Showing 21001 words to 24000 words out of 41150 words
Chapter 8 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
yanda yayansa yamai magana cikin
tsoro yace "Aunty Uwaliya ce aka kwantar asibiti shine akazo akai Inna "
Al'amin ya rik'i Kansa yana fad'in "ya Salam yanzu ya zanyi? Allah ka kawuman mafita"
agogon da ke mak'ali a hannunsa ya duba 4:40 nan take idanunsa suka kad'a sukayi jajir ya
zaiyi Inna bata nan ba zaiyu yaje yayi gaban Kansa ba
ba tare da yardarta ba wani tunani me yazo masa hakan yasa da sauri ya d'auko wayarsa
aljihu ya lalubu number mijin Aunty Uwaliya ya kira sai dai kash wayarsa arufe wannan Karan
kam ba Kansa ba har zuciyarsa ji yake tamkar and'ura masa garwashin wuta akai.
_mai k'aunar ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*K'anwata Hafsat musa Indon k'auye ina tayaki murnar kammala littafinki SAMU DA RASHI
ALLAH UBANGIJI ya k'ara basira da lfyar idanu*
*100 to 105*
Rik'e kansa yayi tare da lumshi idanunsa yana tunanin mafita idan yace zaije unguwar su Aunty
Uwaliya ya tambayi asibitin da suke zai canyi lokacinsa
zuciyarsa ta bashi shawarar ya sake gwada kiran mijin Aunty ko zai samu cikin sa'a yana kira ta
shiga ba ajima ba mijin Aunty Uwaliya ya d'auka
bayan sun gaisa da tambayar mai jiki ya nemi da ya bashi Inna
bayan sun gaisa Inna tace "Al'amin kazo ka tarar bana nan ko"?
"eh wallahi Inna ya jikin nata"?
"da sauk'i ya naji muryarka wani iri ko jikin ne"?
shafa sumar kansa yayi kafin yace "Aa Inna naji sauk'i dama mahaifin Aisha ne ya kirani"
"to Allah yasa lafiya me yace ma"?
nan yayi mata bayanin duk yanda sukayi da Dady
Inna ta d'anyi jim kafin tace "Al'amin ba zank'i auren ka da Aisha ba sai dai ina tsoron kar wani
abu zaima ya biyu ta hakan dan kaje amma in banda haka a ina aka tab'a irin wannan auren"?
"indai wannan ne karki damu kanki Inna Insha Allahu ba abunda zai faru sai alkhairi"
"uhm" ajiyar zuciya tayi kafin tace "kana ganin zaka iya Al'amin yarinyar nanfa 'yar Hutu ce
masu kud'ine akwai nisan ta zara a tsakaninmu da ita mu talakawa ne"
"Inna ai Aishan duk tasan da ko ne waye ta aminta dani dan Allah kisa mana albarka karki ce
Aa"
"uhm shikenan Allah ya sanya Albarka kaje ka fad'awa Baffanka da Malam (mahaifin Meenat)
ka d'aga katefa akwai kud'i sai kayi amfani dasu"
da murnarsa yace "nagode Inna sai dai kin manta na fad'a maki jiya da dare Lawal ya karb'o
man adashina zanyi amfani dasu nagode" daga haka sukayi sallama.
Lawal ya kira ko gaisawa basuyi ba yayi masa bayani da mamaki Lawal yace "Al'amin waci
Betyn wai"?
"kaga had'iye duk tambayar ka daga baya zaka iyayi yanzu ba lokaci"
"OK ganinan dama zanzo gurin ka"
yayi sa'a Baffa na tare da Malam a k'ofar gidan Baffa suna fira dama mak'wabta ne basu da
nisa yayi masu bayani atak'aici"
da Mamaki Baffa yace "ikon Allah wannan wani irin Aure ne Al'amin ba mu kosan da kana
neman yarinya ba sai kawai kazo mana da maganar aure sai kace auren 'yar tsana ba binciki
ba komai"?
Al'amin da ya kejin kamar ya rusa ihu saboda tambayuyin da Baffa kemasa wanda ganinsa duk
b'ata lokacine yace
"kuyi hak'uri Baffa dama ina niyar nazo nafad'a maku to sai aka samu 'yar matsala"
Baffa zaiyi magana Malam da ya kula da duba agogon da Al'amin keyi ga damuwa tattari da
fuskarsa yace
"kaga tashi mutafi babu cikakken lokaci tun da yaran sun fahimci juna ai shikenan magana ta
k'are"
"to muje mu samu abun hawa sai muje gidan" Lawal ne yazo da motar yayansa ya kwashisu
suwa gidansu Bety.
Dady ya karb'esu cikin rashin walwala suka gaisa Baffa ya nemi alfarmar ad'an basu lokace
akimtsa sannan ayi d'aurin auren
Dady yace "yaron naka baima bayani bane ayau d'innan nayi niyar zan aurar da ita idan kun
shirya to idan baku shirya ba sai kuyi gaba na bawa wani"
malam yace ba komai Allah ya sanya Alkhairi ashiryi muki"
ba tare da b'ata lokaci ba aka d'aura auren Al'amin da Aisha akan sadaki dubu biyar kamar
yanda Dady ya yanka masu
ana idar da d'aura auren Dady yasa Yaya Saif ya kira Bety
lokacin da ya shiga d'akinta ya tarar da ita zauni tayi tagumi tana ganinsa tayi saurin tashi tsayi
tana kallonsa zuciyarta na bugawa fat fat fat kamar zata faso k'irjinta ta fito saboda tsoro
tab'e bake yayi kafin yace "ba dai kin nacewa talakan can ba to hankalinki ya kwanta an d'aura
maku auren
amma kisani ko a hanya kika ganni kika ce kin sanni ballatana ki wanko k'afanki kizo gidannan
Wallahi Allah sai na b'abb'alaki"!
jin an d'aura auren ta da Al'amin sai ta tsinci kanta cikin wani yanayi da takasa gane ko miye
farin ciki ko akasin sa
ganin tamasa tsayi batace dashi komai ba sai ya fusata wato ga d'an iska yana mata magana
tamasa shiru
hakan yasa ya fizgota da k'arfi yayi hanya Palon bak'i da ita kira take "wayyo Yaya ka sakarmun
hannu wallahi da zafe wayyo Yaya hannuna zai karye"!
ina sam bai kulata ba ballatana ya tausaya mata ya sassauta rik'on da yayi mata
suna zuwa yayi cille da ita gaban Al'amin k'iris ya rage ya gwara kanta ga hannun kujera
Al'amin kallonta yake ciki da tausayi yau da wani ne ba yayanta ba da sai ya karkarya masa
hannu
lumshi idanunsa yayi zuciyarsa na masa k'ona kukanta yana d'aga masa hankali
maganar da yaji Dady nayi yasa shi saurin bud'i idanunsa yana kallon Dady
"Aisha ga zab'in naki nan na baki sai dai ina so daga yanzu kiciri ne ko wani da ya shafe ni
daga rayuwaki
karki kuskura ki tako gidannan da sunan yaji ko k'ara ziyararma mun yafe
sai ki tashi ku tafe gatanan zaku iya tafiya"
cikin tsananin kuka ta rarrafa zuwa gurin da Dady yake kafin takai Yaya Saif yayi mata tsawa
"zaki tashi ku tafe ko sai na b'abb'allaki"?
ganin tak'i tashi yayu kanta Dady yace "Saifullah k'yaleta ke Aisha maza tashi Ku wuce ko na
k'yaleki da shi"!
yayi mata maganar atsawaci su Malam da sukayi shiru suna mamakin wannan al'amarin me
yayi zafi haka
Malam yace "kuyi hak'uri abun bai kai na duka ba kai Al'amin rik'ota mutafi Alhaji mun tafi Allah
ya huci zuciyarku"
haka Al'amin yarik'ota suka shiga mota kamar ranta zai fita.
har cikin d'akin Inna suka rakata tare da k'ara lallashinta kan tayi hak'uri idan an kwana biyu
zasu je da Kansu su bawa mahaifinta hak'uri da wannan Alk'awarin sukayi masu sallama
Lawal yace "mutumin nima zan fita sai na dawo anjima"
"aha nagode sai najika"
Lawal na fita Al'amin ya rungumita yana bubbuga bayanta ahankali ya fara magana cikin lallashi
"Aishana kiyi hak'uri ki daina kukan nan yana d'aga mun hankali Insha Allahu Dady zai hak'ura
yanzu yana cikin fushi idan an kwana biyu zamuje mu bashi hak'uri kinji Aishana"?
Bety da tunda tajita a faffad'an k'irjinsa kukanta ya d'auke cak sai ajiyar zuciya take yanzun ma
takasa cewa dashi kumai sai sake lafewa da tayi tana shak'akar k'amshin jikinsa.
*kuyi hak'uri da wannan Insha Allahu gobe zanyi maku tpyng ngde*
_mai k'aunar Ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*105 to 1010*
Daina kukan nata yayi masa dad'i kiran sallah yaji anfara yasa ya d'agota yana kallon fuskarta
cike da k'auna yace
"Aishana bara naje nayi alwala na wuce masallaci" kallonsa tayi kamar zatayi magana kuma sai
tayi k'asa da kanta
fuskarsa ya had'a da nata har suna shak'ar numfashin juna cikin muryar k'asa k'asa yace
"meyasa zaki fasa fad'ar maganarki fad'amun abunda ke ranki"
lumshi idanunta tayi cikin jin kunya tace "inasu Inna"?
murmushi yayi kafin yace "Inna tana asibiti wata sister d'inmu ce bata da lafiya Faruk kuma ban
san ina yaje ba"
"yanzu idan ka tafi ni kad'ai zan zauna"? tayi magana kamar zatayi kuka
hancinta ya lakata yana fad'in "oh Aishan tawa matsoraciya ce ashe to tashi muyi alwala sai na
mana jam'i tun lokaci bai tafi ba".
bayan sallah isha suna zauni k'ofar d'akin Inna kwanci take ajikinsa yana wasa da hannunta ya
kira Inna bayan sun gaisa da tambayar mai jiki ta nemi ya bata Aisha
cikin jin kunya ta karb'i wayar zata tashi yayi saurin saki rungumeta kallonsa tayi cikin k'auna
kafin tayi k'asa da idanunta
ta fara magana ahankali "ina wuni Inna"
"lafiya k'alau Humaira ya bak'unta"?
"Uhm ya mai jiki"?
"da sauk'i haihuwa ce har yanzu shiru ai da tuni na dawo gida,
Al'amin ya fad'a mun abun da ke faruwa kiyi hak'uri haka Allah ya k'addarta bawa kuma bai isa
ya kaucewa k'addararsa ba"
sosai tayi mata nasiha kafin daga bisani sukayi sallama tabawa Al'amin bayan sunyi sai da safe
ya d'ago fuskarta yasa hannu yana share mata hawayen da keta zarya afuskarta cikin damuwa
yace
"Aishana kukan ya isa haka kinji"
girgiza kai tayi kafin tace "Yaya Al'amin kaga yanda aurenmu ya zo dan Allah karik'e amana
*KAR KA GUJE NI* duk rintsi"
hannunsa ya had'a da nata kafin yace "har abada Aishana bazan tab'a guje maki ba ke d'in
farin cikina ce rayuwata
guje maki yana nufin rasa farin cikina rasa rayuwata bazan tab'a cin amanarki ba yanda kika
zab'e ni Insha Allahu bazan baki kunya ba"
"nagode Yaya Al'amim Allah ya shige mana gaba"
"amin ya zamuyi kinga har yanzu Faruk bai dawo ba ina so na fita ba jimawa zayi ba"
Sallamar Lawal sukaji yasa Bety saurin janyi jikinta aranta tana hamdala harga Allah tsoron
zama take ita kad'ai cikin gida ba kowa gashi ba NEPA
Lawal ya mik'a masa hannu sukayi musabaha sannan ya juya kan Bety yace "amarsu ta ango
wato keda abokina haka kuka mun akabarni da tsoro da fad'uwar gaba Ku kuma kuna gefi kuna
soyayyar ku"
Bety Sunkuyar da kanta tayi cikin mayafi takasa cewa dashi komai Al'amin yayi murmushi kafin
yace "kamanta baka fad'i d'ayan ba harda fits...
Lawal yayi sauri katse shi "kaifa d'an rainin wayau ne bayan laifin da kamun harda sharri zaka
mun"
"to idan sharri ne kabarni na fad'amata mana"
"o o nak'i ai awuci wurin kawai amma alk'ur'an kun d'au alhakina da yawa"
dariya sukayi kafin daga bisan Lawal ya basu ledar da ya shigo da ita da kula yace "gashi ni
zan wuce sai da safenku Faruk kuma yana gidanmu"
har k'ofar gida Al'amin ya rakashi yana masa godiya.
bayan ya dawu yace "Aishana tashi muje d'aki sanyi ya fara sauka"
d'akinsa ya kaita ko ina tsab tsab tamkar ba d'akin saurayi ba sai k'amshi ke tashi
fita yayi zuwa d'akin Inna ya d'auko Plat da cop sannan ya koma d'akinsa ya zuba mata sinasin
d'aya Plat d'in ya zuba gasashiyar kaza
ya tura mata gabanta "oya canye"
fito da ido tayi cikin shagwaba tace "haba duk ni kad'ai ina zan iya ni bana ma jin yunwa"
harararta yayi sannan yace "kema kin san wasa kike"
kafin tace wani abu har ya matsu ya d'auketa ya d'aurata kan cinyarsa da lallashi da ban baki ya
samu taci abinci sai da ya tabbatar ta k'oshi sannan ya k'yaleta ruwan wanka ya kaimata
yace taje tayi wanka bayan ta shiga shima yaci abincin tana fitowa ya bata rigar barci cikin
kayan da Lawal ya shigo dasu
shima wankan ya shiga ya barta tana shiryawa
rigar iya karta gwaiwa k'aramin hannu take dashi bayan tasa ta d'aura Zane sannan tasa hijab
zama tayi kan katifa tayi tagumi tana jin kewar Aunty da Dady koda wasa bata tab'a kawu wa
aranta watarana zata samu matsala mai girma da Dady Yaya Saif
da zaisa su nisanta Kansu da ita suyi fushi da ita haka ya Allah ka sassauta zukatan su Dady su
daina fushi dani
lumshi idanunta tayi ba tare da ta damu da hawayen da ke bin fuskarta ba
Al'amin da fitowarsa kenan ganin yanayin da take ciki duk sai yaji ba dad'i cikin sanyin jiki ya
shirya cikin kayan barcci sannan ya rufe masu k'ofa
har ya zauna kusa da ita bata sani ba sai da taji ana cire mata hijab ta jiyo firgici ganin shine
yasa ta ajiyar zuciya
ta turo baki cikin shagwaba tace "o o kabar mun hijab d'ina sanyi nakeji"
"o o nik'i idan sanyi kikeji inada abun lullub'a" ya kwai kwaye muryarta ta b'oye fuskarta cikin
hijab tana murmushi
da wayau da lallami ya cire mata hijab da zani ya barta da rigar barcci ya sata k'irjinsa ta lafe
tamar 'yar baby ba ajima ba barcci yayi awun gaba dasu cikin yanayi mai dad'i.
washe gari sunayin sallah asuba ta koma barcci kafin ta tashi har ya gyara gida ya had'a masu
abun kari zai shiga wanka ta farka zaunawa yayi kusa da ita yana kallonta cikin k'auna
yace "sannu Aishana kin tashi"?
zamewa tayi daga kan katefa zata gaishe shi yayi sauri janyota ta fad'a jikinshi kunninta ya
lalubu ya kai bakinsa yana hura mata iska ahankali
tsikar jikinta taji tana tashi tsam jin halshansa na yawu cikin kunninta cikin wani irin salo yasa
jikinta ya fara disko lolí ½í¸œ
sai da yagama kashe mata jiki sannan ya k'yaleta ya kai fuskarsu ya had'i guri d'aya yana
gugan hancinsa da nata yace
"Aishana ina sonki tsakanin jiya zuwa ban san ya zan kwatanta maki irin farin cikin da nake ciki
ba duk da aurenmu yazo awani yanayi,
ina matuk'ar godewa Allah da ya bani ke da narasa ki ban san wani yanayi zan shigaba
Aishana *KAR KI GUJE NI*duk rintsi"
rungumeshi tayi cikin shauk'i tace Al'amin d'ina farin cikina bazan tab'a guje maka ba har abada
fatana na rayu dakai ba anan duniya kad'aiba har Aljanna fiddausi"
cikin jin dad'i yace "Allah ya amsa mana tashi muje muyi wanka"
k'waci jikin ta tayi tashige cikin zanin da suka rufa dashi tana dariya k'asa k'asa tace "o o nidai
idan kafito zanyi"
binta yayi yana k'ok'arin k'waci zanin tak'i ai kuwa ya hau yimata chakulkuli ba shiri ta sakar
masa zanin tana dariya d'aukarta yayi suka shiga wanka sai b'oye fuskarta take ak'irjinsa
saboda kunya.
bayan sun fito ya bud'i jikka kayansa ya d'auko mata wata duguwar Riga bak'a mai kyau ya bata
ta karb'a fuskarta d'auki da mamaki
murmushi yayi kafin yace "kina mamakin me ya had'ani da kayan mata ko?" bai jira amsarta ba
yaci gaba da Magana "matar yayan Lawal ke sayar dasu ranar munje gidan nagansu sun mun
kyau na saya maki guda ukku ina fatan sun maki"
da fara'a tace "sosaima nagode Allah ya k'ara bud'i"
bayan sun gama karyawa yace "Aishana zan fita amma ba dad'ewa zanyi ba"
"to yaushi Inna zata dawo"?
"na manta na fad'a maki d'azun kina barcci munyi waya da ita tana gaisheki da yamma zata
dawo"
"an haihu ne"?
"eh da asuba aka haihu ansamu 'ya macci"
"Allah yaraya"
"amin karki damu ba dad'ewa zanyi ba kinji"?
cikin k'arfin hali tace "Allah ya tsari ya dawo da kai lafiya"
cikin jin dad'i yace "amin Aishana ki kularmun da kanki sai nadawo".
bai jima da fita ba Inna tadawo da farin ciki Bety ta tarbuta "Inna Sannu da zuwa"
"yawwa Humaira ya zaman kad'aice"?
Murmushi tayi batace komai ba sai bud'e d'akin Inna da tayi
Inna tace "ba zama zanyi ba bari na watsa ruwa tukunna ko naji dad'in jikina"
"to Inna bara na kai maki ruwa"
"Aa barshi nagode"
"Haba Aa Inna ki bari na kai maki"
duk yanda Inna taso hanata tak'i sai da tad'ibi ruwa takaimata Inna tashiga wanka tana tasa
mata albarka.
12:30Pm Al'amin suka dawo tare da Lawal da kaya nik'i nik'i yara sun shigo da wasu kayan
lokacin Bety tana kwanci jikin Inna suna fira
shiguwarsu ne yasa ta tashi tana masu sannu da zuwa tare da karb'ar kayan dake hannun
Al'amin
wanda yake ta kallonta cikin k'auna da farin cikin yanda ya tarar da ita da mahaifiyarsa