Showing 36001 words to 39000 words out of 41150 words
Chapter 13 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
haka zaka ce ko"?
bata jira amsar sa ba ta fita tsakar gida ta d'urata a fo aikwa kamar jira take tana azata ta fara
sai da tajira tagama sannan ta wanke mata da sabulu ta dawo falo
ta tarar autan Ummy yazo suna fira da Al'amin
"Aa Auta yau Kaine agidan mu aini fushi nake da kai"
"ayya Aunty kiyi hak'uri muna jarabawa ne shiyasa kika daina ganini"
"oh to ya jarabawa ana dai maoda hankali ga karatu ko"?
"eh Alhamdulillah"
"Allah ya taimaka"
"amin Aunty"
ya amsa yana mai karb'ar Sajida da taketa mik'o masa hannu
Al'amin yace "Auta Dady yana gari"?
"eh jiya sukak'i dawo da babban yayanmu amma naji yace yau da yamma zaiyi wata tafiyar"
"to Aishana ya kamata da anyi Sallah azahar muje mu gaida Dady tun bai bar gari ba"
"eh wallahi duk sanda zamuje bayanan"
"Auta kafad'awa Dady muna nan shifowa kaji"?
"to Yaya sai kunzo mun tafi"
bayan fitarsa ta kwanta k'irjinsa tana fad'in "Habibi tun safe nakjin fad'uwar gaba"
rungometa yayi kafin yace "ki dinga fad'an Innalillahi wa Inna Ilaihi raji'un da Hasbunallahu wa
ni'imal wakeel,
Insha Allahu zaki daina ji kinji Indona"
dukan wasa ta kaima sa ak'irji cikin shagwab'a tace "um um ni bana son sunan nan fa"
"um um ni kuma ina so ya za ayi"?
yayi maganar cikin kwaikwayun muryarta.
Bety da sallamarta ta shiga Falon gidan tana sakin labulen tayi turus sakamakun abunda
idanunta suka gane mata
kamar wacce akayiwa shoken ta jiyo da gudu tana kuka ta wuce Al'amin da ke tsaye bakin get
yana jiran isu cikin rud'u yabi bayanta yana
"Aishana Aishana Aishana ki tsaya nace mineni"!?
_Mai k'aunar Ku_
*Aisha A Yabo*
Fulani
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Burina addu'ata shine na kasan ce da Annabi Muhammad S.A.W a lokacin da nake numfashi
dare da rana ya RASULULLAHI S.A.W kasance akusa dani alokacin da za azari raina ina kallon
ka kana mun Murmushin ka mai d'aukar hankali har raina ya d'auke ba tare da nasani ba Ya
SHAFI'ULLAH kasa hannunka mai tsalki da Albarka acikin Ruwan wanka na su kasance suna
k'amshi daga cikin k'amshinka kasance dani Ya HABIBULLAH Acikin k'abari karkabari amun
tambayoyi Dan wallahi ban San komai ba sai tsantsar k'aunarka Ya KHAIRAL KHANZILLAH
kasance dani a ranar tashin k'iyama ranar da ba mai ceto sai kai ranar da kowa yake takansa
ranar da Iyaye za suce basu San d'ansu ba d'a zai ce bai san iyayensa ba yarda dani na
kasance a inuwar ka adamanka ya Aba Zahra Ameen!* *DANGI ANNABUN
DAI*!!
210
Auta na zuwa ya tarar da Dady suna magana da Yaya Saif afalo
yace Dady "Abban Sajida yace na fad'ama idan anyi azahar zasu zo gaishe ka"
da fara'a Dady yace "Allah ya kaimu da zan fita amma zan jira kawo man amaryar tawa"
Ummy da take fitowa tace "nifa gaskiya zan fara kishi idan dai kana gari baka da lokacina sai na
wannan k'uwailar"
dariya Dady yayi kafin yace "ai kuwa aiki ya same ki mai rabani da My Sajida ai sai Allah ki d'au
na Annabawa kawai"
"lallaima Alhaji aikuwa zan dinga tare k'ofa naga ta inda zata shigo"
Yaya Saif yace "ina kuka samu Baby mai kyau haka"?
yayi maganar yana karb'arta hannun Dady
"wallahi nan mak'otanmu suki muna mutunci da Babar yarinyar" cewar Ummy Yaya Saif ya
zubawa Yarinyar idanu cikin wata irin k'auna
yace "gata da shiga rai inama zasu bani ita"
yayi maganar cikin nuna da gaske yake dukansu dariya sukayi kafin Ummy tace "in banda
abunka kaida ba mata kake da ita ba taya zasu baka 'ya"?
"ai Ummy ko ne zan iya kula da ita ba saida mata ba"
"uhm haka dai kake gani kadaiyi k'ok'ari ka samu mana sirika zaman ya isa hakanan idan kuma
so kake sai Farhan yayi aure yabar ka shikenan
har ya haihu yaransa su fara kiranka Uncle na soro"
dariya yayi kafin yace "O o Dady zanyi Insha Allahu amma nafi so sai anga Bety"
"to Allah ya bayyana mana ita"
cewar Ummy "amin" suka amsa gaba d'aya.
bayan Sallah azahar duk suna zaune ababban falo har su Ilham anata fira Ihsan na kwance jikin
Yaya Saif tana masa shagwab'an sai ya saya mata sabuwar laptop
tana tuna masa Bety yanayin su shagwabar su duk d'aya shiyasa yake ji da ita
Sajida na Hannun Dady yana mata wasa
Yaya Saif yace "Ihsan kin fiya fitina ba kuna da ita ba"
cikin turo baki tace "to ai Yaya ta tsufa pls ka sauya mun"
"to naji anjima zan saya maki"
ihu tayi tana tsallin murna Ummy za tayi magana Sallamar Bety taji hakan ya hanata maganar
ta amsa Sallamar cikin fara'a
daga Dady har Saif jin muryar yasa sukayi saurin kallon k'ofa cikin ikon Allah tana shigowa
idanunta suka fad'a Kansu
da sauri Dady da Yaya Saif suka mik'e tsaye cikin had'a baki suka kira sunanta "Bety"!
juyawa tayi tabar falon da sauri tana kuka.
da mamaki su Ilham ke kallon su Dady Ummy tace "kun santa ne"?
ina basu kula da tambayar da Ummy take masu ba suka bi bayanta
suna fitowa su Bety na shigewa gida.
Al'amin ya rufe k'ofa sannan yabi bayanta kwanci ya tarar da ita kan gado tana kuka
hawa kan gadon yayi ya rungumeta cikin damuwa yace
"wai mi yafaru ne agidan wani ne bashi da lafiya ko mutuwa akayi"?
girgiza kanta tayi tana mai ci gaba da kuka "ko wani abu ya samu Sajida"?
nanma girgiza kanta tayi tambayar duniya yayi mata amma tak'i magana
ransa ne ya b'ace ya janyeta jikinsa cikin fad'a yace
"zaki daina kukannan ki fad'amun abun da ke faruwa ko sai na b'ata maki rai"!
fad'awa jikinsa tayi cikin shisshik'a tace "ashe dama Dady yana da wata mata harda yara nice
basasu shiyasa ya fita harkana
saboda ni tawa Uwar bata raye harda Yaya Saif yafi sonsu dani"!
da mamaki ya d'ago fuskarta yana kallo kafin yace "da gaske su Dady kika gani"?
"eh wallahi su nagani"
"to in banda abinki daga ganinsu sai kice gidan sa ne kika sani ko gidan abokinsa ne yazo"
"uhm Habibi duk yanda kaki da Yaya Lawal zaizo gidannan baka nan yayi d'are d'are falonka
tare damu"?
cikin sanyin jiki yace "Aa amma dai baki da tabbaci kuma ko hakanne zaiyu da yaranta ya
aureta"
mayar da kanta tayi k'irjinsa ba tare da ta sake cewa komaiba
jin ana bugun k'ofa yasa yayi yunk'urin tashi yaje ya bud'e
tarik'e shi "Allah ba inda zaka nasan sune suje yanda basa buk'ata ta nima bana buk'atarsu
Habibi ka ishini rayuwa da 'yata suje na TSA.....
da sauri ya rufi bakinta cikin lallashi yace "haba Aishana meyasa kike haka iyaye sun wuci wasa
ko mai sukai maki dole kiyi hak'uri tunda suka amsa sunan su na iyaye
sannan kina tunanin rashinsu a tare da ke yana mun dad'i ne?
kice baki sani ba ko yaushe ina zuwa tsohun gidanku ina away ko sun dawo bana samunsu
dan haka kisani wallahi nayi matuk'ar farin ciki da ganin su Dady
kima daina fad'an bazan bud'e masu ba ko basu zo ba ni zanje"
tashi tsaye tayi cikin fushi tace "to shikenan idan dai har zaka nemesu nikuma zan barma gidan
yau Kaje na barma su kai da kake da buk'atarsu"!
da sauri ya tashi tsaye yana kallonta cikin mamaki yace "Aisha ni kikewa gorin iyaye ni
kikecewa tunda ni nake da buk'atarsu
kenan nida band iyaye ni nake buk'atarsu ko? nagode kije kiyi duk abunda kikaga dama
iyayanki ne ba nawa ba"!
yayi maganar cikin tsananin b'acin ran da bata tab'a ganinsa ciki ba
yayi hanyar k'ofa zai wuce tayo sauri shan gabansa cikin tashin hankali tarik'ishi tace "wallahi
Habibi ba nufina kenanba taya zanma gorin iyaye wallah...
tureta gefe yayi ya fita d'akin ba tare da yaji sauran maganarba d'aura hannunta tayi aka kamar
zatayi ihu kafin ta mik'e tabi bayansa da gudu tana zuwa yana kullu k'ofa
k'wank'wasa k'ofar ta dingayi tana kuka tana kiran sunansa amma Sam yak'i kulata
a can k'ofar gida ma sunk'i hak'ura da bugun k'ofa da sauri tanufi k'ofar gidan aranta tana fad'in
zata bud'e masu ko Dan ta faranta ran Habibi
tana bud'ewa tayi ido hud'u da Dady kawai sai ta fad'a jikinsa tana kuka
bubbuga bayanta yadinga yi shima kamar zaiyi kuka yace "ya isa haka Bety daina kukan kinji
ina maigidan naki"?
muryar Al'amin taji yana "sannunku da zuwa Dady Ku shigo daga ciki"
bayan sun zazzauna a falo harsu Ummy da Ilham
Dady ya fara magana "kiyi hak'uri Bety ki yafe mun nayi nadama sosai akan abunda na maki"
sake shigewa jikinsa tayi kafin tace bakomai Dady nima kayafe mun rashin biyay... da sauri ya
katseta
" ni baki mun komaiba Bety ni ne namaki naso naja da ikon Allah nagodewa Allah da yabarni
da raina har naganu kuskure na hak'ik'a da ko rabun Sajida zai iya kashe ni"
ya jiyo da kallonsa ga Al'amin "zo nan d'ana"
Al'amin ya matsa kusa da Dady, Dady ya rik'o hannunsa "kayafe min kaji d'ana"
cikin murmushin da ke nuna jin dad'insa yace "bakomai Dady ban rik'ika da komaiba"
"nagode Allah yayi maku albarka Farhan Ihsan Ilham Auta ga Yayarku da nake fad'a maku
Ummy ga 'yarki"
tasuwa sukayi suka Rungume juna cikin k'auna ta 'yan Uwan juna
"Ummy tace ikon Allah Ashe k'aunar da sukewa juna ta jini ce"
cikin sanyin jiki Yaya Saif yace "k'anwata ki yafewa yayanki mai tarin laifuka k'anena kaima ina
mai neman ya fiyarka ni ne na dinga bibiyar duk wajan da kake Sana'a inasa ana koranka haka
nazo na saye gidan da kake zaune nasa suka kureka
duk tunanina idan Bety taji wahala da rashin kula zata sa ka saketa duk sai naga ashe ba haka
bane soyayya ta gaskiya ce atsakaninku
sosai nayi nadama nata neman inda kuka koma ban gane ba suma su Kawu da natambaye su
cewa sukayi basu sani ba
a lokacin Allah ya jarrabce ni da son wata yarinya 'yar talakawa ce sosai anan k'auyen Zariya
motata ta Lalace a hanya ita kuma zata tallan nono
wallahi gani d'aya namata Allah ya jarrabtan da sonta so mai zafi namata magana tak'i kulani
sai 'yan uwanta suka kwatanta mun k'auyensu da gidansu
wallahi maganar da nake maku daga yarinyar har mahaifanta sunk'i su kulani duk sintirin da
nake agarin nasani alhakinku ne ke bibiyata"
zai durk'usa gabansu Al'amin yayi sauri rik'eshi yana fad'in "haba Yaya dan Allah kadaina
wallahi ban rik'eka ba ko abaya na yafema kuma Insha Allahu zan tayaka da Addu'a idan da
Alkhairi Allah yasa matarka ce"
sosai yaji farin ciki har baisan sanda ya rungume Al'amin ba yana fad'in "amin nagode d'an
uwana"
Bety ta tasu ta rungumeshi cikin farin ciki ranar kam sun idar da wunin cikin farin ciki.
da dare kowa ya nufi makwancinsa Bety tsayi wanka ta shirya cikin kayan bacci wanda zan iya
cewa dasu da babu duk d'aya
ta d'auke 'yarsu tanufi d'akin mai gidan zaune ta sameshi kan gado yayi tagumi hannunsa biyu
da alama yayi nisa cikin tunani
kwantar da Sajida tayi kan gadonta sai baccinta take
zuwa tayi ta rungumeshi tare da fashewa da kuka cikin kuka tace "dan Allah Habibi kayi hak'uri
ka yafe mun wallahi abun da kake zato Sam ba haka nake nufi ba har abada bana fatn wannan
ranar tazo
kahimce ni Habibi Dan girman Allah da Manzon Allah S.A.W mijina ka yafe mun"
Rungumeta yayi kafin yace "na fahimceki Aishana baki mun komaiba zuciya ce bata da k'ashi
Dan haka karki dam yawuci
ina taya junanmu murnar sake kasancewa acikin famili"
"nagode Habibi" daganan takai bakinta cikin nasa tana kiss d'insa kamar jira yake shima ya
cab'e daganan fa labari ya fara sauyawa ganin haka yasa nagudu na rufu masu k'ofa.
*Bayan sati biyu*
Dady ne da Yaya Saif sai Al'amin zaune ad'akin Dady suna fira gwanin sha'awa
Dady yace "Al'amin ya kamata ka kaini gun iyayanka mu San juna tunda mun zama d'aya"
shiru yayi tare sunkuyar da kansa hankalinsa ya matuk'ar tashi da wannan tambayar ta Dady
dafa kafad'arsa Dady yayi kafin yace "d'ana fad'amun damuwarka karkaji komai ne mahaifinka
ne karka b'oye mun damuwarka"
ajiyar zuciya yayi kafin yace "jamar yanda Inna ta bani labari bayan na zama saurayi tace ta
tsince ni ne wata ranar juma'a
ta dawo daga tafiya da rana antattafi masallaci ba jama'a taganni a hanya inata kuka lokacin
bazan wuci shekara ukku zuwa hud'u ba
da ta tambaye ni sunana nayi shiru sai Abbu Mami da Dada nake ta kira
tace na nuna mata gidanmu ban bata amsa ba
ta tambaye 'yan tsirarun mutanen da ke wucewa suma basu sanni ba suke cewa
haka ta tafi dani gida mijinta na dawowa ta fad'a masa shima yayi binciki bai samu wanda ya
sanni ba
haka sukaci gaba da rik'ona tamkar d'an cikinsu dama yaransu biyu sun rasu tun suna yara,
sun tsayi mun akan karatuna saga islamiya har boko cikin taimakun Yayan aminina Lawal da
abotarmu ta d'auko asali tun muna yara unguwarmu d'aya muna son juna sosai
komai tare mukeyi,
inada sekara ishirin Baba yarasu haka Inna taci gaba da d'awainiya dani har Allah ya karb'i
Rayuwarta" daganan yayi shiru yana mai zubar da hawaye
" *Alhamdulillah*" naji Dady na furtawa kafin yacigaba da magana "Saifullah wallahi shine tun
ranar da naganka kamanninka suka tsayamun arai
zarge ya shiga zuciyata
kai ne d'ana d'an Yayanmu da ya b'ace tun yana k'arami kunzo ganin d'an uwanka Saifullah
saboda iyayanka basu samun damar zuwa sunansa ba sai bayan suna suka zo
kafito ba tare da sanin kowa ba munta nemanka tundaga k'afafan watsa labarai har wajan
hukuma amma ba labarinka haka suka bar garinnan zuciya ba dad'i
kamanninka da mahaifinka Sak wannan yasa ka tsayamun arai ikon Allah ranar da nabaka
auren Bety Sam ban kula da hakanba saboda banma kallon tsab ba"
wai mai karatu kwatanta irin farin cikin da Al'amin zai tsinci Kansa hum baki ko alk'alamina baza
su iya kawu maku irin farin cikin Al'amin da su Dady suke ciki ba.
_mai k'aunar Ku_
*Aisha A Yabo*
Fulani
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Ya Allah yarda mu so Manzon Allah S.A.W Ya Allah yarda mu nutsi nutsewa wacce babu
tsinkaya aciki sai tsantsar so da k'aunar Annabi S.A.W mu narki zuciya da jini ruhi da gangar jiki
duk acikin Son Annabi domin sonsa ne mafita k'aunarsa ce tsera begensa ne dacewa Annabi
yarda dani Kasan dani acikin masoya yarda na zamu mafi kusa da kai ahannun daman ka ya
Aba Fad'ima* *amin* *dangi Annabin dai* !!
*END END*
*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH*
Rungumi juna sukayi dukansu ukkun suna masu zubar da hawayen farin ciki
Yaya Saif yace ikon Allah "wallahi Dady sai da ka fad'a naga kamanninsa da Uncle d'in India pls
Dady ni zanwa su Uncle albishir"
"Aa ai bazan fad'awa kowa ba sai dai su ganmu dashi d'ana maza tashi kuje kuyi shiri da
bizarmu tasamu zamu India gurin su Yaya daganan sai muwuce Sudan gurin kakanninka da
sauran dangi
Saif kuje ayi duk abunda ya dace gami da tafiyarmu"
"to Dady angama tashi mutafi Yayana dukda dai na baka Bety ni ya kamata kacewa Yaya"
"Haba k'anena ai kamakaru dole dai ni zaka cewa Yaya ko ba haka ba Dady"?
Al'amin yayi maganar cikin fara'a "Dady Yace "sosai Son dole yace Yaya dan Shekara hud'u ba
wasa ba"
haka suka bar gurin Dady cikin farin ciki ak'ofa suka had'u da Ummy zata shiga d'akin tace "Aa
ina zuwa haka sai farin ciki kuke ko ta samu ne"?
Rungumeta Saif yayi kafin yace "sosaima Ummy ke dai shiga Dady zai fad'a maki mun tafi"
"abincin fa"?
Al'amin yace "Ummy sai mun dawo dai" suka bar wajan da sauri
ta kad'a kai sannan ta fad'a d'akin tana fad'in "Alhaji wai me kabawa yarana ne suke ta murna
haka"?
nan ya bata labari sosai tayi farin ciki da tayashi murna.
suna fita gidan Al'amin suka shiga tun daga waje yake kwala mata kira hakan yasa da sauri ta
fito ban d'aki tana fad'in
"Habibi wannan kirafa lafiya"?
tana zuwa ya d'agata sama yana juyi