Showing 33001 words to 36000 words out of 48171 words

Chapter 12 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4631

da naji kin kira da Jidda. Amma kamar yanda kika faɗa zan so ta saboda ke ne".


Yanayin yadda yake magana kaɗai ya isa ya ya baka tausayi. Kuka ne ya kwace mata ganin ta tilasta yayanta yin abinda bai yi niyya ba, ta saka shi yin abinda bai ta6a yi ko tunanin yi ba.


"Yaya ta faɗa a raunane sannan ta rungume shi ta kara fashewa da kuka. "kayi hakuri Yayana na shiga hurumin da ba nawa ba, kuskure na ne dana manta kai kake ikon zuciyar ka ba ni b... Hannun sa yasa ya toshe mata baki bai barta ta karasa faɗar abinda ke bakinta ba. Feena ni ɗin nan naki ne, karki ta6a tunanin da akwai abinda zaki ce kina so inyi kuma ban yi shi ba, muhimmancin ki da darajar gare ni sun wuce nan Kanwata". ya kara kankame ta jikinsa dukkanin su kuka suke yi, lokaci mai tsayi suka ɗauka a haka kafin su saki juna ita kam kasa jure zaman tayi ta koma ta kwanta. Shi kuwa Amar zaune yake yana kallon yanayinta duk tayi sanyi kamar wadda zazza6i ya kama. Sai ya fara jin haushin kansa da bai amince kai tsaye ba gashi ya saka Kanwar shi kuka.


Rarrashinta ya shiga yi yana bata baki, tareda nuna mata abinda zai yi fa ba komai bane kuma shima yana son Jidda ɗin sosai tunda kanwar shi ta yarda da ita. Haka dai yayi ta lalla6a ta har zuwa lokacin komawarta lecture yayi ya koma raka ta har kan sit ɗinta yana rike da hannunta zaunar da ita sannan ya fito ya koma gurin nan ya zauna zaman jiran fitowar ta domin shi baida wata lecture sai gobe.




************************************


Tun daga wannan Ranar Soyayya ta fara kulluwa tsakanin Jidda da Amar, a School kullum suna tare su Uku haka zaka gan su Koda yaushe cikin farin ciki da nishaɗi. Sau biyu tana zuwa gidan su a matsayin kawar Safeenah a can ta kara samun tabbacin su ɗin Yaya da Kanwa ne. Domin a lokuta da yawa tana tsintar kanta da zargin alakar Amar da Safeenah, a cewar ta shakuwar tayi yawa soyayyar da yake nuna mata ta zarce wadda kowane wa yake nunawa kanwar sa. Sau tari danne zuciyar ta take, idan suna wani abu a gabanta kallon masoya take musu. Masoyan ma na musamman waɗanda suke da wahalar samu a wannan lokacin da shi da ita ko wanne yana iya ko'karin sa wajen nunawa ɗan'uwan sa so da kulawa.


To haka dai suka yi ta mulmula rayuwa lokaci na tafiya safina an shekara har da ɗorin watanni jami'a tana level 2. Amar da Jidda suna final year. I zuwa yanzu ya fara son Jidda sosai kamar yadda take son sa, Iyayen su ma sun san da maganar har an sanar da sun kammala karatun su za'a musu Aure. Jidda sai jiji da kai ake a Makaranta ta sami cikar burinta Amar ya zama nata ita kaɗai.


Feena an kare rawar kai rayuwar Makaranta ta fara mata zafi, GA karatu ga katuwar katangar da take gani ta shiga tsakaninta da Yayanta a School koda sun fito sai su ke6e da Jidda su yita hira abinsu su kyale ta zaune ita kaɗai. Wannan wani sabon salo ne da Jidda ta kirkira na nesanta Amar da Feena a Makaranta, sai take nuna masa bai kamata suna hirar Soyayya a gabanta ba kar su shiga hakkinta kuma ma bazasu sami sakewa da kyau su bayayyawa juna Soyayya ba.


Haka suke mata kullum tun abin baya damunta har ta fara shiga damuwa. Yau ma kamar kullum zaune take bisa carpet ɗinsu a garden ɗin School inda suka saba zama. Ta zuba musu ido ko kiftawa bata yi daga inda take tana hango su sai zuba hira suke suna dariya.


"Safeenah Y?" ta tambayi kanta "me yasa kika ɗauki farin cikin ki kika kyautar ga wata? Me yasa kika yarda da mace akan gudan jinin ki?, me yasa???"


Sai kawai ta fashe da kuka...










To fah🤔
Fans ku taya ni ganin wannan drama 🤣
















*Yar'mutan Arkilla* ✍
[12/12/2017, 9:46 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*....... *40*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
We are here to educate motivate and entertain our readers.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________
















Amar da Jidda kam suna can suna kwasar love, sam basu san halin da take ciki ba. Zumbur ta mike ta ɗebi jakar ta, Allah yasa key na motar su yana hannunta. Da gudu ta ratsa cikin makarantar kamar wacce aka yiwa mutuwa kuka take sosai har ta isa parking space da remote ta fara buɗe lock na motar sannan ta buɗe ta shiga.


Hannun ta bai wani faɗa da tukin ba dan bata maida hankali ba, sam bata ta6a tuka mota ita kaɗai ba. Haka ta figeta ta tafi cikin kunan rai. Ikon Allah ne kaɗai ya kai ta Gida a motar ma tafe take tana kuka.


Wani mahaukacin horn da ta saki gaba ɗaya layin saida ya ɗauka, da gudu Mudi ya buɗe kofar bayan ya tabbabar motar gidan ce. Kamar zata tashi sama haka ta shiga gidan gurin tsayuwa ne birki yaki mata, a yadda ta zo haka ta kauru da wata sabuwar motar Dady dake ajiye a gurin. Sai ji kake gau...


Da gudu Momy Yusra ta fito itada ma'aikatan suka yi rige-rigen isa gareta, hankali tashe suka buɗe motar "innalillahi! wa inna ilaihi raji'un" abinda Momy ta faɗa kenan cikin kuka ganin Safeenah kife akan sitiyarin motar bata ko matsawa. Jikinta har 6ari yake ta fara kiciniyar ɗago ta, "ku taimaka min Feena zata mutu" Momy ta faɗa cikin kuka, Iya ce ta kama mata ita suka sakata a wata motar. Ilu ya ja su sai asibiti har suka isa Momy bata daina Kuka ba, tana rungume da Feena wadda take ji tamkar ta tashe ta. Da isar su nurses suka taresu, akan kujerar nan ta marasa lafiya suka ɗora ta suka gungura ta zuwa cikin asibitin.


Ba jira aka shigar da ita emergency word, likitoci biyu ne suka hau kanta dressing suka fara yi mata inda kanta ya fashe gurinda ta bugu. Sannan suka hau aikin ceto rayuwar ta. Momy sai Kuka take Iya na Rarrashinta, ko mayafi babu a kanta daga ita sai kayan jikinta sai ɗankwalin kanta. Haka tana so ta kira Dady ta sanar masa amma bata zo da waya ba.


6angaren Amar kuwa time ɗin shiga lecture ne yayi suka juyo suka dawo inda suka bar Feena sai basu ganta ba, daga nan hankalinsa ya fara tashi. Tare suka nufi department ɗin su dan ganin ko ta koma class ne. Can ma wayam babuta babu dalilin ta. Da sauri ya nufi inda suka yi parking motar su kamar zai tashi sama. Duk yadda Jidda taso su jera sai da ya bata rata dan yadda yake tafiyar bada wasa bane.


Wani irin bugu yaji zuciyarsa tayi tamkar an doka masa guduma a kirji, sakamakon ganin babu motarsu a inda yayi parking. Bisa dole ya kai hannu Ya dafe saitin zuciyarsa saboda yadda yake ji kamar zata faso kirjin ta fito. Ya tabbatar ba lafiya ba, dole akwai wani abu domin Feenarsa bata ta6a yi masa haka ba.


Dai-dai lokacin Jidda ta iso inda yake, ganin yanayin sa ne ya ɗan dakusar da ita ga korafin da taso ta yi mishi na ya barta baya.


Bangare ɗaya kuma haushi ne ya lullu6eta ganin yadda karamar yarinya ke juya mata saurayi. Wani irin tsaki taja kamar zata tsinke harshenta, lokacin da taga ya ciro waya yana searching number ta tabbatar ita zai nema.


"Hmm lallai Amar yanzu a kan kanwar taka kake duk wannan damuwar?, ai ba cewa aka yi wani abu ya same ta ba, kawai fa dan taga ka damu da ita ne yasa take duk wannan abun duk inda ta tafi ai zata dawo ne. Dan Allah zo mu tafi."


Amar dake nema layin Feena, wayar har ta gama ringing ta yanke ba'a d'aga wa. Sai yaji saukar kalaman Jidda tamkar tana yi masa feshin tafasashshen ruwa a kirji. "Ke! Ya daka mata tsawa, tareda ɗaga hannunsa sama kamar zai daketa sai kuma ya sauke tareda furzar da wata iska mai zafi. Ya nuna ta da yatsa yace cikin tsananin fushi da 6acin rai "wacce ce ke da har kika isa ki shiga tsakani na da kanwata, Kim kuwa San wace ce Safeenah?, tabbas baki sani ba da bazaki fara tunkarata da magana irin wannan ba. To ina miki kashedi na karshe akan aibata kanwata ko faɗar wani abu da bai dace ba a kanta. In ba haka ba... " bai karasa ba ya juya a fusace ya kama hanyar ficewa daga School ɗin da kafa.


Tamkar wadda aka dasa haka ta sandare, zuciya da kwakwalwarta sun cika sun batse da mamakin Amar. Fargaba da tsoro suka koma kama ta." Wannan wace irin Soyayya yake wa Safeenah?" ta san ba wanda zai amsa mata wannan tambayar. Wasu siraran hawaye suka fara zariya a kumatunta, tana son Amar duk tsanani tana ji a ranta zata iya jure komai domin shi. Amma wannan ya gagare ta, ta kasa hakura da kakkarfar alakar dake tsakanin shi da kanwarsa. Komai yayi mata zata iya shanyewa amma idan ta ga yadda yake rawar jiki da Feena yana faranta mata sai taji ta kasa jurewa duk da tasan matsayinta gare shi na kanwa ne. Kuka mai karfi ya kwace mata.


Amar yana fita gate ɗin makarantar ya tari mai mashin ya hau bayan ya kwatanta masa inda zai kai shi. Karo na farko daya fara hawa mashin a rayuwarsa. Har wani jiri yake ji yana ɗiban sa daga sama, da sauri ya kulle idon sa gam, bai koma buɗe su ba sai da yaji mai mashin ɗin yana cewa "ranka ya daɗe mun zo layin...












*follow us on this details :*
----
*like our facebook page :*
↓↓
*Fb.me/zamaniwritersassociation*
----
*check our blog's*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*your comments and reports are highly welcome on this email address:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*














*Nasmat* ✍
[12/15/2017, 7:34 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*....... *41*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
We are here to educate motivate and entertain our readers.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________














Ai kuwa gwara da yayi mishi maganar domin mai babur ɗin ya ɗan wuce gate ɗin gidansu kaɗan. Da sauri ya umarce shi da ya ajiye shi nan, hakan kuwa aka yi ya tsayar da babur ɗin shi kuma ya sauka yana kallon gate ɗin gidansu bugun zuciyarsa na kara tsananta.


Gudar ɗari biyar ya ciro daga aljihunsa ya bawa mai babur, bai tsaya jiran canji ko jin wani abu ba ya juya ya tunkari kofar gidan. Mai babur kam sai washe baki yayi yabi shi da addu'ar "na gode Allah ya saka da alkhairi" da isar sa bakin gate ɗin ya fara bugawa yana haɗawa da kiran sunan mai gadin wato Mudi.


Jin muryar Amar ce yasa ya buɗe kofar cike da jimami, tun kafin ya shiga yake tambayar Mai gadin "Feena tana ciki kuwa?" alamun tashin hankali karara a fuskar shi, kamar wanda yasan abinda ya faru. Amma tambayar da yayi ta nuna baisan komai game da hatsarin da ta samu a cikin gidan ba.


"Mudi" ya kira Sunan yana girgiza shi domin ya lura kamar wani tunanin yake. Mudi yai firgigit! Ya dawo hayyacinsa "baka ji tambaya ta bane?" Amar ya koma tambayar sa fuska cike da damuwa. Mudi ya nisa yana cewa "to ka shigo daga ciki mana in yasa sai kaji komai a nutse."


"ya kalle shi kallon tuhuma kafin yace "me ya faru da kanwata?" yayi tambayar ne saboda ganin damuwa da jimami karara a fuskar Mudi. Ya kaɗa kai yana share kwallar da ta gangaro masa a kumatu. Sannan ya dubi Amar ya ce "kayi hakuri Amar komai mukaddari ne daga Allah, ban san me ya tashi hankalin kanwarka ba sai dai na ganta ta shigo cikin matsananciyar damuwa. Tunda nake ban ta6a ganin Uwar ɗaki a yanayi irin wannan ba. Yadda take tuka motar ma ya bayyana karara cewa tana cikin damuwa ne... "


Mudi ya kwashe duk yadda abin ya faru ya gaya wa Amar, daga karshe ya sanar masa suna Asibiti. Tunda ya fara maganar Amar bai koma iya ɗaga harshensa da sunan yayi magana ba, haka bayan ya gama gaya masan ma bai ce komai ba ya juya yana layi, yana dafa bango. Da sauri Mudi ya kai masa agaji ta hanyar riko gefen kafaɗarsa domin a yadda yake ya tabbata idan ya bar shi kasa wanwar zai zube.


Amar ya fizge hannunsa daga rikon da Mudi yai masa, kana ya wuce cikin gidan. Kai tsaye inda motar tasu take ya nufa. Dama a buɗe take yana zuwa ya faɗa cikin ta yai mata key. Dai-dai nan Mudi ya isa gare shi yana faɗin "a'a Amar, bai kamata kayi tuki a wannan yanayin ba, ka dube kafa..." "buɗe min gate." Amar ya buɗi bakin sa dakyar ya cewa Mudi. Mudi yayi jugum kamar ba zai motsa ba yana jinjina abin a ransa "kar fa azo ayi faɗuwar guzuma" yace a ransa ya na kallon Amar da yanayinsa.


Ɗago kai yayi cikin wani yanayi ya koma maimaita abinda ya faɗa "buɗe min gate nace." sauyin da Mudi ya gani a idon Amar yafi komai tsorata shi, domin idon sun kaɗe sun canja kala daga fari zuwa ja, wasu igiyoyin jini suka rarratsa a cikin kwayar idon na shi. Babu shiri ko neman karin bayani Mudi ya nufi gate da saurin sa tun mummunan abu bai faru ba. Domin a yadda yaga Amar zai iya yin ɗaya a cikin biyu idan ya dakatar da shi, ko dai ya 6alla kofar ya fita ko kuma shima ya faɗar masa a nan. Domin su ganau ne ba jiyau ba, dangane da irin Soyayyar dake gudana tsakanin Yaya da kanwar.


Yana ɗaga gate ɗin Amar ya figi motar nan ya cilla kanta waje, ji kake kiiiiiii... Karar murɗe sitiyari domin yin kwana a ɗora motar bisa titi. Mudi ya dafe kai yana faɗin "ya Allah ka kare wannan bawan naka ka kai shi inda ya nufa lafiya" (to nima dai Nasmat addu'ar da na yiwa Amar kenan).


A Asibiti kuwa cikin mintuna talatin Likitocin nan suka sami nasarar ce to rayuwar Safeenah. Bayan numfashinta ya dawo dai-dai suka ɗora mata drip da allurar bacci saboda jikinta ya saki kwarinsa ya dawo. Hankalin Momy da ɗan kwanta, tana zaune gefen gadon hannunta rike da na Feena tana kara karanto mata wasu addu'oi tana tofa mata a jiki.
















*Nasmat* ✍
[12/16/2017, 10:15 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*....... *42*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
We are here to educate motivate and entertain our readers.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________














Cikin matsanancin tashin hankali ya isa asbitin. Kai tsaye office ɗin babban likitan ya nufa domin shine family doctor ɗin su. Dr. Kamal na zaune yana nazarin wasu takardu na resold ɗin gwajin wani majinyaci, sai ji yayi an banko kofarshi an shigo ba tareda neman izni ba. Ya ɗago kai da sauri a ɗan razane. Amar ya gani tsaye a gabansa yana sauke manya-manyan numfashi hatta sallama da ta wajabta bai yi tunanin yi ga likitan ba balle gaisuwa.


"Dr. Wane hali kanwata take ciki?" tamayar da ya jefa masa kenan bayan ya isa gaban teburin likitan ya ɗora hannayensa duka biyu akai sannan ya zubawa Dr. Ido yana jiran yaji ta bakin sa.


Dr. Kamal ya san komai gameda soyayyar yaya da kanwar nan, domin shine likitansu. Ba tun yau ba ya saba ganin ire-iren hakan daga kowanen su idan ɗan'uwan sa bashi da lafiya.


Wannan yasa ya mike daga kan kujerar sa ya zagayo inda Amar yake tsaye yana hawa da sauka na numfashi wato yana jan iska yana feshewa cikin matsananciyar damuwa. Likitan ya dafa kafaɗarsa ya fara rarrashin sa yana kwantar masa da hankali, tareda tabbatar masa ba wani ciwo taji sosai ba. Duk wannan jawabin na likita ai sawa Amar nutsuwa ba daga karshe ya kama hannunsa ya kai shi har ɗakin da suka kwantar da Feena.


Har lokacin da suka shiga Momy na nan a inda take zaune, hannunta rike da na Feena idanunta sun yi ja sosai alamar kuka tayi ba kaɗan ba. Likitan yayi sallama Amar kuwa da sauri ya isa ga kanwarsa dake mike akan gadon kamar matacciya.


Feena! Ya kira sunanta da karfi bayan yayi zaman dirshan bisa gadon yana kokarin tallbo ta zuwa jikinshi. Da sauri likita ya dakatar da shi a ɗan tsawace yace "kai Amar, baka gani da karin ruwa a jikinta ne?" Amar ya dubi hannun Feena wanda aka ɗaura mata karin ruwan hawaye tam a idonsa ya koma maida kallonsa ga likita yace "ya zan yi Dr. Ina son jingina ta a jikina, ina son na ra6eta Dr. Bazan iya kallonta nesa da ni a wannan yanayin ba." tausayin shi ya kama Momy da likitan Momy ce ta mike a hankali ta ɗaga kan Safeenah ta ɗora bisa cinyarsa, hannun ta da take rike ta mika masa ya kama hannun ya rike shi gam hawaye na ci gaba da gudana a kumatunsa. Momy ma kukan take tausayin kanta da Amar take ji idan suka rasa Feena ta kasa tantance ida da shi wa zai fi shan wuya.


Likita kuwa jikinsa ne yayi sanyi likis ganin inda soyayyar yan'uwantaka ta gaskiya da gaskiya take, ya kurawa Amar ido lokacin da aka ɗora masa ita a ciyarsa ya lura ya sami salama ga abinda yake ji a zuciyarsa domin yadda yake sauke ajiyan zuciya manya-manya tamkar wanda yayi gudu na kilo meters. Ya rumtse ido yana nazari "shin shima da yanada kanwa zai so ta haka?" (tabbas wannan abin tambaya ne likita, inma dai na tambaye ku readers shin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login