Showing 9001 words to 12000 words out of 41150 words

Chapter 4 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2874

kunya taiwa Aunty bayani

Aunty tayi shiru tana kallon Bety kafin daga bisani tayi Murmushi tace "Betyna kice na fara shiri
nayi suruki"


Bety tabar d'akin da gudu tana dariya.

sanda ta k'arasa d'akin yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka k'awata parlour'n yana
latsi latsin waya

sallamarta ne yasa ya d'ago fuskarsa ciki da annuri

sanda idanunta suka sauka kan fuskarsa ba k'aramin firgita tayi ba

nunasa tayi tana fad'in "d..d..a..m..a..n k...kk.aini"?

tana fad'i tare da juyawa zata bar palour'n saurin shan gabanta yayi tare da durk'usawa kan
guiwowinsa ya had'i hannayen sa guri d'aya

ya fara magana cikin marairaice wa "Aisha na zan iya juran dukkan hukuncin da zakimun ciki
kuwa harda rama abun da namaki

Amma Dan Allah Dan darajar Annabi S.A.W Aisha na *KAR KI GUJENI*"

ya k'arasa maganar kamar zaiyi kuka.


*TURK'ASHI! MASU KARATU KU BIYUNI DAN JIN YANDA ZATA KAYA TSAKANINSU SHIN
WAYE WANNAN A.A? ZATA HAK'URA KOKUWA?*


_MAI K'AUNAR KU_

� *Aisha A Yabo*�

� Fulani�����
�����
������
�����
*KAR KA GUJENI*
������
�����


� *Aisha a yabo*�
Fulani�


® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*


*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*

*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_


*INA MATUK'AR GODEYA DA JIN DAD'IN ADU'AN KU GARENI FNS ALHMDLH NA SAMU
SAUKI NAGODE ALLAH YA BAR K'AUNA*


*40 to 50*


Zaunawa tayi gabansa cikin d'aure fuska tace "sai fa na rama marin da akamun ihin" ta fad'a
tana turo baki

cikin sauri yace "eh na yarda idan har ramawar zaisa ki hak'ura bisimillah"

kawar da kanta gefi tayi tana murmushi kafin tace "ya zanyi dole na hak'ura domin hannuna
bazai iya kaiwa ga fuskarka ba da niyar mari"

cikin farin ciki yace Aishana da gaski kin hak'ura ba zaki *gujeni ba*?"


girgiza kanta tayi tana dariya k'asa k'asa ajiyar zuciya yayi tare da yin dariya marar sauti

"Aishana da kin gujeni wallahi da ban san ya zanyi da rayuwata ba ke d'in wani b'angarice ga
rayuwata

Sonki yayiwa Zuciyata mamaya lungu da sak'o na Zuciyata zallar k'aunarki ne ke yawo ajinin
jikina

Aishana zaki Aure talaka mai sana'ar kafinta"?


k'asa tayi da kanta ji tayi gabaki d'aya kwarjinsa ya cika palon wata irin kunyarsa takeji wannan
yasa takasa cewa dashi komai

ya marairaici fuska kafin yace "Dan Allah kice wani abu tun kan na zautu Aishana"

"Ina sonka fiyi da tunanin mai tunani bazan iya rayuwa ba farin cikina ba Al'amin ka kasance
farin cikina kaid'in rayuwata ne duk rintsi *KAR KA GUJENI*Al'amin"

kallonta yake cikin tsananin shauk'i kalamanta sun faranta ransa

cikin jin kunya tace "ka zauna a k'asa"

"barni anan d'in zaman yamun dad'i"

cikin shagwab'a tace "Uhm um ni dai ban yarda ba muje ga kujera ka zauna kaji"

ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka cikin sauri yace "Aa basai kinmun kuka ba muje"

bayan ya zauna ta zuba masa kunun aya a kup ta bashi cikin ladabi ya karb'a yana murmushi

zata zubo masa abinci yace "Aa Alhamdulillah wannan ya ishini nagode"

ta shagwab'i fuska zatayi magana yayi saurin taran hanzarinta "kimun uzuri Aishana sai da naci
abinci kafin nazo nan"

"to me yasa zakaci bayan kasan zaka zo nan ni dai karka koma"

"shikenan Aishana bazan koma ba kin hak'ura"?

yayi maganar yana mai zubamata idanunsa cikin salon kallonsa dake k'ara mata sonsa

"Uhm ai bana fushi da kai yasu Inna da Faruk da Lawal"

"dukansu suna lafiya"

sunjima suna fira har goma tayi basu kula ba haka masoyan suka rabu ba son ransu ba.


ad'an k'ank'anin lokaci masoyan sukayi wata irin shak'uwa dukansu burinsu su kasance a inuwa
d'aya.


tana makaranta Dady ya dawo sai d'uki take ta koma gida harsu Meenat na mata tsiya

suna fitowa Zee ta shiga motarta tana Bety tace "KD zakiyi hutun k'arshan maku kenan"?

"eh kin San na fad'amaku zamuyi bikin Sister d'ina kano gobe da safi zamu tafi"

"oh na manta agaida momy"

"tab Allah nima ba zaku barni ba bari na d'auko kayana mutafi" cewar Meenat


Zee tace "kinga Ku tafi tare da Beety kunfi kusa sauri naki"

daganan sukayi sallama da Zee tawuce.


a hanya Beety take tunanin yanda zatayi "ba zata iya cewa da Meenat d'ai daga cikin Driver ya
kaita gida ba

hakanan tana jin nauyin su had'u da Al'amin ko wani nashi musamman yanzu kullum Al'amin
sai yamata k'urrafin tadaina zuwa gurin Inna

Inna sai jajan rashin ganinta take itakam kunya takeji ba zata iya zuwa ba"


sanda suka isa Unguwar Sun tarar da samari k'ofar kantin Lawal sunata cafta Al'amun na daga
gefi yana latsi latsin waya


3kwata ne jikinsa bulu sai teshat fara mai k'aramin hannu gashin kansa da yake a nad'aid'ayi
sai shik'i yake

ya mata kyau sosai mts! tsakin da tajini ya sata saurin jiyuwa tana kallon Meenat da mamaki


"ke kuma ke dawa"? cikin nuna takaicin abun da zata fad'a tace "acikin samarin can kin kula
da wani

wanda yayi shigar 'yan iska mai 3kwata da farar teshat"?

cikin tsananin bugun Zuciya tace "eh amma miye daga ganin mutum zakice dashi d'an iska"?

cikin yatsinar fuska tace "saboda na tsaneshi iyayanmu maza aminan junani sunyi alwashin
had'amu Aure

wai dan yana d'an rainin hankali d'an iska aranar da ya fara zuwa gurina bud'an bakinsa wai

shifa ba sona yake ba kawai zaiwa mahaifinsa biyayya

dan nid'in Sam ba kalar maccin da yake so bace"

ta k'arasa maganar tana k'wafa

cikin k'ok'arin b'oye tashin hankalin da take ciki tace "to ke kina Sonsa kenan"?


"wa! hud'ijjam kema dai kamar bakisan wacece Meenat ba aini talaka komai kyansa baya cikin
tsarina

shiyasa anan taki na mayar masa da raddi nace dashi daina ganin kyanka zai rud'ani kud'i
sune kyau agurina tsana kuma wacce nakema ta zarta wacce kakemun Dan haka Umma ta
gaida Aysha

in tak'aice maki labari na haukace masu bana so Abbana ya dage dole sai anyi ganin nak'i na
kwantar da hankali yasa babansa yace

tunda bana so a hak'ura kar azo ayi matsaluli su kunnu kai da k'yar Abban ya yarda aka fasa"

"gaskiya Meenat bakya kyutawa miye aibun talaka idan dai yana da kyan hali Meenat dugon
burinki yayi yawa ki dinga sassautawa rayuwarki"

dariya Meenat tayi kafin tace "Bety ba zaki gani illa da ciyon da ke k'unshi acikin talauci ba


saboda kin tasu cikin arzik'i gaba da baya dan haka duk abunda zance ba zaki gane ba"

"uhm ba wani nan kawai ki sauya tunani Meenat"

"um kinga bara na wuce dan ko zamu shekara ina maki bayani ba zaki gane ba"

ta fad'a tare da bud'i k'ofar motar da dama sunjima da yin pakeng bayan ta fitone take cewa "ba
zaki Shigaba"?

"Aa sai dai wani lokacin ki gaida su Umma"

"tom zasuji sai nazo karb'an tsaraban Dady"

cikin Murmushi Meenat tace "muna maraba daganan sukayi sallama.

ko da suka zo wycewa su Lawal ne kawai Al'amin baya gurin.

tana shiga gida suka had'u da Aunty Palo hannunta rik'i da plet anyanka kayan furut

ta rungume Aunty ta baya cikin murna tace "Aunty ina Dadyna"?


cikin dariya Aunty tace "oh Bety tunda Dady ya dawo shikenan ko gaisuwa ba zamu samu ba"?


dawowa tayi gabanta tarik'i kunni cikin marairaicewa tace "yi hak'uri Auntyna ai ban isa ba na
k'usa naga Dadyna"

"yana d'akinsa da gudu tabar gurin ta haura Sama

a hankali ta bud'i k'ofa tsayi ta tarar dashi yana waya yaba k'ofa baya

da sauri taje ta rungumeshi tana "Oyo yo Dady" cikin sauri ya katsi kiran

ya jiyu da ita gabansa cikin farin cikin ganin 'yar tasa yace "Betyna haka kika k'ara girma da
kyau wai me Auntynki ke baki kike k'ara hawa kamar farashin mai"?


turo baki tayi cikin shagwab'a tace "Dady nifa har rama nayi saboda kewarku"

"kai 'yar gidan Dady anya kuwa"?
"Allah Dady"

ta fad'a dai dai sanda suka zauna bakin gado

Dady yace ya makaranta kina dai maida hankali ko"

"eh Dady"
"to karatunki na arabikfa"?

"inayi Yasayyadi kwana2 baizo ba Babansa aka kwantar asibiti amma ina betan karatun"

"ayya Allah ya bashi lafiya"
"amin Dady ina tsarabana"
hancinta yaja yana fad'in bakinki baya mantawa da tsaraba

na sayo amma sai anbani labarin da akamun alk'awari"

dariya tayi kafin tace "Dady zan fad'ama amma ba yanzu ba"

"shikenan nima tsarabar ba yanzu ba"

janyi jikinta tayi ta koma gefe tana bubbuga k'afa ta fara "Aa Dady ni ni yanzu za aban"

janyota yayi jikinsa cikin lallashi yace "shikenan yi shiru zan baki amma dai ki tuna girman
Alk'awari"

murmushi tayi cikin jin kunya tace "zan fad'ama Dady amma sai ka rufi idonka"

"tom na yarda" ya rufe Idanunsa yana murmushi

taje dai dai kunninsa ta rad'a masa "Dady dama zan fad'ama kayi suruki" tana gama fad'a tabar
d'akin da gudu

da sauri Dady ya bud'i idonsa Wanda tuni murmushin da ke fuskarsa ya b'ace

wayarsa ya d'auka ya kira Aunty ba ad'auki dogon lokaci tashigo d'akin

ko gaisuwarta bai tsaya amsawa ba yace "da saninki Humaira ta fara Soyayya"?

cikin sanyin jiki tace "Aa sai dai ranar da ya fara zuwa nima nasani"

cikin b'acin rai yace "wato itace amanar da nabar maki ko?

to wallahi ki gaggauta walwali wannan al'amarin tun kan rayuka su b'ace kin San alk'awarin da
aka k'wulla tun shekarun baya ke baki isa kisa na warwareshi ba"

zatayi magana yayi saurin katseta ta hanyar d'aga mata hannu cikin tsawa yace b'acemun da
gani bana buk'atar jin komai daga gareki lallai kiyi abun da nace"!

cikin sauri tabar d'akin tana Shari hawaye.

wayar Yaya Saif yakira bai jira ya gama gaisuwar da yake ba yace "duk abun da kake Saifullah
kabarshi ina so gobe na ganka Nageria"

ya katsi kiran ba tare da ya saurari tambayar da Yaya Saif ke jihu masa ba.


_mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

�fulani�����
����
������
�����
*KAR KA GUJENI*
������
�����


� *Aisha a yabo*�
Fulani�



*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*







*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_


*HAR ABADA KEWARKI BAZATA TAB'A GUSHEWA BA IDANUNA BA ZASU DAINA ZUBAR
HAWAYEN RASHINKI BAZAI TAB'A ZAMA SABO GAREMU BA UWA MA BADA MAMA UWAR
KUWA hjy ZAHRA A. YABO ALLAH UBANGIJI YAJIK'ANKI DA RAHAMA YA HASKAKA
K'ABARINKI DA DUKKAN NI'IMUMI ALLAH UBANGIJI YA DAWWAMAR DAKE A FADAR
ANNABI MUHAMMAD S.A.W*

*50 to 60*


Bety tana zuwa d'aki wanka tayi tana cikin shiri wayarta ta fara ringing

tana dubawa taga Al'amin cikin farin ciki ta d'aga kiran tare da yimasa sallama cikin 'yar siririyar
muryarta

bayan sun gaisa yace "Aishana kin kyauta kin shigo unguwarmu inata murna zanga sanyin
idaniyana koda naje gida bake ba 'yan rakiyanki"

rik'e baki tayi tana murmushi tace "lah Yayana wa ya fad'ama nazo"?

"au kin d'auka bazan gane motanku ba"?

"oh kayi hak'uri Allah inajin kunyar Inna kuma k'awata na kawo inata sauri nazo naga Dady
kasan na fad'ama ya dawo yau da safe"

"sun dawo lafiya"?
"lafiya k'alau kasan miye harfa na fad'a masa maganarka"

"da gaske Aishana"?

"Allah Yayana na fad'amasa"

cikin farin ciki yace "gaskiya Aishana naji dad'i gobe Insha Allahu zanzo na gaida Dady"

"tom Allah ya nuna mana" haka masoyan suka cigaba da firarsu sun jima kafin nan sukayi
sallama.


Tana shan Ice craem Aunty ta shigo d'akin yanayin da taga Aunty ta firgita cikin sauri tace
"Aunty me ya sameki afuska naga tayi kumburi idanunki sunyi ja kamar kinyi kuka"?


zama tayi kusa da Bety kafin tace "na d'an bugi fuskana ne a k'ofa Bety inaso ki bani hankalinki
nan muyi magana"

ta fad'a cikin tsurawa Bety ido cikin sanyin jiki da fad'uwar gaba tace "to Aunty"

"Bety kin sani mahaifinki na tsananin Sonki haka ya nuna maki gata fiyi da tunani mai tunanin
tun tashinki baki tab'a neman abu kin rasa ba

da zarar kin nuna kina son abu ko baki furta ba da hanzari zai maki duk abun da zai b'ata maki
rai yana gudunsa

burinsa ko yaushe ya ganki cikin farin ciki shin Aisha da akwai abun da zai nema a gunki ki k'iyi
masa"?


zuwa lokacin Bety jikinta duk yayi sanyi bugun zuciyarta sai k'aruwa yake tanaji kamar wani abu
marar dad'i ke shirin faruwa da ita,

sai da Aunty ta sake maimaita mata tambayar cikin sanyin murya tace "Aa Aunty babu"

ta bata amsar a tak'aici
ajiyar zuciya Aunty tayi kafin tace "Aisha tun kina da shekara bakwai mahaifinki da amininsa
Alhaji ma'azu sunyi alk'awarin had'aku Aure da d'ansa fa'iz wanda yanzu haka yana singapor a
can yayi karatunsa yake kuma aiki babban likitan zuciya ne


anasa ran dawowarsa jibi kuma dama shi akejira ya dawo ayi bikin ku

ina rok'onki da kiyi hak'uri ki cire Al'amin a zuciyarki kiyiwa mahaifinki biyayya ki amince da
zab'insa"

ta k'arasa maganar tana mai kallon wani gefen

ban san taya zan kwatanta iya tashin hankalin da Bety ta tsinci kanta ba

cikin muryar kuka tace "amma Aunty me yasa baku fad'an da wuri ba? har sai da zuciyata tafara
son wani sannan za azo man da zancin wani anmun adalci kenan?"


Aunty ta dafa kafad'anta cikin tsananin tausayinta tace kiyi hak'uri Dadynki ne ya hana afad'a
maki ya kuma hana Fa'iz zuwa saboda baya son ki had'a karatunki da soyayya"


"uhm tom Aunty zanyi yanda kuke so"

daga haka bata sake cewa komai ba tayi kwanciyarta taba Aunty baya

ganin tayita magana Betyn tak'i tace da ita komai yasa tabar d'akin cikin tsananin tausayin Bety.

ranar kam Bety duk nacin barcci hak'ura yayi yabarta tunaninta "me zata fad'awa Al'amin ya zai
d'auketa marar cika Alk'awari mak'aryaciya??


ya zata rayu da wanin Al'amin? ya Allah gani gareka ya Allah ka kawo man mafita Alfarmar
Annabi S.A.W"


ganin kukan bazai fisheta ba yasa taje ta d'auro Alwala ta fuskanci gabas tana fad'awa mai
kowa mai kukanta.


washe gari sai sha biyun rana ta farko saboda rashin barccin da bata samu tayi ba sai da tayi
wanka ta shirya cikin Pakistan duk da batayi kwalliya ba hakan bai hana kyanta fitowa ba,


wayarta ta d'auko bayan ta kwanta kiran Al'amin ta tarar ba adadi sai sak'on da ya turo nmata

_Slm Aishana da_ _fatan kin tashi lafiya_
_Aishana ina kika_ _shiga inata kiran_ _wayarki bakya_ _d'agawa?_
_Aishana ban san_ _meyasa ba tun jiya_ _naketa jin fad'uwan_ _gaba har zuwa yau_ _d'innan
sai k'aruwa yake_
_ina cikin damuwa sosai Dan girman_ Allah da ma'aiki S.A.W ki d'aga kirana _ko zanji sanyi a
raina_"
_mijinki Insha Allahu_


tana gama karantawa ta cusa kanta cikin filo tana kuka fad'e take "Yayana kayi hak'uri ban
gujeka dan ina k'inka ba sai dan ba yanda zanyi"


tana haka Aunty tashigo cikin sauri ta k'arasa gurinta tallabota tayi jikinta tace "Bety kukanne
har yanzu


Dan Allah kiyi hak'uri ki daina sawa kanki damuwa adu'a itace abunda yafi ya kuma kamata
awannan lokacin ba wai kuka ko damuwa ba "

da lallashi da ban baki akasamu tayi shiru ta d'anci abinci kad'an suna haka Yaya Saif ya shigo
d'akin

Aunty ta gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa fita tayi d'akin

Yaya Saif ya zauna bakin gado ta fad'a jikinsa tana kuka bayanta ya dinga shafa cikin sigar
lallashi yace


"fad'amun damuwarki k'anwata idan bakya Son Fa'iz fad'amun baki da wanda yafi ne duk
duniyarnan nima banda wacci tafeki


matuk'ar bakya Sonsa ba zaki Aureshi ba bazan bari farin cikinki ya sub'uce saboda wani ba"


cikin kukan farin cikin samun mafita tace "Yaya nifa bana Sonsa ban tab'a ganinsa ba ban san
ya kalarsa yaki ba kawai ace shi zan aure

kumani koma nasan sa banayi inada wanda nake So idan narasa shi shi komai zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login