Showing 42001 words to 45000 words out of 48171 words

Chapter 15 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4649

da cewa inda kuruciya a lokacin nasan iya wahala da bakin cikin da Umma take ji idan ba'ba Larai na zagi da hantara ta, sau tari Umma har kuka take yi. Ina son ki Umma Allah ya kai rahma kabarinki." gaba ɗaya suka amsa da ameen.


Jikin kowa a gurin sai da ya yi sanyi babu shakka su kan su shaida ne akan abubuwan da ta faɗa gameda shi. Amar ya cancanci sunan da ta bashi na *JA'JIRTACCE* Kamar daga sama suka ji muryar Hajiya Ummu tana faɗin "wlh karya ne, wannan ba yar' ka bace yar' ka ta daɗe da mutuwa wlh karya suke baka da wata ya' a duniya."


Ta jima a gurin tana sauraron maganganun da suke akan Feena taji komai har labarin da Amar ya bayar na rayuwarsu ta baya. Wata irin ɗimuwa da tashin hankali ne suka kusan zautar da ita bata san sanda ta fara sambatun ba.


Nan fa aka hau kallon-kallo tsakani Dady da Momy kafin ya juya ga Hajiya Ummu yace...




















*Nasmat* ✍
[1/11, 8:03 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*....... *48*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________










📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com












"Ummu, me kika sani akan ya' ta da har zaki yanke hukunci karaf ɗaya kice ta mutu?" nan fa Hajiya Ummu ta hau so she-so she da kora kunya da hauka tana faɗin "to shekara nawa da 6atan yarinya babu ta babu labarin ta sai yau da rana tsaka ace wai Safeenah ce ita?, haba ni wlh inba yau ba ma ban ta6a sanin tsinto yaran nan kuka yi ba." Alhj Wakkala yayi murmushi "wannan ne hujjar ki?" tace "eh" tana damke cikinta dake mata wani irin juyi. Ya kar6o tsinkakkiyar sarkar nan daga hannun Momy Yusra ya ɗaga mata yana faɗin "to mu kuma ga tamu hujjar, na san dai zaki iya gane wannan sarkar ko?" Hajiya Ummu ta waro idanu dan babu shakka ba zata iya manta wannan sarkar ba, muhummiyar kyauta ta farko da yar' ta fara samu kenan.


"gareta aka samu wannan?" ta tambaya a matukar tsorace tana ja baya. Alhj ya tabbatar mata da hakan. Bata koma cewa komai ba ta juya da gudu ta nufi ɗakinta cikin maysanancin tashin hankali.


Nan dai Alhj da Hajiya Yusra Ummy da Aunty Sumayya haɗa da Amar da Safeenah suka kasance cikin farin ciki da annashuwa. Nan da nan ya shiga kiran yan'uwa da manya-manyan abokansa da kusa da na nesa yana shaida musu Allah ya bayyana 6atacciyar yar'sa Baby. Haka Ummy ma ta kira Saudiya ta shaida musu wannan daddaɗan labari na bayyanar jikarta yar wajen Yusra.


Kafin kace me gidan ya fara cika da yan'uwa masoya da makota duk wanda yazo yaji labarin sai al'ajabi ya cika shi, sai dai kaji kowa na faɗin "ikon Allah kenan sun reni yar' su da kan su."


Bikin birthday kam ya tashi daga karamin biki ya koma gagarumi. Hatta cake saida aka koma yin order wani abinda da masu da shi cikin kankanin lokaci aka kawo. Gaba ɗaya farfajiyar gidan aka yiwa sabon tsari dan yawan jama'a ɗakinta ba zai ɗauka ba. Ansha addu'a manyan malaman nan sun jima suna jero wa Allah (s. w. a) kirari suna yabo da godiya gare shi. Haka iyayen da bakin nasu. Amar da Safeenah sun zama tamkar wasu taurari a wannan taron idon kowa a kan ta, ita kuma tana makale da shi.


Ana cikin taron bikin ne wata yar'aikin gidan ta fito da gudu kanta a fashe jini yana zuba, ta dafe gurin tana haki tana kiran "Hajiya! Hajiya!.


Ta faɗa jikin Hajiya Yusra. Abinda ya ja hankalin kowa zuwa gare su kenan aka rufu a kan ta ana tambayar abinda ya same ta.


Bata jita komai ba ta fara koro musu bayani cikin mawuyacin hali kamar kaha : "Hajiya babba ce naji tana waya cikin tashin hankali tana tambayar wata da ban san ko wacce ce ba, tana cewa ashe dama bata kashe yar' nan taka data bata aikin kashewa ba?,


Ashe sace yar' kawai tayi ba tareda ta kashe ta ba kuma ta kar6ar mata kuɗi har miliyan gama?. To shine ni kuma na tsorata da jin hakan na fara salati, dan dama bata san ina ɗakin ba. Shikenan tana gani na ta fara duka na cikin firgici tana cewa gwara ta kashe ni akan na tona mata asiri shine ta yi min haka dakyar na ku6ita na taho nan." ta karashe maganar a wahale tana dafe kai jama'ar dake wajen suka ɗauki salati da salami cikin alhini da matukar mamakin jin wannan maganar. Alhj da Hajiya Yusra kamar sun sandare Ummy ta fara girgiza kai tana faɗin "tabbas hausawa sun yi gaskiya da suke cewa 'makashinka yana jikin ka'." kafin wani ya furta wani abu yar aikin nan ta nisa tana ambaton Sunan Allah rayuwarta ta fice. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" abinda ɗaukacin mutanen dake gurin suka shiga ambatawa kenan.


Dai-dai nan kuma Hajiya Ummu ta fito da gudu da iccen mofa a hannunta tana muzurai...


Amma halin da ta tsinci ma'aikaciyar tata Zainab ya tsorata ta matuka. Hajiya Yusra ta zubo ruwan gorar dake ajiye a gurin ta shafe Zainab. Ai kuwa Hajiya Ummu na ganin haka ta juya da gudu ta nufi kofar gate dan ficewa daga gidan domin ta tabbatar dubunta ta gama cika yau.


Cikin tsawa da ɗaga murya Dady ya bawa security umarnin su rikita. Ai kuwa kamar jira suke suka riko ta suka nufo inda mutanen suke da ita. Da sauri Dady ya ɗaga musu hannu alamar dakatarwa yana cewa "kar ku zo min da ita nan, ku ajiye min ita can ɗakin mai gadi kafin nayi waya ma'aikata su zo su tafi da ita. Bana bukatar sake ganin ta a rayuwa na tsane ta. Na tsane ki Ummu kuma kije na sawuwaka miki na yanke igiyar aure dake tsakani na da ke kuma cutar mu da kika yi Allah ya isa ba zamu ta6a yafe miki ba. Babu shakka ko yanzu Allah (s.w.a) ya nuna miki karfin ikon sa da kuma ɗinbin adalcinsa ga waɗanda aka zalinta."


Hajiya Ummu ta dafe kai ta fara rurin kuka da tirje-tirje. Nadama da dana sani ne fall a zuciyarta, da tasan irin wannan ranar zata zo mata da bata aikata abinda ta aikata ba. Amma inaa azal ta rigaya babu sauran gyara...






















*Nasmat* ✍
[1/11, 10:17 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*....... *49*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________










📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com










Cikin tsananin 6acin rai Dady ya kaɗe rigarsa ya shiga cikin gida yana danna wayar hannunsa bisa dukkan alamu yan' sandan yake nema.


Babu shakka wannan ranar ta yau tazo musu da abubuwan al'ajabi daban-daban na farin ciki da na bakin ciki harma da na ban mamaki. Wai ace Hajiya Ummu ce da kanta zata saka a sace masa yar guda gudar yar' sa harma da cewa a kashe ta. Taron mazajen da suke wajen ne suka taimakawa yan sanda wajen basu cikakken bayani akan abinda ya faru matan kuwa tuni suka watse.


Tsananin tsoro da al'ajabi ya kama Amar da Feena su kam basu ta6a tsammanin rashin imanin Hajiya babba ya kai har haka ba.


Washe gari da safe aka dawo da gawar Zainab bayan an kammala bincike a kan ta aka suturta ta aka kai ta makwancinta. Hajiya Ummu kuwa tana can a hannusu labarin aika-aikarta ya gama zama gari abinka da an ta6o masu da shi har gidajen TV aka rika yaɗawa, danginta kuwa ruɗani suka shiga Mubbarak ma tun daren jiya ya tattare ya bar gidan ya koma gidan iyayensa. Ma'aikatan gidan na cikin alhinin rashin yar'uwarsu Zainab haka iyayenta ma da labari ya riske su hankali tashe suka iso Kano.


Bayan sati Uku komai ya lafa al'amura sun fara zama dai-dai gidan ya dawo ramin kura (daga ita sai ya'yanta) wato daga Momy sai yaranta Amar da Feena da kuma Dadyn su da kuma bakinsu Ummy da Aunty Sumayya da malaman nan. Allah sarki rayuwa kenan Safeenah sai take jinta tamkar wata sabuwa tana jin Momy kamar wata Bakuwar ta haka Ummy ma ita yadda suke tarairayarta suna kara saka ta a jiki har kunya yake bata. Shi kuwa Amar farin ciki ne ya lullu6e ruhinsa Safeenah mafi soyuwar zuciyarsa ta sami cikakken gata wanda baida tawaya.


Sati uku su Ummy suka yi cikin farin ciki da daɗin rai kamar kar su tafi amma da yake ya zama dole haka suka shirya suka yi sallama suka koma cike da farin ciki na wannan gagarumin lamari da tsarin Allah. Safeenah hadda kukanta kamar dai yadda ta saba idan zata rabu da Ummy, to balle ma yanzu da suka fi shakuwa da juna domin kasa rabewa take yi tsakanin soyayyar da Momy ke nuna mata da wadda Ummyn ke mata.


Bayan sati ɗaya da tafiyar su Ummy ne aka kara buɗe sabon shafin rayuwar farin ciki a gidan. Dady da Momy ji suke kamar su haɗiye Safeenah a yan kwanakin nan Sam basa iya yin nisa da ita, musamman Momy sau tari sai dai ta zuba mata ido hawayen farin ciki na bin kuncinta. Haka Amar ma basu ware shi ba, duk wata soyayya da zasu nuna wa Feena shima da tashi saboda Amar mutum ne wanda daraja da kimar sa bazasu ta6a barin idonsu ba. Iyayensu ne suka rike musu yar'su suka reneta cikin aminci, bayan mutuwar su kuma shi ya maye gurbin ya zame mata gata a lokacin da bata da shi.


Hutu ya kare suka koma school sai dai a kwana biyun Dady ya lura Feena bata son zuwa makarantar koda zasu tafi sai ta murtuke fuska ta fita tana fushi. Yau ma gaba ɗaya ki tayi tace ita ba zata je ba. Ya daɗe yana nazarin ta, tana kishingiɗe bisa kujera sai hura hanci take tana hararar Amar dake tsaye a kanta yana magiyar ta tashi su tafi ta ki.


A hankali ya kira sunanta "Safeenah" ta amsa kanta na kallon inda yake "na'am Dady" "me yasa ba zaki je makaranta ba?" maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka fara bin kuncinta tana sharewa. Mamaki ya kama Momy Amar harma da Dady. Momy Yusra ta kalle ta cikeda fargaba "Feena baki da lafiya ne?" ta girgiza kai "lafiya na kalau Momy, kawai ni ba zani school ɗin bane." Amar ya kara tsurewa dan ya san laifin nasa ne ya jangwalo rigima. "saboda me?" Dady ya tambaya yana kallonta. Sai ta daina share hawayen ta fashe da kuka. Cikin kukan ta fara magana "Dady yaya ne fa ya yi sabuwar budurwa mai shegen nacin tsaya, ko bai neme ta ba sai tazo muna hirar mu ta addabemu da shegen surutu sai iya yi baka gani ba fa har nunawa take yi tafi ni son shi."


Ta karashe zancen tareda saka wani sabon kukan. Maganar Safeenah ta bawa dukkan su dariya banda Amar da yasha jinin jikinsa dan yasan tashi dariyar zata fi ta kowa yi mata ciwo.


Iyayen suka kalli juna suka yi murmushi. Amar kuwa tsugunawa yayi gabanta ya marairaice murya "yanzu Feena wannan dalilin ne yasa zaki daina zuwa makaranta? Wa yace miki ni zan yarda da akwai wadda ta fiki so na a duniya?, wlh babu ita ni kam na san kin fi kowa so na a duniyar nan Safeenah."


Ta murguɗa baki ta juya masa baya "amma ai baka ta6a gaya mata haka ba, sai wani ji da kanta take in ta ganka." Amar ya kunshe dariyar da ta ciko bakin sa yace "in ji wa? Allah a gabanta ma zan faɗa. Zo mu tafi, a gabanki zan sanar mata hakan." ya kama hannunta ya mikar da ita yana bata mayafi dan tuni ya ɗauko mata jakar litattafanta. Har suka fita iyayen basu koma cewa komai ba.


Bayan tafiyar su ne Dady ya kalli Momy yace "alhamdulillahi Yusra kinga hakar zata cimma ruwa, babu shakka tunanin ki ya zo dai-dai." dariya ta yi tana faɗin ai dama na gaya maka Allah ya saukake komai. Har zai yi magana wayar hannunsa tayi kara alamar shigowar kira ya ɗaga da sallama yana murmushi tareda sallama. "Allah ya taimaki Alhj wannan aikin da ka bayar komai ya kammala an riga an canza komai kamar yadda ka bukata." sai da mai maganar ya kai aya sannan Alhjn ya fara magana "masha Allahu malam sabo, Allah ya saka da alkhairi insha Allahu gobe da sassafe zan shigo na gani in ya so bikin buɗewar ya kasance ranar litinin." a haka suka yi sallama ya kashe wayar yana daɗa godiya.


Bayan ya kammala ne yake gaya mata wannan kamfanin nashi na buga atamfofi ne yasa aka gyara tareda sauya masa sabon tsari sai ta shirya domin ranar da za'a buɗe shi gagarumin biki za'a yi.


Momy tayi murmushi "kaji habibi bikin ma hadda wani gagarumi?" ya mike yana faɗin sosai ma kuwa domin kudurina a ranar na musamman ne. Ni zan fita." "to Allah ya kiyaye ya dawo da kai lafiya, Allah kuma ya kai mu jibin mu sha biki." ta faɗa da tsokana. Bai ce komai ba ya fice yana dariya.


Momy bata san yadda suka kare a makaranta ba ta dai ga Safeenah an dawo ana ta kyalkyala dariya kamar ba ita ta fita tana sharar kwalla ba.


Ranar monday ta zo inda Dady ya sa aka shirya gagarumin taro a harabar wannan kamfanin nashi. Misalin karfe tara da rabo kowa ya hallara a farfajiyar katafaren kamfanin wanda yasha gyara da sababbin tsare-tsare ya koma kamar sabon guri. Bayan manyan malamai sun buɗe taro da addu'a aka fara gabatar da abinda ya tara su a gurin wato buɗe kamfanin. Inda aka fara da zuge wani babban kyalle wanda aka rufe allon dake ɗauke da sunan kamfanin a jiki. Ai kuwa sai ga sunani ya bayyana raɗau cikin tsarin rubutu mai kyau da ɗaukar hankali. Ga sunan kamar haka : *JA'JIRTACCE WAX & MATERIALS LIMITED.*


Tsananin mamaki ya kama Hajiya Yusra da yaranta musamman Amar domin a sanin shi wannan shine sunan da kanwarsa ta bashi. Bai kara tsinkewa ba sai da Dady ya kama hannunsa ya fara jawabi tareda damka masa takardun kamfanin a gaban waɗannan dubban mutanen. Ya kuma shaida musu ya mallakawa Amar wannan kamfanin daga yau kamfanin ya zama mallakinsa halak malak. Aka hau tafi da haska su da camera. Tsabar farin ciki Safeenah sakin hannun Momy tayi ta tafi da gudu ta rungume mahaifinta tana hawayen farin ciki, tareda taya yayanta godiya. Haka Amar ma rungume Dady yayi yana hawaye dan nuna farin cikin sa ga wannan dankariyar kyautar da bai ta6a tsammani ba.


Abokan Dady da manyan yan' kasuwa da suka halarci bikin suka rika taya shi murna. Haka taro ya watse suka koma gida cike da murna.


















*Nasmat* ✍
[1/12, 11:06 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


........... *JA'JIRTACCE*... *50* last page
... *The end😇*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀






*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_____________________________________
​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.
_____________________________________


©
Yar'mutan
Arkilla✍
____________










📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION


📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com








Rayuwa kenan. Hausawa suka ce kwanci tashi asarar mai rai. Haka rayuwa ta ɗore musu cikin farin ciki da nishaɗi kankanin ta na saudiya kuwa kullum suna manne a waya, sun maida zuwa saudiya kamar shiga kasuwa domin bayan kowane sati biyu sai sun je suyi weekend can sannan su dawo. Feena tasan da yawa dangin mahaifiyarta kuma suna zumunci sosai. Alhamdulillah yau Amar ya kammala karatunsa cikin sa'a da nasara resold yayi kyau inda ya cinye komai 100%. Ya zama kwararren masani akan harkokin kasuwanci da kuma fannin na'ura mai kwakwalwa wato computer. Gagarumar walima Dady ya haɗa masa suka sha shagali da addu'oi. A cikin satin kuma ya fara aiki a sabon kamfaninsa wanda dama akwai komai na dangane da kayan aiki ma'aikata ma tuni aka nema sai kira kawai aka yi kowa ya fito. Masha Allah kamfani ya fara aiki da sa'a kuwa domin abubuwa sai ha6aka suke yi. Amar yana aiki tukuru yarinya yake jin kansa tamkar wani daban saboda sauye-sauyen da ya samu a jiki da ma rayuwarsa duka. Feena kuwa maraici ne ya fara shigar ta a Gida da makaranta rayuwa babu Amar ba daɗi, har gara ma na gidan ta zuwa har can ta same shi har ma ta taya shi wasu ayyukan amma a makaranta shiru ne gata bata da wata kawa balle saurayi ba wanda yake ra6ar ta.


A daddafe ta samu ta kammala ragowar shekara ɗaya da ta rage mata. Kasancewar cos ɗaya suka karanta abin ba wahala. Kafin fitowar takardunta kullum tare suke fita da Amar office har Dady da Momy suka fara faɗa wai zata je ta hana shi aiki da surutun ta. Shine ya gaya musu ai aiki take taya shi kuma takardunta na fitowa zai bata babban aiki yadda bazata yi nisa da shi ba. A cewarsa office ɗinta na nan yana jiran ta. Dady yace "to da kyau ku ci gaba da tarawa kan ku aiki, Amar kullum ina gaya maka ka bar Safeenah ta saba da nisantar ka ka ki, shin idan tayi aure ya zaka yi?" Amar ya sunkuyar da kansa kasa sai hawaye bai iya cewa komai ba ya tashi ya fice. Wunin ranar kam haka ya kare masa tamkar wanda aka zarewa laka, izuwa yanzu ya kasa tantance wane irin so ne yake yiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login