Showing 15001 words to 18000 words out of 48171 words

Chapter 6 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt

Advertisement

20 Jan 2025

4633

Allah ya saka maka da alkhairi miji na". Ya mayar mata da martanin murmushin da tayi mishi kafin yace "to ku tashi muje muci abinci ko". Tace "yadda kace". Cikin salo da kashe ido tayi maganar ya faki idanun yara dasuke can suna badali da ice-cream ya manna mata kissa a gefen farar fuskar ta sannan ya mike ya kama hannun Amar itama mikewar tayi taja hannun Feena suka nufi danning aria,




a dai-dai tsakiyar falon sukayi kicibis da Hjy Ummu dawowar ta kenan daga aiki. Turus tayi ganin sabon al'amari a gidan nasu. Hjy Yusra da Alhj kam sam basu lura da yadda ta d'auki abin ba suka tare ta da murmushi as usual "sannu da dawowa aunty". Yusra ta fad'a tana kallon Hjy Ummu bata amsa mata ba saima wani wulakantaccen kallo da tabita da shi daga ita har Alhjn, amma me gabanta ne yayi mummunar fad'uwa lokacinda idonta suka sauka kan yarinya Feena take taji tsoro da wata irin fargaba sun mamaye zuciyar ta a ranta kuwa tambaya take wacce ce wannan mai kama da Yusra? Domin ita kam da kallo d'aya ta hango yawan kamanni da yarinyar take yi da Yusra


















*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *20*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍










FOLLOWING US AS:
----
Like us page.
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION
----
Check us blogger.
Zamaniwriters.blogspot.com
----
Email us your comment and reports.
Zamaniwritersassociation@gmail.com
----




*Rayuwar makaranta dad'i banison tuna baya 😰 , never ever forget you guys. (Asiya Isah & Sumayya Isah) har yau ana tare* 🤝😘










Cikin matsanancin tashin hankali ta zaburi gabban jikin ta, a sukwane ta isa bangarenta. Mijin da matar harma da yaran suka bita da kallo sai dai kowa da abinda yake sakawa aransa domin kuwa yaran kallon mamaki suke mata had'eda tsoro su kuwa iyayen ko ajikin su domin kuwa inda sabo ya isa su saba da irin halayyarta.




Suka girgiza kai suka wuce danning abinsu. Tashin hankalin Hjy Ummu sai kara ninkuwa yake, mayafinta kawai ta jefar akan gadon ta ajiye jakar hannun ta tashiga warwareta domin fiddo wayar ta. Tana cirowa ta saka kiran wata number data lalubo a makance. Takuwa ci sa'ar samun number dukda a tsorace da hakan takira domin Eysha bahaguwar yar'bariki ce bata cika barin waya a kunne ba.




Ringing biyu ana uku aka d'aga da "hello, uwargida agidan wakkala kinci naki kinci na dangi, Ummu kinci dubu sai ceto, yau kin tuna da tsohuwar kawarki?". Tayi tambayar da yanayin wasa domin kuwa ta dad'e rabonda taji wayar Ummun indai ba ita takirata dakanta domin su gaisaba.


Babu wasa ko sonjin wani dogon surutu a tattare da ita yau, hakan yasa ta takawa Eysha birki, cikin wani yanayi na tsoro ta fara maganar da murya kasa-kasa wadda ta tabbatar ko a d'akin mutum yake bazai tabajin metake cewa ba.


"Eysha, magana nake so muyi dake, akan wnnan aikin da kikamin a shekarun baya na yar'gidan nan". Wani irin dumm! Eysha taji tamkar anbuga guduma a kirjin ta domin tsawon rayuwarta duk da zinace-zinacen da take bata taba jin nauyi da bakin cikin suba kamar yadda take jin na wannan mummunan aikin data aikata ba, tun bayanda ta aikata abin yazo yayi sanadiyyar rayukan tsofaffi guda biyu iyayen Alhj, takuma jefa Alhj da Hjy Yusra cikin mawutacin hali sai ta tsinci kanta dajin haushin kanta, na biyewa Ummu su aikata wannan mummunan laifin abinda koda wasa ba aikin mutum bane domin kuwa raba d'a da Uwa sai Allah. Ayanzu Eysha tayi matukar nadama akan abinda ta aikata.




Shirun da Hajyn taji ne yasa ta sakeyin magana "Eysha kina jina kuwa?". "ina jinki hjy menene" Eysha ta fad'a tareda danne takaicin ta da takeji. "dama tambayar ki zanyi kawata, wai dan Allah kin kuwa kashe yarinyar nan kamar yadda mukayi alkawari dake?". Sai taji tambayar a wani bambarakwai takaici da tsanar halin bakar kawar tata suka sake cikata amma saita danne ta wayance da fad'in "wannan kuma wace irin Tambaya ce Ummu?". Tayi maganar cikin bacin rai alamar antabo ta. Shiru ne ya ratsa daga kowanne bangare wani tunani ne ya zowa hjy Ummu wanda yasa tai Allah wadai da saurin bakin da tayi nayiwa Aminiyarta wannan tambayar, amma dayake an dad'e a bariki sai ta wayance da fad'in "kiyi hakuri kawata, na kwanta baccin rana ne nayi mafarki da yarinyar shiyasaka duk na tsorata". "na fahimce ki amma karki koma tunkarata da irin wannan banzan tambayar, nice fa Eysha saikace baki san waye ni ba". "Afwan kawata abar maganar, y kike?".




Eysha tayi hanzarin katse wayar domin ta kara gamsar da kawarta cewa ta bata mata rai da wannan tambayar tata. Hjy Ummu ta kalli wayar ta sauke numfashi tace "fushinki ai mai sauki ne nasan 200k zasu hutar dake, amma kasancewar yarinyar nan a raye zai iya sawa na rasa rayuwata". A wurin tayiwa Eysha transfer na (200,000) sannan ta ajiye wayar ta fad'a bayi zuciyar ta na kara bata tabbaci akan tunanin da yazo mata daga baya, wato wad'an nan yaran dai ya'yan d'an'uwantan nan ne na saudiya (yayan hjy Yusra take nufi) tasan bazai wuce hutu aka kawo suba, Domin kuwa babu yadda za'ayi Alhj yaga batacciyar yar'shi ta bayyana sannan farin cikin sa ya tsaya iya haka inaaaaa, ai da ace hakan d'inne da tuni gidan yagama cika da batsewa da mutane domin bazasu iya boye farin cikin su ba.


Wanka tayo ta fito cikin kankanin lokaci tagama shirin ta cikin wata arabian gown ta feshe jikinta da turaruka ta nufi falon domin kara samun tabbacin daga ina yaran suka zo, kuma su waye su?
















*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *21*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍








*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*












*Alhamdulillah hakika Allah shine abin godiya, kusha sha'anin Ku ZAMANAWA lokacin kune Yan baiwa, tauraruwar Ku na haskawa nikuwa Nasmat burina ya cika, ⭐⭐⭐⭐⭐ a yau kune Shining stars a online writers. Ya Allah Kaine maiyi kuma Kaine mai isarwa ya Allah ka kara d'aukaka ZAMANI WRITERS* 🙏










_______________________________
Da murmuhin ta ta isa gare su, sam basuyi mamakin hakan ba domin sanin da qukayi mata na tsayin shekaru haka take yanzu-yanzu ne ta sauya.


tayi sallama suka amsa, ta zauna kan kujerar dake kusada ta alhjn a gefen hagu. Amar da Feena kam mikewa sukayi domin suna jin tsoron hjyr, dama sun gama cin abinci hira kawai sukeyi da sababbin iyayen nasu..


Ya kama hannun kanwar sa suka koma tsakiyar falon hjy Ummu ta bisu da kallo ta kasan ido, ganin yadda gashin kab yarinyar yayi tsayi har wucu tsakar bayanta ya kara tabbatarwa hjy Ummu tabbas wad'annan irin sai dai larabawan.


A hankali ta kalli Yusra "me aka girka yau?". Cikin sakin fuska ta amsa mata "priderice ce sai farfesun kifi dana kayan ciki, akwai had'in fruitsalad"




tayi murmushi irin na naji d'in nan, saka min duka dai-dai ciki na". Tayi murmushi ta mike tayi seaving hjyr kamar yadda ta bukata Alhj dai baice komai ba sai ido dayake bin su dashi, a zuciyar shi ko yana yaba kyawun rayuwa da halayyar Yusra, da ace ba haka take ba da gidan shi ya zama dandamalin masifa,


domin ya lura wasu abubuwan dagangan Ummu take mata su domin neman taki yi, a tashi hankalin gida. ta fara cin abincin cikin d'asashi da yanga abin ya bashi dariya "Uwargida ran gida, hjy Ummu kina sha'anin ki wlh".


Yayi maganar yana murmushi dama neman hanyar magana take "Uhum to me kuma Ummu tayi?". "a'a ni na isa infad'i laifin manya?". Alhjn yafad'a cikin dariya "Hmmm ana min abubuwa a gidan nan idan nayi magana kuma ace Ummu ta cika mita, idan nayi shiru kuma ace na nuna halin ko in kula". Ya komayi murmushi a karo na biyu


"tofa yau kuma me akayiwa sarautar mata?". Ta yatsina fuska "sarauta dai, uhum". Sai kuma tayi shiru "to ko ba haka bane?". "Alhj kenan, abufa ake yi amma sam ni ban cancanci a gayamin ba, yanzu sabida Allah yara fa na gani a gidan, amma a cikin ku ba wanda ya gayamin su waye, balle insan daga ina suke, idan nayi magana kuma kai da kanka zakace na cika magana".




Alhjn yai murmushi yace "to ai jiya suka iso kekuma kina busy da ayyukan ki, ni yaushe ma naga fuskar ki dazan tsaya yimiki wani bayanin?". Ya fad'a cike da tsokana murmushi kawai tayi Alhjn ya d'ora da cewa "yaran Yusra ne, nan zasu cigaba da zama da mu insha Allahu".


Wani irin dukan kirji taji, dukda zuwa yanzu ta tabbatar yaran yan'uwan Yusra ne aka kawo mata daga kasar su, amma miye na wani anan zasu zauna? Ta tambaya a zuciyar ta.


A fili kuma tace "Oho dama nikam naga kama domin da gani d'aya za'a gano irin larabawan ne". Yusra da tunda suka fara maganar batace komaiba tayi murmushin jin dad'in yabon da tayiwa yaran nata. Alhjn ma murmushi yayi ya mike yana fad'in "nizan fita daga can zan lalubo musu malamin lesson su fara d'aukar darasi kafin asaka su a makarantar".


Wani haushi ya koma tirnike hjy Ummu. Yusra kuwa dad'ine ya lullubeta tashiga yiwa mijin nata addu'a da fatan Alkhairi har yabar falon hjy Ummun bata koma cewa komai ba .






















*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *22*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍












*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*








Mike tayi cikin bacin rai ta ture kujerar da take kai ta nufi d'akin ta. Yusra ta bita da kallon mamaki kamar ba ita ake taba hira da ita yanzu ba. Kai kawai ta girgiza tare da cewa "Allah ya baki lfy"


Itana dai mikewar tayi ta koma tsakiyar falo inda yaran suke suna wasa da sababbin kayan wasar da Dady ya siyo musu.


ta zauna a cikin su sukaci gaba da wasar tare tanajin dad'i sosai yadda yaran suka saki jiki da ita bama kamar Feena ba wadda kallonta kad'ai saita jefata cikin farin ciki


haka kuma wani lokacin har mamaki take wane irin so ne Amar yake yiwa kanwarsa Feena,


sau tari idan da manya aguri yaran sukayi abu sai sun basu mamaki domin irin kulawar uwa da uba yake bata


Sam bai had'a Feena da komai ba yana sonta kamar rayuwar sa zahiri da bad'inin shi.


hakan na kara sakawa hjy Yusra soyayyar yaran ji take dama ya'yanta ne su, da tayi farin ciki da irin son da sukewa junan su. Haka itana Safeenar bata kaunar tayi wani abu da zai batawa yayan nata rai
basa rabuwa ko kad'an inba lokacin bacci yayi ba. Nan ma dakyar da fama suka Saba kwana daban-daban, tare suke cin abici a plat d'aya da spon d'aya wani lokacin ma sai dai yabata a baki ko kuma ta bashi.


yaran suna burge kowa. Yau ta kama laraba ranar da Amar da Safeena suka cika sati d'aya a gidan sun saba da yanayin gidan da mutanen cikin sa


sun gama gane halayyar kowa. Kuma suna taka tsan-tsan da abinda zai had'asu da kowa a gidan musamman hjy Ummu wadda suke kira da mama, dakuma yaron ta Mubarak


wad'anda suka lura har nema suke su musu laifi su hayyako musu da masifa. Tsakanin su da Umman su Yusra da Dady kuwa sai godiya, domin suna nuna musu so da kauna iyaka.




Sati d'aya malamin lesson yayi yana koyar dasu ya gano yaran sunada ko'kari da kwazon karatu ya gayawa Dady a saka su a primary kawai.


Hakan kuwa aka yi a (Iman international schools) aka saka su. Inda suke samun kulawa daga malaman makarantar sabida darajar wanda yakawo su ga kuma lesson da ake musu a gida.


Ga islamiyya da suke zuwa akowane yammaci. Masha Allah rayuwar yara dai ta haska, kullum ka gansu tsab-tsab da su. motar su ta kansu aka ware musu duk inda zasu ita ake kaisu da ita


farin ciki da canjin rayuwa ya bayyana karara ajikin yaran cikin sati uku kacal sai gasu sunyi kyau sun Kara haske ga wata ni'ima da Allah ya basu ta yalwar jiki dukkan su sun kara kiba sun mulmule. abin dai gwanin sha'awa sai dai ace tubarkalla


yara kam sun sami gata duk yadda hjy Ummu da yaron wajenta suka kai ga son su shiga rayuwar yaran su takura musu sun gagara saboda yaran basa shiga sabgar su, haka Allah yayi su basu da kwaramniya ko kad'an




Haka rayuwa ta rika tafiya satittika suna ture watanni watanni, yau Amar da Safeena watannin su uku a gidan alhaji Tijjani wakkala


a yau ne kuma suka ga antashi da shirye-shiryen biki a gidan nasu sai kawata gida ake ana mishi decorations, musamman d'akin nan da tunda suka shigo gidan basu taba ganin an bad'eshi ba. (d'akin baby, batacciyar yar' hjy Yusra, kuma ya d'aya tilo ga Alhj Tijjani wakkala)




d'akin yasha gyara da Kayan kawace gurare da turaruka gaba d'aya gidan ya d'auki haske da sheki ko ina ka gifta sai kaci karo da turaren wuta irin na larabawan asali


kayan sakawa kuwa na musamman aka siyo wa yaran yan saiti Kala d'aya dasu da Mubarak haka iyayen suka yi ado na alfarma.


a d'akin kowa ya hallara inda aka tanadi kujeru da shimgid'u na alfarma. Karfe Tara dai-dai mutanen Saudiyya suka iso Ummin hjy Yusra da Yayan ta da kuma matar yayan ta,


Tareda rakiyar manyan malaman nan guda biyu kamar yadda suka saba a kowace shekara.....














*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/26/2017, 6:52 PM] My Number: ........... *JA'JIRTACCE*....... *23*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*


*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍








*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*


_MARUCI MAKARANCI, HAKA MAGANAR TAKE 👌🏼 wannan shafin naka ne kai kad'ai *Autan writers, 'KING BOY ISAH'* kai d'in na daban ne kamar yanda rubutun ka ma ya bambanta, gabadai-gabadai *Autan Mu* Nasmat tana yin ka sosai da sosai😍 ka huta na waje na, ana tare matuka 🤝_












Da guda hjy Yusra ta isa ga mahaifiyar ta ta rungumeta,
itama ummyn sakin jakar hannun ta tayi ta rungume Yusra yar'ta mace d'aya da Allah ya bata.


Sai kuma su duka biyun suka fashe da kuka mai tsanani da tsuma zuciya,
ganin Ummy ta biyewa Yusra suna ta rusar kuka yasa yayan ta ya matso gare su ya d'ago ta


cikin harshen larabci yake maganar yace


"kiyi hakuri kanwata Allah babu inda baya yin ikon sa,


ba mamaki yarinyar nan bata mutu ba domin kuwa ni ban taba jin hakan ajikina ba"


Yusra ta kankame shi lokacinda kukan ta ya kara tsanan ta itama dai da larabcin take mishi magana


"a'a d'an'uwa na ni kam inaga baby bata raye, domin na tabbabar duk wayanda suka saceta ba dan kud'i suka d'auke ta ba, da tuni sunyi magana an basu kud'in"


matar yayan ta ta d'agota itama dai hawayen take yi tace


"yar'uwa Yusrah kiyi hakuri ki dogara ga Allah shikad'ai ya barwa kansa sani akan batan wannan yarinyar,


yau tsawon shekaru takwas kenan muna had'uwa anan saboda ita ki sani addu'oin mu bazasu tafi a banzaba muddin yar'ki tana raye na tabbata Allah zai bayyana miki ita"


sosai taji sanyi a ran ta da jin maganganun Raudah matar yayan ta.


suna cikin wannan halin ne Alhj Tijjani ya sauko daga kan bene da alama daga d'akin sa yake.


ya caba ado da wata dakakkiyar shadda bakin sa har kunne farin cikin sa na ganin sirikan sa ya kasa boyuwa.


mutanen da suka d'auke shi tamkar d'an cikin su.


da hanzari ya karaso garesu ya zube kasa yana kwasar gaisuwa gaban Ummy.


farar dattijuwar tasa hannayen ta ta d'aga shi ta mikar dashi tsaye suka gaisa cikin girmamawa da mutinta juna


sannan daga bisani ya juya ya gaisa da shaihunan malaman da suka zo daga Saudia


wad'anda duk shekara sai sun zo a irin wannan ranar domin yin addu'oi ga batacciyar yar'su Baby.


A taice dai yau ne ranar da suke bikin zagayowar shekarar haihuwar ta wanda suke yi a kowace shekara.


sannan a bangare d'aya a yi saukar alkur'ani da yanka tareda karanto manyan addu'oi akan idan tana raye Allah ya bayyana musu ita ya dawo musu da yar'su cikin salama,


in kuwa ta rigamu gidan gaskiya to Allah ya jikanta da rahmar sa yakuma bawa iyayen ta hakurin jure rashinta


in da rabon wata haihuwar a gaba Allah ya basu wasu masu albarka.


to yau ma dai kamar kowanne lokaci masaukin su aka fara kai su suka huta sannan aka gabatar musu da abinci da abin sha na musamman da aka tanada domin su.


Sukaci, suka sha Sannan sukayi wanka kowannen su ya sauya kaya


sannan ne dukan su suka d'unguma zuwa d'akin Baby, inda suka tarar an gama tsara komai kamar dai yadda aka saba.


Duk wannan hidindimu da hayaniyar da ake hjy Ummu ko lekowa batayi ba, tana can d'akinta tai d'ai-d'ai akan gadon ta tana murmushi a ranta cewa take


"hakika iska na wahalar da mai kayan kara, wlh ita kam baza'ayi wannan wahalar da ita ba ta gaji da yiwa matacciya hidima"


hatta zuwan su Ummy duk a kunnen ta kawai kin tasowa tayi.


Daga karshe ma tashi tayi ta yi wanka ta shirya cikin shirinta na suwa offices ta fice bayan ta tura Mubarak makaranta.


da shigar su d'akin suka fara cin karo da manya-manyan hotunan Baby na jarantaka da aka manna ajikin kowane bango dake d'akin


sai tarin kayan wasan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login