Showing 3001 words to 6000 words out of 48171 words

Chapter 2 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4651

ya tallawa Lado shi a ka, habawo nanfa kato ya ware baki yasaki uban ihu ya dafe gurin yashiga lalube da kaiwa iska duka, jini kuwa ya balle daga goshin shi sai hargowa yake. Amar ya gama rikicewa da rud`ewa, babbar amina dake ajiye a kuryar d`akin ya bud`e ya d`auko wani kullin keda ya cusa a aljihun wandon shi.




daga can yajiyo muryar ba'ba Larai tana fad`in me nake ji haka? Kai Lado meya sameka? ga dukkan alamu fitowa takeyi daga d`akin ta nanfa Amar ya tashi Safeena yaja hannun ta suka fita d`akin da gudu ba'ba Larai sai inuwarsu ta gani sun fice fit ga kukan d`anta da ihunsa sun cika gidan " ku la'anannu me kukayiwa Lado? ta karasa d`akin da sauri halin data ganshi ya sakata kuka taja hannun sa zuwa tsakar gidan ta shiga wanke masa jinin kafin ta barbad`a mishi dakakkiyar bagaruwa maganin tsayar da jini da kashe zogi


Amar kuwa yana fita gidan ba'ba Uwale ya nufa ya buga kofar yakai sau biyar amma ba'a bud`e ba dama yasan sun isa yin bacci, jin ana fitowa daga gidansu yasa ya koma jan hannun Kanwar shi suka kama hanyar fita daga cikin kauyen da gudu. Hanyar kasuwa suka d`auka duk da cewa darene sosai amma hakan bai hana suka sami mutane a kasuwar ba keburori ne masu loda kayan amfani da aka siya amotoci za'a kaisi birnin kano, cikin alamar maganar kurame Amar ya umarci Feena da tayi shiru dasand`a ya lallaba yana janye da hannun ta dakyar ya d`agata ya jefata a babbar motar kafin shima ya kama ya hau wani lungu suka samu inda aka rage d`an fili a mitar suka tsuguna, sunaji aka sallami masu lodi aka tashi motar tafara tafiya. Cikin duhun daren Amar yayiwa yan tsirarrun gidaje da d`akunan garin su kallon bankwana batareda yasan inda zasu ba shidai yasan duk inda zasu gwara su tafi su rayu, dan ya tabbatar wannan fasa kan daya yiwa Lado ba makawa idan yakama su zai iya kashe su duka. Cikin wannan halin ne ya lura da kanwarshi na kyarmar sanyi ga wajan da taji ciwo duk jinin ya bata mata gefen fuska, da sauri ya janyota kusa da shi ya yaga habar rigarshi ya fara goge mata jinin duka sannan ya koma yago wani kyallen ya d`aure mata kan. Yajata zuwa jikinshi ya rungume ta cikeda tausayin rayuwar su a nan ne yaji jikinta zau da zafi alamar zazzabi zai kamata nanfa hankalin shi ya kara tashi




*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *5*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍




"Feenah gurin yana miki ciwo ne?" Ya tambayeta cikin inna-inna ta yanayin fargaba. Feenah ta gyad`a mishi kai ba tareda tayi magana ba dan ita kad`ai tasan azabar zogin da wajan yake mata, musamman daya d`aura mata kyallen rigar nan kasancewar rigar tana da detti sosai. "Wayyo Allah kanwa ta Allah ya baki lfy sannu kinji,". Ya fad`a yana bubbuga bayan ta alamar rarrashi. Wasu za'fafan hawaye suka silalo daga idonshi, tunawa yakeyi da lokacin da Umma tana raye, baisan lokacin da yafara sambatu ba, "kin gani ko Umma na, saida nace karki tafi, karki barmu da wad`ancan azzaluman Umma ki kalli yanda suka maida miki mu, yan gayun yaranki sun dawo yan daud`a, d`an dako da yar'talla haka suka maida miki mu Umma, yau gashi ma sun rabomu da gidan Umma bansan inda zamu ba" sai kuma ya fashe da kuka kafin ya cigaba da cewa "kalli halin da suka jefa miki yar'amanar ki, sun illata miki Safeenarki Umma meyasa kika zabi tafiya akan zama damu?" Ya koma fashewa da kuka ya kara kankame Feenah domin yasan Umma bazata taba amsa mishiba. Safeenar ce cikin yanayin zazzabi take tambayar shi "Yaya gurin Umma zamu je? Yaya dama kasan inda Umma take shine tun da can baka kaini ba? Sai itama ta fara kuka.


Ganin hakan yasaka ya tsayar da nashi kukan ya shiga rarrshin ta dan kar zazzabin ya karayi mata karfi, haka yayi ta bubbuga bayan ta yana mata wakar dasukeyi a islamiyyarsu da suke zuwa kafin rasuwar Umma, wakar "IYAYE NA NE GATANA", Safeenah na son wakar sosai shiyasa suka haddace ta, a duk lokacin da suke cikin damuwa sukan rerata tare ko kuma idan Safeenar tana kuka sai Amar yayita rera mata wakar har sai tayi bacci. Yanzun ma kuwa hakan akayi yanayi yana zubda hawaye, tun tana ajiyar zuciya mai nauyi har bacci yayi awon gaba da ita, a hankali shima ya d`an zame ya kwanta, ya gyara mata kwanciya a gefen jikin sa ya shiga tunanin koya rayuwar shi data kanwar shi zata kasan ce nan gaba? Bai sami lokacin yin wani dogon tunanin ba dan shima baccin ne ya d`auke shi,


Ba'ba Larai da kanta ta biyo bayan yaran cikin daren nan tadinga neman su ko wanne lungu da sako na kauyen zuciyarta cikeda mugun nufi akan su, sai dai bata gansu ba. tayi kofa ta koma gida, a ran ta cewa take duk inda suka shiga ai zasu dawo haka ta koma gida tana ta faman sababi da la'antar Amar da Safeenah, Lado na kwance yayi wani shame-shame a taburma abin dariya kan nan nashi ya kumbura yayi suntum dakyar yake numfashi, shima dai rayawa yake yi a ran sa duk ranar da ya warke ciwon nan ba abinda bazai iya yiwa yaran nan ba. (Nikuwa Nasmat nace daga baya kenan lolz)


Amar da Safeenah sunyi bacci sosai domin kuwa basu suka farkaba sai wuraren karfe goma na safiyar Al'kamis. Amar ne ya fara farkawa fuskar kanwar shi yafara kallo kafin komai, wurin da kanta ya bugun ya d`anyi kunburi kad`an a hankali ya zameta daga jikinshi sai yashiga mamaki ganin har yanzu motar tafiya take yi, yasan dai tun daren jiya ta tashi gashi har gari ya waye rana ta haska ko ina, to ko ina wannan motar zataje? Ya tambayi kansa tambayar da bashida amsar ta kawai dai abinda yasani shine koma inane zataje to gurin yanada nisa sosai. Yana cikin saka da warwara Feenah ta farka ahankaki ta fara bud`e idonta bata diresu ko inaba sai kan fuskar yayan ta shima dai ita yake kallo suka sakewa junan su murmushi. Ta yunkura zata tashi Amar ya taimaka mata ta hanyar tallabota da hannayen sa duka biyu, suka fuskanci juna yace sannu Feenah ya kikejin gurin yanzu? Ta koma sake mishi wani murmushin a karo na biyu tace naji sauki yaya, ya kai hannu ya taba jikin ta sai baiji irin zafin da yayi mata jiya ba Alhamdu lillah ya fad`a yana kallon ta. Yaya, ta kira sunan shi na'am kanwa ta, ya amsa yana kallon ta cike da kulawa. kafin ta fad`i abinda ke bakinta sai sukaji motar ta shiga wani guri mai yawan mutane anata hayaniya


Da sauri Amar ya mike ya leko ta bayan motar dan ganin inda suka shigo. ikon Allah wani babban birni ya gani guda sukutum yana cike da mutane sai hada-hada ake da kai komo, da sauri ya juyo ya riko hannun kanwar tasa ya mikar da ita "zoki gani kanwa ta" mamaki da al'ajabi suka mamaye ta "nan kuma ina ne yaya? Anan Umma take? Ta jero mishi tambayoyin a d`okance. Murmushi yayi mata a madadin amsoshin tambayoyin ta ya safa kanta nan wata duniyar ce kanwa ta, ki kalla ki gani komai nasu daban yake da inda muka fito. Feenah tabi wurin da kallo cikeda mamaki yaya wai ina zamu je ne? Inda Allah ya kai mu Feenah ni kaina bansan inda zamuje ba. Hawaye suka silali daga idon shi dai-dai da tsayuwar motar a tsakiyar kasuwar dawanau, tuni kasuwar ta fara cika da masu kawo kaya kowa sabgar gabansa yakeyi hakan yasa babu wanda ya lura da fitowar yaran daga cikin motar da tsayuwarta ya sakko da kanwarshi sannan shima ya diro ya kama hannun ta suka bar gun suka nausa cikin kasuwar ba tareda sanin inda suke ko inda suka nufa ba.




*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *6*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍






Tafiya sukayi mai tsawo wadda ta rabasu da kasuwar ta sada su da wata babbar anguwa mai d`auke da manyan gidaje da shaguna a gefen titi, nan ne Safeenah ta fara gazawa yunwa take ji da kishrwa ga azababben ciwon da kanta yake mata. Tirjewa tayi ta tsaya Amar ya kalle ta da alamar tambaya, cikin yanayin gajiya tace "yaya ni na gaji kuma Wlh yunwa da kishi nake ji". nan da nan tausayin kanwar tashi ya kama shi. cikin tausasa murya yace "kiyi hakuri Feena anan bansan abinda zanyi in sami kud`i ko abinci ba, amma saboda cika alkawarin danayiwa Umma na kula da ke ba abinda bazan iya ba". Yana kaiwa nan ya kama hannun ta suka nufi wani babban shago dake gaban su. Suna zuwa yayi sallama, ba Wanda ya kulasu a haka yafara rokonsu "dan Allah bayin Allah Ku taimaka mana da sadakan abinda zamu ci saboda Allah" wani gaye dake tsaye akofar shagon ya d`aga mishi hannu yace "yi hakuri ka kara gaba" Amar yayi shiru yana kallon biredi dake ajiye a kan teburan su. Gayan nan ya daka mishi tsawa "zaka bar nan kosai na mangare ka, sha'shashu kawai banga amfanin iyayen Ku ba indai bazasu iya cida Ku ba"




Amar yayi kasa da kansa lokaci d`aya wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatun sa. Yaja hannun kanwar shi suka nufi shagon gabada wannan. Hajiya Yusra dake tsaye cikin babban shagon tabi bayan su da kallo, yanda tagan su a hargitse kayan jikin su a yayyage sai suka bata tausayi ga uban raunin dake kan karamar yarinyar, ta tabbatar koda sunada iyaye to marasa karfi ne domin kuwa babu wata Uwa dazata iya kallon ya'yan ta cikin wannan dettin ta barsu dashi sai dai in batada halin gyara musu.


A shago na gaban ma basu sami komai ba haka aka Kore su, dama mazauna wajan sun fara gajiya da yawan mabarata musamman kananan yara wayanda ya kamata ace suna makaranta. A ganin mutanen iyaye irin wayan nan yaran sun maida rayuwar ya'yan su tamkar jarin kasuwanci su suke turasu kasuwanni da tashoshi, har ma da madakar motoci.


Haka Amar ya ding a bin shagunan d`aya bayan d`aya yana baran abinci wa kanwar shi, amma abin kamar had`in baki duk inda suka je korar su akeyi ana hantar su tareda fad`ar bakaken maganganu akan iyayen su abinda yake tilastawa Amar zubda hawaye kenan. Ji yayi Feena ta tsaya ga tafiyar da sukeyi da nufin zuwa wani shagon ya juyo da sauri ya kalle ta Feena lafiya? Hawaye ya gani yana zuba a kan kumatun ta tace "yaya dan Allah ka daina rokon su ni na daina jin yunwa dan Allah yaya" ka karashe maganar da kuka mai sauti. Shima kukan ne ya subuce mishi suka dinga kuka ba mai rarrashi ya jata jikinshi ya rungumeta a lokacin ne yaji zafin jakin ta ya tsananta da sauri ya janye jikinshi daga cikin nata "Safeenah me yake domin ki? Kan ne yake miki ciwo? A razane yake mata wayannan tambayoyin shiru tayi bata ce dashi komai ba yaja hannun ta suka nufi karkashin wata baranda wadda ba kowa acikin ta ya zaunar da ita agefe shima ya zauna ya fuskance ta.




Kanwata ya fad`a yana taba kumatun ta da bayan hannun shi ta amsa dakyar a lokacin jikinta yafi kowane lokaci zafi. Yace "kan ne yake miki ciwo?" Tace "eh" "sannu kinji" yace mata ta gyad`a kai gawaye nabin kumatun ta. nan da nan jikinta ya fara kyarma ta zame daga zaunen da take ta kwanta a kasa. Nan fa hankalin Amar ya kara tashi baisan sanda ya fashe da kuka ba, ya d`auki kanta ya d`ora a cinyarshi ya fara sambatu. "Dan Allah Safeenah karki min haka, kin sani ke kad`ai kika rage min Abba ya tafi Umma ma ta bishi yanzu Feena idan kika bisu nikuma dawa zan rayu?, Dan Allah kitsaya ki rayu da d`an'uwanki". Ya koma fashewa da kuka




"Hajiya Yusra dake tsaye a Kansu itama kalaman Amar sun sakata kuka, ta share hawayen dake fuskar ta ta tsuguna gaban yaran tace "sannu yaro", Amar ya d`ago a d`an tsorace ya zuba mata ido, murmushi tayi mishi tace me ya sami kanwar taka ne?" Saida ya kalli Safeenar sannan yace "kanta ne ya bugu tun jiya ya saka mata zazzabi gashi kuma tanajin yunwa da kishirwa, dan Allah ki taimake ni da abinci inbata kar ta mutu" wasu hawayen suka koma zubo masa


Hajiyar ta kara nutsewa cikin tausayin su takai farin hannun ta ta taba jikin yarinyar zafin da taji ya tsorata ta, zazzabi ne mai karfi yake addabar ta. da sauri ta d`ago tace da Amar "zan taimake ku yanzu kuwa" ta saka hannu cikin handbag d`inta ta ciro dalleliyar wayarta tayi searching wata number tayi dialling, ringing biyu aka d`aga da harshen turanci yayi magana da wanda ta kira d`in wanda nake kyautata zatan direban ta ne, misalin gun da take tayi mishi. ba jimawa sai gashi da wata irin had`ad`d`iyar mota doguwa mai kofofi shida a kowane bangare, da gudu ya fito ya bud`e mata motar ganin ta nufo ta d`auke da karamar yarinya, Amar na biye da ita a baya






*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:42 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *7*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍






Tana zuwa ta saka yarinyar, sannan ta juyo ta kama hannun yaron shima ta saka shi itama ta shiga driver ya rufe ya koma mazaunin sa ya tayar saida ya hau titi sosai sannan ta gaya mishi asibiti zai kai su, Emanuel ya kad`a kan motar ya d`orata a hanyar asibitin da ake kula da lafiyar su Hajiyar.


Hajiya Yusra tajawo Safeenah ta sakata jikinta sosai ta rungumeta duk yawan dettin dake jikin ta, da kuma rashin sanin inda yaran suka fito bai dameta ba, yanayin yarinyar kawai take kallo dan zazzabin nata kara tsananta yake yi. Haka ma Amar duk tsari da daular dake tattare da motar Hajiya bai d`auki hankalin shi ga barin kallon kanwar shi ba, hannun shi na rike da nata duk kuwa da cewa tana rungume a cinyar Hajiyar, motar kuwa mota ce wadda bai taba ganin irinta ba. Motar Hajiya Yusra cikinta ya kasance tamkar wani karamin falo, kujerun ta suna zagaye da wani d`an karamin table na glass ba a jere kujerun suke ba kamar kujerun motocin daya taba gani.


A farfajiyar asibitin drivern ya nemi guri yayi parking ya koma fitowa da gudu ya bud`e mata kofar ta fito d`auke da yarinyar a hannu tayi cikin asibitin yaron yana biye da ita da sauri-sauri gudu-gudu suke tafiyar. Da shigar su nurses suka karbi yarinya suka shigar da ita. Ita kuma Hajiya sai ta nufi office d`in likitar su Dr.Batul, Amar kam wayanda suka d`auki Feena yabi aka kwantar da ita a gadon asibitin suka fara bata taimakon gaggawa wannan raggan dake d`aure da kanta suka kwance suka shiga wanke raunin. Suna cikin yi Hajiya ta shigo tareda likita Dr Batul ta duba yarinyar ta d`aura mata drip sannan ta rubuta mata magunguna ta bawa Norse d`aya tace "taje ta karbo su yanzu su bata". Ta juya taja hannun Hajiya suka koma office d`inta


Dr. ta kalli kawar ta Yusra tace "ke kuwa ina kika samo wayannan ditty?" Hajiya tayi murmushi tace Wlh a hanya na same su suna bukatar taimako ne shiyasa na taimake su" tayi shiru tana kallon yanayin fuskar kawar ta'ta. Batul ta yatsina fuska tace "to ai da kud`i kika bawa iyayen su su kaita asibiti ba sai kin bawa kanki aiki ba"


Ta sauke numfashi tace "bana tunanin suna tare da iyayen su, but ban tabbatar ba nidai su kad`ai na gani"


Tace "hmm Allah dai ya agajeji da zuciyar kin nan, ta cika tausayi kar wata rana a d`ana miki tarko da abin tausayin"


Yusra ma murmushin tayi tace "Allah ma ba zai bari ba kawa ta, yanzu gaya min wane hali yarinyar take ciki?"


Tace "batada wata matsala wannan buguwar da kanta yayi ne kawai sai yunwa data addabeta, amma da zarar ruwan suka shiga jikin ta zataji saukinta kafin taci abinci"


Hajiya Yusra ta dafe kanta "Oh Allah ya bata lafiya", ta mike tana fad`in "bari in tashi in bawa d`an'uwanta abincin tun shima bai fad`imin ba in boni" ta fice da sauri


Dr. tabi bayanta da kallo tana murmushi a ranta tace "Yusra bazata canza ba.
Zaune ta sami Amar a kan gadon da Safeenah take kai, nurses sun fita bayan sun bata magunguna har tayi bacci yana rike da hannunta wanda aka d`aurawa Karin ruwan, ya zuba mata ido yana hawaye. Ita kuwa baccinta take hani'an bai d`auke kansa daga kallon dayake mata ba, ya dai amsa sallamar Hajiyar. Kasa da shi ta zauna tace "Alhamdulillah likita tace da zarar ta farka shikenan kayi hakuri ka daina kuka kanwar ka bazata mutu ba kaji" ya gyad`a mata kai


Emanuel yayi nocking door aka bashi iznin shiga ya shigo sai da ya tsuguna har kasa sannan ya mikawa Hajiyar wata leda d`auke da abinci take a way gidan biyu da robar ruwa data lemuka bibbiyu ta karba sannan ya mike ya fita. Ta bud`e ta fiddo takeaway d`aya da roban ruwa da lemu ta ajiye a gabanahi ta bude abincin masha Allah pride rice ce wadda taji Corry da kayan vegetables ga wata lafceciyar cinyar kaza an kifa akan abincin. tace "kaci abinci kafin kanwar ka ta farka itama ga nata nan"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login