Showing 1 words to 3000 words out of 41150 words

Chapter 1 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2880

�����
�����
������
*KAR KA GUJENI*
������
�����

� *Na Aisha A Yabo*�
fulani �


*Pure moment of life writers*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot

_wa d'anan sune shafukan mu da zaku ziyarta Dan samun k'ayatattun littafanmu_


*5 to 10*


Allah ne kawai ya kaita gida lafiya da k'yar ta iya saita kanta bayan ta ajiyi motar a gurin da
aka tanada dan ajiye mota ta shiga cikin gidan zauni ta tarar da Aunty da 'yan aikinsu suna kallo
falon k'asa

murmushi tayi cikin k'ok'arin boye damuwarta tace "Aunty kallo kuke"?
"uhm Bety su Ma'u dai ke kallo nikam hankalina na gunki ya mai jikin"?

sai yanzu ma ta tuna da abun da ya fitar da ita har ta had'u da azzalumin da yayi mata a bun da
ba a tab'a yimata ba a rayuwarta

nisawa tayi kafin tace "Alhamdulillah yaji sauk'i su DADY fa"? Aunty tace "basu dawo ba dama
zullumina kenan tun d'azun Alhamdulillah gashi har kin dawo cikinsu ba wanda ya dawo"

"OK bari na shiga ciki" tana tafiya take amsa gaisuwar su Ma'u tana shiga d'akinta Alwala tayi
ta gabatar da sallah magrib bata bar gurin ba sai da tayi isha'i

ba yanda Aunty batayi da ita ba taci abinci tak'i ce sai Holandia kawai ta d'an sha

"Aunty tace "wai me ya sami fuskarki ne tayi haushi idanunki duk sunyi ja"? cikin kawar da kai
tace "bakomai Aunty kawai na tausayawa Meenat ne Abban ta bai da lafiya sosai"

"Ayya Allah ya bashi lafiya" ta fad'a ba dan ta amince da maganar Bety ba.


da dare ma sai sarkin b'araye ne ya saceta barce ne tayi ciki da mafarkin Al'amin yana marinta
harda duka. wannan kenan


Al'amin suna shiga gida Inna da take tan kad'an garin da zasuyi tuwo tace "A'a Babana ya naga
kun dawo miye ya b'ata maku kaya haka"?

Cikin furzar da numfashi yace "wallahi Inna wata 'yar iskar yarinya ce tayi mana haka" Lawal ne
ya bawa Inna labarin Abunda ya faru

ai kuwa ta hau bakinta fad'a take masa "haba Babana meyasa zaka dake ta nifa bana son zafin
zuciyarnan naka haba ace mutum bshi da wani abu sai zafin zuciya ko namiji ne ka ce kasakar
masa k'awanji ballatana macci ni dai wallahi banji dad'i ba

dan Allah kasanyawa zuciyarka salama haba!" ganin yanda ta d'au zafi yasa ya sassauta murya
yace "Dan Allah Inna kiyi hak'uri nima ban san ya akayi na mare ta hakan ba raina ne ya b'ace
kiyi hak'uri kinji Innata"?

ya k'arasa maganar yana mai d'aura kansa a kafad'anta shafa sumar Kansa tayi cikin muryar da
ke nuna ta sauko tace "bakomai Babana ni dai fatana ka rage zafin rannan kaji"?

"to Inna Insha Allahu kiyi mun adu'a" "inayi Babana Allah dai yayi maku Albarka"


"Amin" ya fad'a tare da mik'ewa d'akinsa ya nufa bayan sun shiga Al'amin yaciri kayan ya sanya
jallabiya bak'a duk da rigar ta d'anji jiki hakan bai hana kyansa fitowa ba tamkar balarabi
kasancewar fari ne

d'ura kayan yayi kan kujera yayi kwanciyarsa kan 'yar k'aramar katefarsa Lawal ya dube shi da
mamaki yace "ya zaka kwanta ko kafasa tafiyan"?

"mts eh nafasa kaje kawai" daga haka bai saki cewa komai ba ya rufi idanunsa

Lawal kad'a kai kawai yayi ya ficewarsa ba tare da ya saki cewa komai ba.

ga baki d'aya ranar Al'amin baiyi barccin kirki ba kukanta ya tsaya masa a rai haushin kansa ya
keji "meyasa ya mareta?"

haka dai yayi barccin ba cikin natsuwa ba.


*BAYAN KWANA BIYU*

tana kwanci ajikin Yaya saif tana danni danni waya Yaya Saif yace "wai Bety yaushi ne
makarantar ku zasu janyi yajin aikin"?

"cikin ya tsinar fuska tace Yaya nima ban sani ba wallahi" "Bety wallahi dan kin nacewa
makarantar nanne kawai amma ni a India naso kicigaba da karatunki kika k'i"

"uhm ni dai nafi son nan" "aifa nikuwa naga ranar da zaki gama makarantar da wannan shigen
yajin nasu na tsiya"

murmushi tayi tare da saurin canza maganar "Yaya Dady yace jibe zakuje Sudan ka
karb'omun turare da lalle gun 'yar tsuhuwa" ( kakarsu)

"au ke bazaki bane"? "eh Yaya saboda ko yaushi zasu iya janyi yajin aikin"

ba dan komai ta dujewa tafiyan ba sai dan Farhan sarkin nacenta k'arar da wayarta keyi ne ya
katsi firar tasu ganin Meenat ce yasa ta tashi zauni ta d'aga kiran cikin fara'a

"oh Meenat ba kiyi fushi ba"?
"kema kinsan ko banyi fushi ba zanji haushi"

"nasani kiyi hak'uri dan Allah wallahi su biyu ina shirya zuwa sai uzuri ya gitta amma kina raina
ya jikin Abba"?

"da sauk'i amma fa ban d'auke maki zuwa ba"

cikin murmushi tare da duban gefin Yaya Saif taga ya tashi baya falon hakan ya mata dad'i tace
karki damu jibe Insha Allahu zanzo"

sun jima suna fira kafin daga bisani sukayi sallama


ranar laraba a hanyarsu ta dawowa daga filin jirgi rakiyarsu DADY tacewa drv su wuce Hayin
ma'azu

sanda suka isa dai dai kwanar da zata sadata da gidansu Meenat tace "suyi pakebg"

ba musu suka bi Umurninta cikin takun k'asaita ta fito iscod d'inta ne a bayanta sun kai su goma


Al'amin ne zauni a kantin Lawal suna fira akan idonsu motoce biyar sukayi Pakeng ganin
wacce tafito cikin mortar ba k'aramin d'agawa Lawal hankali yayi ba musamman da yaga
gurinsu suke nufuwa

nan taki yaji yawun bakinsa ya k'afe jikinsa ya fara rawa cikin sark'ewar murya Lawal yace

"shikenan Al'amin zafin kanka ya janyo mana masifa ka duba yarinyar nan tazo mana da
k'attan samudawa wayyo Allah na shikenan nasani k'arshinmu yazo
b'abb'alamu zasuyi tuni fitsari ya fara zubu masa k'afafunsa sai karkarwa suke


uban gayyan ko ajiknsa kallonta yake fuskarsa murtuk'i hankalinsa kwanci ko d'ar baiji ba jira
yake yaga da wacce tazo ashiryi yaki da duk yan da tazo masa.


_mai k'aunar ku_

� *Aisha A Yabo*�

fulani����
�����
������
*KAR KA GUJENI*
������
�����

� *Na Aisha A Yabo*�

fulani�

*Pure moment of life writers*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_


#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS

#http://www.fascbook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot

*10 to 15*


Sanda ta k'araso gurin kallo d'aya tamasa ta d'auke kanta domin ba zata manta fuskarsa ba
wani irin firgici da bugun zuciya take ji jin take tamkar a lokacin ya ke marinta sam mantawa tayi
da zata sayawa mara lafiya kayan dubiya da bazata tsaya gurin wannan azzalumin ba runtse
idanunta tayi kafin daga bisani ta bud'esu cikin k'arfin hali da k'ok'arin boye yanayin da tashiga
ta dubi Lawal da yake cikin kantin yanata had'a uban gumi tace

"dan Allah ina son drinks" cikin rawar murya yace "w..w..a.ni iri kikeso"?

"uhm koma wani irine" "to to k'wara nawa"? "katan hud'u"

"ranki ya dad'i katan biyu ne yayi saura"
"OK ba damuwa kawo sai ka had'oda sweet da biskit"

nan take ya had'a mata iscod d'in suka d'auka inda tabiya shi kud'insa tabar gurin cikin tsananin
bugun zuciya.


bayan tafiyarta Lawal ya fito yana sharci gumi tare da sauki ajiyar zuciya "wai Allah ya somu
alk'ur'an har nafara hangoni a mak'abarta"

Al'amin da ke kallonsa duk yanda yaso had'i dariyar da ke tasu masa kasawa yayi ai kuwa
dariya yake sosai da tafara k'ular da Lawal

"kaifa d'an iskane miye zaka wani sani gaba kana dariya kamar kaga sabon kamu"?

ganin Al'amin ya k'icewa da shi komai sai dariya yake yana nuna shi hakan yasa ya kai dubansa
gurin da Al'amin ke nuni Wandon sa yayi shakaf ko ba afad'a ba yasan fitsari ne wannan ya
wuce akirashi da gume


shafa kansa yayi ciki da kunya yama rasa me zaiyi cikin dariya Al'amin yace "wallahi Lawal
tsoronka yayi yawa haba kamar macci yanzu miye abun tsoro a wad'annan mutanan"?

harararsa Lawal yayi kafin yace lallaikam d'an rainin hankali agunka ne ba komai ba wad'annan
bani ba ko kai sarkin cika bakin idan ka shiga hannunsa wallahi komai ba zaka iya ba, da kake
cewa tsoro kamar macci yo idan maza suna guri ai banbancinmu da macci k'alilanne"

cikin k'ok'arin had'i dariyar yace "haba wa ni d'in wallahi kaima kasan wasa kake ko sunfi
wad'annan masu kama da dodanni nafi k'arfinsu kawai malam kazama namiji kuma wallahi
maza kaje kaciri k'azantar nan"

ya k'arasa magar yana harararsa mts Lawal yayi tsaki tare da barin gurin ya nufi gida dan sauya
kayan jikinsa

wani yaro ne yazo wucewa Al'amin ya k'wala masa kira "faruk' zunan" da sauri faruk' ya k'arasa
yana fad'in gani yaya"

yauwa maza d'auki butar nan a kwai tsintsiya a bayan k'ofa shiga cikin zakaga inda ruwa ya
zuba ka k'ara ruwan kashare sosai kaji"?

yaron ya amsa da to cikin k'ank'anin lokace ya gyara wajan da taimakun Al'amin" faruk' zai
wuce yaga waya ak'asa yace "lah yaya ka yarda wayarka" ya fad'a bayan ya d'auko wayar

Al'amin ya karb'a cikin mamaki dan shi dai wayarsa gata a hannunsa Lawal kuwa wayarsa ba
irin wannan bace

yana duba scrm d'in wayar yaga hoton bety ya cika scrm d'in ko shakka bayayi wayar 'yar gidan
Lawal ce hakanan ya tsinci kansa da shiga ma'adanar ajiyi hotona yana kallon hotonan ta ne da
sukafi yawa


wani irin yanayi mai wuyar fassarawa da bazai iya tantanci ko na miye ba ya kejin yana ratsa
zuciyarsa da jinin jikinsa, tura hotonan yayi a wayarsa tare da sa numbarsa cikin wayarta yayi
fulashin d'in wayarsa sannan ya kuma wayarta ya goge tasa, ya bawa faruk' wayar yace "ungu
maza ka shiga layinmu duk inda kaga motoce sun tsaya ka tsaya anan idan kaga wata zata
shiga mota ka bata ka fad'amata inda tayar"

bayan tafiyar faruk'u ya fara jin haushin kansa miye zaiyi da numberta ko hotonanta shi baima
San dalilin da yasa ya d'auka ba mts yayi tsaki kafin ya mayar da wayar aljihunsa.

da murna Meenat ta tarota sai rawar jiki take sai da takaita guri Ummi suka gaisa tare da
tambayr mai jiki Ummi tace "yaji sauk'i ai har yafita yau"

"Masha Allahu Allah ya k'ara sauk'i" "amin 'yar nan sannu da k'ok'ari mun gode sosai" tafita
tabarsu Meenat tace "ban zaci zaki gani gidannan ba"


"haba Meenat me kika mai dani zuwana fa biyu gidanan" dariya Meenat tayi kafin tace "hakane
fa mutuniyar k'wak'awalwarki naja"

"uhm ke dai ki kasani" sunjima suna fira kafin tayi masu sallama bayan tsarabar da tayi , masu
harda dubu goma tabawa Ummi sai godeya suke mata,

har mota Meenat ta rakota faruk'a da yake gefi a tsayi yazo da sauri yace "Aunty ga wayarki kin
yar a k'ofar kantin Yaya Lawal"

cikin sauri ta karb'a tana fad'in "oh na gode sosai kinga halina ko sam ban kula ba gurin na
bashi kud'i nasan nayar da wayar"

Meenat tace "anci sa'a raboce baki yar a idon b'ata gariba"

"wallahi kuwa" tabawa faruk' dubu d'aya yak'i karb'a ya bar gun da gudunsa hakanan sai taji
yarun ya burgeta har take tambayar Meenat sunansa

"faruk' kenan d'an k'anwar Inna Haulatu ne amma a gurin Inna yaki babansa ya rasu tun yana
wata biyu"

wani irin tausayi da k'aunar yaron taji ya shigeta farat d'aya tace da Meenat "Insha Allahu zan
saki zuwa ki kaini gidansu"
"to sarkin tausayi sai na ganki ta fad'a tana dariya Bety murmushi kawai tayi tashiga mota.
*wannan kenan*


_mai k'aunar ku_

� *Aisha A Yabo*�
fulani����
�����
������
*KAR KA GUJENI*
������
�����


� *Na Aisha
A Yabo*�

fulani�

*Pure moment of life writers*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com





*15 to 20*

An janyi yajin aiki sun koma makaranta sun cigaba da karatunsu hankali kwanci da dare daga
k'arfe 8:00 ya sayyadi yana zuwa yayi mata karatu zuwa 9:00 suke tashi.



*WACE CE BETY?*


asalin sunanta Aisha 'yan asalin Sudan ne mahaifinta Alhaji sufiyan da mahaifiyarta safna
dukansu 'yan famili d'aya ne sun kasance 'ya'ya ga Baffa Hamid da Baffa Ahmad wanda suke
uwa d'aya uba d'aya,

Baffa Hamid yaransa hud'u Sumayya ce babba sai sufiyan Asiya auta Alk'asim,

Baffa Ahmad yaransa biyu Muhammad Safna,
Sufiyan da Safna suka had'a kansu inda iyayansu sukayi farin ciki cikin k'ank'anin lokace akayi
aurensu watansu d'aya a sudan suka tattaru suka dawo nagiria kasancewar anan yake
kasuwanci


Kaduna garin gwamna anan ya sauka da amaryarsa Unguwar kinkinau anan ya tambatsa
had'add'in gidansa naji da gani ban san ya zan kwatanta iya had'uwar gidan ba naira dai ta
kuka,

rayuwar gidan gwanin sha'awa suna matuk'ar tattalin juna soyayya sukewa juna har karasa wa
yafi son d'an Uwansa Abokinsa Alhj ma'azu mak'ota ne gida d'aya ne tsakaninsu shi ya samu
masa 'yan aiki acikin 'yan aikin a kwai Abu Amma tun zuwanta safna ke kiranta da cikakkin
sunanta Zainab
tana matuk'ar son zainab saboda na tsuwarta hakan yasa ta janyota jiki tamkar k'anwarta,

shekararsu biyu da aure Allah ya albakaci su da samun k'aruwar kyakyawan babynsu Zo kuga
murna tun daren suna 'yan Sudan suka cika gida ranar suna a kasawa Baby Saifullah kusan
rainunsa duk Zainab ce banci kad'ai ke rabasu yanada shekara ukku Zainab tayi Aure da Isa
drvn DADy Anan cikin gidan Akwai b'angarin da ba kuwa nan suka zauna inda Momy Safna
tayiwa Zainab komai da ya kamata Uwa tayiwa 'yarta daga Zainab har iyayanta adu'an gamawa
da duniya lafiya da sakamako mafi tsoka a gurin Ubangiji sukewa Momy da Dady domin duk
wani gata sun mata shi.

aurenta bai hanata zuwa b'angarin Momy ba da mijinta ya fita tare da Dady zataje gun Momy
sai sun dawo sannan ta koma b'angarinta.


Saifullah nada shekara goma har sun ciri rai da saki haihuwa sai gashi Allah ya bata wani cikin
wai zo kuga murna gun su Momy da Saif tun kafin a haihu babu ne kawai basu saya ba

saif duk suka fita da yaga kayan wasa sai yace asayawa Babynsu idan sweet ko bisket aka
saya masa sai ya dinga kukan sai ansayawa Baby haka dai suke nuna so da tattalin baby tun
bai fito duniya ba.

wata tara da kwana goma cif da k'arfe goma na dare Allah ya sauketa lafiya a cikin gidanta
tasamu 'yarta kyakyawa kamarta sak ba abun da tabari na momynta.

ranar suna aka rad'a mata Aisha Humaira suna kiranta da ( *BETY D'IYATA A YAREN HINDU*)

HUM mai karatu fad'ar irin so da gatan da akewa Bety Alk'alamina yayi kad'an ya kawo maku
kullum zaka ganta goyi a bayan Zainab sai idan za tasha mamma ko baci ke rabasu idan Saif
ya dawo makaranta kacukan lokacinsa nata ne,


lokacin da takai shekara d'ai da wata bakwai Zainab tayi yayenta shak'uwarsu da Zainab ba zai
kwatantu ba ko Momy da Dady bata yarda dasu idan tana hannunta Saif kad'ai take yarda
dashi.

*BAYAN SHEKARA HUD'U*

ranar asabar ba boko Saif ne da Bety b'angarin Zainab sai wasansu suke yana mata doki sai
b'angala dariya take Uncle Isa da Aunty (haka Saif ke kiransu)suka fito Uncle yace to 'yan
gidan Aunty ku tashi muje ya fad'a yana rik'o hannun Saif Aunty ta d'auki Bety suka nufi gurin
su Momy
sun tarar da ita shirya su kawai take jira Momy ta mik'i tare da fad'in "yauwa dama Ku nake jira

Bety zo muje"

Bety ta mak'i kafad'a alamar bazata ba Momy tayi murmushi kafin tace "daman nasan ba zuwa
zakiyi ba waya isa ya rabaki da Auntynki" ta kalli Saif tana fad'in "d'an gidan Momy zo muyi
tafiyanmu"

cikin b'ata fuska kamar zaiyi kuka yace nima Momy bazani ba tunda Bety ba zata ba" rik'i baki
Momy tayi kafin tace "iyye wato haka zamuyi ko Saif shikenan nayi tafiyata"

ta d'auki jikka tana fad'in "Zainab zamu tafi ga yaranki nan ki kula dasu da gidan kiyi ta hak'uri
da yarintarsu

"to Momy Allah ya tsare ya dawo daku lafiya" ta rakata har mota tayiwa yaranta kiss sannan ta
shiga mota Uncle yaja suka kama hanyar Abuja bikin 'yar Abokin Dady Alhji ma'azu wanda ya
koma Abuja da zama Dady yana legos daga can zai wuce gurin d'aurin Auren.

ga ba d'ya tun tafiyarsu Momy Zainab take junta wani iri jikinta takeji tamkar ba nata ba, su
Momy ko minti talatin da barin Kaduna basuyi ba Sukayi hatsari da taimakun mutane da wani
bawan Allah da yazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login