manta.” INNALILKAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UNA abinda SUHAIL da JAMAL suke ta nana tawa
MANAL ce, ta turo ƙaramar ƙofar get ɗin ta shigo har lokacin tana shan lemon ta wanda babu komai aciki se fata se gwaguya take sam bata lura dasu ba ganin tana neman shigewa ciki yasa JAMAL ya ƙwalla, mata kira “MANAL” da sauri ta wai go kasa ƙarasawa tayi sema kafe shi da ido da tayi can kuma tace. “laaaaaaaaaah Dr,. JAMAL kai ne dama zaka kuma zuwa in da nake ina JAMSY ban kuma ganin ta ba” gabaɗaya ta jeromai tambayoyin a lokaci guda kuma cikin murna, “waca tambaya zan amsa miki?" dariya tayi tace. “wallahi dik na ruɗe ne ” se yanxu SAUHAIL ya magantu dace wa. “ ki cire wannan ɓawon lemon daga bakin ki, ” se yanxu ta lura da SUHAIL cire wa tayi cikin jin kunya ta kuma sunkuyar da kanta ƙasa. “ daga ina kike ?” cewar JAMAL in ina tasomayi “uhum uhum naje barane kuma ban samo komai ba se wannan lemon da kuka gani” da suri SUHAIL ya juyar da fuskar sa sabida wasu hawaye da suka taho mai ace yarinya ƴar masu kuɗi wadda batasan wani abu waishi talauciba ita ce take yin bara kai duniya ba matabbata bace....
“me yasa kika fita bara bacin na san da mutane agidan kuma da abinci” JAMAL ya kuma jefo mata wata tambayar. ƙwallace ta silalo daga idon ta tace. ai basa nan sunyi tafiya amma sun kusa dawowa” ta faɗa yayin da ƙwallar data maƙale akwarin idon ta ta samu damar gan garowa. iska me zafi , SUHAIL ya furzar yace. “ka gani ko JAMAL na faɗama nina san ganin ta da nake yi a mafarki ba'a banza ba dan Allah ka duba kaga wannan tanƙameman gidan ace ita kaɗai zata kwana acikin sa dan haka yanzu zamu tafi da ita gida ba zata sake kwana a cikin gidan nan ba ” “A'AH SUHAIL hakan bame yuwa ba ne gwara mu barta anan nina san yanda zamu muɓullowa lamarin dan haka kabar komai a guna ” Seya juya inda MANAL take tsaye ta tsura musu ido cike da tsoro dan gani take kamar cutar zasu yi
“kin ga MANAL ki kwantar da hankalinki baxa mu cutar dake ba hasalima ceton ki zamu yi kishiga ciki xamuje mu dawo kin ji ” kai ta ɗaga mai alamar to fita suka yi daga gidan suka shiga motar su SUHAIL ya kalli JAMAL yace. “ina zamu?” “kasuwa zamuje muyi mata siyayyar kaya dana abinci danna lura akwai yinwa atare da ita in yaso gobe se mu dawo kafin nan ta dawo hayyacin ta ” “ eh kuma fa haka ne” cewar SUHAIL. tin daga burosh kilin sabulun wanki dana wanka kayan kwalliya takalmi kayan sawa hijab dogayan riguna pants shimi brxy kai kaya kawai suke jida kamar za'a haɗa lefe shi kuwa SUHAIL komai ya gani ɗauka yake har seda JAMAL yace ya isa ɓan garan kayan abinci suka nufa komai da ake buƙata na girki seda suka siya mata sannan suka se mata da faffe gurin biyan kuɗi suka je suka biya akasa musu amota sannan suka dawo gidan mamaki ne ya kashe MANAL kai ba ita ba hatta dame gadi se da yayi mamaki gainin tulin kayan da suka shigo dasu ɗakinta suka kai suka dire mata tarada gaya mata gove zasu dawo zokuga kukan farinciki gurin MANAL se godiya take musu SUHAIL kuwa se kallon ta yake ji yake kamar ya tafi da ita ya raba ta da wannan wahalalliyar rayuwar amma bara ya jira yaga wana mataki JAMAL xe ɗauka shima megadi ba,a barshi abaya ba seda suka danƙa mai kuɗi masu yawa suka ce yasa musu ido akan MANAL kada ya kuma bari taje ko ina. sannan suka kama hanyar gida.....
Cikin dare SUHAIL ya kasa bacci fuskar MANAL kawai yake gani koya rufe idon sa ita yake gani yanda yaga rana haka yaga dare gari na wayewa yayi wanka yaje ya gaida memartaba ya gaida mahaifiyar shi da sauran matan baban shi. ko karin kumallo be tsaya be yi ba ya kama hanyar gidan su JAMAL. “a'ah lale marhabin yau kai ne agidan namu SUHAIL lallai yau za'ayi ruwa da ƙanƙara” cewar wata dattijuwar maga wacca ba-zata wuce shekara hamsin ba. sosa ƙeya SUAHIL yayi yace. “ina kwana” “ MOMY lpy lau ja'iri dole ka sunkuyar da kai dik yanda akai akwai abin da ya kawo ka danna san ruwa baya tsami banza har da zaka dako wannan uban sammakon ka taho seka shiga shima ɗayan mashirir cin ɗan uwan naka yana ciki be ma tashi daga bacci ba”. “to MOMY na barki lafiya” sim sim ya shige ciki yana shiga ɗakin ya ganshi akwance bashi da niyyar tashi duka ya ɗala mai, agigice JAMAL ya tashi har yana bigewa da bango dariya SUHAIL yasa har da riƙe ciki shima JAMAL ya daddage ya ɗala mai dindu tsut SUHAIL ya dena dariyar sabida yaji zafin dukan “ashe babu daɗi ni kayi min ”
gabaki ɗayan su sukasa dariya.
“kaga malam katashi Ka shirya Mu tafi in yaso ko ahanya ne seka karya danna matsu inji yaya MANAL ta kwana” harara JAMAL ya ɓalla mai yace. “saboda wata MANAL se naƙi karyawa agida na tafi hanya ina cin abinci to bara kaji babu inda zani se na karya kuma anutse Idan zaka jira kajira” tsaki SUHAIL yayi tarada faɗawa kan gadon, shi kuma JAMAL ya shige banɗaki wanka yayi ya shirya sannan suka nufi babban farlon gidan karyawa sukayi sannan suka kama hanya. “kace akwai ta inda zaka ɓullowa lamarin yarinyar nan ta yanda zamu kuɓutar da ita cikin sauƙi" SUHAIL ya faɗa lokacin daya karya kwana.” "eh ƙwarai haka ne a gani na ba shigar sauri zamu yiwa waɗan nan mutanen ba danna lura wannan ALAJI BUKARR ɗin ba ƙaramin mugu bane don haka cikin hikima da bara zamu bi komai zamu sa me gadin gidan yarin ga yi mana si ai din dik abinda yake faruwa da zaran anxo gaɓar daya dace mu tema keta semu te maka mata ammafa shima ba bayyana kan mu zamu yi ba se dai mu tura wasu idan suka gan mu tarada ita tofa zata kuma shiga wani halin Ko suyi mata wani abun kaga kenan lamari ya ɓaci" cike da gamsuwa SUHAIL yace. “haka ne dik abinda ka faɗa yayi Allah yasa mu dace” gaba ɗaya suka amsa da amin. daidai lokacin JAMAL ya cinna hancin motar cikin gidansu MANAL bayan sun gaisa dame gadi sukace yayo musu magana da MANAL....
tin da ta doso su SUHAIL ya saki baki yana kallan ta har seda JAMAL ya xungure sa sannan ya ankare sanye take cikin hijab ruwan ƙasa yayi mata kyau tsakanin jiya da yau ta canza ta fara dawo wa MANAL ɗin asali har ƙasa ta tsuguna ta gaida su suka amsa tace “su Shigo ciki binta suka yi har xuwa ɗakin ta ruwan da suka seyo mata ta kawo musu suka sha gefe ta koma tana wasa da yatsun hannin ta shiru babu wanda yace komai. JAMAL ne yayi gyran murya gamida cewa... “MANAL” ɗagowa tayi ta kalleshi yaci gaba dacewa “sunana JAMILU UMAR ABDULLAHI ɗan gidana seneto UMAR ABDULLAHI amma amfi sani na da JAMAL. wannan abokin nawa sunan shi SHAMSIDDIN ɗa ne ga sarkin masarautar *ZAKI* ana ce mai SUHAIL shine wanda ake sa ran ze hau milki nan ba da jimawa ba kinji daga inda muke dan haka kema munaso musan labarinki.” gefan hijab ɗin ta tasa ta share ƙwallar data xubo mata nan ta shiga basu labarin ratuwar ta tin daga farko har ƙarahe ba itaba su kansu seda suka xubar da hawaye musamman SUHAIL wai dama da gaske ana irin wannan ratuwar ace ɗan uwan mahaifinka ya dinga axabtar dakai har da yi maka mummunan fata ke duniya ina zaki damu rarrashin ta suka yi sannan sukai mata sallama tara da yi mata alƙawarin zasu dinga zuwa suna ganin ta tin daga wannan rana sesu SUHAIL sun xo tarada yo mata siyayyaya nan da nan MANAL ta murmure hasken ta ya dawo kyawun ta ya kuma fitowa tayi ƙiba fatar nan tayi luwai kamar ta Jarirai gwanin sha'awa ta samu kayan more rayuwa uwa uba kwanciyar hankali babu kyara babu tsan gwama bare marin manca hanya.
MMN HIBBA
RAMIN MUGUNTA
(Ka gina shi dai-dai da kai)
WRITER
SUMAYYA ABDULLAHI
ALHUSEEN (MMN HIBBA)
07073193332
Da sunan Allah mai rama mai jin ƙai dikkan yabo da godiya su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yai kowa yai komai ya halicci mutum da aljan yai ruwa yai iska ya Allah ina rokon ka da kasa na fara wannan littafin a sa'a ka kuma ba ni ikon rubuta abinda ze am fanar da al-umar Musulmi baki ɗaya.
littafin RAMIN MUGUNTA ƙiƙrarran labari ne ban yi shi dan cin zarafin wata ko wani idan littafin yayi dai-dai da yana yin rayuwar ki to kiyi haƙuri ba da nufi ba
GARGAƊI
ban yar da ba ban amince ba wani ko wata tayi amfani da wani sashi na wannan littafin ba ko a ɗora a wata midiyar kamar yanda aka yi min a baya dan haka a kiyaye wannan haƙƙi na ne kuma mallaki na ne idan ana son hakan to a nemi izini na.
NA GODE
15-16
FILIN SAUKAR JIRAGE NA MALAM AMINU KANO.
A hankali jirgin ya sauka ƙasa tara da sakin wata lafiyayyar iska me ratsa zuciya, sannu a hankali fasinjoji ciki suka soma fitowa ɗaya bayan ɗaya canna hango ALAJI BIKAR da iyalan sa sun yi kyau fatar nan see sheƙi take su NABILA da ZAINAB sun koma tamkar ƴan india dan kyau musamman NABILA fatar nan tayi luwai luwai kamar ba ƴar hausawa ba idan ba magana tayi ba zaka taɓa cewa ta san wani abu wai shi hausa DIREBA ne yazo ya ɗauke su dam dam dam gaban MANAL ya yanke ya faɗi lokacin data jiyo maganar su a tazane ta juya ta kalli ɗakin ta wanda yake shaƙe da kayan abincin da su SUHAIL suka kawo mata jiya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai take ambato hijab ɗin ta ta saka ta fito harabar gidan dan gudin kar ace bata zo tare su ba tin da ta fito suke bin ta da kallo DADY da yake waya kasa ci-gaba da yin wayar yayi ya saki baki galala yana kallonta ita kuwa MANAL tsugunawa tayi har ƙasa tace. “DADY sannun ku da dawo wa ya hanya” babu wanda ya iya tanka mata se na mujiya da suka zuba mata NABILA kasa ɓoye abin da ke ranta tayi tace. “ke muna fuka ƴar iska ƴar tasha mu xaki yiwa daɗin baki gidan ubanwa kika samu kuɗin da har kika ɗinka sutura masu tsada irin wannan se ta juya gurin DADY wai dady baka gani ne baka kayan da suke jikin ta ba? ka duba da kyau komu da muke da gata bamu taɓa sa irin wannan tsadaddun kayan ba dama na faɗa muku in dai taga bama nan se ta kawo kwarton ta gidan nan kuma gashi idan ba maza take biba uban wa ze siya mata kaya masu tsada kamar haka” “kin faɗi gaskiya NABILA don haka DADY muna so ka ɗauki mummunan mataki akan ta ko dai ka kore ta ko kasan yanda zaka yi da ita na gaji da ganin wannan shegiyar yarinyar me kama da aljanu” ceawr ZAINAB. “kuma dai kwa faɗa ƴaƴan nan dana bashi shawarar yanda zeyi da ita ai ƙiyawa yayi gashi nan tana kawo mana ƴan iska cikin gida." cewar MOMY ta faɗa a fusace. DADY kuwa cewa