Showing 30001 words to 33000 words out of 41150 words
Chapter 11 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
tashi tsaye arud'i tana tambayarsa "Habibi
lafiya?"
murmushin k'arfin hali yayi kafin yace mata "bakomai Aishana"
ya fad'a yana mai zaunar da ita shima gefenta ya zauna yace "Aishana kin san abaya na fad'a
maki yanda mukayi da su kawu ko"?
cikin k'aguwa tace "eh na tuna"
"to yanzu sunzo suna buk'atar na basu gida saboda rashin biyansu kud'i har karo biyu kiyi
hak'uri Aishana na kasa rik'eki yanda ya kamata muhallin da zan suka ki yau yana neman ya
gagare ne"
ya k'arasa maganar yana mai zubar hawaye
hannun shi ta rik'e cikin nata tana murzawa ahankali ta fara maga cikin natsuwa tace "ka daina
fad'an hakan habibi Ubangiji ya sani nima kuma na sani baka gaza da komai ba gurin kula da
hakk'ina ta ko wani b'angare
kana iya k'ok'arin ka jarabawa ce da bawa bai isa ya kauce mata ba dan haka karka damu ina
tare da kai akowani yanayi
fatana Ubangiji Allah ya bamu ikon canye jarabawar Allah ya kawo mana d'auki alfarmar Annabi
S.A.W"
rungometa yayi cikin tsantsar farin ciki yace "nagode Aishana Allah yayi maki albarka Allah ya
faranta maki fiye da yanda kika faranta mun"
"amin Habibina yanzu ya zamuyi"?
"tafiya zamuyi Aishana sai dai zaki jira na je na dawo"
"to Allah yasa su d'aga ma k'afa har ka dawo d'in"
"amin"
ya fad'a yana mai tashi tsaye har ya kai k'ofa tace "lah Habibi namanta na fad'a ma Yaya Lawal
ya dawo har ya zo bai tarar da kai ba"
cikin farin ciki yace "yaushe yazo"?
"bai jima da fita ba ka dawo amma yace mun zai dawo"
"Allah sarki Lawal zanyi k'ok'ari idan komai ya daidaita na nemeshi"
daga nan ya fice d'aki yana jin wani abun aransa.
yana fita ya tarar da su kawu suna ganinsa Baffa yace "ya naga ka fito ka kad'ai"?
"kuyi hak'uri Baffa a yau d'innan zan bar gidan amma kumun alfarma naje na samu wani gurin
sai nazo na tafi da iyalina"
"uhm raina mana hankali dai kake so kayi wani gurin kake da shi"?
"Aa ba zan rainawa iyayena hankali ba gaskiya ne banda wani gurin amma ba a rasa na Allah a
ko ina"
"kai dai kasani duk inda zaka ba abun da ya shafe mu ayanzu dai muke buk'atar gida ba sai
anjima ba ihen"
Lawal da tun fitowar Al'amin yazo sai dai sam hankalin su bai kai kan shi ba yace "Ku daina
tada jijiyoyin wuya Kawu Baffa yanzu zai bar maku gidan
kuma Allah ba azzalumin bawa bane dan kunga k'asa ta rufe idon Inna shine kuke neman Ku
tozarta amanar ta
uhm idan dai duniya ce wallahi kuje ta ishi kowa Riga da wando"
daga haka bai safe cewa komai ba ya fad'a gidan yana k'wala sallama
yabar su kawu cirko cirko suna mazurai shima Al'amin bai ce da su komai ba ya bi bayan
amininsa.
"Bety Bety kina ina"
cikin sauri ta fito ban d'aki tana fad'in "Yaya Lawal lafiya"?
"lafiyar kenan fito da kayanku mu tafi"
za tayi magana idanunta suka kai kan Al'amin da ya keyi mata alamar tabi umurnin Lawal
kayan sawar su kad'ai suka d'auka sai wata 'yar ma dai daiceyar jaka da Al'amin ya d'auka
har suka shiga motar Lawal magana bata had'asu ba Lawal sai hirarsa yake da Bety
murmushi Al'amin yayi kafin yace "wai mutumin laifin me nayi ake ta shamun k'amshi haka"?
Lawal ya sakar masa harara kafin yace "oho shafa kaji"
dariya Bety tayi kafin tace "ni dai idan laifi mukayi muna bada hak'uri ayi mana afuwa"
"uhm K'yale ni da shi Bety wai duk yanda muki da Al'amin yana cikin wani yanayi da ya kamata
ace na sani ya b'oye mun sai dai naji abakin wasu
agurin su Sageer nake jin komai sai gashi ina zuwa ba tarar da su Kawu na masa tijara
kuma da banzo ba shikenan sai dai na shafa naji ba kwanan hakan ya kyauta kenan"?
"Aa gaskiya amma kayi hak'uri"
Al'amin ya karb'e kayi hak'uri Lawal bana so ne na d'aga maka hankali shiyasa na b'oye ma
halin da nake ciki"
"hum Al'amin ai babban tashin hankalina nazo na tarar ba kanan ban kuma san inda zan gan ka
ba"
"kayi hak'uri ni dai"
"to idan banyi ba dukan ka zanyi"
"idan dai har dukan nawa zai sa ka daina fushi dani ina maraba" yayi maganar yana dariya
nan take aminan suka ware suna hira cikin nishad'i basu jima ba suka isa Malali kai tsayi ya nufi
wasu tagwayen gidaje masu kyau da tsari komai iri d'aya
gidan da ke hannun dama yayi hon mai gadi ya bud'e masu k'ofa
bayan yayi pakeng suka fito ya fito da key cikin aljihu ya bud'e masu k'ofa da mamaki suka
bishi bayan shi
gida ne mai kyau dai dai misali komai cikin tsari yanayin sa tamkar gidan turawa sai da ya
nuna masu ko ina na gidan
farkon shiga babban falo ne sai d'akuna ukku kowani da toilet acikin bedrooms komai wait
babban falon yana set biyu komai na falon yana da ash an bolec reid labulayen ma da tayes
duk kala d'aya ne sai kayan kallo irin ba zamani
sai kitchen shima dai dai gwargwadu an k'awata shi da kayan zamani
bayan sun dawo falo Lawal yace "Al'amin ya kaga gidan"?
cikin murmushi yace "gida kam masha Allah yayi kyau gwanin sha'awa"
"alhamdulillah ga key gidan ka ne halat malak kamar yanda ka sane mun yiwa juna alk'awari
idan Allah ya hore muna zamuyi tagwayen gidaje zamu zauna guri d'aya za muyi aure rana
d'aya
Allah ya cika mana d'aya burin na zama guri d'aya aure ne dai bai nufa muyi tare ba saboda
naka rabon yafi nawa zafe"
ya k'arasa maganar cikin tsokana kafin yaci gaba da magana "kuma kamar yanda Yaya ya
sama mun aiki a Abuja kaima ina farin cikin shaida maka ya d'auke ka aiki a Sabon kamfaninsa
da ya bud'a a garinnan amatsayin manaja
da zai kira ka ya fad'ama ni na hana nace zan zo da kaina na fad'ama Dan na karb'i goron
albishir"
daga Al'amin har Baty suman zaune sukayi sun zubawa Lawal idanu ba tare da sun iya cewa
da shi komai ba.
*kuyi hak'uri da wannan Muna hidima ne*
_mai k'aunar Ku_
*Aisha A yabo*
FulaniHy
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Jikukin Annabi S.A.W yau gani gaban Ku nayi durk'usu Ku sanya mun Albarka Ku yarda dane
Ku Kaine gaban Kakan Ku yasan dani acikin masoyan sa ta hak'ik'a. wallahi shaihanai 'ya'yan
Nana fad'ima asoku adace da samun rabo mai d'aurewa har gaban Ubangiji ak'iku atab'e
tabewa har ga Ubangiji na gaishe Ku shurafa'u.*
*Allah ya k'ara mana soyayya da kusance*
*160 to 170*
Al'amin tsabar farin ciki rungume Lawal yayi kawai sai ya fashe da kuka "haba mutumin miye
haka dan Allah ka daina kukannan bana so"
cikin muryar kuka Al'amin yace Lawal ban da bakin yi maku godeya tun muna yara kuke
taimako na Yaya bai banbanta ni da kai ba komai yama yana mun,
Ubangiji Allah ya saka maku da mafificin alkhairin da kuka mun Allah ya biya ku da gidan
aljanna fiddausi alfarmar Annabi S.A.W"
cikin sanyin jiki da jinjina aminta irin ta Lawal da Habibin ta tace "amin summa amin Yaya Lawal
muna godeya sosai Ubangiji Allah ya faranta maku fiye da yanda kuka faranta mana,
Alhamdulillah Allah mun gode ma"
cikin murmushi Lawal yace "amin na gode da addu'oin ku ni zan tafi gida sai mun had'u anjima"
Al'amin yace "ai ba zaka barni ba tare zamu fita"
"Aa ni baza ka bini ba haka kawai kasa Bety tace nazo na d'auke mata miji kaga har ta fara
harara na"
rufe fuskarta tayi tana dariya tace "lah Yaya Lawal yaushe akayi haka"
"yanzu mana"
ya fad'a yana dariya Al'amin yace "Lawal Allah ya shirye ka ni kasan ma me na tuna"
"Aa sai kafad'a" "hahahahaha ranar da wani yaga motoce sabo da tsabar tsoro sai da ya sake..
Key d'in mota Lawal ya jefa masa yana dariya yace "wallahi zan sab'a ma Al'amin"
yana maganar tare da tashi tsaye "madam na gudu tunda mijinki ya kure ne"
haka suka bar gidan suna raha
bayan fitarsu ta sake gyara gidan duk da bai da wani datti sannan ta duba kitchen taga akwai
kayan abinci sai ta dafa masu jalof d'in kuskus da busasshin kefe bayan ta kammala girkin tayi
wanka ta shirya cikin dogowar Riga ta atamfa
ta zauna falo tana kallon tashar larabawa.
da dare ya d'auke ta suka je gidan Yaya suka masa godeya matarsa sai meta take masa sai
yau yaga damar kawo masu matar shi dai hak'uri kawai yake bata.
Alhamdulillahi cikin k'ank'anin lokace rayuwa ta sauya masu ya fara aikinsa cikin gaskiya da
rik'on amana
zamansu da Baty k'auna ce da tsantsar kulawa tuni ta fara zuwa awo ta hanyar shawarar wata
mak'wamciyar ta
wacce sukayi sabo sanadin ya ranta kwanan su ukku da dawowa Unguwar ta raku Al'amin har
bakin get har zata shige sai budurwar wacce bazata wuce shekara goma sha shidda ba tayi
mata sallama
Bety ta amsa cikin fara'a budurwar tace "Sunana Ilham kinga gidanmu can gaban gidanku
amma tun jiya na ganki kin raku mijinki naji kin tsaya mun arai har na fad'awa Ummyna amma
dai baku jima da dawowa ba ko"?
cikin Murmushi tace "Allah sarki sannu Ilham eh bamu jima da dawowa Unguwar ba"
"haba nikam nace sababbin dawowa ne"
"wallahi kuwa munyi tsaye awaje bisimillah shigo daga ciki"
"Aa nagode ina sauri zamuje d'auko Dady kinga yayana can yana ta mun hon dama ganinki ne
yasa na tsayar da su sai na shigo" ta fad'a tana mai barin gurin da gudu
daga ranar Ilham tana zuwa wajan ta har ranar Ummyn su tazo da dare suka gaisa shak'uwa
mai k'arfe ya shiga tsakanin Bety da su Ilham.
*Ina labarin Dady*
bayan tafiyar Bety duk sai yaji gidan ya masa fad'e zuciyarsa ta masa nauye wannan yasa ya
yanki shawarar barin gidan gaba d'aya yakira Yaya Saif ya bashi umurnin ya sallame dukan ma
aikatan gidan da kud'ad'e masu yawa.
da safe suka rufe gida Yaya Saif da Dady suka nufi Sudan sai lokacin iyaye da 'yan uwa sukaji
abun da ya faru aikuwa Dady yasha fad'a kamar zasu dake shi
Baffa yace "ilimin ka da girman ka basu amfane ka da komai ba tunda har ka biyewa rud'un
duniya
ka guje 'yar ka da matar ka saboda abun duniya miye illar talaka uhm? sam ba irin tarbiyar da
muka d'aura ka akai ba"!
ya k'arasa maganar afusace yayansu yace "ai sai mu shirya gobe mu tafe ka kaimu gidan yaron
dan baza ayi wannan haukan damu ba sannan ayi bekon ita Zainab d'in"
cikin muryar nadama yace "kuyi hak'uri na yanki hukunce cikin fushi ban san yaron ba ban San
daga ina yazo ba"
ga baki d'aya d'akin ya d'au Innalillahi wa inna ilaihi raji'un
cikin tashin hankali hajyarsa ta tasu ta kifa masa mari tana magana cikin kuka "amma anyi
shashan yaro yanzu ka d'au marainiyar yarinya ka bawa wanda baka San ko waye ba,
baka san daga ina ya fito ba to wallahi duk inda zakaje ka nemomun jika sai ka nemota ba
ruwana"!
Dady yayi k'asa da kansa yana jij zafe azuciyar sa sanadin biyewa zuciya yau ya kai shi ga
nadama, ya sanya mahaifiyarsa kuka
cikin fushi Yaya Saif yace "wai sai fad'a kuke da tada jijiyoyin wuya shi Dady miye laifinsa ai
itace mai laifin ita tace taji ta gani ba shikenan ba"
"uwar ka nace uwarka shashan banza wato da kai aka had'a bake aka cutawa 'yar uwarka ko to
kun kyauta"
ranar kam daga Dady har Yaya Saif basuji da dad'i ba gurin famili
washe gari Baffan Dady dana Momy Safna da Babban ya'yansa sukak'i shigo jirgi zuwa nageria
Yaya Saif kuwa run adaren yayi tafiyansa ba Wanda yasan ina yaje ba kuma wanda ya
nemeshi.
hotal suka sauka sai da sukayi sallah la'ar sukayi wanka sukaci abinci sannan suka nufi zariya
cikin angayar Motocen Dady
kyakyawar tarba suka samu gun Inna kamar ba abunda ya faru bayan sun natsu d'akin Abban
Aunty aka sauke su sannan aka kira k'anin mahaifinta
bayan sun sake gaisawa Abbun Safna yayi gyaran murya kafin yace "to Malam ba komai ne ya
kawo mu ba sai dan mu bada hak'uri akan rashin hankalin da yaron mu yayi
adubi girman Allah ayi hak'uri wallahi bamu da masaniya akan d'anyen hukuncin da ya yanke
ayi hak'uri ta koma d'akinta"
Malam Kawu yace "maganar gaskiya da shi kad'ai yazo gidannan ko kallo ba zai ishe ni ba
albarka cinku ne yasa na zo maganar komawar yarinya kuma yana gurinta idan ta amince LA
ba asa"
ke Zainab ina kiki ne"?
"na'am Kawu" ta amsa daga d'akin Inna
bayan ta shigo tasamu gefe ta zauna Dady ya d'ago ya kalleta wani irin abu yaji ya suke
zuciyarsa tamkar kibiya da bazai iya tantanci ko miye ba
maganar Kawu ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya fad'a
"ke Zainab iyayan mijinki sunzo bada hak'uri da Neman ki komawa d'ansu me kika gani zaki
koma koku Aa"?
Dady tuni ya jik'i shakaf da gumi wani irin tashin hankali da bai tab'a ji ba arayuwarsa ne ya
ziyar ce shi shin idan Zainab ta fallasa asirin zamansu wani hukucin zai fuskanta agurin
iyayansa?
_mai k'aunar ku_
*Aisha A Yabo*
Fulani
*KAR KA GUJE NI*
*Aisha A Yabo*
fulani
*®Real Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Tabbata ttar soyayya itace ka so masoyan Wanda kake so Sahabbai Masoya Annabi S.A.W
Soyayyar Ku gare ta daban ce zuciya da baki baza su kwatan ta tsantsar k'auna ta gare Ku ba
daku nayi rik'o daku nake kamun k'afa Ku kaini har gaban Annabi Muhammad S.A.W*
*Ina yinku irin sosai d'innan 'yan Aisha A Yabo Hausa Nvl&Aisha A Yabo Lvly true FNS*
*170 to 180*
Sai da Kawu ya sake mai maita maganar sannan ta fara magana cikin girmamawa tace "Kuyi
hak'uri Kawu Baffa abar zan cin komawa ko hakan bata faru ba dama zaman nawa na d'an
lokace ne"
Baffa yace "Zainab me yasa zaki ce haka mun sani ba akyauta maki ba amma duk da haka
muna mai baki hak'uri Insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba"
"Baffa kuyi hak'uri wallahi bank'i maganar ka ba amma dama can hakan zai faru abisa alk'awari
da yarjejeniyar da mukayi da Dadynsu Bety kuma gashi nan a tambaye shi"
dukansu da ke d'aken suka mayar da kallonsu kan shi Yaya yace "Sufyan fad'a mana abun da
ke faruwa"
Dady k'asa yayi da kansa cikin muryar rud'u yace "Yaya ba komai kawai shirmin ta ne"
Kawu ya hau kanta da fad'a "Zainab bana son shashance da yawo da hankali idan komawan ne
ba zakiyi ba sai ki fad'a ba wai sai kin mana yawo da hankali ba"!
ganin yana son d'aure ta da dawo da laifin kanta taga gara kawai ta fad'a
cikin nafsuwa ta walware masu irin zaman da sukayi da Alk'awarin da sukayi har kawu dalilin
saken da yayi mata
ai gaba d'aya d'akin ya d'au salati masu Innalillahi nayi
cikin tsananin b'acin rai Baffa yace "Sufyan ka kyauta Allah ya saka ma da Alkhairi kayi duk
abun da ya dace"
ya juya kan Kawu da ya daskare ya kasa cewa komai saboda tsabar takaici da b'acin rai
"Malam Dan Allah ayi hak'uri bamu da masaniya akan komai hak'ik'a Zainab tayi k'urciya da ta
fad'a tun farko da hakan bai faru ba
Zainab ban San me zance ba amma nasani ko ban fad'a ba Allah zai yi maki sakayya"
Uhm ajiyar zuciya kawu yayi kafin yace "ai Sufyan bai da laifi mutumin da ya fad'a maki gaskiyar
baya sonki to name zaki nace kice sai kin raini yaransa ko ke kika haife su
ai kya hak'ura ki barsu ballatana ba dangin iya ba na baba kin cotawa kanki abanza
kai kuma mun barka da Rabbul Izzati ya mana sakayya"!
ya bar d'akin afusace Zainab itama bayansa tabi jiki ba k'wari su Baffa suka bar gidan dan basu
da kalamin magana.
awashi gari suka wuce Sudan ba tare da sun kula ban hak'urin da Dady ke basu ba.
Iyayen sa da 'yan uwa sunyi bak'in cikin jin wannan labarin kowa fushi yake da shi yayi zuwa
ban hak'uri har ya