Showing 9001 words to 12000 words out of 48171 words
Chapter 4 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
gurin. Sai da motar tayi nisa har ta bacewa ganinta sannan ta ajiye yarinyar a gefen hanya. take ta gaggauta barin gurin ta kama hanya taje wata kasuwa ta hau motar kano ta koma
A gidan Alhaji Tijjani kuwa hankula ne suka tashi a lokacin da aka tabbatar da batan jinjirar da aka haifawa Wakkala babu inda ba'a bincika ba amma bata gidan haka ya tabbatar musu da cewa d`aukar ta akayi Alhajin da Hajiya duk a sume aka kaisu asibiti. Babu irin cigiya da binciken da ba'ayi ba amma ba'a gano yarinyar ba tun daga wannan ranar bakin ciki da damuwa suka dankare zukatan masoyan biyu duk wani mai kaunar su sai da ya tausaya musu a ranar bakin ciki ya kashe mahaifiyar Alhaji saboda tanada hawan jini mijinta farin dattijo ya kwanta jinya. Hajiya Ummu dad`i kamar ta zuba ruwa kasa tasha miliyan Goma tabawa kawar ta Eysha sannan ta bazama duniyar bokaye gurin neman asirin da zai hana Alhajin sake haihuwa har abada. Allah ko ya amsa musu dan tun daga wannan jinjirar Hajiya Yusra bata koma yin koda batan wata ba, idan sukaje asibiti sai ace lafiyar su lau lokaci ne bayyi ba
Daga baya mahaifin ahi ma Allah yayi masa rasuwa shi kuwa Alhaji Wakkala Allah ya jarrabeshi da masifar son yara kamar me Gashi shi kad`ai ne baida wa ba kani balle ya ga ya'yansu yaji dad`i. Hakan yasa Hajiya Ummu ta d`auko d`an yayarta Mubarak tana rikon shi
Wannan kenan
*cigaban labari*
Dam! Gaban Yusra yai mummunan fad`uwa a lokacin da idonta ya sauka ga Safeenah
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *12*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍
Ji tayi kamar taga wani Abu da ta taba sani a baya, kamar photo haka ta tsaya a kofar idon ta kir akan yarinyar tabbas tasan fuskar nan inji wani sashe na zuciyar ta. "Eh kin Santa mana tun bayan wasu awanni da kika fara ganin ta" Zuciyar ta ta tabbatar mata inda tasan yarinyar, sannan tacigaba da kawo mata dalilai da hujjoji Wato lokacin da kika fara ganin ta kyau da hasken fuskar basu fita haka ba shiyasa yanzun kika ganta kamar wata sabuwa. Wannan duk bayani ne na zuciyar Hajiya Yusra wanda ta koro mata a dalilin sarkakiya da ta shiga na tunanin ta taba sanin fuskar Safeenah. Tamayar da kofa ta rufe sannan ta karasa shigowa. Sai a lokacin yaran suka sanda shigowar ta'ta gaba d`aya suka kalle ta fuskokin su d`auke da murmushi, itama dai murmushin take ta isa gare su ta shafa kawunan su tace "yarana kunga yadda kuka canza?, kai masha Allah gaskiya kunyi kyau"
sunji dad`in yanda ta yaba kyan na su dan su Kansu sunajin kan su daban. Suka kara fad`ad`a fara'ar su dai-dai nan Dr. Ta shigo hannun ta rike da wasu files da Jaka tace "yi hakuri na tsaya had`a kayana ne," ta fad`a idon ta akan Yusra "Bakomai kawata, ya kika ga yara na?" Sai a lokacin idon ta yakai garesu "wow! Masha Allah gaskiya na tayaki murna Yusra" Dr.Batul ce mai wannan maganar fuskar ta d`aukeda murmushi ta koma cewa " to ko dai zamuyi raba dai-dai ne?" Ta fad`a cikeda tsokana Yusra ta harare ta kafin taja hannun yaran ta nufi kofa tana cewa "to sarki had`ama babu naki a nan, yar rainin hankali su kuma yaranki hud`u ki kaisu INA?" Dr. tayi dariya "to sarki rowwa na bar miki Allah ya taya ki riko" tana maganar tana binsu a baya tare suka fito farfajiyar Asibitin suna tafe suna hira yaran na rike a hannun Yusra inda sukayi sallama kowacce ta nufi inda motar ta take, har zasu shiga Amar yayi wata irin zabura kamar wanda aka tsikara "Innalillahi" ya fad`a yana laluben aljihun wandon sa ganin ba wandon shi bane ya tuna masa an cire mishi wan can a lokacin da za'ai mishi wanka. da karfi ya kwace hannun shi daga cikin na hajiyar ya juya da gudu ya koma d`akin da suka fito. da sauri Hajiya tabi bayan shi tana tambaya "Amar lafiya? Ina zaka?" Inaa ko juyowa baiyi ba, dole tabi bayan shi tana rike da Feena dake ta faman Jan hannun ta da nufin suma suyi gudun su same shi.
Toilet d`in d`akin ya fad`a yana dube-dube amma me? Baiga Kayan da aka cire musu ba, ba nashi ba na Feena ya koma fitowa da gudu zai bar d`akin a kofar suka ci karo da su Hajiya harma da Dr. "Kai Amar lafiya, me ka ke nema?" Hajiyar ce mai wannan tambayar "Umma kaya na wanda aka cire min su nake nema" ya fad`a lokacin da kwalla suka cicciko masa ido. Hajiyar tayi ajiyar zuciya tace "banda abinka Amar ai ka gama da wannan Kayan zo mu tafi sababbin kaya zan saya muku masu yawa" ta karashe maganar tareda mika hannun ta zata riko nashi.
Yai baya yana girgiza mata kai "a'a Umma akwai wani Abu mai muhimmanci a cikin wannan kayan dan Allah suna ina?" Ya yi tambayar a lokacin da hawaye suka fara gangarowa bisa kumatun shi "haba Amar meye abun?, kayan nan fa an riga an saka su a shara". "Shara" ya fad`a ido waje "wane sharar?" "Dan Allah wane shara?, Ku taimaka Ku nunamin sharar Alkawari na d`aukawa Umma'na gashi zai karye, Ku taimake ni amanar Umma ce." duk wayannan maganganun cikin kuka Amar yake yin su, Al'amarin da yabawa su Yusra da Dr. mamaki to meye a kayan da yaron yake yiwa kuka haka? Dr. ce ta dafa kafad`ar shi tace "to ya isa Amar bari inkira nurses d`in in tambaye su inda suka kai kayan"
Tana rufe bakin ta sukaji an turo kofar d`aya daga cikin nurses d`in nan ce sai da ta rusina ta gaishe su baki na ruwa tace "Hajiya wani muhimmin Abu na gani a cikin Kayan yaran nan, lokacin da naje jefarwa ya fad`o" tana maganar ne tana kallon Hajiya Yusra
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *13*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍
"Wai Alhamdulillah, to gashi ma an gani, kawo nan, mun gode fa" duk Hajiya Yusra ce mai wannan maganar cikin fara'a da jin dad`in bayyanar abin duk da batasan asalin mene ne ba, sai dai ta san samun shi d`in shine kwanciyar hankalin su baki d`aya, duba ga yadda yaron ya d`aga hankalin shi akan shi
Norse ta mike tareda mikowa hajiya karamin abin dake d`aure a cikin leda, wuf ! Amar ya damke ledar yana fad`in "mun gode sosai Allah ya saka miki da alkhair" sai da ya bawa Hajiyar dariya, nurse d`in ma sai da ta dara sannan ta juya ta fice. ya kanannad`e abun ya cusa a aljihun wandon shi, sannan Hajiyar ta kama hannun shi suka tafi. Dr. Tace "Yusra wannan yaron naki akwai rigima yanzu haka abun wasa ne yake yiwa rigima haka" hajiyar tace "bar shi ya yi ai rayuwar yaran kenan" suka yi dariya a nan suka yi sallama kowacce ta nufi motar ta suka shiga.
Wata kebabbiyar anguwa aka shiga dasu wadda bata cika yawan mutane ba, tituna ne layi-layi sai maka-makan didaje na Masu kud`i babu alamar karamin gida ko ginin talakawa a anguwar. A kofar wani gidan suka faka driver yayi horn wani jibgegen inyamuri ya bud`e musu gate tare da rusunawa yana mika gaisuwa ga Hajiyar. A filin parking ya tsayar da motar sanna ya fito da sauri ya bud`e musu kofar suma suka fito. nan fa Amar da Safeenah suka koma asalin su na kauyawa, suka hau kallace-kallace da waige-waige. Sun kasa tantance wannan wane irin gida ne wanda ko a mafarki basu taba ganin irin shi ba
Murmushi tayi ta kama hannayen su suka shige ciki zuciyar ta cike da farin ciki wanda ita kanta batasan na meye da meye ba, domin a ganin ta farin cikin da take ji a ranta ya zarce na samun yaran kawai, ji take kamar ta cike wani gurbi ta data rasa a rayuwar ta. "Salamu Alaikum" tayi sallama a falon gidan na su wanda yake a had`e Wato (general falo) Alhaji Tijjani (wakkala) dake zaune a falon ya mike a d`okance ya taro ta "wa Alaikissalam, mata ta, where have you been?" Ya fad`a tared marairaice fuska "kin tada hankali na, tun d`azu nake neman wayar ki sai tayita ringing ba'a d`agawa" tace "oh (habibi) Wlh ban lura ba nasaka wayar silent ne, saboda ina asibiti" "asibiti kuma?" Ya fad`a a tsorace yana kallon ta "me ya
same ki?"
(Hhhh) tayi dariya sanah ta bashi ransa "ba abinda yasame ni sai alkhairi, yarinya ta na kai asibiti" cike da mamaki ya kalle ta "yarinyar ki kuma?" Ya tambaya cikeda neman karin bayani. Tace "eh gata nan" ta bashi amsa tana nuna Safeenah dake makale a gefen ta. Sai a lokacin ya lura da yara biyu dake bayan ta, idon shi kyar akan Feena sai ji yayi wani Abu ya taso daga kasan kirjin shi ya soki zuciyar shi cusss
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *14*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍
Hannun shi ya saka ya d`an tura Yusra gefe d`aya ya kurawa yarinyar ido na lokaci mai tsawo. Yusra dake gefe itama saida taji wani Abu, tausayin mijin ta ya kama ta, ko shakka babu tasan tunanin su ne yazo d`aya Wato yana yiwa Safeenah kallon batacciyar yar'su ne. a ganin su da tana raye tare da su da yanzu ta kai sa'ar wannan yarinyar ko ma ta fita
Ya tsuguna gaban Feena ya zuba mata ido tare da kamo duka hannayen ta biyu ya rike su gam. "Kyakkyawar yarinya" ya fad`a yana kara karewa fuskar ta kallo "Yusra ina kika samo yara haka? Ko yaran wacce ce a cikin kawayen naki?" Lallausan murmushi ne ya wanzu a kan kyakkyawar fuskar ta, ta matso kusa dashi ta kama hannun yaran taja su zuwa kan lafiyayyun kujerun dake zagaye da falon tana fad`in "ka cika sauri habibi zo ka zauna in maka bayani" yabi bayan ta da ido kafin ya mike shima ya nufi kan kujerar dake makoftaka da ta'ta ya zauna, har yanzu bai d`auke idon shi daga gare ta ba bayani yake son ji game da yaran dasuka matukar burge shi kuma suka shiga ran shi farat d`aya
Yara kam sam hankalin su baya kan su, tuni sunyi nisa da abinda suke na raba ido suna karewa kayan alatun dake falon kallo, ji suke kamar wata duniya ce ta daban ta wasu jinsi suka zo sabanin waccan da suka baro ta karkara. Murmushi ta komayi tana kallon fuskar mijin nata yanda ya kagu yaji inda ta samo yara, addu'a ta fara yi a ran ta Allah yasa ya karbi uzurin ta wato ya yarda da kudurin ta na rikon yaran da take so suyi. Sannan tace "Habibi wayan nan yara da kake gani sakon Allah ne zuwa gareni, domin Allah shi kad`ai ne yasan yanda nake azabtuwa da yawan tunani da damuwa na rashin haihuwa tun daga kan yarinyar mu da aka sace har yau abin baibar zuciya ta ba," tayi shiru tana goge kwalla. Kafin taci gaba
-"a hanya ta ta dawowa na had`u da su cikin mawuyacin hali suna neman taimako na taimaka musu," sannan na nemi sanin iyayen su domin sanin inda zan kai su ko wayanda zan nema na hannun ta su gare su. sai suka gayamin su bakin ne daga kauye suka zo kuma su marayu ne" nan dai Yusra ta kwashe labarin su Feena kamar yadda Amar ya gaya mata ta nawa Alhaji
Shi kan shi sai da jikin shi yayi sanyi sosai da jin labarin yaran da irin matsi da takurar da suka sha a wannan shekarun na su daya kamata ace suna samun gata da kulawa ta iyaye, tareda koyarwar addini ba dai talla da dako ba. Ya sauke numfashi ya fuskanci matar tashi yace "Yusra zamu taimaki yaran nan kamar yadda kika kudirta a ranki zan zame musu Uba muddin kika zame musu Uwa"
Murmushin jin dad`i ne ya subuce mata, tace na gode sosai Habibi Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, idan munada rabo muma Allah ya bamu namu masu Albarka." Ya amsa da "Ameen Yusra" tajuya ga yaran wayanda ke can kan plasma t'v suna shafawa suna kallon kan su a ciki kasancewar a kashe yake.
"Amar", ta kira sunan a hankali "kuzo ga Abba" ta fad`a fuskar ta a sake. Yaran suka zo gaban ta suka tsaya suna kallon Alhajin "lah Umma wannan shine Abban mu da kika ce yana gida?" tace "eh shine wannan kuje ya saka muku Albarka" suka kalli junan su Amar ya sakewa Feena murmushi sannan ya kama hannun ta suka je har gaban Abba suka tsuguna "sannu Abba" suka fad`a tare Alhaji Wakkala ya d`agosu tare ya mikar dasu sannan ya nuna musu gefen shi yana cewa "a nan zaku zauna kusa da Abba kunji yara na" Amar ya amsa da "to Abba" domin Safeenah kam har tayi tsalle ta haye kujerar, Amar da Abban suka kalle ta. Alhaji ya koma fad`awa tunani Wanda shi kan sa baisan na meye ba, kawai dai kallon fuskar yarinyar yana saka shi tunani
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *15*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍
Amar kuwa dad`i da farin ciki ne suka lullube shi, yau ga Safeenar shi tana farin ciki, gasu a sabuwar duniya inda yake kyautata zaton rayuwar su zata haska da iznin Allah
Karar takun takalmi sukaji tana sakkowa daga saman bene cikin takon nan nata na nuna isa da kasaita ta iso gaban Alhajin cikin shirin ta na fita office hannun rike da jaka da key d`in mota, Sai faman shan kamshi take tana yatsina. "Zan fita" ta fad`a tana yage baki tana tauna cingam. Alhaji Wakkala ya sauke numfashi yace "Wai sabida Allah Ummu sai yaushe zaki canza? Tun wayewar garin nan fa wannan shine ganin farko kika yimin amma ace sam ba zaki iya gaida ni ba sai dai Zaki fita ko?"
Ta had`e fuska tareda juya mishi baya "inaga baka so a gaishe ka bane shiyasa ban gaida kai ba, Dani da kai wa Allah ya ce yaje yaga lafiyar wani idan gari ya waye?, duk yau kafarka ta leka d`aki na? To kamar yanda bazaka canza ba haka nima bazan taba canzawa ba" taja dogon tsaki tayi ficewar ta. tabar Alhaji da Hajiya Yusra da kallon inda tabi
Haka yara ma suka bita da kallon mamaki. Safeenah ce tazo gaban sabuwar Ummar su ta tsaya fuskar ta cike da damuwa tace "Umma wannan fa wacce ce?, naga tana da fad`a sosai amma dai nazata dake mu ba ko?" ta karashe maganar cikin marairaice fuska. Hajiya ta shafi kanta "ba abinda zatayi muku Feena kuzo mu karasa d`aki" tarika hannayen su suka haye saman bene tana cewa Alhajin "ina dawowa Habibi, bari in kaisu masaukin su". yaran kuwa sai d`ari-d`ari suke da hawa saman saboda tsoro abinka da ba' saba ba
A can saman da suka nufa sashe uku ne da wasu bangarori guda biyu, sashe na bangaren dama shine na Hajiya Yusra, na hagun shine na Hajiya Ummu, sai wanda akayi shi tsakiyar su Wanda shine sashen Alhaji. Kai tsaye sashen ta tanufa da su, yara suka tsinci kansu a wani wuri da zasu iya kira da Aljannar duniya. Sanyin A.C da wani lallausan kamshi ne suka yi musu maraba.
Bada labari ko fad`ar kayatuwar sahen kamar bata lokaci ne dan sai in shafe shafuka masu yawan gaske garin yin hakan readers imaging.
Sashen babban ne mai d`auke da d`akunan bacci biyar falo uku, d`akunan baccin Hajiya Yusra biyu ne da falo d`aya, sai na batacciyar babyn su d`aya mai had`e da falo Wanda har yau yake kebe a matsayin nata, duk wasu kaya da aka saya mata na barka da wayanda yan'uwa da abokan arziki suka kawo mata suna nan ajiye a d`akin, a cikin shi suke gudanar da birthday d`in haihuwar ta wanda suke yi duk shekara. Bayan shi akwai d`akunan baki guda biyu had`e da falo d`aya. direct d`akin ta ta nufa da su har kan gadon ta ta zaunar da su. Yara sai raba ido sukeyi suna mamakin ikon Allah
Wata yar kararrawa ta danna wadda kai tsaye take kai sakon nema ga Masu aikin ta dake can kasa, ba jimawa kuwa sai ga wata dattijuwa ta shigo d`akin da sallamar ta Hajiya ta amsa mata fuska a sake. Sai da dattijiluwar ta rusuna tace "Hajiya gani kina bukatar wani Abu ne?" "Eh Iya dan Allah yara nake so ki turomin Yan'mata wayanda kika yarda da hankalin su guda biyu" ta d`an numfasa wanda ya bawa wadda ta kira da Iya damar cewa "to Hajiya kamar masu me kenan?"
Tace "wayanda zasu iya kula da yara, su dinga yi musu wanka da kula da abincin su" tace wannan ba matsala, yara muka samu Uwar d`aki na?". Tayi tambayar tana kallon yaran dake zaune gefen hajiyar sunyi shiru suna sauraren su.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:45 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *16*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Na
Nasmatu Muhammad
Yar'mutan Arkilla✍
"Eh yara na ne ana zasu ci gaba da zama tare damu" ta bata amsa a takaice. "Allah sarki kyawawan yara, ai da gani nasan wayannan irin larabawa ne". Iya ce mai maganar idon ta a kan Safeenah