Showing 21001 words to 24000 words out of 48171 words
Chapter 8 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
haɗewa
Shi kanshi Amar bai taba ganin kyawun Safeenah ya bayyana kamar na yau ba. Sam ya gagara raba idon sa da kallon ta Murmushi kawai ya tsinci kansa da yi tareda tunkarar ta da hanzari cikin takunnan nasa na babban yaro.
Murmushinta ta kara faɗaɗawa ta nufe shi da zummar rungume shi yayanta Amar wanda tafi so akan komai da kowa a a cikin mutanen wannan duniyar nan
Abin da ya rage su haɗu kalilan ne hakan yasa Feena ta ware hannayen ta duka tareda lumshe idonta,
Kyakkyawar runguma taji an yi mata tareda manna mata kiss a wuyan ta cikin wani yanayi wanda ya rungume ta ya matsi kuibinta sai a Lokacin hancinta ya bambance mata kamshin turaren Amar da na wanda taji ya rungume ta
Da sauri ta buɗe kwayar idon ta tareda zuba su akan sa cikeda tsantsar mamaki
*Ya Mubbarak* ta faɗa tana ko'karin raba jikinta da nashi
*Afwan my fans, nasan ban kyauta ba dana tsayar da rubutu ba tareda sanar muku ba. Ku sani Nasmat batada burin batawa kowa da niyya kumin afwa hakan ya faru ne bisa wasu dalilai na sirri masoyana Kuna raina much love to you guys* 😍😘
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *27*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Mubarak ya sake mata wani lallausan murmushi, wanda bai ta6a yi mata irinsa ba tunda Allah ya haɗa zaman su a gidan.
Mamaki ya kara turnuke ta dai-dai lokacin da Amar ya karaso gaban su, su duka biyun ba wanda yayi magana sai dai kallon-kallo da suke wa junansu Mubarak yana yi mata wani kallo ne wanda ta rasa dame zata fassara shi, ita kuwa kallon mamaki da tantama take masa a ranta tana kissima abubuwanda bata tunanin kasancewarsu tsakanin ta da shi.
Duk tarin farin cikin dake cike da zuciyar Amar ya kau, sai ya tsinci kanshi cikin bakin ciki da jin haushin yadda Mubarak ya rungumi kanwar tashi kodan basuda jituwa dashi-dashi ne oho.
Bai jira komai ba ya kama hannun ta, ya jata zuwa wani gefe na 6angaren garden, duk wannan abin da ake yi babu wanda idonsa ya kai garesu saboda abin ya faru ne a kofar shiga main Palo na gidan, su kuwa mutanen da suka halarci bikin suna can tsakiyar gurin kowa da abinda yake yi.
A kan wata kujerar roba ya zaunar da ita ba tareda yace mata komai ba, shima ya zauna yana kallon ɗaya gefen ranshi a 6ace.
Kirjinta ne ya hau dukan uku-uku badan komai ba sai dan tarin 6acin rai da ta hango a cikin kwayar idon yayan nata.
Lokaci mai tsawo ba wanda yayi magana a cikin su, hankalin Safeenah ya koma tashi "me ya 6ata ran Yaya Amar haka?" ta tambayi kanta
Shi kuwa Amar zuciyar shi ce ta kasa nutsuwa "me wannan yake nufi?, a lokacin da Feena ta fito ta nufo shi da murmushi ya ɗauka gunshi ta nufo ashe ba shi ta nufo ba, dama akwai wata alaka ta jituwa tsakanin ta da Mubarak amma take nuna kamar ba ruwanta da shi?".
Sai kuma yaji haushin ta ya kama shi ya kara kama shi, cika yayi bam kamar zai fashe, yayin da yake dukan teburin dake tsakiyar su a hankali da hannunsa daya dunkule.
Feena ta kasa jurewa zafin da zuciyar ta take mata na ganin fushin yayanta, abokin tafiyar da rayuwar ta.
Tafin hannunta ta ɗora akan nashi dake kan table ɗin a hankali ta kira Sunan shi, "Yaya, wai meke faruwa ne ni ban gane makaba waye ya 6ata maka rai, nima kake neman 6ata nawa bayan kasan yau Ranar farin ciki ce a garemu baki ɗaya?.
Nasan ka fiye da kowa, kar kayi tunanin wani shiri ne tsakani na da Ya Mubarak, wlh ko magana baya yi min in ba ta faɗa ko hantara ba, ni kaina ina cike da maimakin abinda ya faru yanzu kuma yaya wlh na ɗauka kaina shiyasa na rike shi".
Ta karashe zancen tana share hawaye domin ganin yadda ɗan'uwan nata ya ɗauki zafi.
Ya yarda da Feena da kuma kalamanta, amma abinda Mubarak ya aikata ya kasa gogewa a zuciya da kuma kwayar idon shi, ganin zai rushe farin cikin da ta daɗe tana gidana ma wannan Ranar yasa ya kakaro murmushi yana faɗin "shikenan ai my Feena, ya wuce amma ki kiyaye domin Mubarak da Mamanshi mugaye ne, a koda yaushe basuda burin da ya wuce su cutar da mu, karki yarda wata alaka ta shiga tsakanin ki da shi kinji kanwata?".
Ya faɗa yana share mata halayen data fara yi, yace "karki yarda ki 6ata adonki, bakiga yadda kika yi kyau ba".
"Allah yaya?, wlh kaima kayi kyau sosai". Ta faɗa cikin sakin fuska da murmushi
Amar ya ciro wayarsa ya fara ɗaukar su hoto suna ta dariya
6angaren Mubarak kuwa daɗi ne ya lullu6e shi ganin yadda ran abokin faɗan shi Amar ya 6aci, koba komai ya sami hanyar da zai rika tusa mishi bakin ciki kamar yadda shima yake ji idan ya ga yadda Dady yake nan-nan da shi.
Tofa🤔
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/27/2017, 4:57 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *28*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Suna cikin ɗaukar hotunan ne suka ji shigowar motoci a gidan, hakan ne ya tabbatar musu da isowar Ummy Mahaifiyar Hjy Yusra.
Da gudu Feena ta nufi inda aka faka motocin tana tsallen murna, Amar yabita da kallo kafin daga bisani shima ya bi bayan ta, amma shi kam ba gudu yake ba (uhum Amar fa an girma lolz) .
Ummy na fitowa suka rungume juna itada Feena, kowanne su na bayyana irin farin cikin da yake ciki na ganin juna.
Dai-dai nan Hjy Yusra da Amar suka karasa gurin har kasa ta zube ta gaida Mahaifiyar tata, Amar ma haka ya gaisheta, Ummy ta ɗagota tana murmushi "Yusra na same ku lafiya?". Izuwa yanzu bakin Ummy yaji hausa sosai "lafiya lau Alhamdulillahi Ummyna ya hanya?". Haka dai suka shiga gaishe-gaishe wannan karon Ummy ita kaɗai ta zo sai kayan tsarabar ta.
Saboda karancin lokaci ko hutawa Ummy bata yi ba aka fara gudanar da bikin, inda mutane suka fara cike table ɗin dake gaban Feena da kyaututtuka, gaba ɗayan su kawayen Hjy Yusra ne.
Sai ɗaukar hotuna ake ana ajiye gifts, daɗi takeji kamar me, haka taro ya watse bayan anci ansha kuma an nishaɗantu.
Bayan sallar magariba ne suka hallara a babban falon gidan bayan kowa yayi wanka yayi salla, yau wani sakalci Feena take ji saboda ganin Ummy da tayi, kwance take bisa carpet ta ɗora kanta bisa cinyar Ummy tana zuba shagwa6a, wai taron nan duk ya gajiyar da ita.
Ita kuwa Ummy sai sannu take mata, haɗe matsa mata kafafuwanta. Momy Yusra Dady da Amar duka sun zama yan'kallo, a 6angare ɗaya kuma suna jin daɗin yadda Ummyn take tarairayar Feena tana nuna mata so.
Dady yai murmushi kana yayi maganar cikeda tsokana, "Ummy karfa ta karya miki kafa" da sauri Feena ta ɗago "kai Dady dan Allah ka bari, ni ina naga nauyin da zan karya wannan tsohuwar da Kuka riga kuka ginata da beta". Itama dai da tsokanar tayi magana dan sun saba irin wannan da Dad, yanzu sun saba sosai wasa sukeyi tsakanin su da Iyayen, kai ka ce a gidan aka haife su.
Ummy tace "Ke, lallaima Feena baki ganki bane kin girma fa". Ta shagwa6e fuska "amma ai ban yi girman da na wuce hawa cinyarki ba ko?".
Su duka sukayi dariya, Dady ya kawar da zance a lokacin da ya zura hannun shi aljihu ya ciro wani makulli sabo fill, ya kira ta da cikakken sunanta "Safeenah" "na'am Dady" ta amsa tareda tashi zaune tana kallon Dadyn, yace "ga yar karamar Kyautata a gare ku keda yayanki, wannan makullin motor ku ne kwananta biyu da zuwa, tana nan ajiye a parking space wadda kukaga an lullu6eta ɗin nan, kyauta ce dana baku.
Amar yarona ka girma na yarda da nutsuwa da kyan hankalin ka, zan sa Ilu ya koya maka tuki sai kufara kai kanku makaranta, kaga nan gaba kaida Feena zaku rika tafiya".
Safeena ta daka uban tsalle "Wayyo Allah daɗi, kai Dady amma wlh ka gama min komai, Allah dai ya biya ka da Aljannarsa maɗaukakiya". Dady ya amsa da "ameen ameen".
Amar ya kara matsawa dai-dai da kafafuwan Dady ya rusuna, yana daɗa yi mishi godiya, Dady ya shafa kansa "bakomai yarona kai dai ka dage da karatu ka kuma ɗore da kyawawan halayenka dana sanka da su, Allah yayi muku albarka". "Ameen Dady". Suka amsa a tare.
Wannan kyautar ta Alh bakaramin faranta ran Momy Yusra tayi ba, ta daɗe tana yi mishi godiya Ummy na taya ta, yace "haba wannan ai yiwa kai ne, yara namu ne ga baki ɗaya"
Ummy ma kwance Jakarta tayi, inda ta ciro tata kyautar a cikin wani ɗan karamin box ta buɗe
Wata dankariyar sarka ce mai matukar kyau da sheki sai walwali take tana ɗaukar ido, wannan ko ba'a faɗa ba sun san zinari ne. Ta ciro ta tana kallon inda Safeenah take, "zo nan". Ummy tayi maganar a takaice
Feena ta baro gaban Dady ta dawo inda Ummy ta tsuguna zuciyarta cike da farin ciki, Ummy ta kwance sarkar nan ta ɗaurawa Feena a wuya, sannan ta ciro ɗan kunnen ta saka mata bayan ta cire wanda ke sanye a kunnenta.
Feena ta kalli yadda sarkar ta kwanta a wuyanta, da sauri ta rungume Ummy tana yi mata godiya. Iyayen kuwa bakaramin fami ganin wannan sarkar yayi musu ba, sai dukan su sukayi shiru suna tuna wancan lokacin kamar dai haka, haka Ummy ta sakawa Baby sarkar nan da hannun ta.
Amar kanshi bin sarkar yayi da kallo zuciyar shi naso ta zargi wani abu.
Murna da farin ciki sun cika Feena ta rarrafa gaban Momy Yusra tana faɗin "Momy kalla, kalli sarkar da Ummy ta siyo min", Bakina sam yaki rufuwa saboda murna, amma ga maimakin ta sai taji Yusra batace komai ba, hasali ma gaba ɗaya yanayin ta ya sauya.
Ganin yaran zasu fahimci wani abu, Dady yayi saurin dafata "ya dai Yusra?". Ya kalli Amar yace "kuje, kuce Ilu ya nuna muku sabuwar motar ku". Suka mike suka fita cike da murna, a lokacin ne kuma Yusra ta sami damar fashewa da kuka.
Amar kuwa suna fita ya kama hannun Feena zuwa ɗakinshi a madadin inda suka nufa, zuciyar shi cike da tantama, so yake yaje ya tabbatar domin wannan sarkar da Ummy ta sakawa Feena a wuya tayi matukar kama da wadda Ummanshi ta bashi kafin rasuwar ta.
Wadda tace masa da ita aka tsinci Safeenah, kuma ta umarce shi da ya rike sarkar da aminci, ya kula da ita sosai domin tabbas sarkar ta musamman ce, dukda batasan takamaiman matsayin sarkar ba, amma tunda take bata ta6a ganin sarka mai kyau kamar ta ba.
kuma tana tunanin ko da ita za'a iya gano asalin Safeenah.
Wardrobe ɗinsa ya buɗe, kana ya sunkuya can kasanta ya ɗauko ɗaurin ledar ya fara kwancewa yana kallon Safeenah,
wadda har yanzu bata sami damar yi mishi magana ko tambayar abinda hakan yake nufi ba.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/28/2017, 9:59 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *29*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Bayan ya sami nasarar kwance kullin ledar ne ya zaro sarkar dake cikin ta, naɗe a cikin wata takarda. Safeenah kanta data kalli sarkar saida ta koma kallon ta wuyan ta, wadda Ummy ta saka mata yanzun nan. "Yayana wannan fa?" a ina ka samu?"
Baisamu nutsuwar bata amsa ba har saida ya karaso gabanta, yasa hannunsa ya ɗago sarkar da aka sa matan yana kare mata kallo, domin tantance bambancinta da wannan wadda Ummansa ta bashi.
Ya kuwa gano bambancin domin wannan tata ta jaranta karma ce, kuma zagayayya kamar sifar kwallo. Bayan wannan ma da rubutun larabci a jikinta wanda a yanzu zai iya karantawa, (Marhaba) haka aka tubuta ajikin wancan karamar. Sa6anin wannan da aka rubuta Sunan Safeenah da manyan haruffa na larabci.
Ya kara duban sarkokin ya cika da mamaki, ganin duk irin daɗewar da wannan karamar tayi haskenta da shekinta suna nan kamar na wannan wadda aka bawa Feena yanzu. Hakan ya daɗa tabbabar wa Amar cewa lallai maganar Ummanshi ta tabbata akan cewa wannan sarkar ta musamman ce.
Ya rumtse idonshi tareda damke sarkar a tafin hannunshi, yana tunano maganganun Ummanshi akan Safeenah, "Abinda yaya Larai take faɗa akan Safeenah gaskiya ne Amar, tabbas ita yar'tsintuwa ce. Sai dai hakan bai isa yasa akirata da shegiya ba, kai inma hakan ɗin ne meye laifin yarinya?". Maganar ta dawo raɗau a kunnen sa, tamkar a lokacin take gaya mishi ita.
"Babu Umma, wlh bata da laifi" ya faɗa cikin rauni kamar mai shirin fashewa da kuka Safeenah ce yaji ta dafa kafaɗarshi tana faɗin "Yaya, wacce ce batada laifin?"
Da sauri ya juyo ya kalleta, a lokacin idon shi sun fara kawo kwalla. Ganin zata gane kuka yake, yasa yayi saurin rungume ta dai-dai lokacin da halayen ke fitowa daga idonsa.
Tausayin rayuwar Feena ya kara lullu6eshi. A wani 6angaren na zuciyarshi kuma godewa Allah yake daɗa yi, akan taimakon da yayi musu ya inganta rayuwarsu ta hanyar haɗa su da waɗanan bayin nashi Momy Yusra da Dadynsu Alh Wakkala.
Cikin dabara ya kai hannunshi bisa kumatunsa ya goge hawayen fuskarshi, domin yasan da zarar ta gani yanzu itama zata saka kukan.
A sannan ne ya raba jikinshi da nata ya ɗagota suka fuskanci juna. "Kanwata Feena kinsan ina kaunar ki, Umma ma tana sonki sosai, ita ce ta bayar da wannan tace na baki, kuma tace taki ce tun kina jinjira". Ya faɗa yana nuna mata sarkar, lallausan murmushin nan nata ta sake mishi, alamun farin ciki ne suka bayyana karara a fuskarta. Ta kar6i sarkar "Allah sarki Ummana, ina kaunar ki Umma. Allah ya kai rahma kabarinki". Da sauri ta fara kiciniyar cire sarkar da Ummy ta saka mata domin maye gurbin ta da wannan wadda Umma ta bayar a ajiye mata.
"a'a kanwata, kar kiyi haka". Amar ya yayi maganar yana janye hannuta ga barin abinda take ko'karin yi. "me yasa?". Ta tambaye shi fuskarta cike da damuwa.
"Feena Umma tamu ce a kowane lokaci zamu iya amfani da abinda ta bamu, waɗannan bayin Allah kuma sune suka ɗauke mu a matsayin nasu, irin Soyayya da kulawar da suke nuna mana ko a gurin Iyaye sunada wahalar samu Safeenah. "Kiyi hakuri da wannan ta Umma har zuwa wani lokacin, yanzu ki zauna da ta Ummy idan kika cireta sam bazata ji daɗi ba". Shiru tayi na ɗan lokaci tana nazarin kalaman sa, tabbas abinda ya faɗa gaskiya ne.
"Shikenan Yaya, amma zuwa yaushe zan saka ta Ummana?". Tayi tambayar cikin sanyin jiki, da alama hakura kawai tayi amma tana muradin sarkar.
Yai murmushi "bafa ta Umma bace, taki ce". Ta kalle shi "to ai itace ta bani". Shiru kawai yayi dan bazai iya gaya mata yanda abin yake ba. Hannu ya zira ya kar6i sarkar ya maida ta cikin takardar nan ya ninketa, sannan ya saka a leda ya maidata inda ya ɗauko ta. Ya juyo ya kama hannunta suka fice.
Direct compound ɗin gidan suka nufa inda ake ajiye motocin gidan, Feena ce mai kwallawa Ilu direban gidan nasu kira. Cike da murna da farin ciki. Da hanzarin sa ya taso yana faɗin "Uwar ɗaki fita zamu yi?" Sunan da duka ma'aikatan gidan suke Kiran ta da shi kenan. "A'a Ilu, Dady ne yace ka nuna mana sabuwar motar da tazo jiya tamu ce, mu aka siyawa". Tayi maganar da yanayin nan nata na yaranta. Ilu ya hangame baki yana kallon Amar "gaskiya na taya ku murna domin ko Alhaji bai ta6a hawa motar da takai kuɗi da kyawun wannan ba". Ya karashe maganar lokacin da yake yayewa motar rufin da akaimata.
"wow" Safeenah ta faɗa cikin kwalalo ido waje. Amar kansa ya jinjinawa kyau da girman motar daɗi ne ya lullu6e zukatan matasan biyu. Tayi tsalle ta rungume yayanta "wayyo Allah yaya, daɗi zai kashe ni". Tare suka karasa gaban motor key ɗin ta saka ta buɗe kofar ta shiga shima ta buɗe mishi 6angaren driver ya shiga ya zauna yana karewa cikin motar kallo.
Wannan karon kasa 6oyewa yayi, hawayen farin cikin da suka gangaro daga idanun shi. Feena tayi saurin kai hannunta ta share mishi. "Meye haka kuma yaya?, me ya saka ka Kuka?". Shiru yayi na wasu dakiku yana kissima yadda rayuwa take tafiya da tsare-tsaren ta.
"Kinga rayuwa ko kanwata?, kinga yadda abubuwa suka canza daga tsanani zuwa daɗi ko?, shin ke baki ji wani iri ba Safeenah?". Ita ɗinma hawayen ne shar a fuskarta. "na gani yaya wannan duka ikon Allah ne, shi ne mai maida zafi sanyi ya kuma juyar da sanyi ya koma zafi, babu abinda ya gagari Ubangiji haka malamin islamiyyar mu yake gaya mana".
Ta matsa daf da shi ta kwantar da kanta bisa kafaɗarshi "haka Allah ya tsara mana tamu rayuwar Yayana, mu godewa Allah dan na tabbatar wannan shi ne Alkhairi akan zaman mu kauye". Ya share mata hawayen yana faɗin "Allah ya jikan Umma yayi mata rahma". tace "ameen ya Allah".
Makullin ta mika masa ungo yaya tayar mu tafi,