Showing 27001 words to 30000 words out of 48171 words
Chapter 10 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
iri ɗaya kala ce kawai ta bambanta, amma saida tayita zugashi akan wai ta su Feena tafi tashi kyawu.
Rayuwa kenan mai hali baya canjawa, ta sakanta yaronta Mubarak ta nuna mishi jin daɗin duniya tun bai tauna ba balle ya haɗa, yaro ɗan 22years yasa yayi shaye-shaye, ya nemi mata, ya saci kuɗin Dady idan ya gani, kasancewar yana gaban su a karatu yanzu haka yana jami'a matakin farko, Sam babu jituwa tsakanin sa da Amar domin ko wannen su kallon tsana yake yiwa ɗan'uwan sa, dambe suke yi sosai, domin wasu lokutan ma idan yana neman Amar da rigima ta kan Safeenah yake farawa wadda yasan muddin ya ta6ata to dole Amar zai kula shi.
Yau ranar girkin Hjy Babba ne, saboda haka bayan sun kammala hira Hjy Yusra da Feena suka nufi ɗakinta, Amar kuma ya nufi nasa ɗakin. Bayan yar hirar da suke yi a ɗakin sai ta kwanta tayi shiru tana nazarin sabon al'anarin da take ji a jikinta yau, tax juyin duniyar nan tana neman bacci ya ɗauke ta amma bata samu ba, zogi da raɗaɗin da take ji a mararta sai kara yawa yake yi, tun tana iya jurewa har ta fara kuka kasa-kasa.
Momy Yusra dake gefenta tayi zaraf ta tashi zaune, Safeenah? Lafiyar ki kuwa? me yake damun ki?". Ta jero mata tambayoyin lokacin da take ɗago ta, ta mikar da ita zaune tana nazarin fuskar ta, wadda duk ta kumbura kana idanunta sukayi jajir.
"Safeenah lfy? What's wrong with you?" cikin kukan ta nunawa Momy mararta da yatsa, alamar a nan take jin ciwon, hankalin Momy yayi matukar tashi, da sauri ta mike tsaye tareda mikar da Safeenah da nufin ta kaita asibiti.
Abinda ta gani a jikin bedsheet ɗinta ne ya ganar da ita matsalar Feena, sai jikinta yayi sanyi, hankalinta ya ɗan kwanta. Feena kam idonta a rufe sai Kuka take tana gimtse fuska, lebenta har ja yayi saboda cizon da take masa. Jin Momy ta tashe ta tsaye kuma tayi shiru yasa ta buɗe idonta ta sauke su kan Momy, fuska a marairaice tace "Momy marata, wlh ciwo take min sosai, ganin kan Momy na kallon gadon yasa itama tayi can da idonta, ai kuwa karaf suka sauka akan jinin da ya fara fitar mata a jiki har ya 6atawa Momy zanin gado, cikin rashin fahimta ta kalli Momy "na shiga uku na yau me zan gani, Momy mutuwa zanyi?, yan'ciki na ne suka fashe ko me wlh ina zubar da jini". Sai kuma ta fashe da Kuka ta kankame Momy, kuka take sosai tana jerowa Momy tambayoyi waɗanda Momy ta rasa yadda zata amsa mata su.
A madadin haka sai ta kama hannun ta suka shiga toilet ta cire mata kayan jikin ta, sannan ta tsabtace mata shi ta nayi tana mata sannu, ita kuwa ta gama tsurewa, gaba ɗaya tunanin ta ya bata yan'cikinta ne suka fashe kuma babu makawa mutuwa za'ayi, wannan tunanin yana cikin abinda ya hanata tsagaita kukan da take.
Sabon pad da pant Hjy ta ɗauko ta haɗa mata, da kanta ta manna mata always ɗin a jikin pant sannan ta bata tace ta saka, ba musu ta kar6a ta saka, sai dai har yanzu bata daina kukan ba.
Hjy Yusra kuwa banda rarrashinta ba abinda take, saida ta tabbatar ta kimtsa ta Da wasu kayan sannan ta riko hannunta zuwa ɗakin ta yake bedsheet ɗinanan ta shimfiɗa wani, ta zaunar da Feena gefen gadon sannan ita kuma ta koma toilet, ta kama zanin gadon nan dai-dai inda ya 6aci ta wanke shi tas, abinda bata ta6a yi ba a rayuwar ta, sannan ta dawo ta zauna gefen Feena wadda har yanzu Kuka take, tana ganin ta ta fara rokon ta akan ta barta ta tafi gun Yayanta ta ganshi kafin ta mutu.
Momy ta tattara nutsuwarta ta fuskanci Safeenah, tace "Feena ina son ki saurare ni da kunnen basira, kuma kiyi amfani da duk wani abu da zan gaya miki".
Safeenah tayi zuru tana kallon Momy, cikin yanayin damuwa da tashin hankali.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *34*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Cikin sanyi da lalkausar murya, ta fara yiwa Safeenah bayanin wannan hali da ta tsinci kanta a ciki, ta tabbatar mata da cewa al'ada ta fara (haila) wato menstruation a turance, sosai ta wayar mata kai akan messes, kuma ta fahimta domin an jima ana yi musu bayanin lalurar a islamiyya, tasan abubuwa da yawa akan sa, kamar barin salla da mai lalurar zai yi har zuwa ranar da zai yanke, da yadda zai tsabtace jikinsa ya koma salla a lokacin da ya yanke, da nisantar ta6a alkur'ani mai tsarki da dai sauran su.
Sai taji kunyar Momy ta kama ta, ta rufe fuska da tafukan hannayen ta, na gane Momy Malaman makarantar mu suna yawan gaya mana wannan abin da hukunce-hukuncen sa, kuma duka na sani in Allah ya yarda zan zamo mai kiyayewa. Momy taji daɗin yadda yarinyar ta fahimta, tayi murmushi tana faɗin gud girl, dare sosai suka kai suna hira Momy na kara wayar mata kai akan abinda ya shafi al'ada, ta tabbatar mata da dole ne mai wannan abin ya zama cikakken mai tsabta, baya ga wanna ta nusar da ita abubuwa masu yawan gaske, daga karshe ta rufe da nasihohi masu sanyi da ratsa jiki.
Duka dai Safeenah ta fahimce ta, magunguna Momy ta haɗo mata tasha sannan ta kwanta bayan tayi filo da cinyar Momy dake kwance, wai a haka zatafi jin daɗin kwanciya, Momy dai bata ce komai ba, saima shafa kanta da ta shiga yi, a hankali kuwa bacci yayi kasa da ita.
Saida ta tabbatar tayi baccin sannan ta ɗaga ta ta gyara mata kwanciyar ta, ta rufe ta Da mayafi, sannan itama ta kwanta tana mai cigaba da kallon fuskar Safeenah, fuskar da tafi soyuwa a cikin zuciyarta.
Washe gari suka tashi kamar yadda suka saba, da asuba kenan Momy ta ɗauro alwala ta tashi salla, Feena kuwa toilet ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi tayi wanka, ta fito lokacin Momy ta idar da salla tana addu'a, hakan yasa Feena ta fara tsane jikin ta tukunna, sannan ta fara shafa lafiyayyun lotions ɗin su, bayan ta kammala ne ta ɗauko wata doguwar riga ta saka, kasancewar da yawa kayan ta a ɗakin suke, sai da Momy ta shafa addu'a sannan ta tashi, ta ninke sallaya ta mayar, a wardrobe ɗin ta koma ɗaukowa Feena wani sabon pad da wani pant ta bata, ita ta koya mata yadda zata rika haɗa su, ta kuwa iya duk da tana jin kunyar Momy sosai.
Lafiyar gado ta koma bi ta lafe saida gari ya waye, sannan ta farka a lokacin Momy ta fita kitchen, ganin haka yasa ta shige toilet wani wankan ta kuma yi sannan ta fito ta shirya, cikin wata atamfa super yar' asali, kalar light green, ɗinkin riga da sket, kayan sun mata kyawu matuka, ta taje lafiyayyen gashin kanta, ya kwanta ya luf-luf, ta ɗaure shi da ribbon kalar kayan jikinta, ta naɗa ɗankwalin tayi kyakkyawan ɗauri ɗan yayi, yarinya ta fito fes da ita.
Suna zaune a kan dinning suna cin abinci, Momy da Amar wanda duk hankalin shi na kan kanwarsa, wadda tun ɗazu yaso yaje ya taso ta Momy tace ya barta tukunna tunda bata jin daɗin jikin ta, sai yayi duk hankalin sa ya tashi, abincin ma sakawa kawai yake ba tareda gane takamaiman ɗanɗanon sa ba. Momy ta lura da yadda yake kimsa abincin tamkar wanda aka yiwa dole, sai ta basar ta kyale shi, domin tasan damuwar sa Feena ce.
Tare suka juyo lokacin da suka jiyo takun takalmin ta, tana sakkowa daga kan benen, Amar kam kasa hakura yayi, da sauri mike yayo kanta, "Safeenah kanwata, ya jikin naki?". Yayi maganar lokacin da ya riko hannunta, murmushin nan nata ta sake mishi, kafin tace "lau nake Yayana, fatan kaima haka, barka da safiya".
Ta shafi kumatun ta yana faɗin, "na shiga uku Momy, Feena ta fara 6oye min damuwar ta, kinga wai bata gaya min batada lafiya ba". Momy tayi dariya tana cewa "nima ai ba gaya maka nayi ba kawai dai cewa nayi karka taso ta saboda bata jin daɗi". Ajiyar zuciya ta saki jin Momy bata gayawa yayan nata abinda ya faru da ita a daren jiya ba, "bana son damuwar ka ne Yayana, tunda na riga naji sauki to miye na gaya maka?". "Shikenan amma kin tabbata kin ji sauki ko?". Ta gyaɗa kai "sosai ma kuwa, kaikam zo mu ci abinci". Ta kama hannun sa suka isa gun dinning, ta ja mishi kujera shima ya janyo mata suka zauna fuskoki da zukatan su tas da farinciki. Momy kam nata ido ne, domin ta riga ta saba, tunda take a duniyar nan bata ta6a ganin soyayyar yaya da kanwa kamar irin ta su Feena da Amar ba.
Sai a lokacin ya ware, ya saki jiki ya ci abincin sosai, haka itama, sai watanni suke da labarun raha, Yusra kam banda dariya ba abinda take, haka Dady ya fito ya same su, sosai zuciyarsa tayi fari, soyayyar yaran ta kara samun muhalli a rayuwar sa, domin ya yarda a yanzu yaran sune farin cikin Matarsa da shi kan shi ma.
Tare suka mike suka taro shi, Amar ya kar6i jakar shi Feena kuma ta riko hannun shi suna mishi ina kwana, ya amsa cikin fara'ar nan tashi da sakin fuska, idon sa akan Matarsa yace "Maman yara, a nata hira ko?" "barka da safiya, an tashi lafiya". Ta gaishe shi kicin fara'a, ya amsa mata cikeda jin daɗi, Mubarak dake bayan shi sai hararar Hjyr da yaranta yake, Dady ya kalle shi "boy ba zaka gaida Maman ka ba?", ya kara tamke fuska, ya kalle ta kasa-kasa "ina kwana" Yusra tayi murmushi "lafiya lau Mubarak, ka tashi lafiya?" bai koma tanka mata ba ya fice daga falon yayi waje. Dady ya girgiza kai, ya kalli Yusra "ki kara hakuri da halayyar Ummu da yaron nan Mubarak, dan Allah Yusra kar ki yarda kisa wata damuwar a ranki kinyi?". Yana gama faɗin haka ya juya "ni Na fita" "a dawo lafiya Alh, Ubangiji Allah ya tsare ka, ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah ya bada sa'a da rabo mai albarka ". "ameen Yusra nagode da addu'a Allah ya albarkaci rayuwar ki da ta yaran ki". Ya fice yaran suka rufa masa baya dan yi masa rakiya.
Kwanci tashi ba wuya a gurin Allah. Rayuwa ta nisa lokuta sun shuɗe, abubuwa da yawa sun faru, an rasa da yawa kuma an sami da yawa, Amar da Safeenah an girma, ya kammala secondary har ya sami gurbin karatu a jami'a, Safeenah ma ta kammala secondary tana jiran sakamakon jarrabawa.
Suna sami kulawa sosai, sam basu ta6a tunanin samun irin wannan gatan ba a rayuwar su, sau da yawa sukan ke6e wasu lokuta domin yin addu'oi ga Iyayen rokon su Alh Wakkala da Hjy Yusra, alkhairin waɗannan mutanen a gare su abu ne mai wahalar samu a wannan rayuwar
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *35*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Safeenah yan'mata jarrabawa ta fito harma an sama mata gurbin karatu a jami'ar bayero inda Amar yake level 1, yau itace rana ta farko da zata fara shiga jami'a, ta riga kowa farkawa a gidan, tunda tayi salla ta nufi kitchen, ta samu ma'aikatan nata kiciniyar harhaɗa break, ta saka hannun ta suka cigaba da aikin tare, kamar yadda Momy Yusra take yi.
Shida da rabi Yusra ta iso kitchen, sosai try mamakin ganin Feena da yadda ta zage take aiki, "Feena dear, ya akayi yau kika rigani tashi?" murmushi tayi tareda juyowa ta kalli Momy, tana sosa kyeya "uhum, ba komai Momyna kin san yau ne zan fara zuwa school, kuma da lecture karfe takwas zan fara, shiyasa na tashi da wuri". Dariya sosai Momy tayi "Feena ho, yarinya ta ba dai zumuɗi ba, to kawo aikin maza kije ki fara shiri dan nasan yau wankan ma na musamman za'ayi". Kunya ce ta kama ta, sumi-sumi ta ra6a Momy ta wuce, ta shiga ɗakinta kai tsaye toilet ta nufa, ta haɗa ruwan ɗumi ta shige cikin su, mintuna goma tayi tana wankan sannan ta fito, tabbas maganar Momy tayi fari domin yau komai na musamman tayi, bayan kwalliyar ma takai mintuna talatin tana canje-canjen kaya duk wanda ta saka sai taga kamar basu mata kyau ba ta cire, haka Momy ta shigo ta same ta duk ta cika gadonta da kaya, "ikon Allah". Momy ta faɗa tana kallon Safeenah, "wannan kuma miye Feena?" "yauwa Momy pls zo ki taya ni za6a, na rasa kalar kayan da zan saka, pls Mom". Momy tayi murmushi "lallai yau naga yar jami'a, Feena tun ba'a shiga ba?" tayi dariya ta rufe fuskar ta da tafukan hannunta "Momy bazaki gane ba, kin san ina bin yaya wasu lokutan, wlh baki gani ba yadda yan'jami'a suke kure wanka".
"To naji zo ki gani" ta kama hannun ta ta zaunar da ita tukunna, sannan ta shiga duba kayan dake baje bisa gadon, can ta hango wani swiesless red colour, mai kananan flowers, masu kalar milk ta ɗauko shi ta bata, "ki saka wannan na tabbatar zai amshi jikinki". Ta kar6a da sauri tana godiya, "thanks Mom" ta manna mata kiss a kumatu, Yusra tayi dariya tana girgiza kai. Da kanta ta ninke ragowar kayan da Feena ta fitar ta mayar dasu cikin wardrobe ta rufe, ta bar ta nan tana saka kaya.
Saida suka kusa kammala break sannan ta fito, cikin takun nan nata na kasaita ta sakko daga upstairs, tare suka maida hankalin su gareta, Amar da Momy kenan, suka zuba mata ido kamar yau suka fara ganin ta, saida ita iso inda suke sannan suka iya ɗauke mata ido, kowannen su da abinda yake ji a ransa. Ita dai Yusra kallon tsaf takewa Feena dan ganin yau ta fito ita sak, a lokacin da take budurwa kamar haka take ba ba wani bambanci. Shi kuwa Amar kallon da yake mata na daban ne dan tunda take ado bata ta6a yin wanda ya fitar da ita kamar wannan ba, kayan sun kama jikinta sosai sannan sun bayyana kuruciyar ta ainun, tsayayyar budurwa yar shekaru ashirin cif-cif, fuskar nan tata ta shimfiɗu da rantsattsiyar kwalliyar ta, kayan jikinta ɗinkin doguwar riga ne fited gown sai takalmi da hand bag ɗinta milk colour haka siririn mayafinta ma, ɗaurin ɗankwalin ya zauna ɗan tamkar anan aka halicce shi.
Ji yayi sassan jikin sa sun yi sanyi, zuciyar sa ta dugunzuma, ya rasa gane gabanta dangane da kwalliyar Safeenah, shin daɗin ganinta yaji ko akasin hakan?. Ita ce ta katse masa tuna ni da zankaɗeɗiyar muryar ta, tana faɗin "badai har Dady ya fita ba?". "hmm Feena manya, kin kuwa san lokacin da kika 6ata kina shiri?". Momy ta tambaye ta, sai taji kunya ta kama ta. Amar kam bai sami damar yin magana ba sam ya kasa gano yanayin da yake ciki.
Zungurar shi tayi bayan ta zauna, tana faɗin "barka da safiya Yaya" "yauwa barka dai Feena kin tashi lafiya?" tayi murmushi "lafiya lau, amma Yaya baka ce nayi kyau ba" tayi maganar tana zun6uro baki, "ni na isa, ai dama jira nake ki zauna in tambaya any ba canjin fuska kika yi ba?" yayi maganar yana murmushi. Momy ta ka6i maganar sosai kuwa Amar ni kaina ina tantama, yau sai naga fuskar kamar tawa. Dukkan su suka yi dariya
Sama-sama tayi break ɗin, cike da zumuɗin zuwa makarantar tana yi suna mata dariya, da haka har ta kammala ta kira Uwani mai dafa musu abinci tace ta kawo mata abinda suka yi, ba jimawa ta dawo ɗauke da leda babba a hannunta ta bawa Safeenah, ta kar6a tayi godiya suka mike, suka yiwa Momy sallama suka fita, ta bisu da kallo cike da sha'awa.
Tafe suke tana zuba masa hira da tambayoyi, waɗanda ya kasa amsa mata ko ɗaya, saboda tsantsar takaicin da ya tsinci kansa daji gameda shigar da tayi, shi kansa ya kasa gane kansa yau ne rana ta farko da ya fara jin ciwon kar wasu su kalleta, saboda tsantsar kyawun da tayi, musamman a sanin da ya yiwa jami'a akwai da yawa waɗanda basuda aiki sai kallon kyawawa irinta, wasun ma har da tanka musu suke.
Dogon tsaki ya ja lokacin ya dai-daita tsayuwar motar a harabar makarantar, da sauri ta kalle shi "Yaya lafiya?" saida yayi ko'karin dai-daita nutduwar sa sannan ya kakaro wani murmushi da bai wuce le6en shi ba, yace "ba komai, wani malami na tuna ɗan tsurku ne, shi zai ɗauke mu anjima". Tayi dariya "lallai Yaya an zama yan gari, a malaman ma har da yan tsurku".
Bai tanka mata ba, sai dai dariyar yaken da yayi mata, suka buɗe kifofin motar suka fito, fuskokin su ɗauke da yalwataccen murmushi, ita dai Safeenah murmushin farin ciki take da murnar ranar ta ta farko a jami'a, shi kuwa Amar yana yi ne dan karta gano halin damuwar da yake ciki.
Haka suka tsatsa cikin makarantar hannayen su sarke da na juna, suna tafe tana zuba shiko yana binta da murmushi. Sannu a hankali yan'matan dake kai koma a tsakiyar makarantar suka fara maida hankalin su akan kyawawan matasan, yayinda da yawa daga cikin su suka raina kansu, suka kuma tabbatar da dalilin Amar na rashin sake fuska