Showing 6001 words to 9000 words out of 48171 words

Chapter 3 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4641




Yaron yabi plet d`in abincin da kallo har cikin zuciyar shi yana son abincin tabbas yanajin yunwa bama kad`an ba sai dai Sam ba zai iya cin abinci ba Feena ba. Ya d`auke kanshi daga kallon abincin ya mayar da ganinshi ga yar'uwar shi, cikin tausasa murya yace wa Hajiyar "nagode amma bazan iya cin abinci babu ita ba








*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *9*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍






Dr. ce taja hannun Yusra suka fice tana cewa yaran "muna zuwa" kai tsaye office d`inta suka nufa. Bayan sun zauna ta kalli kawar ta'ta tace "kawata nima fa yaran nan sun fara burge ni, shin kin sami jin wani labari game da su?" Hajiya Yusra ta muskuta ta gyara zamanta fuskarta d`auke da mayalwaci murmushi tace "naji komai game da su kawata su d`in marayu ne kuma daga kauye suka zo wahala ce ta fiddo su, nan ta bayyana mata duk yanda Amar ya gaya mata ta, daga karshe tace "in takaice miki labari dai yanzu nima na sami ya'ya Allah ya bani masu d`ebemin kewa" tana fad`in hakan kwalla suka cicciko daga idon ta, taja gefen gyalenta ta share hawayen. Dr.Batul ta d`an harare ta kinga matsalarki Yusra dan Allah ki daure ki manta baya ki fuskanci gaban rayuwar ki, kisani abinda ya faru akan ki rubutacciyar kaddara ce kuma jarrabawa ga rayuwar ki data Alhajin duka kiyi hakuri kinji kawata".




Hajiya Yusra taja numfashi cikin kuka mai sauti da rawar murya tace "nasani Batul kawai tunani nayi da ya'ta tana nan da yanzu itama ta girma, ba mamaki ma da takai wannan yarinyar" tausayin ta ya kara lullube Dr. Tace "hakane Yusra a wannan shekarar ne yarki zata cika shekaru takwas ko a mace ko a raye" itama dai hawayen ne suka silalo mata domin tausayin kawar ta'ta da tuna baya da sukayi. Shiru ta ratsa office d`in na wasu yan dakiku




Dr. ce ta kauda shirun da cewa "bari muje mugani ko sun kammala cin abincin", sai da ta tashi sannan ta mikar da kawar ta'ta tsaye tissue ta yago daga kan table d`inta ta shere mata hawayen fuskar ta, sannan taja hannun ta suka fice daga office d`in tana cewa "ki aika yaron can ya siyo musu Kayan sakawa akwai a wajen asibitin nan zan saka ayi musu wanka su canza kafin Ku tafi gida". Hakan kuwa akayi kafin su shiga d`akin ta kira Emanuel tace "yaje ya siyo kayan sakawa kwatancin na yaran nan da muka zo dasu na mace da namiji" duk da harshen turanci take masa maganar ya amsa da "yes maa" ya juya ya fice da sauri




Koda suka shiga d`akin sai suka tarar Safeenah tana ta tari Amar ne keta faman bubbuga kanta yana hura mata iskar bakin shi a ka, da sauri Hajiya Yusra ta isa gare su ta kama yarinyar tana girgizata "Amar meya sami Safeenah?" Yusra ce tayi wannan maganar cikin kid`ima da rud`ewa. Yana zubda hawaye ya nuna mata robar lemun cock data basu yace "wan can abin tasha shine ta kware ta dinga tari" Dr tayi murmushi ta kalli Safeenah wadda zuwa lokacin tarin ya lafa mata tace "ayya rashin sabo ne inaga da karfi kika zuki lemun, sannu kinji" Safeenah ta gyad`a kai kawai dan bakaramin zafin abin taji a makogoro da kwakwalwar ta ba.




Duk abin nan da taji kuwa bai hanata d`aukar robar ta karashe sauran daya rage na saboda taji dad`in abin sosai. Sai dai wannan karon a hankali ta dinga kurba har ta shanye shi Tass dai-dai da shigowar nurses d`in da Dr ta kira. Da shigowar su tayi musu umarni da suyiwa yaran nan wanka yanzu. Ai kuwa ba bata lokaci d`ayar ta ja hannun Safeenah tana mata yan wasanni tashige toilet d`in d`akin da ita, sai da ta cire mata kaya sannan ta kara tsinkewa da yawan dettin dake jikin yarinyar "ya Rabbi" ta fad`a tana kallon fuskar Feena wadda ita kanta fuskar a dankare take da tarin dettin balle kuma uwa uba wato kan yarinyar wanda duk ya cukurkud`e ya cure guri d`aya sai kace abinda aka sakawa ruwan gam kan tarin dattin dake cikin shi, ai nurse kam kasa jurewa tayi sai da ta leko d`akin ta umarci yar'uwar ta data kawo mata wani sabulu mai karfi da man wanke kai










*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *8*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍








Hajiya Yusra ta kurawa yaron ido cike da mamakin kalaman sa, sai kuma taji tausayin shi ya kama ta, wannan wane irin So ne yake yiwa kanwar shi? ta maida kallon ta ga Safeenar wadda har yanzu bacci takeyi baccin da ba wanda yasan lokacin da zata farka tamatsa daf da Amar ta dafa kafad`arshi ta sanyaya muryar ta tace "yaro ka daure kaci abinci ba abinda zai sami kanwar ka data farka itama zan bata nata kaji" sai a lokacin ya daga kai ya kalli Hajiyar yace "kiyi hakuri Umma tunda muka taso haka muke ban taba cin abinci babu ita ba haka itama tare muke cin komai randa bamusamu ba muyi hakuri, rashin lafiyar ta bazaisa in karya wannan dokar ba zan jira ta na kowane lokaci indai har zata farka" ya karasa maganar lokacin da wasu sababbin hawaye suka gangaro daga idon shi. Tausayi al'ajabi da sonjin labarin yaran suka dirarwa Hajiya Yusra lokaci d`aya ta rungume Amar itama hawaye na bin kuncin ta




tace "yaro gaya min sunan ka da kuma wani abu gameda Ku Wato labarin Ku hakika zan taimake Ku da duk abinda nake da shi" ta raba jikin ta da nashi ta zuba mishi ido tana sauraren ji daga gareshi. Shiru yayi na lokaci mai tsayi wanda har sai da Hajiyar ta fara cire rai da zaiyi magana can ya sunkuyar da kansa kasa yace "Suna na Amar, kanwa ta kuma Safeenah, daga kauye muka zo kuma mu marayu ne Abba da Ummar mu duka sun rasu a hannun Ba'ba Larai muke kishiyar Mahaifiyar mu........**************************


Nan dai Amar ya kwashe kaf Abinda ya sani ya gaya mata har dalilin daya rabo su da gida da yadda suka tsinci Kansu nan bai boye mata komai ba sai labarin asalin Safeenah Wanda yayiwa kansa alkawarin bayan shi ba wanda zai koma sani, domin guje mata tsana da hantara irin wadda ba'ba Larai tayi mata zai ci gaba da kasancewa Yayan ta Uwa d`aya Uba d`aya


Hawaye ne sharkab a kan fuskar Hajiya Yusra wasu na ture wasu hakika labarin rayuwar yara biyun ya girgizata ya kuma kara nunka tausayin da take musu a ran ta, Rayuwa kenan ita a nasu gidan neman haihuwar suke ruwa jallo amma ta ga'gare su ga wasu Allah ya basu suna neman hallakawa. Sake rungume Amar tayi a karo na biyu wannan karon kukan ta hadda sauti cikin kukan tace "Allah yajikan Mahaifiyar Ku Amar, hakika kuna cikin garari da matsin Rayuwa amma inaso daga yau kai da kanwar ka kudaina kallon kanku a matsayin marayu" Amar ya d`ago da sauri ya kalli fuskar Hajiyar ta gyad`a mishi kai "eh daga yau Ku ba marayu bane kunada Uwa kuma kunada Uba, Amar nice Ummar Ku Abban Ku kuma yana gida" Amar ya kalleta zuciyar shi cike da farin ciki damashi tunda ta d`auko su yaji hankalin shi ya kwanta da ita. har ya bud`i baki zaiyi magana sukaji an ce "Umma?"




Tare suka juya ga mai maganar Safeenah ce wadda tun d`azu ta farka tana kallon su kuma tana sauraren su. Cikin sakin fuska Hajiya Yusra tace mata "eh Umma, zaki yarda ki d`auke ni a matsayin Umman ki?" Feena ta washe baki"eh Umma" dad`i ya lullube Hajiya Yusra ta shafi fuskar Safeenah tace "na gode ya'ta, ya kike jin jikin naki?" Amar ma goshin ta ya dafa yace "ya kikeji yamzu?" Murmushi tayi musu tace "dad`i nakeji sosai yau nasami Umma, yanzu ba abinda yake min ciwo" sai kuma ta marairaice fuska tace "sai dai har yanzu inajin yunwa" ta kalli Hajiya Yusra tace "Umma zaki dinga bamu abinci?" Hajiyar tayi murmushi tace "duk irin wanda kike so kuwa" Safeenah taji dad`in maganar ta kara fad`ad`a murmushin ta tace "na gode Umma" Da waya Hajiya Yusra ta kira kawar ta Dr Batul ta shaida mata farkawar yarinyar, ba jimawa kuwa ta shigo ta cire mata Karin ruwan sannan ne Hajiya taja hannun su duka biyun takai su toilet ta wanke musu hannayen su suka fito tare. Wani Capet Dr ta bata ta shimfid`a musu tsakiyar d`akin suka zauna, ta bud`e musu abincin nan da tasa aka siyo musu ba musu suka fara ci fuskokin su cikeda annuri da murnar samun abinda suke so, lafiyayyen abinci wanda basu taba koda ganin irin sa ba. Sai dai hakan bai sa su sauri ko ribibin cin abincin ba, a hankali suke ci dukda da hannu suke cin abincin bai hana tabashi a baki ya bata ba


Haka Hajiya da Dr. suka saka su gaba suna kallo cike da mamakin irin kaunar da suke wa junan su, Hajiya Yusra a ranta ta jinjinawa duk Uwar data haifi yaran nan, dan had`a kan yara da koya musu son juna haka ba karamin Abu bane










*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:43 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *10*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍








Nurse d`in ta amsa da "OK" ta fita d`aukowa ba jimawa ta dawo da duka kayan da ta bukata ta kai mata toilet d`in, da taimakon yar'uwar ta'ta ta samu suka wanke kan yarinyar ya fita fess sannan suka mata wanka suka fito da ita. A lokacin Dr da Hajiya Yusra basa d`akin sun fita zaga marasa lafiya Yusra ta basu sadaka tunda Allah ya kawo ta, a kan gado suka sauke Safeenah bayan sun nannad`e ta da towel. Suka kama hannun Amar shima suka shiga dashi, daga sosai sukayi dashi akan ya cire Kayan sa a mishi wankan Sam ya ki yarda su tube shi yace musu "ni bazaku min wanka ba nariga na girma ai ni nake yin wanka da kaina a gida, harma in yiwa kanwa ta". Dakyar da rarrashi suka samu ya bari suka tobe shi suka mar wanka wanda shi d`in ma ba karamin datti aka kankara daga jikin shi ba kanshi ma yasha wanki da man da suka wanke na Safeenah domin shi d`in ma gashi ne curkus a kan nashi ba gyara ba aski. Suka gama suka fito dashi a lokacin Feena har ta fara gyangyad`i wani irin dad`i na iskar duniya dataji yana shigarta ta ko'ina ita kanta yarinyar tasan wanka rahma ne kuma ta yarda da hakan




Suka shafe su da lafiyayyun mayuka lotions sannan suka saka musu sababbin Kayan da aka siyo musu. Masha Allah Kayan d`ass a jikin su kamar abinda aka gwada, kananan kaya ne yan kanti, Kayan sun masifar yi musu kyau barimma Safeenah da take fara suka kama gashin kanta suka shafe shi da mayukan kai nan take kan ya d`au Kelli da sheki. Yarinyar ta burge nurses d`in ashe kyakkyawa ce boye a cikin detti haka suka dinga fad`a da harshen turanci d`ayar ta ciro wani tafkeken ribbon dake kanta kasancewar guda biyu ta saka. Ta d`aurewa Feena kai da shi haske da sirrin kyawunta suka kara bayyana ba make-up ba komai gashi da wanka d`aya ta bayyana yar gayu mai kyau da yalwar Gashin kai dana ido hakama gashin girarr ta baki ne sid`ik kwantacce.




Amar ya zuba mata ido ko kiftawa bayayi ganin Safeenar shi yake kamar wadda aka canza lokaci d`aya ta sauya ko lokacin da Umma ta nan tana yi musu wanka Feena batayi kyaun haka ba. Ita kanta Feena daban take jin kanta wani irin dad`i ne ya lullube ta data kalli yayan nata yayi matukar kyau kamar ba Amar mai dako ba, duk da kasancewar shi baki sai dai shi black beauty ne tare suka yi taku d`ad`d`aya suka isa ga junan su sannan cikin had`a baki wajen cewa junan su "kinyi mutukar kyau kanwa ta" "kayi mutukar kyau yaya na" sai kuma sukayi dariya jin sun fad`i Abu d`aya, nurses d`in ma dariya suka yi.




Aka turo kofar aka ahigo Hajiya Yusra ce da Dr.Batul suka dawo




*wacce ce Hajiya Yusra?*
Hajiya Yusra matashiyar mace ce yar kimanin shekaru talatin da hud`u a duniya. Farar mace ce doguwa mai dara-daran ido farare kal kamar madara kyakkyawar gaske ce mai murzajjen jiki da lafiyayyar fata, kana ganin ta kaga girman a.c, hutu da Naira, Mata ta biyu kuma abar So ga Alhaji Tijjani Wakkala. sanan ne ne kuma fitacce a ciki da wajen kasar nan, shahararren d`an kasuwa ne kuma d`an siyasa Masu fad`a aji a majalisar Tarayya. Asalin ta yar kasar saudiyya ce a wani zuwa da Alhaji Tijjani yayi can a lokacin aikin hajji anan kusada masaukin su anan gidan su Yusra yake, gani d`aya yayi mata yaji ta kwanta masa a rai gashi kuma a lokacin iyayen shi na raye kuma sun matsa masa akan ya karo aure domin tun lokacin da ya auri matar shi ta fari hajiya Ummu ko batan wata basu taba yi ba samada shekaru sha'uku, wannan ne yasaka iyayen su ke fata da burin ya kara aure dan acewar su ba mamaki matsalar daga matar tashi ne.


To Allah dai bai tabbatar ba sai a lokacin da yaga Yusra dayake lokacin ma da iyayen shi yazo bayan kammala aikin hajji yasa suka nema mishi Auren ta. Iyayen ta mutanen kirki Masu son mutane suka karbesu hannu bibbiyu kuma suka bashi Auren ta, basubar kasar ba sai da aka d`aura Auren aka danka mishi matar shi suka dawo Nigeria tare da rakiyar yayun ta maza biyu da kanwar Umman ta.




Kwatsam sai Hajiya Ummu taga Alhaji ya dawo da Amarya balarabiya ai kuwa sai da hankalin kowa ya tashi a gidan ta dinga hauka da zage-zage bata bar kowa ba. Amma ya ta iya da ikon Allah dole ta hakura ta rungumi kaddara, Amma tasha jinya har asibiti sai da ta kwanta saboda Karin Auren










*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:44 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *11*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍








Ta yarda Auren Hajiya Yusra da Alhajin ta kaddara ce amma tace "har abada bazata taba d`aukar Yusra a abokiyar zama ba sai dai kishiya, kishiyar ma abar ki. Haka dai Alhaji ya tursasata zama da Yusra dole sai dai ba zaman lafiya kullum cikin cemini-cemini da neman fitina take dayake ita Yusrar ba fitinanniya bace bata kula ta gashi kuma a lokacin batajin Hausa dayawa mugayen maganganun da Hahiyar ke jifanta dasu batasan me take cewa ba sai dai wad`an da ta fad`a da harshen turanci dan itama hogaggiyar yar'boko ce kuma yar'siyasa ma'aikaciyar gwamnati. Haka Rayuwa ta tafi musu cikin yanayi na zaman doya da manja. Hahiya Yusra bata ciki watanni uku a gidan ba Allah ya bata ciki ai kuwa nan hankalin Hajiya Ummu yayi masifar tashi, duniya tayi mata zafi tace ina wuta ta fad`a? Haukacewa ne kawai batayi ba. Alhaji da iyayenshi kuwa farin ciki ne mara misaltuwa ya mamaye zukatan su abinda ko a mafarki nemanshi yake yau gashi Allah ya bashi murna ya hau yi da ririta Yusra wadda ita abin har kunya yake bata




Yayi bari da dukiya bayin Allah sunsha sadaka a dalilin samun wannan cikin a gidan Wakkala ma tawakkali ga Allah Rabbi, kirarin Alhaji Tijjani Wakkala kenan. Haka sukayita renon cikin cikin marari da tsantsan so da kauna a lokacin Alhaji Tijjani ya d`auki son duniya ya d`orawa amaryar shi da abinda ke cikin ta, Wanda a bangaren Hajiya Ummu babu abinda ta tsana a duniya sama da su, neman hanya take wadda zata samu ta hallaka su kota halin ka'ka amma bata samu ba. Bakin cikin duniya ya ishe ta


Iya mahaifiyar Alhaji da kanta ta tare gidan domin kulada Yusra da cikin ta sai nan-nan ake da ita har Allah yasa cikin ya isa haihuwa ranar wata assabar biyu ga watan August na wan nan shekarar Yusra ta haifo santaleliyar yar'ta mai d`iban kama da ita tubarkalla haka duk Wanda yayi arba da jinjirar ke fad`i


Kwanaki uku da haihuwar yarinyar iyayen Yusra da yan'uwa na saudiyya suka iso ga sanin Alhaji na kusa dana nesa sun fara hallara gida ya fara ciki ya kacame da yan'uwa da abokan arziki masu zuwa ganin baby. Hakan yasa aka warewa yarinyar d`aki d`aya na musamman saboda hayaniyar mutane mutum uku ne ke kula da ita mata duka Yan aikin gidan Amma dayake ance mai son abinka ya fika dabara sai da Hajiya Ummu ta kulla tuggun da ta saka wata shakikiyar kawarta Eysha ta sato mata babyn tace "Eysha wannan ita ce abar danafi tsana a rayuwata domin duk sauran Masu sauki ne, ki tafi da ita nesa da garin kano sannan ki kashe ta ki jefar da gawarta karnuka su cinye"




Eysha rikakkiyar karuwa ce yar maye amma hakan bai makanta zuciyar ta da har xara iya yin kisa ba, ta amsawa Hajiya Ummu da "to" ta fice da yarinyar a sace. Kasan cewar mutane Yan barka da sukayi yawa a gidan yasa tsaro yayi rauni a gidan ba Wanda ake bincike




Bata zame ko'ina ba sai tasha ta hau motar sokoto da Tatar ana jiran mutum d`aya, da suka iso sokoton ma sai da ta nemi motar wani kauye ta hau domin sirranta abinda tayi nufin aikatawa. Saida taga motar takai wani karamin jeji inda ba yawan mutane sai dai tana hangen wani karamin kauye daga nesa tasa motar ta ajiye ta a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login