Showing 12001 words to 15000 words out of 48171 words
Chapter 5 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
tana mata murmushi Feena ma murmuahin ta mayar mata. Ta juya ta fice. Iya ita ce shugabar ma'aikatan gidan baki d`aya, ita take kula da su kuma take ba su umarnin aiki na kowanne sashe na gidan wanda gaba d`aya san-sanin su a kasa yake, sai aiki ko bukatar wani abu ta taso ake kiran su.
kamar mintuna biyar sai ga Iya ta dawo da yara wasu yan'mata guda biyu, wayanda basufi shejaru 16 to 18 ba dukkan su suka zube bisa guiwoyin su suka gaida Hajiyar ta amsa sannan ta kare musu kallo ba laifi ta yaba da tsabtar jikin su ta kalli Iya tace "nagode Iya zaki iya tafiya" itama dai godiyar tayi sannan tajuya ta fita. Hajiya ta kalli yan'matan "sannunku yara ya Sunan Ku?" d`aya ce ta bata amsa"suna na Aysha, wannan kuma Laure" Hajiya tace "Madalla Aysha yaran nan nake so Ku dinga kula da su, yanzu shi kad`ai ne aikin Ku a gidan nan, yimusu wanka da kula da abincin su kuyi ko'karin ba su duk abinda suka ce suna so" tayi shiru na dakiku kad`an yaran kuwa na tsugune suna jiran umarnin ta
"Kuje d`akunan bakin nan Ku gyara kowanne ya zamana kowaccen ku ta d`auki d`aki d`aya da kuma yaro d`aya, kubar min su nan zamu shiga gari, kuje ku fara gyaran d`akunan duk abinda babu kumin magana". Suka amsa da to suka mike cikin ladabi suka fita. Da kanta ta shiga kitchen ta had`owa yaran abinci chicken Pepe soup ne da tuwan sakwara miyar agushi, ta kawo ta ajiye musu a dining table ta koma ta had`o musu kalolin drinks ta kawo duk tq jere sannan ta shiga d`akin ta fito dasu ta zaunar dasu bisa table d`in ta basu abincin sai da ta tabbatar sun fara ci sannan ta mike ta koma kasa inda ta baro mijin ta, ganin baya falon yasa ta koma dawowa saman a d`akin shi ta same shi yayi zurfi wajan kallon photon jaririyar yar'su da aka sace musu, ko sallamar datayi baiji ba balle ya amsa mata.
Akalla takai mintuna uku a kan sa amma Sam bai San da shigowar ta ba, sai da ta kai hannu ta rufe fuskar photon sannan ya Ankara da shigowar ta nannauyan ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa yayi rigingine kan resting chair da yake zaune a kai. Ta zuba mishi narkakkun idanun ta masu kawar mishi da damuwa cikin tausasa murya tace "Habibi Y? Me yasa kake ko'karin illata kan ka ne? Shin ka manta da shawarwarin da likita ya baka?" Alhajin yayi kasa da kan sa zuciyar shi cike da damuwa yace "ban manta ba Yusra, amma ya zanyi? I have no choice my wife, dole in yi tunani ya zama dole in tuna da gudan jini na".
Ya juyar da kan sa gefe idon shi na fitar da hawaye, tausayin mijin nata ya kama ta tasan dole ne domin ita kan ta hakuri take yi, amma ya zasuyi? Basuda abin yi wanda ya wuce hakuri, amma a zahirin gaskiya ita kam yau Allah ya rage mata damuwar dake addabar zukatan na su, ta dalilin samun yara biyun nan sosai ta sami sassauci a zuciyar ta. Itama dai hawayen ne ya zubo mata sai da ta share sannan ta zauna bakin gadon shi ta zuba mishi ido ina so ka saurare ni Habibi. Yarda da kaddara wajibi ne ga kowane musulmi ita kuma kaddara suna ta tara akwai mai kyau wadda zatayi sanadin haska rayuwar d`an Adam, kuma akwai akasin ta wadda Kusan ita ce ta same mu Habibi meyasa ba zamu karbeta hannu bibbiyu mu godewa Allah ba?"
-"ka duba kagani yarinya d`aya muka rasa gaahi Allah ya bamu yaran har guda biyu, shin duk da hakan bai can-canci mu gode masa ba?" Ya d`ago kai ya kalle ta "yara fa kika ce Yusra shin ke a tunanin ki d`an wani zai iya maye gurbin wannan yarinyar a rai na?"
*Yar'mutan Arkilla* β
[11/26/2017, 6:47 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *17*
ππ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkillaβ
"Never", ya fad`a yana kad`a kan shi, hankali na ya kwanta da yaran sosai, sai dai kin san bazasu iya maye min gurbin (baby) ba, Sunan da suke kiranta da shi kenan idan zasuyi maganar ta. Yusra ta sauke numfashi tare da sunkuyar da kanta kasa, tunani ta shiga yi tabbas maganar mijin ta gaskiya ne, soyayyar d`a da iyayen sa ta daban ce wadda babu mai iya samun irin ta sai dai shi d`an
A sanyaye ta koma kallon photon yarinyar dake sanye da wasu jajayen kaya na sanyi masu had`e da hula kayan sun mata kyau sosai. Kyakkyawar fuskar nan ta'ta tayi fess da ita. A ran ta ta koma rayawa "ko tana raye ko ta mutu? Allahu a'alamu" idanun ta suka kawo kwalla a lokacin da wani sashe na zuciyar ta yace "ai duk wanda ya sace ta badan karbar kud`in fansa ba kin san kashe ta zai yi, ba zai bar ta a raye ba." Yusra ta kankame mijin ta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, kukan da yazame mata jiki a duk lokacin da tayi irin wannan tunanin.
Alhaji Tijjani na matukar tausayawa matar tashi fiye da shi kan shi, domin yasan duk yanda ya kai ga son yar'tasu bai kai gareta ba ita da tayi d`awainiyar cikin ta da kuma nakudar haihuwar ta. Ya kwantar da murya ya shiga rarrashin ta, lokaci mai tsayi ta d`auka kafin tayi shiru. muryar ta can kasa tace mishi "dama ina so mu fita da yaran nan in siyo musu Kayan sakawa da na amfanin gida harma da kayan wasa". Yayi murmushi yace "an gaishe ki Maman yara, wannan ba komai amma kid`an huta tukunna" yayi maganar yana gyara mata kwanciya akan gadon. Mintuna kad`an bacci yayi awon gaba da ita, murmushi ya koma yi sannan yaja mayafi ya rufe mata jikin ta ya mike a hankali ya fice daga d`akin
Kai tsaye d`akin ta ya nufa inda ya Tatar da yaran sun gama cin abinci sun baje kasan Capet suna wasanni. Da ganin shi suka nutsu suka zauna guri d`aya Amar ya kalle shi cikin girmamawa yace "barka da shigowa Abba" jin haka yasa Feena ita ma ta kwaikwaye shi "barka da shigowa Abba" ya amsa da "yawwa yaran Abba" ya kama hannun Amar "my boy kuzo muje mu sha ice cream sannan a siyo muka kayan wasa dana sakawa ko?" kafin Amar yayi magana Feena tayi tsalle ta rike d'aya hannun Abba "yawwa Abba nima zani" ya shafi kyakkyawar fuskar ta yace "dama tafiyar taku ce yarinyar Abba" ta falle baki tana dariya dad'i kaman me ji take kamar yau ta fara zuwa duniya tun bayan da Allah ya amshi ran Umma Feena bata taba yin farin cikin irin na yau ba.
hakan ba karamin faranta wa Amar yayi ba sai yaji ya kara son Alhajin da Hajiya fuskokin su cike da annuri ya rika hannayen su suka fita a parking space ya tarar da drivern dake kai Mubarak (yaron da hajiya Ummu ke riko) makaranta ya yana jiran sa, da gudu Mubarak d'in ya fito daga cikin gidan ya makale Dady kamar yadda yake Kiran shi Dady ya saki hannun Amar ya shafa kan Mubarak yana cewa "yaka ke yaro na, ka tashi lafiya". "lfy kalau Dady fatan kaima" "am good, za'aje school ko?" "eh" inji Mubarak hankalin shi akan su Safeenah domin sai a lokacin ya lura da su. "Dady su waye wad'an nan?" Yaron ya tambaya yana kallon su yaran "Mamyn ka ne yau suka zo, kaga ka sami abokai ko?" yaron ya yatsina fuska "Dady ni bana so kawai suyi tafiyar su, ni ko a school banida aboki" yayi maganar da yananyin bacin rai Alhj Wakkala yayi murmushi "kayi sauri ka tafi karka makara" bai koma cewa komai ba ya nufi motar da ake d'aukar shi da ita yana waigen su Amar ranshi a bace.
Alhj yaja hannayen su ya nufi motar shi inda driver yariga ya shiga yana jiran su. zuciyar shi cike da mamakin karamin yaro Mubarak amma hjy Ummu ta bata shi da kin mutane, su basa son kowa sai kan su. ya jinjina kai a zuciyar shi yace Allah ya kyauta.
*Yar'mutan Arkilla*β
[11/26/2017, 6:48 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *18*
ππ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Nasmatu Muhammad
(Yar'mutan Arkilla)β
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
(Ali ishor supermarket) can ya shiga da su wurinda kasaitattun mutane ke baje kolin siyayyar kayan su dana yaran su, nan ne ya basu dama ta su zabi duk abinda suke da bukata yana biye dasu a baya yaran suna matukar burge shi. musamman Feena wadda yake kallon ta kamar wadda ya taba sani a fuska.
Ya lura kusan basu san komai ba a wurin saboda haka kyale su da siyayyar bata lokaci ne, da kan sa ya shiga zabar musu kayan sakawa iri-iri kayan wasanni da na amfanin su kamar su brush, macline da dai sauran su. Sai da ya kammala had'a nasu kakkaf sannan ya shiga had'owa batacciyar yar'su nata. Hakan kuwa abu ne da yariga ya zame musu al'ada dashi da Yusra duk lokacin da suka ga wani abu na wasan yara daya burge su sai sun saya mata, a d'akin ta suke tara kayan duk tsawon shekarun nan
ya gama jibga kayan suka je gurin biyan kud'in, inda makudan kud'in da ya cire ya bayar suka kusa tsorata Amar da Safeenah daga nan da aka saka musu kayan a mota basu tsaya ko ina ba sai gurin wasan yara wannan Umarnin Alhj ne.
Ya fito da yaran suka shiga ciki, driver kuwa ya gyara parking a inda zai jira fitowar su. Babban gurin wasa ne kuma sananne a garin Kano gurin ya kasance kayatacce inda aka tanadi kayan wasar yara iri dabam-daban, nan fa yara suka fara sakewa tun suna d'ari-d'ari da Alhjn har suka saki jikin su sunata wasanni yana taya su sosai yayi amfani da hikima wajen jan su a jiki domin yana so ya riki yaran ne kamar yadda matar sa tace, yana so ya zame musu Uba makusanci mai kula dasu mai yawan fara'a da walwala gare su.
Sun manta da komai sai wasanni suke Alhjn yana bin su kamar zai kama su, su kuwa suna zillewa haka sukayi ta shiga cikin kyawawan fulawoyo masu ado na jajayen furanni ma'abota faranta rai na yara da na manya.
Ba iya yaran kad'ai ba hatta Alhjn kanshi yau yana cikin farin ciki wanda ya dad'e bai ji irin sa ba. ya yarda da tunanin zuciyar shi na cewa "hakika yaran nan alkhairi ne a gare su, da shi da matar sa". domin ko ba komai zasu rage musu damuwa da bakin ciki na zama shiru babu yara.
zasu rage musu kewar baby dake jefa zukatan su cikin tawaya da kunci. basu suka koma gida ba sai misalin sha biyu na rana yara da Alhj suka fito sunata dariya. abin yabawa ma'aikatan gidan dake zaune a farfajiyar gidan mamaki suka bisu da kallo zukatan su cike da mamakin wannan canjin na uban gidan su.
Har zuwa lokacin Yusra bata tashi bacci ba koda suka shiga gidan yayi shiru ba motsin kowa kasancewar Hjy Ummu ta fita aiki, Mubarak ya tafi School ga kuma Mamyn su na bacci. Sai Laure da Aysha yaran da zasu cigaba da kula da Amar da Feena suna ta goge-goge a sababbin d'akunan da aka basu dan zama da yaran, su Alhj ya kira ya hannunta musu duka siyayyar yaran yace su had'a kayan kowanne a kaishi mazaunin sa sannan su yiwa yaran wanka kafin ya fito yana gama basu Umarnin hakan ya wuce yana yiwa yaran murmushi suma abinda suka bishi da shi kenan
zukatan su fari kal sunajin kan su kamar ba a duniya suke ba Aysha ta kama hannun Feena tana cewa "ni zan rika kula dake daga yau, ya sunan ki?" "Safeenah" ta bata amsa Laure ta kalli Amar "kaifa fine boy?" Yace "suna na Amar"kowacce ta kama hannun d'aya suka nufi d'akunan su masu had'e da falo d'aya amma d'akunan daban-daban ne kofofin su suna kallon juna suka shiga dasu a falon suka tsaya suka rarraba kayan Aysha ta kwashe na Feena Laure kuma ta d'auki na Amar suka shige d'akunan kowa da nashi
Amar da Feena basu fahimci komai a lokacin ba a zaton su dan za'ayi musu wanka ne yasa aka shiga dasu gurare dabam-daban bayan anyowa Feena wanka Aysha ta shafe mata jikin ta da mayukan jiki masu kyau da santsi tayi mata make-up dai-dai iyawar ta bayan ta taje mata lallausan gashin ta ta tufke mata shi da band mai kauri.
doguwar riga ta saka mata baka mai dogayen hannu rigar ta shiga da yanayin jikin yarinyar sosai, tayi kyau kamar yar'tsana a cikin kayan da suka zo da su Aysha ta d'auko mata cocolet babba ta bata Feenah tace "ba wannan nake so ba" Aysha yace "to wanne kike so kanwata?" da sauri ta kalle ta
"kiyi hakuri kar ki koma kirana da wannan sunan" Aysha ta kalle ta da mamaki "me yasa Safeena?" ta d'an bata rai "saboda yayana kad'ai yake kirana da hakan, kuma nafi jin dad'in shi a bakin shi karki koma fad'a nidai ki ce min Feena kinji yaya" Aysha tayi murmushi domin yadda yarinyar take magana cike da yaranta tace "to nima kar ki koma cemin yaya" "meyasa" Feena ta tambaye ta tana kallon fuskar ta "saboda yayi kama da wanda kike gayawa yayan ki" ta karadhe tana dariya Feena tace "to mezan ce miki?" "Anty" aysha ta fad'a tana shafa kan yarinyar mai wayau da saurin shiga rai.
"to yanzu gaya min me ki ke so Feena?". tace "wannan mai sanyin na cikin ko'ko kuma hadda kankara gareshi, ni sunan shi ne ban sani ba". Aysha tayi dariya sosai kafin tace "na gane, inaga ice-cream kike so, zo mu tafi". ta kama hannun ta suka fita a falo sukayi kicibis da Laure ta fito da Amar cikin shirin wasu kayan kanti masu kama da jamfa sun masa cif-cif dai-dai jikin sa
*Yar'mutan arkilla* β
[11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *19*
ππ»
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
(Yar'mutan Arkilla)β
FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----
*Soyayya rayuwa ce, mutane kuma rahma ne, kauna Abu ce mai muhimmanci da tsayuwa a rai. Samun wayannan abubuwa a had'e kuwa sai mai tsananin rabo da kyakkyawar sa'a π, Oh! Allah gaskiya ni mai mutukar sa'a ce domin na had'a duka wad'annan abubuwa daga gareku masoya naπ* *ina da mutane ga so da kauna da suke nuna min a bayyane kuma a aikace, INA yin Ku sosai masoya nah!*ππ
Yana ganinta ya sake mata murmushi itama ta mayar mishi suka karasa inda suke tsaye ya kama kumatun ta "kinyi kyau kanwata". dad'i sosai taji a ranta kafin itama tayi tsalle ta lakuto hancin sa "kayi kyau sosai yayana". Yace "to naji amma ai bankai Feena ba".
Su Aysha suka yi murmshi tace "to kizo muje in baki abunda kika ce, ko kin fasa?". "a'a ban fasa ba, yaya zo muje musha wannan abin da Abba ya siyo mana". Ba musu yabi ta inda taja hannun shi suka nufi falo Aysha da Laure na bin su abaya , yaran suna birge su. Acan suka baje bisa capet kowannen su rike da robar ice-cream yana sha. Sunayi sana taba kallon TV wanda yake bakon al'amari a gare su kasancewar kaf kauyen su basu taba ganin irin shi ko mai kama da shi ba. A hakan momyn
A haka Hjy Yusra ta fito ta same su, itama dai ta canza shiga tayi wanka ta caba ado naji da fad'a sai tashin kamshi take suna ganin ta suka fara fara'a musamman Feena da ta mike ta taro momyn tana fad'in "momy kinga muma an mana wani wankan hadda kaya aka sauya mana".
Yusra tayi murmushi tace "gud hakan yayi kyau baby nah, kinyi kyau kuwa". Feena ta saki murmushi lokacin da Yusra ta ja hannun ta suka zauna kan kujera d'aya tace "momy to baki ce yaya yayi kyau ba". Yusra tayi dariya lokacin datake kallon Amar tace "ni na isa? Kayi matukar kyau yayan Feena nah". Amar ma murmushi yayi kafin yace komai Feena ta karbe da "kema fa kinyi kyau momy nah".
Yusra ta zubawa yarinyar ido ganin yadda murmushin ta da yanayin maganar ta sak kamar na wata da ta sani sosai ta sakawa zuciyar ta kaimi wajen tunani da son gano shin da wacce fuska ce Feena take mata kama?
Tabbas tana kama da wata da ta sani to amma wacece? Muryar Abba taji a gefenta yana fad'in "Yusra wannan kallon haka karki cinye min kyawun yarinya". firgigi ta dawo daga nisan tunanin da tayi ta maida kallon ta gareshi wanda taga ashema har ya zauna a kusa da ita amma ita sam bata san da zuwan shi ba
tayi murmushi "Habibi ai yar'taka ne tayi kyau yau, a ina suka sami sababbin kaya?". Amar dake makake a gefen Dady yayi karaf yace "ai Abba ne ya siyo mana masu yawa ne ni da kanwata, kuma harda gun wasanni muka je". Sosai Yusra taji dad'in lamarin ta maida kallonta ga mijin nata tace "oh my Habibi gaskiya bansan taya zan gode maka ba, ina sonka da yawa Alhjna".
Abban yayi dariya mai sauti "nima haka matata farin cikina, ki sani indai har hakan zai faranta miki rai to zan cigaba da rikon su Amar tamkar ya'yan da na haifa da cikina". "ina godiya