Showing 30001 words to 33000 words out of 48171 words
Chapter 11 - JAJIRTACCE Book Complete Hausa Books by Nasmatu Muhammad--.txt
gare su. Wata ɗaya daga cikin tawagar kawayen Jidda tace "wai zankaɗi, wanda yake da wannan santaleliyar budurwar dama yaushe zai tsaya ta kan mu.
Jidda wata department met ɗinsa dake zaune da kawayen nata, ta kura musu ido, zuciyarta na tafarfasa, nan take tsanar Safeenah ta tsargu a cikin zuciyarta, ji tayi kamar ta tashi taje ta shake yarinyar har sai ta mutu.
Tofa🤔
Wace ce Jidda?, me kuma Feena ta kashe mata da shigowar ta jami'a?.
Ku biyo ni domin jin dalilin, yanzu ne wasar zata fara 😎.
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[11/27/2017, 8:10 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *36*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Har kofar ɗakin karatun su ya raka ta tareda, bayan ya nuna mata inda zata same shi idan ta fito. Duk zumuɗin da take saida ya kau, lokacin da taga Amar zai tafi ya bar ta, shiru tayi tana kallon shi kafin kace me sai hawaye shar a fuskar ta. Nan da nan hanklin sa ya tashi, ya kama hannunta suka kauce daga kofar ajin saboda masu shiga, "haba Feena, haba mana kanwata, so kika karatun yau ya wuce ni?". Ta girgiza kai alamar a'a, yace "to in haka ne meyasa kike kuka dan zan tafi"? Cikin shagwa6a da yaranta ta fara magana" Yaya ni bana so ka barni ne, bansan kowa a nan ba, nidai zan bika naku ajin". Kusan dariya maganar ta'ta ta bashi, sai ya daure yace "Feena manya, ta ya zaki bini ajin mu bacin kema ga naku ajin nan, kuma fa zaman na ɗan lokaci ne da zarar kuka gama wannan lecture ai muna tare ko". Yayi maganar da sigar rarrashi. "To shikenan ka tafi karka makara, da zarar na fito zan same ka acan" "yauwa Feena na, sai mun fito ko" ya faɗa yana share mata hawaye da handkerchief ɗan dake hannun sa, saida ya manna mata kiss a gashi sannan ya kama hannunta ya shigar da ita cikin class ɗin, a kujerar gaba ya zaunar da ita kusa da wata ɗaliba, sannan ya juya ya fice yana yi mata murmushi.
Ta bishi da kallo sai da ya kurewa ganin ta, sannan ta sauke numfashi ta kira kanta bisa table. Amar kuwa yana fita ya nufi department ɗin su, sauri-sauri yake tafiyar saboda lokaci baya so ya haɗu da fushin fitinannen Malamin nan nasu.
Abu kaɗan ya rage ya kaureta saboda yadda ta tari gaban shi bada sanin sa ba, yaja ya tsaya yana kare mata kallo cikeda mamaki. Duk da yau ya fara ganin ta hakan bai hana shi gano tana cikin 6acin rai ba, ya tambayi kansa a ran sa yace "wannan kuma me na mata?" Jidda kuwa sai cika take tana batsewa akan dalilin da bai sani ba, "Ke lafiya, kika zo kika tare min hanya?" yayi mata tambayar a tsawace. Amma ga mamakin sa sai ta tintsire da dariya a madadin amsa tambayar shi, abinda ya kara harzuka Amar kenan. Ya canza hanya zuwa gefen ta ya cigaba da tafiya "dakata Amar" yaji ta faɗa cikin tsawa, sai yaji yana son sanin dalilin da yasa ta tsayar da ɗin, cak! yaja ya tsaya ba tareda ya juyo ba, hakan bai dame ta ba, ta fara magana cikin 6acin rai,
"yau shekara ɗaya kenan ido na yana kan ka, tun randa na fara ganin ka naji ina kaunar ka, ina ta fara da soyayyar ka tsayin lokacin nan, ganin baka kula ko wacce mace yasa nake shayin tunkarar ka, amma yau sai gashi ka bayyana da wata mace a gabana, wannan yana nufin kana soyayya, kana kula mata, amma sai ka nuna kamar baka San komai ba"
Tayi shiru sannan tayi taku ta isa gaban sa, Amar wanda yayi tsaye tamkar wanda aka dasa kallon ta yaci gaba da yi ba tareda ya iya ɗaga harshe ya mata magana ba, Jidda ta sauke numfashi sannan ta kwantar da murya lokacin da hawaye suka fara bin kuncin ta.
"Amar ina son ka, ina maka son da ban ta6a yiwa wani irin sa ba, a baya na zata baka kula ko wacce mace ashe hauka nake kana da wacce kake so, kar ka yi min haka Amar, idan ka su6ucemin zan rasa rai na, shekara ɗaya nayi ina renon son ka, na roke ka karka nisanta tsakanina da kai". Ta karashe maganar cikin kuka tareda durkushewa gaban sa, hanklin sa ya kara tashi, ganin yadda mutane ke kallon su yasa dole ya sassauta zuciyar sa, yace "naji, duk naji abinda kika faɗa, amma dan Allah ki tashi kinga mutane sai kallon ki suke, ba a haka ya kamata muyi maganar ba".
Jidda ta tashi tsaye tana sharar kwalla, ta kalle shi "ya kake so nayi?, haka zan cigaba da zama muddin baka saurare ni ba". Yayi ajiyar zuciya sannan ya kwatanta mata inda zasu zauna bayan lecture, yace ta same shi can. A kan haka suka raba zuciyar sa cunkus da mamaki da kuma tsoron abinda ke shirin faruwa da shi...
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[12/6/2017, 5:40 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *37*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
A ɗakin karatun ma haka ya kasance sama-sama yake jin abinda ake yi. Har aka kammala kwakwalwar sa bata ɗauki komai ba. (Allah sarki Amar)
To haka ma 6angaren karatun su Feena ɗaliban sun yaba sosai da irin son da wannan da ya kawo ta yake mata, a tunanin su Amar saurayin ta ne.
Maryam wadda ke zaune a kusa da ita, ita ce ta fara yi mata magana "sannu frnd suna na Maryam Muktar, da fatan zamu zama abokai". Murmushi kawai ta mata ba tareda tace komai ba ta koma kifa kanta da table. bata koma ɗagowa ba sai lokacin da ta ji shigowar Malamin da zai ɗauke su lacture.
Mintuna biyar da zaman shi sai gata ta iso, Feena ita ce wadda ta fara zuwa bayan fitar Malamin su. Amar na zaune yana nazarin abin yi, saka yake yana warwarewa tunda yake bai ta6a Soyayya ba, yau da rana tsaka wannan ta bijiro masa da ita. Tambayar kansa yake anya kuwa zai iya?, to inma zai iya ta ina zai fara?". Yana cikin wannan yanayin ne ya ji an rufe masa ido ta baya, kamshin turaren da yaji ne ya tabbatar masa Safeenah ce. Dan haka yasa nashi hannayen ya janyo ta, ya zagayo da ita gaban sa kana yayi ko'karin danne damuwarsa yana faɗin "barka da fitowa yar' jami'a". dariya tayi sosai saboda yadda yayi maganar. "Allah yaya yau ina cikin farin ciki".
"Naga alama ai" ya faɗa yana murmushi. Duk wannan abin da suke yi akan idon Jidda, tana kallon su kasancewar itama fitowar ta kenan daga class, ta nufo inda ya kwatanta matan.
Tun daga nesa idanuwanta suka yi tozali da tauraron nata, duk da cewa babu wata fara'a ko murmushi akan fuskar tashi ita ganin kyanshi take tamkar sabon wata tsayuwar yau. Sai murmushi take, tana ji a ranta ta sami shiga ganin yadda ya bawa ganawa da ita muhimmanci har ma ya rigata zuwa wajen. Ganin Feena tayi kamar wadda aka jeho daga sama ta nufi inda Amar ɗin yake zaune. Hakan ne yasa dole taja ta tsaya tana kare musu kallo, a take zuciyar ta ta ɗauki zafi, wani kululun bakin ciki ya tokare mata a makogwaro, "dama ya kira ta nan ne dan ya ci mata mutunci?". Ta tambayi kanta, tambayar da batada amsar ta
Ta kasa karasawa gurin, ta kuma kasa juyawa ta koma cikin Makaranta. A gaban idon ta Feena ta fito musu da kayan abinci, a plate ɗaya ta zuba musu, dambun nama ne wanda yaji haɗi yasha kaya, sai robar ruwa ɗaya da ta lemun fanta, nan ma kofi ɗaya ta dire a tsakiyar su. Abinda ya daɗa tunzura zuciyar Jidda kenan. Wato komai ma ɗaya suke amfani da shi. Ta jinjina lamarin a ranta, tareda kissimawa tana so ta tantance irin soyayyar dake tsakanin su.
Can taji zuciyarta na gargaɗin ta akan ta hakura da wannan guy ɗin, tunda har ta ga da wadda yake so kuma ta tabbata wannan ta fita da komai da ɗa namiji zai so a jikin mace, Sai dai ita ta girme ta da shekaru wata zuciyar ta ce mata "a kul karki yarda ki sadaukar da soyayyar ki saboda wata macen, kamata yayi ki dage kema ki nemi soyayyar sa kamar yadda ta nema ta samu. Namiji ai tsamiya ne ki tsotsa ki bani in tsotsa.
Hannun ta tasa ta share zafafan hawayen da suka fara jerin gwano bisa kumatunta. Igiyar so na janta, zuciyarta na dad'a yin nutso a tafkin kaunar sa. Saida ta danni zuciyarta sosai sannan ta iya takawa ta isa inda suke zaune. Dakyar harshenta ya iya dai-daita kalmomin Sallamar da tayi musu. Tare suka amsa Sallamar kamar yadda suka ɗago kai tare suna rige-rigen ganin wadda ke musu Sallamar. Wani irin faɗuwar gaba ne ya riske shi a sakamakon ganin wadda ke tsaye a gaban sa. Feena kuwa murmushi ta koma saki ganin bakuwar fuskar da bata sani ba, "sannun ku da hutawa, Amar gunka na zo". Ta faɗa kanta na kasa tana ko'karin danne damuwar ta. "Bismilla zauna" ya faɗa yana nuna mata wani 6angare na lallausar grass carpet ɗinda yake zaune akai.
Zuba mishi ido tayi tana mishi kallon tuhuma, ganin duk yadda ta kai ga dannar fusatacciyar zuciyar ta Amar yana son yaga ya kular da ita. "inba haka ba Akan me zata ce tana son magana da shi sannan yace wai ta zauna a nan, yana nufin a gaban budurwar sa zasu yi maganar?" ta koma tambayar kanta. A fusace ta ɗago kai tareda zarewa bakinta sakatar da tasa masa tace...
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[12/8/2017, 7:41 AM] Yar'mutan Arkilla ✍: ........... *JA'JIRTACCE*....... *38*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
........... *JA'JIRTACCE*....... *25*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
"Haba Amar wai wane irin wulakanci kake so ka min ne?". Yadda tayi maganar a fusace ya bawa Safeenah da shi kanshi Amar ɗin mamaki. Bata tsaya nan ba ta cigaba "ka kuwa san hukuncin wulakanta ɗan Adam, anya kuwa kasan irin nauyin da zuciyata take ɗauke da shi akan ka?". Amar ina son ka naji ko a gabanta zan faɗa ina son ka zan iya faɗe a gaban kowa ina kaunar ka, wlh idan ka cutar da ni Allah bazai barka ba" sai ta fashe da Kuka. Kuka take sosai zuciyarta na mata raɗaɗi.
Amar kam ya narke gaba ɗaya jikinsa ya sanyaye, ya kasa koda kwakwaran motsi ne balle ya iya ce mata wani abu. Safeenah ce tayi karfin halin mikewa tsaye, cikin sanyin jiki ta nufo inda take. Domin zuwa yanzu ta fahimci inda maganganun bakuwar tasu suka nufa, duk da cewa bata ta6a jin labarinta a bakin yayanta ba ta lura da akwai alakar Soyayya tsakanin su. Sai wani abin dariyar da ta lura budurwar yayan nata ta ɗauka ita ɗin Sonta yake yi ko kuma itama budurwarsa ce.
"Haba mana Auntyna me yayi zafi haka?, dan Allah zauna" ta kama hannun ta ta zaunar da ita bisa carpet ɗinda suke kai Jidda sai sharar kwalla take kanta na kasa tana tunanin mafita ga wannan kaddarar da Ubangiji ya saukar mata ta son maso wani. "Yaya kaɗan bamu waje mana, ina son mu ke6e nida Auntyna". Tayi maganar tana kallon sa mikewa yayi ba tareda yace komai ba yayi gaba ya bar su a gurin ya tafi a makauce domin ko harbeshi za'ayi bai san abinda yake tunanowa ba a lokacin kawai dai yaji zuciyarsa cike da tunanuka.
Kusan mintuna da tashin sa su duka ba wadda tayi magana lokaci mai tsayi can Feena ta nisa tace "kiyi hakuri zan miki shishshigi akan abinda ya shafi rayuwar ki, da fatan hakan bazai zama laifi ba?" jin bata ce mata komai ba yasa ta cigaba da magana "kafin mu tsunduma cikin maganar mu zan sanar miki da abinda na lura baki sani ba. Bata jira cewar ta ba ta ɗora wancan da kike gani ba saurayi na bane kamar yadda zuciyar ki ta baki, shi Yayana ne".
Da sauri Jidda ta ɗago suka yi ido biyu da Feena wadda ita ma ita take kallo. Murmushi tayi sannan ta gyaɗa mata kai alamar tabbabarwa. Daɗin wannan furucin ya lullu6eta, farin ciki mara misaltuwa ya ziyarci zuciyarta. A 6angare ɗaya kuma kunya ce ta lullu6eta ta kara kasa da kanta tana Murmushi.
Safeenah tace cikin zumuɗin son jin kokof "Ke budurwar shi ce?" Jidda ta kaɗa mata kai alamar "a'a. Mamaki ya kama Feena kuma bata 6oye ba tace" to amma naji kina maganar kina son sa". Nan Jidda ta warwarewa Feena komai akan irin son da takewa yayanta Amar da tsayin lokacin da ta ɗauka tana yi mishi shi. Allah sarki Feena gwanar tausayi hadda yar kwalla ta rarrashi Jidda ta bata hakuri tareda tabbabar mata cewa insha Allah zata shawo mata kan Amar zai so ta kamar yadda take kaunar sa. Sosai taji daɗin alkawarin da Feena ta mata nan da nan ta saki jiki da ita suka hau hira da dariya har ma tana cin abincin nasu da Safeenah ta saka ta ci dole.
A haka ta ciro wayarta ta saka kiran layinsa, ringing biyu a na uku ya ɗaga wayar bata bari yayi magana ba tace "kazo mun gama maganar" yayi mamaki sosai yadda yazo ya same su sun baje sunata hira da wadda ta zo tana ta kuka, "hmm Feena hoo" ya faɗa a zuciyarsa cikeda mamakin me ta gaya mata wanda ya faranta mata haka.
Zaman sa keda wuya Jidda ta mike ta ɗauki jakar ta ta tafi tana murmushi, ya bita da kallon mamaki ita kuwa Feena dariya take kyalkyalawa.
Saida ta kurewa ganinsa sannan ya juyo ga Feena "ke me kika bata ne naga duk haukar tata ta kwanta har tana murmushi" ta kwashe da dariya hadda kwanciya saida ta ɗora kanta bisa cinyoyinsa sannan ta fara magana "abinda take so na bata yaya" ya bata da kallon mamaki "abinda take so?" ya tambaya yana kallon fuskarta. "eh mana kasan me Jidda sunan ta kuma tanada kirki, ta tsinci kanta cikin sarkakiyar so da kaunar ka. Ni kuma a matsayin kaunar ka na yi mata alkawarin samun ka, a takaice dai na gaya mata kaima zaka so ta. Dan Allah yaya ka tausaya mata ka so ta, kasan shi so mummunan akasin sa shine ka nemi wanda kake yiwa shi ka rasa".
Ido kawai ya zuba mata yana kallon yanda le6enta yake motsawa, kwakwalwarsa na jinjina lamarin "yaushe Feena ta San wani abu so har tasan yadda ake ji idan aka kama da shi?".
Kallon da yake mata ne ya tabbar mata da tunani yake, ta hura masa iskar bakinta a fuskarshi. Firgigit ya dawo daga dogon tunanin tareda sauke nannauyan ajiyar zuciya.
"Me yasa kika gaya mata hakan nan, shin kina da tabbacin zan so ta ne da kika mata alkawari bayan kin san girma da darajar alkawari?" yayi mata tambayoyin ne yana kallon cikin kwayar idonta, domin kan cinyarsa kanta yake ita ɗin ma shi take kallo. Tambayoyin da ya mata ne suka haddasar mata da mutuwar jiki, tunaninta ya sarke ta kalle shi duba na nutsuwa tace "saboda na yarda da kai, nasan zaka so ta saboda ni, Jidda tana cikin wani hali na soyayyar ka idan bata sami so daga gareka ba zata iya samun matsala"
Kamar wanda aka data haka ya kame kam idonsa akan ta, anya kuwa Feena tasan matsala ta so, anya tasan asalin abinda ke zuciyarsa, ta yaya zata kyautar da zuciyar da ba tata ba?. Akan me zata ɗora shi akan hanyar da bansan ta ba?"...
*Yar'mutan Arkilla* ✍
[12/8/2017, 9:10 PM] Yar'mutan Arkilla ✍: .......... *JA'JIRTACCE*....... *39*
👇🏻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
*Na*
Nasmatu Muhammad
*(Yar'mutan Arkilla)*✍
*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*
Hannayensa ya saka ya tashe ta zaune, suka fuskanci juna a kwayar idanun shi ta fahimci babu wasa a tattare da shi. "Feena". Ya kira sunan ta da murya mai sanyi da rauni wadda bata ta6a jin shi da irinta ba. Bata iya amsawa ba sai dai kanta da ta ɗaga tana kallon yanayinsa bai damu da rashin amsawarta ba ya fara magana... "ban ta6a yin Soyayya ba kin sani, ban san yadda take ko yadda ake yin ta ba, ban ta6a jin so na wata ya'mace a zuciyata ba sai na Umma da ke!" ya nuna ta da yatsa sannan ya ɗora "sai kuma Mommyn mu (Yusra). Yau kin zo min da maganar na so wata" da sauri ta ɗago ta kalle shi jin muryar shi ta canza, tsoro ne ya lullu6eta ganin yadda yanayinsa ya sauya idanun shi suka kaɗa suka canza launi daga fari zuwa ja... Hankalinta ne ya tashi, hawaye suka fara bin kuncinta Sam bata ji daɗin ganin halin da ta jefa yayanta ba. Maganar sa ce ta katse mata tunani "zan so ta Safeenah, zan so wannan budurwar