Showing 45001 words to 48000 words out of 48171 words

Chapter 16 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4632

Feena wanda idan ya ji an yi maganar aurenta sai hankalisa ya tashi ya nemi nutsuwarsa ya rasa.


Magana ta gaskiya ya kasa gane komai. Da dare misalin karfe takwas da rabi bayan sun kammala cin abinci ne Dady ya kira su zuwa ɗakinsa gaba ɗayan su harda Momy.


Da suka je ɗin ma ya ɗauki lokaci mai tsayi kafin yayi maganar da ban san yadda yaran zasu ɗauke ta ba. Can bayan shirun ya fara da kiran sunayensu a sanyaye "Amar da Safeenah" suka amsa a tare suna nazarin yanayinsa. Ya fara maganar cikin waswasi na samun nasara ko akasin hakan "ba komai yasa na kira ku nan ba sai dan sanar da ku wani al'amari da na lura har yau ku kun kasa sanin shi da kan ku, ko in ce kun San shi amma kun kasa gano shi." ya takaita yana kallon fuskokinsu. Sai da suka kalli juna sannan suka kalli Dady cikin rashin fahimta, sai ya yi musu murmushi sannan ya ci gaba da magana. "lokaci yayi da ya kamata ace kowannen ku ya mallaki muhallin sa na rayuwa, wato ya kamata ace yanzu dukkan ku kuna da aure" tare suka waro ido suka kalli Dady fuskokinsu cike da damuwa. Amar ya maida kansa kasa Safeenah kuwa kukan shagwa6a ta saka tana tirje kafa "Dady wlh ba zan yi auren nan ba, ba ku kuka ce idan nayi aure ɗauka ta za'a yi a tafi dani wani gidan ba? Shikenan an raba ni da ku an kuma raba ni da yayana. Wlh bazan yi ba." ta faɗa cike da hakikancewa tana matse kwalla. Momy tayi murmushi tace "kenan kina nufin har abada ke ba zaki yi aure ba?" ta gyaɗa kai alamar eh. "Koda ace yayan naki za'a aura miki ba zaki yi ba?" Dady ne ya watso mata wannan tambayar da tasa dukkan su ɗagowa suka zuba masa ido da alama maganar ta zo musu a bai-bai. Yayi murmushi sannan yace "mu yara bane kamar ku, mun riga mun fahimci matsalar ku mun kuma san maganin ta dan ba zamu tabbata daku babu aure ba kuma Allah bai haramta auren a tsakanin ku ba. Ni da Momynku mun yanke hukuncin haɗa ku aure domin hakan shi kaɗai ne mafita ga ɗorewar rayuwar ku cikin farin ciki." daga Safeenan har Amar sai suka ji kamar Dady yayi sa6o domin su a ganin su ai babu aure tsakanin su dan basu ta6a kawowa ba ko a mafarki. Wani irin nauyi ne ya sauka bisa kirji da kawunansu. Babu wanda ya iya furta komai amma harta Allah jin maganar suke kamar ma haramun aka faɗa. "Dady" Feena ta ambata cikin nauyin baki "Safeenah" shima ya kira sunanta a madadin amsa kiranta "Dady yayana ne fa" tace tana kallon iyayen nata. "To Safeenah yayanki uwa ɗaya ce ta haife ku ko uba ɗaya?"


Sai a lokacin tunanin Feena da Amar ya harbo musu wanna "ai kuwa tabbas da akwai aure tsakanin su amma taya zai kasance? Ta yaya zai kalli idon Safeenah ya furta mata kalmar soyayya? " Amar ne mai wannan tunanin cikin zuciyarsa. Ita kuwa Feena farin ciki ne ya lullu6e ta ciki da waje wanda har saida ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta. A ranta take kissimawa shikenan yaya Amar ya zama nata, yanzu babu wata macen da zata koma ra6arsa sai ita. Ta saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta tana murmushi, al'amarin da ya faranta ran iyayen nasu kenan domin hakan ya tabbatar musu cewa tana so kuma ta amince.


Shi kuwa Amar tsananin mamaki ne ya kama shi "me hakan yake nufi? Kenan Safeenah ta yarda da aure tsakanin ta da shi? Ko dai bata fahimci abinda ake nufi ba?". Can ya tsinkayo muryar Dady yana cewa "yauwa yar albarka dama nasan zaki so yayanki kamar yadda kike faɗa kin fi kowa son sa a duniya to yau gashi nan zai zama mallakin ki duka." ta mike da gudu tana dariya ta fice daga ɗakin. Momy tace "ja'ira ai wannan tata kuruciyar ta daban ce, dama haka take so ya daina kula kowa sai ita kaɗai." Alhjn ma dariyar yayi yace "ai gaskiyar ta gwara ta rike yayanta da kanta." Amar kam ko motsin kirki ya kasa yi ya rasa gane yanayin da yake ciki shin farin ciki ne ko kuma kunyar su Dady?


"Amar" Dady ya kira sunan sa. "Na'am Dady." Ya amsa dakyar. "har yanzu baka ce komai ba, shin ka kar6i kanwar ka a matsayin mata ko ko kana da wani za6in daban?" ya tsagaita yana kallon sa. Jin bai ce komai ba yasa ya ci gaba da magana "Amar nifa ba zan maka dole ga auren Safeenah ba, kuma dan baka aure ta ba sam bazan zarge ka da wani laifi ko kuskure ba domin ni nan shaida ne a kan son da kake yiwa Safeenah ko ni da na haife ta ba zan kaika son ta a aikace ba sai dai ko na faɗa a baki."


Kunya da nauyin Dady suka lullu6e Amar hakika shi kansa yasan ko yace baya son Feena karya yake, sai dai son da yake mata bashida alaka da aure ko soyayya dan a yadda yake jin son ta a ransa ma ya zarce irin son da saurayi zai yiwa budurwa ko matar da zai aura. "to amma tunda har Safeenah ta nuna ta amince zata aure shi ta yaya shi zai ki?". Kan sa na sunkuye a kasa yace "ba haka bane Dady wlh ina kaunar Safeenah son da ya zarce wanda saurayi zai yiwa budurwa ko matar da zai aura. Soyayyar aure ce ban ta6a yi mata ba ban kuma ta6a kallonta da wani nau'in so wanda ya zarce na wa da kanwarsa ba. Amma hakan ba zai sa naki auren Feena ba tana so na ina sonta nida ita mun fi kowa kusanci da sanin halayyar juna, ko dan gudun abinda zai faru da ni idan aka aurar da Safeenah ga wani zan aureta. Dan na tabbata Allah ne kaɗai ya san yanda zan zama ranar da kanwata tayi nisa dani. Dady nida Safeenah muna kaunar junan mu nasan so ba zai gagara ba. Mun gode da zurfin tunanin ku akan rayuwar mu Allah ya saka da mafificin alkhairinsa amin."


Dady ya sauke numfashi yana kara yaba hankali da nutsuwar Amar. Yace "haka muke son ji Amar tashi ka tafi Allah yayi muku albarka" ya amsa da "ameen" Momy ma addu'ar ta bishi da ita zuciyarta kal da farin ciki


Amar kam dakyar ya iya mikewa ya fita dan a lokaci ɗaya yaji kunyar waɗannan karmtaccin mutanen ta lullu6e shi.


To fa wani sabon al'amari tun daga ranar da aka yi wannan maganar Safeenah ta shiga yin baya-baya da Amar bawai na ki ba a'a yanzu wata irin kunyarsa take ji, idan yana guri sai ta noke babu yawan surutun nan ba tsalle da direwa a jikinsa. Shi kan sa nauyin yi mata magana yake yi idan yana kallonta. Amma abin mamaki sai suka maida rayuwarsu cikin waya wato a waya zai kirata su rakashe da hira kamar ba su ɗin ba, wasu lokuta ma harda taɗin soyayya suke ta6awa.


Dady da Momy kam ba jan lokaci Shirye-shiryen biki suka fara, daga Safeenar har shi ido ne nasu dan su Momy ne suke yin komai tun daga kan haɗa lehe har zuwa sauran kashe-kashen kuɗin da ake basu nemi komai a hannun Amar ba duk kuwa da cewa yanzu ya fara zama babban attajiri domin kamfani yana juyawa akwai kasuwa riba tana shigowa sosai. Ba'afi wata ɗaya da yin maganar ba suka ga an kawo iv an saka ranar biki a sati biyu masu zuwa. Farin ciki a zuciyar Safeenah ba'a magana haka Amar ɗin ma duk da baya nunawa.


A ranar larabawan saudiya suka sauka garin Kano wannan karon hadda Malam Mahmud mahaifin Hajiya Yusra wanda kafarsa bata ta6a takowa Nigeria ba, a cewarsa sai ya shedi ɗaurin auren jikarsa, farin ciki ya cika Hajiya Yusra domin tunda aka auro ta kafarsa bata ta6a zuwa gidan ba balle ya zauna yau gashi taci albarkar haihuwa mahaifinta ya zo gidanta har zai zauna na sati biyu. Su Aunty Sumayya sune iyayen Amarya na kurkusa ita da wata kawarta da suka zo tare ne suka dage da gyara Amarya ta ciki da waje. Gida ya ɗauki baki harda dangin Dady na nesa duk sun fara zuwa, kullum cikin tarbar baki ake.


Abu kamar wasa ranakun sai sauri suke kamar abinda ake turawa. Yau ne sati biyun da aka ɗiba suka cika, kuma yau ne dubbban ja'a suka shaidi ɗaurin auren zaratan masoyan Safeenah Tijjani (wakkala) da yayanta Amar Abubakar. ɗaurin auren da ya bar tarihi a cikin garin Kano a ranar gaba ɗaya gidajen TV da suke Kano aikin da suka wuni yi kenan na nuna wannan bikin da shahararriyar walimar da abokan Dady suka shiryawa amarya da ango. Hajiya Yusra da nata kawayen ma ba'a barsu baya ba. Biki kam yayi biki duk da ba wata bidi'a na party ko wani shagali amma sai da ka kwana uku ana jera walima a ko wace rana da Malaman da zasu yi. A kwana na ukun ne kuma amarya zata tare a rantsatstsen gidansu da Dady ya gama shirya musu komai na jin daɗin rayuwa a cikin sa. Gidan a bayan layinsu ne babu nisa da gidan Dan haka karfe takwas na daren aka kaita gidan mijinta bugun zuciyarta Amar. Ranar kam munga amarya wadda ba rakiyar kawaye domin bata da kawa ko guda ɗaya, haka yan kai amaryar suka barta ita kaɗai kamar mayya kafin shigowar angon. Shi kam ya samu rakiyar abokan aikin shi da yaran sa na kamfani, sune suka rako shi kuma suka musu addu'ar neman zaman lafiya da kariya daga sharrin sheɗan sannan suka yi sallama suka tafi.


Sam taba zama irin amaren nan masu nuna tsoron mazajen su a ranar da suka tare gidajen su ba, domin ta san nata angon amintacce ne. Tayi amanna cewar Amar ba zai ta6a cutar da ita ba.


Bayan kwana biyu su Ummy yan biki suka yi shirin komawa kasarsu, har gidan su je ita da Malam suka kara yiwa yaran nasiha tareda kara nusar da su gameda aure da manufofinsa. Sannan suka yi musu sallama suka tafi. Babu shakka dukkan su sun ji daɗin wannan faɗakarwa ta Malam da matarsa domin a da suna ganin kamar bazasu iya zaman da ake kira na aure da junan su ba, a tunaninsu tunda an ɗaura ai shikenan sun sami lasisin zama guri ɗaya na har abada ba wai sai sun yi wasu abubuwan ba. Amma zuwan Malam ya tunatar da su aure fa ba abin wasa bane ibada ne Shi kuma abinda suke ko'karin kaucewa sunna ne na Ma'aiki (s.a.w) a domin hakan ne kowannen su ya shirya tsab domin kar6ar ɗan'uwansa a matsayin abokin zamantakewar aure.


Yau sati uku da yin auren Alhamdulillah Amarya da ango sun zama ɗaya. Farin ciki da jin daɗin su ya kara nunkuwa


Ganin darajar juna da mutunta juna ya karu a tsakanin su, ko wannen su ko'kari yake ya nunawa ɗan'uwansa irin son da yake masa. Sai a lokacin suka yarda kuma suka gane cewa Dady da Momy gata suka yi musu da basu bari suka rabu ba. Sai godewa Allah suke da kuma iyayensu da sukayi wannan tunanin na haɗa su aure. A yanzu sun yarda kasancewar su ma'aurata shine hanya mikakka ta ɗorewar rayuwarsu a tare har abada.


Safeenah ta yarda Amar shine rayuwarta, kamar yadda shima yake ji a ransa babu mace kamar Feena a wannan duniyar yana kaunar ta ta ciki da waje yana jinta tamkar kurjin da ya fito ma mutum bisa zuciya.


Kimanin watanni bakwai da auren ciki ya bayyana a jikin Safeenah wanda ko Amar bai san da shi ba har saida ya ganshi ya fara girma. Allah sarki Momy da Dady harda hawayen farin ciki suka yi da labari yaje musu cewa Safeenah nada ciki wata biyar.


Amar kam nan ya kara sukurkurcewa ya zama bawan Safeenah in tari zata yi idonsa na kanta kullum cikin bautawa bukatun cikin nata yake kasancewar cikin yazo mata da laulayi ga yawan kwaɗayi yau wannan gobe wancan. A nan ne ta kara yarda da Amar ya cika *JA'JIRTACCE* domin duk abin nan bai ta6a nuna gajiyawa da bukatun ta ko kasawa duk kuwa da cewa aikin office na taruwar masa ta dalilin tsayawar da yake yi da ita yana bata kulawa ita da cikin ta. Amma ko sau ɗaya bai ta6a korafi ba.


Rayuwa kenan. Ranar wata litinim da sassafe ciwon nakuda ya sallamowa Safeenah. Nan fa aka ga tashin hankalin *JA'JIRTACCE* domin ko a asibiti da suka je kasa barin ɗakin haihuwar yayi duk da cewa tareda Momy suka tafi amma Amar ya kasa fita ya bar Safeenah cikin wannan halin duk kuwa da rokon da likitoci suke masa akan ya fita sam yaki dole suka hakura suka kyale shi suka koma kan mara lafiya. Da taimakon Allah da na likitocin Safeenah ta haifo yaranta biyu tagwaye mace da namiji a gaban Amar bayan tasha bakar wahala. Nan da nan kukansa ya tsaya farin ciki ya maye gurbin damuwar ganin yaran da uwar duka suna cikin koshin lafiya. Allah sarki Safeenah tausayin iyaye mata ne ya kara cika ta musamman yadda taji azabar haihuwa sai ta kara jinjinawa Momy da jarumtar ta da bata haɗiyi zuciya ta mutuba a lokacin da ta gama wahalar haihuwarta kuma aka sace ta.


Da wannan take tausayawa ya'yan da basa tausayin iyayensu ba kuma sa yi musu biyayya kamar yadda addini ya tanada. (nima dai Nasmat nace ya'ya mu kula musan su waye iyaye kuma muyi ko'karin kyautata musu. Allah yasa mu dace.)


Nan da nan labarin haihuwar Feena ya karaɗe dangi na kusa da na nesa suka sani. Tsakanin Amar da su Dady bansan wanda yafi wani murna da wannan haihuwar ba. Yara kam an kasa kwantar da su koda yaushe suna sungume ga Momy da Amar lokacin salla da bacci ne kawai yake raba su. Idan Momy ta kaɗaitu ita kaɗai har kuka take yi, tana kara sallamawa lamarin Ubangiji. Wai yau ita ce da jikoki ya'yan yar'ta. Haka Dady ma abinda ba'a cewa komai


Kwanakin su uku a asibiti aka sallame su suka koma gida. Kai tsaye gidan Dady aka wuce da su, inda zata fi samun kulawa ta manya. Washe gari Ummy ta iso ita kaɗai cike da zumuɗin ganin ya'yan jikarta. Suka haɗu ita da Momy gurin kula da Feena wajen gasa mata jikinta da wankan jego, sai kuma faman da ake yi da ita wajen shayar da yaran wai bata so tana jin ciwo. Haka zasu yi ta lallai6a ta har ta yarda ta bawa yaran abincinsu.


Amar kuwa ya zama daddawar ɗaya, kullum yana nan like da su hatta gurin aikin ya daina zuwa ɗakinsa dake gidan ya gyara ya tare a ciki. Tun Ummy na masa tsaya har ta gaji da kanta ta kyale shi bacci ne kawai yake raba shi da Safeenah da yaransu hatta abinci tare suke ci a ɗakin da take.


Tun ana gobe daren suna baki suka fara zuwa ciki kuwa harda Aunty Sumayya da maigidanta Uncle. Wannan karon basu zo da yara ba


Malam ma bai sami zuwa ba saboda gabatowar watan azumi suna Shirye-shiryen taron sa. Sai video calla da sue yi da shi yana ganin kyawawan yaran masu kama da iyayensu.


Ranar suna ta zo inda yara suka ci sunayen su na Hassan da Husaina ba'a canza masu wani ba. Alhamdulillah biki yayi biki dabbobin da aka yanka a wannan sunan ba zasu irguba domin kuwa Dady ji yayi kamar ya tashi gidan gonarsa duka, dan dama yana da takaicin yankan da bai yiwa mahaifiyarsu ba a lokacin haihuwarta sakamakon sace ta da aka yi. Allah sarki Dady ya hana Amar yin komai hatta kayan Feena da jinjiranta duk shi yasa aka haɗo musu.


Bayan kwanaki uku da sunan yan biki suka watse su Ummy ma duk sun tafi. Sai da Dady yayi da gaske sannan Amar ya fara zuwa office nan ma baya kai lokacin tashi sai dai yaje ya duba yadda al'amura ke tafiya ya dawo dai-dai lokacin da ya tabbatar Dady ya fita. Ita dai Momy nata ido ne domin tasan ikon Allah ne kaɗai ya isa raba tsakanin Amar da tilon yar' tasu Safeenah.


Watanni biyu cif Feena tayi a gidan iyayenta aka ce za'a maida ta gidan ta wannan karon Momy da kanta ta ɗebe kunyar yar fari ta gyara yar'ta. Amar kuwa duk wani abin amfani dake gidansu sai da ya fidda shi ya canza wani hatta kayan sakawa wasu sababbin aka zuba da sabon tsari.


ɗaki na musamman aka ware wa twins inda aka zuba musu kyawawan gadajen baccin jarirai da sef da kuma tulin kayan wasa iri daban-daban. Hmm wani abu sai mai hali. Ranar tarewar kuwa kamar ranar biki haka kawayen Momy suka zo da kyaututtukan su Feena da ya'yan ta saune kuma suka maida ta gidanta bayan an kara yi mata nasiha aka kara mata masu aiki mutum biyu waɗanda zasu taya ta renon yan'biyu.


Wani sabon shafin soyayya ne aka buɗe a gidan ma'auratan wanda ya kusa nunka na farko da suka yi. Ya'yan su sun zama taurarin su ababen so da kaunar su. Tuni Amar ya tashi daga yayana ya koma *JA'JIRTACCE* a bakin Safeenah inda ita kuma take amsa sunan kanwata har kwanan gobe.


6angaren addu'a kuma basa mantuwa da Umma da Abbansu kullum addu'a suke Allah ya jikan Umma da Abba Allah kuma ya kara haskaka rayuwarsu da farin ciki.








Nima Nasmat nace ameen ya Allahu, fatan alkhairi ga ilahirin rayuwar Safeenah da *JA'JIRTACCEN* yayanta harma da yaransu baki ɗaya.


Fatan alkhairi gare ku masoya makaranta wannan littafi a duk inda kuke. Alhamdulillah a nan na kawo karshen wannan labari mai ɗauke da sakonni bila adadin da fatan masu karatu sun amfana.


Yar'mutan Arkilla na godiya bisa goyon bayan ku da juriyar bibiyar littafin ta. Kaunar da kuke nuna min a koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login