Showing 39001 words to 42000 words out of 48171 words
Chapter 14 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
taya su da addu'a amma muddin aka aurar da ɗayan su za'a sha fama musamman ita Feena da take mace ɗaukar ta za'a yi a kai ta wani guri."
Alhj ya sauke numfashi domin ya gano inda maganar matar tasa ta nufa abinda ta faɗa gaskiya ne sai dai su dage da addu'ar neman sauki daga Allah.
Amar da Feena kam suna fita garden suka nufa a can suka baje suna ja'jantawa juna abinda ya faru, yana bata hakuri tana bashi yana mata alkawura itama tana mishi wanda duk dai akan kula da ita ne da kuma yin duk abinda take so.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da gudana. Kamar yada ya kudurta a ransa tun daga ranar ya bar Jidda da shirginta tayi waya tayi aike tayi zuwa da kanta duk a banza. Karshen ta ma har gurin Momy ta zo kamun kafa amma ba'a dace ba Momyn kanta hakuri ta bata dan bata san yadda zata yi ta tilasta Amar ya so ta ba.
Bisa dole ta bar shi ba dan ranta na so ba.
Tun daga lokacin ya fara gwagwarmaya da rayuwa, ga karatu ga takurar da Dady yake masa akan lallai ya fito da mata ya masa aure domin su a ganin su kasancewar shi da Safeenah a koda yaushe shi ne ya hana ita ma ta samu saurayi ko mijin aure. Sai dai abinda basu sani ba shi ne ko a school masoyanta ba zasu kirgu ba. Ita ɗin ce dai bata basu fuska balle su sami damar furta mata abinda ke ran su. Hujjarta kuwa ita ce bata son aure tunda ta ji ance idan aka aurar da ita ɗaukar ta za'a yi a kai ta gidan wani har ma ana cewa zata rabu da kowa harda yayanta wannan kenan.
Duk wata budurwar da ya fara nema da zarar ya je da Feena ya gabatar da ita da kuma dokokinsa akan ta sai lamarin ya lallace, wasu yan'matan har bakaken maganganu suke ya6a masa. Haka zaka gansu kullum indai aka je da Feena gun budurwa to da Kuka take dawowa. Abin yana damun ta sosai ganin yayan nata ya gagara samun macen da zata so shi ta so kanwarsa.
Momy kam nata ido ne, domin bata san wani abin yi da wuce addu'a ba.
(ni kuwa Nasmat cewa nayi "kuruci dangin hauka" lolz)
*************************************
Yau gidan Alhj Tijjani Wakkala an tashi cikin farin ciki da kuma jimami domin safiyar yau ta kama ranar zagayowar shekarar haihuwar 6atacciyar yar su wato (Baby). Bikin da basu ta6a tsallake shekara ba'a yi shi ba. Sai Shirye-shirye suke an gama gyare gidan tsab. Momy da Dady su tafi ɗauko Ummy da yan rakiyar ta airport. Amar kuwa yana can da masu decoration suna karasa gyara ɗakin na Baby inda ake gudanar da birthdayn. Feena kuwa tuni ta gama shirin ta cikin haɗaɗɗiyar gwon ɗinta red color gashi nan yasha gyara an tufke shi guri ɗaya an ɗaure shi da wani tafkeken band shima red ne haka takalmin dake kafarta da pos dinta ma red color ne. Budurwar ta fito shar da ita, a hankali ta taka zuwa gaban mudubi kai kace ɗanyen fure ne ke rausayawa. Tsayuwa tayi tana karewa kanta kallo kafin daga bisani ta saki wani lallausan murmushi, ita kanta ta San ta haɗu.
Cikin zumuɗi ta juya ta nufi ɗakin yayanta, ta shiga da sanɗa tana waige-waige kamar 6arauniya ta buɗe wardrobe ɗinsa sannan ta tsuguna can kasa ta lalubo ɗaurin sarka nan da yace Umma ta bata ita.
Wani irin daɗi da farin ciki ne suka lullu6e ta a lokacin da idonta suka yi arba da rantsatstsiyar sarkar zinarin, mai tsananin haske da sheki. Hannunta har rawa yake gurin sakawa tun kan yayanta ya gani tana tsoro kar ya hana ta sakawa. Sai da ta gama saka sarkar sannan ta matsa gaban madubinsa ta kalli kanta, duk da cewa sarkar ta ɗan matse wuyanta hakan bai hana bayyanar kyawun da sarkar tayi mata ba. Ta zauna ɗas! Sai taji tunda take saka sarka ma bata ta6a saka wadda ta ka6e ta kamar wannan ba. Ta ɗora hannunta bisa sarkar tareda lumshe idonta, a fili ta shiga kwararowa Ummanta addu'ar neman rahmar Allah da jin kansa.
"Ameen ya Allahu" ta ji an amsa addu'arta a bayan ta. Da sauri ta buɗe idonta. Karf! Ta sauke su a nashi, Amar ne jingine da kofar ɗakin ya harɗe hannayensa fuskarsa ɗauke da murmushi. "Kin yi kyau kanwata." ya faɗa a sanyaye. Murmushin ta mayar masa tana kallon sarkar tace "kayi hakuri Yayana naga kamar baka so in saka kyautar Umma." da sauri ya girgiza kai "ni na isa?, wannan fa ba kyauta Umma ta baki ba, taki ce ta kanki inji Umma." ta kalle shi cikin rashin fahimta. Da sauri ya dawo hayyacinsa ya kuma fahimci su6ul da bakan da yayi. Sai yayi hanzarin kawar da maganar da cewa "zan shiga wanka, fiddo min kayan da zan saka." ya shige bayin da sauri.
*Nasmat* ✍
[1/10, 5:30 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *46*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
Murmushi tayi tana kallon kofar toilet ɗin kafin ta girgiza kai ta nufi wardrobe. Kayan da zai saka yau sababbi ne na musamman suka siyo kamar yadda suke yi a kowace shekara. Tana cikin fesawa kayan turare ne taji tsayuwar motoci a harabar gidan na su, hakan ne ya tabbatar mata da isowar bakinsu. Wato Ummy da tawagarta. Da gudu ta fice daga ɗakin ta nufi harabar gidan tana tsalle da ihun murna zataga yar tsohuwa Ummy kamar yadda take kiran ta, dattijuwar da take ji da kaunarta har cikin ranta.
Ummy ma ta kagu taga Safeenarta hakan yasa ta saki fara'a a lokacin da ta hango ta ta nufo inda suke da murna. Ummy ta saki hannun jikinta Sagir ta rungume Feena cike da farin cikin ganin ta. "Oh wannan yar' haka kika kara nauyi? To sake ni kar ki yadda ni." inji Ummy cikin raha da wasa. Feena tayi dariya tana ko'karin raba jikinta da na Ummy tana faɗin "naci beta ne, kin san fa Momy da Dady ba karamin daɗi suke bani ba..." ciwon da taji a wuyanta ne ya hana ta karasa maganar cikin daɗi, sai ta karashe da faɗin "...wash!" tana rike wuyanta. Ummy tayi gaggawar rike ta a jikinta dan kar ta ji ciwo saboda sarkar wuyanta ce ta makale a jikin babban mayafin na Ummy. A hankali ta fara ko'karin cire sarkar Safeenah na aikin wash! Wash! sai dai cikin rashin sa'a sarkar ta tsinke kat!
"Innalillahi! Wa inna ilaihiraji'un." Feena ta faɗa da karfi cikin kwalalo ido waje, kafin ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka. Abinda ta bawa su Dady matukar mamaki. Ta tsuguna ta ɗauki rabin sarkar da ya faɗi kasa ta fara ko'karin haɗa su tana sharar kwalla tana faɗin "shikenan sarkar da Umma ta bani, yau na fara sakawa gashi ta tsinke." Momy ta sauke numfashi tana faɗin Allah ya shirye ki Feena wlh kin tsorata ni wacce irin sarka ce wannan?" a sanyaye ta Mike tana nuna musu sarkar da yadda ta zama. Tana sharar hawayen tana cigaba da cewa "ban ta6a sakawa ba sai yau tunda nake"
Ummy da Momy suka kaiwa sarkar cafka a lokaci ɗaya ko waccen su ta zari rabin suka kura mata ido suna nazarin sarkar da abinda suke so su gano game da ita.
Kamar haɗin baki tare suka ɗago kai idanunsu kan Feena, gaba ɗaya jikinsu rawa yake yana karkarwa bakunansu na motsi amma duk sun gagara furta komai. Al'amarinda ya jefa Dady da Feena da matar yayan Mommyn cikin ruɗani. Dady ya matsa kusa da su ganin hawaye sun wanke fuskokin uwa da yar', yace Ummy lafiya kuwa me ya faru ne?" Ummy ta kasa magana tamkar wadda aka zukewa jini haka ta silale zata zube kasa sarakuwarta tayi gaggawar riko ta tana faɗin "subhanallahi Ummy" Alhj ya kara ruɗewa yace ta shiga ciki da ita. Momy Yusra ta fashe da kuka ta kara kankame ragowar sarkar dake hannunta ta fuskanci Safeenah bakinta na rawa hannayenta na karkarwa ta buɗi bakin dakyar tana faɗin "Feena! A ina kika samu sarkar nan, wacce ce Umman da ta baki wannan sarkar?" tsoro da firgici suka kara kama Safeenah ga tashin hankali da ta ga iyayen nasu sun shiga. Ta gagara magana ita kanta jikinta kyarma yake. Momy duk ta ruɗe ta fita hayyacinta ta koma baya ta cakumo rigar Dady tana girgiza shi "habibi sarkar Baby ce, sarkar da Ummy ta sa aka buga mata a lokacin haihuwarta." Dady ya zamo ido yana kallon Yusra cike da tantama bakinsa ya kasa furta komai. "wlh ita ce habibi, dan Allah ka tambayi Feena ta gaya mana inda ta samu." Wani sabon kuka ya su6uce mata.
Dady ya nufi Feena dake gefe ta zubawa sarautar Allah ido. Ya kama hannayenta duka biyu ya rike a nashi "ya'ta Safeenah ki taimake mu ki gaya mana ina kika sami wannan sarkar?" ganin hawayen Dady ya kara tashin hankalinta. Haka sauran manyan malaman nan biyu suma hawayen suke ganin halinda Yusra da Alhj suka shiga suka isa gaban Feena babban ne ya fara mata magana "haba yar nan ki yi magana mana, ki taimaka ki gaya musu inda kika same ta sarkar tasu ce ta yar'su ce data 6ata."
Tirkashi! Nan fa ɗimuwa da kiɗima suka kara kama ta. Ta fara ja da baya tana girgiza kai, zasu sa zuciyarta ta buga akan abinda batada masaniya a kai. Kanta har wani juyi yake ta juya da gudu ta koma cikin gidan tana kwalla wa yayanta kira. A falo suka yi kici6is da shi yana tsaye a kan Ummy dake kuka kamar ranta zai fita tana rokon shi ya gaya mata inda suka sami sarkar nan da ke wuyan Safeenah.
Tana zuwa ta rungume shi cikin tsananin kuka ta fara magana "yaya dan Allah ka gaya musu sarka ta ce da Umma ta bani, suna nunawa kamar sun San sarkar har suna cewa sarkar Baby ce yaya pls ka yiwa Dady da Momy bayani." dai-dai nan su Dady da suka biyo bayan Feena suka shigo, fuskar kowannen su sharkaf da hawaye. Suka saka Amar gaba wanda hankalinshi ya gama tashi zuciyarshi ta shiga kai komo. Bakinsa na son magana amma ya rasa me zai furta, su Dady suna son sanin gaskiya game da sarkar ta yaya zai iya furtawa a gaban Feena ya gaya musu cewa ita ɗin yar'tsintuwa ce?
Yana cikin wannan halin ne yaji an tsuguna an kama kafafun shi, ruwan hawayenta na kwaranya bisa takalminsa. Cikin matsanancin tashin hankali ya yi gaggawar ɗago ta da hannayensa ya fashe da kuka yana faɗin "a'a Momy daraja da kimar ki sun wuce hakan, kin fi karfin komai a gurina Momy zan gaya miki zan sanar daku abinda ban ta6a sanarwa kowaba, abinda na sirranta yau zai bayyana. Na tabbatar kunada alaka da labarin nan." ya sulale ya zube kasa a inda yake tsaye haka Feena ma domin tana manne da shi, ji yake tamkar an zare masa duk wata laka dake jikinsa. Gaba ɗaya suka zuba masa ido cike da kaguwa ta jin abinda zai faɗa gameda sarkar Baby...
*Nasmat* ✍
[1/10, 7:41 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
........... *JA'JIRTACCE*....... *47*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_____________________________________
©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
Feena ta yi zurum tana yiwa Amar wani kallo wanda bata ta6a yi masa ba dan a zamnta da shi bata ta6a ganin yana shar6ar kuka haka ba.
"Wannan sarkar ta Feena ce. Kamar yadda Ummata ta sanar mini." yayi shiru yana jan numfashi kafin ya cigaba... "Feena ba Kanwata bace kamar yadda kuke tsammani." alamun mamaki karasa suka bayyana a fuskokin ilahirin mutanen dake wajen musamman Safeenah wadda ta kara gwale ido numfashinta na zariya kamar zai kwace ya fice daga gangar jikinta. Babu wanda ya sami damar yin magana saboda tsananin mamaki hakan yasa Amar cigaba da magana.
"Kamar yadda Ummana ta gaya min tsintar Feena suka yi a gefen hanya ita da Abbana, a lokacin Feena na jinjira wadda bata wuce yan kwanaki da haihuwa ba...
******************************
Kaf Amar ya kwashe labarin rayuwar su da Safeenah a kauye har barowar su gida ya gaya masu har izuwa lokacin da Momy ta gansu ta taimake su ta ɗauko su.
Ya ɗora da cewa "na cigaba da kasancewa yayan Safeenah ne saboda guje mata tsangwama da kyara bana so a koma ce mata yar tsintuwa balle har a kwatanta ta da shegiya. Dama Umma ta faɗa cewa ba mamaki wannan sarkar ta zamo silar gano asalin iyayen Safeenah, Allah ya jikan ki Umma yau ga iyayen Feenarki sun bayyana, Allah ya faranta iyayen yar' amanarki Umma."
Ya ɗago manyan idanunsa da suka sha kuka ya kalli su Dady da Momy harma da Ummy yadda suka yi jage-jage da kuka yace "in dai wannan sarkar yar' ku ce to ba makawa Safeenah ita ce yar' ku Baby." Dady da Momy a tare suka tankwashe kafa suka yi sujjadu shakur, suna Kuka suna rera kirari ga Ubangijin talikai gagara misali suna godiya ga Allah tareda kara sallamawa karfin iko da adalcin Ubangiji ga bayinsa masu gaskiya.
Ummy ma ba'a barta baya ba saida ta ɗaga hannayenta sama ta godewa Allah. Dady ya juya ga Safeenah wadda tunda Amar ya fara bada labari a kanta take sandare tamkar gangar jikin da babu rai a cikinta.
Janyo ta yayi ya rungume ta tsam yana sauke numfashi yana cewa "lale marhabin da bayyanar ki gareni Safeenah, ya' ta gudan jini na Baby muna kaunar ki. Rahamar Ubangiji taje ga kabarin uwar da ta rene ki Allah ya jikan wannan baiwar tashi yasa aljanna ta zamo makomar ta." "ameen" inji Amar yana matse kwalla.
Yau kam duk wani lungu da sako na zuciyarsa a cike yake tam da farin ciki, ga Safeenah ga asalin iyayenta. Ba shakka ya taya ta murna na kasancewarta ya' daga tsatson Momy da Dady nagartattun mutane waɗanda suka san darajar ɗan adam, suka san mutunci mutane waɗanda basu ɗauki abin duniya a bakin komai ba. Feena kam shiru take a jikin Dady wanda tunda ta fara girma baya ra6ata da jikinsa har yanzu bazata iya rarrabe halin da take ciki da mafarki ba, jira kawai take ta farka.
Momy ta janyo guiwar ta ta haɗa Safeenah da Dady duka ta rungume su wani irin sanyi da daɗi ne ya ratsa zuciyarta ta lumshe idonta hawayen farin ciki na cigaba da kwaranya. Tace "Allah bai sanar da ni gaibi ba amma tsananin kamar da nake yi da Safeenah na matukar bani mamaki, na daɗe ina nazarin abin a raina haka kawai sai inji kamar ku ɗin ya'ya na ne waɗanda na haifa da cikina."
Dady ya kar6e da cewa "Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin raba mu da ke, gashi ya dawo mana dake mun rene ki da hannunmu, godiya ga Allah da ya bamu ikon tarbiyantar dake bisa turba ta gari. Ya Allah kai ne kayi wannan shirin Allah mun gode maka." Aunty Sumayya matar uncle Al'ameen ta share hawaye ta kara saita wayar hannunta wadda tunda aka fara badakalar take ɗaukar su video. Ummy ta muskuta cikin tsananin farin ciki tace ku sako min jika ta nima in rungume ta." suka yi murmushi cike da jin daɗi suka sake Safeenah, Ummy ta ware hannayenta tana murmushi tace "zo nan jika ta." ba yadda ta iya haka ta tafi ta rungumi Ummy. kamar dai hoto haka aka rika sarrafata sai dai har yanzu ta kasa furta koda kalma ɗaya.
Zuwa yanzu ta gama tabbatarwa kanta cewa ba mafarki take ba, wannan al'amarin na zahiri ne. A duk sanda ta kai dubanta ga Amar sai ya sake mata murmushi, kawai sai ta fashe da kuka al'amarinda ya bawa dukan su mamaki.
Da sauri Amar ya matsa daf da ita ya riko hannunta a'a kanwata yau ba ranar kuka bace godiya zaki yiwa Allah da ya bayyana miki asalin iyayenki na gaskiya. Ki godewa Allah Feena iyayenki na son ki ki kalli yadda suke tafiyar da rayuwa cike da so da begen ki dukda bakya tareda su, kullum addu'oi suke a gare ki. Zukatansu na cike da jimamin 6atan ki. Ashe kina tare da su a kowace shekara ke kike wakiltar Baby a wannan bikin na zagayowar shekarar haihuwar ta she ke ce ita. Ashe sunanki kike amsawa, ashe bikin ki ake Safeenah ki godewa Allah iyayenki mutanen kirki ne Masu zuciyar taimakon marasa gata da badan haka ba da baki dawo garesu cikin sauki haka ba."
Ta juya da sauri ta rungume shi tana kara tsananta kukanta cikin kukan ta fara magana "yaya dama kasan ba uwa ɗaya uba ɗaya suka haife mu ba amma baka ta6a gaya min ba? Yaya kai ɗin na daban ne ban ta6a jin cewa kai ba jini na bane soyayyar uwa da uba da yan'uwa duka ka haɗa kake bani. Yaya banida bakin godiya gareka ka sadaukar da abubuwa da yawa saboda ni, saboda farin cikina. Ka bar abubuwa da yawa saboda ni duk da cewa kana son su. Ka kwana da yunwa ka bani abinci. Ka nuna min so da gata tun bamu san kanmu ba. Yayana kai ɗin *JA'JIRTACCE* ne wannan sunan shi yafi dacewa da kai. Nasan ba zaka ta6a yi min karya ba, yaya na kar6i Momy da Dady a matsayin iyayena na gaskiya amma hakan ba zai shafewa Umma matsayinta na uwa a gare ni ba.
Duk