Showing 39001 words to 41150 words out of 41150 words

Chapter 14 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2875

da ita sai da ya gaji dan kansa ya direta kan gado ya
rungometa yana fad'in "Albishirinki"

Bety da take ta kallonsa tana mamakin wannan farin ciki da take gani afuskarsa tace "goro"

"nasamu iyayena da 'yan uwana"

fito da ido tayi cikin sauri tace "dan Manzon Allah"

"S.A.W wallahi kuwa ashe Aishana bayan k'auna ta aure da nake maki har k'auna ta jini ce
ajikna shiyasa nake jin sonki fiye da tunanin mai tunani"

"Habibi kasani aduhu yimun bayani yanda zan gane"

nan take ya bata labari ihun murna ta saki "Wayyo Allah Allah na Allah nagode ma da ka nuna
mun wannan babbar ranar"

" *Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah*" suka furta atare sun jima d'aki suna farin ciki kafin
ya tuna ya bar Saif a falo

da sauri ya mik'i "Aishana na manta Saif na falo yana jirana zamu fita"

sai da suka gaisa da Saif da taya juna murna Sannan suka fita ita kuma ta rufe gida ta nufi
wajan Dady.


Dady yasa Al'amin ya kaishi gurin Yayan Lawal yayi masa godeya Sosai tare da addu'a Allah ya
biya shi da mafificin alkhairinsa.


Lawal farin cikin da yayi na samun iyayan Al'amin baya misiltuwa yace dole dashi za aje yaga
mahaifan amininsa dan haka tare Dady ya shirya masu tafiya

cikin Sati na biyu komai na tafiya ya kankama ranar talata suka nufi Legos daga can suka hau
jirgi sai India shigar safe sukayi shatar tx sukayi har unguwar da Uncle Muhammad yaki zaune
(yayan momy Safna

bayan sun shiga gidan shiru kamar ba kowa Dady ya kira sa da waya bayan ya d'aga kiran
Dady yace "Yaya gamu fa acikin gidanka sai dai kamar ba kowa"

cikin farin ciki yace "haba Masha Allah gamu fitowa duk suna barcci ne gamu nan sannun Ku da
zuwa"

ba ajima ba Abbu da Mami suka fito Al'amin yana ganinsu yaji kamar yaje ya rungumesu wata
irin k'aunar su ce yaji tana ratsa jini da zuciya

muryar maminsa ya tsinkayu tana maraba da k'aramin mai gida zuwa ba sanarwa"

"wallahi kuwa mun sameku lafiya"?

"lafiya k'alau Ummyn yara sannunku da hanya"

"yawwa Aunty Yaya mun sameku lafiya"

Uncle yace "Masha Allah Ashe anga Bety shine baka kira ka fad'amun ba"

"ayi hak'uri Yaya na bari ne sai munzo shiyasa"


nanfa aka shiga gaishe gaishe Bety taje jikin Uncle ta kwanta a kafad'arsa takai bakinta dai dai
kunninsa cikin rad'a

tace "Uncle kalli wanda ke gefen Dady sosai"

shafa kanta yayi kafin yace "Me nine"? yayi tambayar dai dai sanda idanunsa suka fad'a kan
Al'amin da shima shi yake kallo firgici ya mik'e tsaye

"Sufyan waye wannan Maminsu kalli wani ikon Allah"!

itama Mami kallonsa take ciki da firgici Dady yayi Murmushi kafin yace Alhamdulillah Yaya Ku
kwantar da hankalinku wannan da kuke gani ba kowa bane face d'anmu da ya b'ata a shekarun
baya wato *ABDULHAKEEM*

nanfa aka shiga maida zance Rungumeshi sukayi suna mai godeya ga Ubangiji

da yanuna masu d'ansu da har sun ciri tsammani auta Salma ta fito tana hamma da Alama
barcci ta tasu

ganin su Bery da Ilham yasa tazo da sauri ta fad'a jikinsu tana "Oyo yo" Mami tace "Salma ga
yayanku *Hakeem* da ya b'ata

da sauri taje ta fad'a jikinsa tana ihun murna

nanfa gidan ya kacame da murna baki har baka Sajida 'yar dangi har na rasa wa yafi sonta
tsakanin iyaye da kakanni.

nan aka kira 'yan uwansa biyu da ke aure Mumbai Fatima da Ruk'ayya duka k'anninsa ne cikin
dare suka isu ranar kam kwana hira akayi.


satinsu d'aya suka nufi Sudan Al'amin ko nace *ABDULHAKEEM* yaga soyayya da gata agun
iyaye da dangi Lawal sai mamaki yake Ashe haka amininsa yake da gata ji yanda shi Kansa
ake nuna masa k'auna da kulawa duk saboda *Hakeem* Allah da iko yaki

walima akayi Sudan saboda murnar ganu d'ansu nda akayi sadaka sosai ga mabuk'ata

uhm abu dai sai sambarka.

asati na biyu Dady dasu Lawal suka shirya dawowa Nageria su *Hakeem* da iyayansa zasu
wuce India Abbu yace ba zai iya nisa da su ba.


*Bayan shekara d'aya*


Bety tana kwanci jikin *Hakeem* cikin shagwab'a tace "Habibi yaushe zamu je Nageria? ina so
naje "

"Aishana kinfiya son yawo me zakiyi a can duka duka yaushe muka dawo naga dai su Dady
basu jima da kumawa ba 'yan matan Ummy sunzo mana Hutu yau satinsu ukku da komawa"

"uhm um Habibi ka manta Auntyn Zariya ta haihu ina so naje suna Dan Allah Habibi karka ce
Aa"

"kiyi hak'uri da sunannan ga bikin Saif da Lawal saura wata d'aya kuma duk a Kd za ayi idan
angama sai kije

Zariya kimata kwana biyu kinji 'yar k'anwata"

ya k'arasa maganar cikin lallashi murmushi tayi kafin tace "na hak'ura Habibi Allah ya nuna
mana"

"amin ya kamata ki bani baby hakanan tunda dai Mami ta k'wace mana Sajida"

yana maganar tare da shafa mararta

"wasa kasa shiyasa babyn baizo ba"

"iye haka kika ce aikuwa zaki sani daga yau zan ciri wasa aikin zan dingayi tuk'uru ba dare ba
rana"

cikin dariya tace "o o bafa haka nake nufi ba"

"koma ya kike nufi za kiyi bayani ne yarinya"

kiran wayarsa ce ta katsi hirar tashi tayi taje ta d'auko masa wayar number Nageria ce sai dai
ba suna

yana karb'a yayi tsaki tare da katsi kiran da mamaki tace "meyasa Habibi kasani ko wani na
gida ne"?


"wata ce ke yawan damuna"


"iye wata"?

tayi tambayar firgici zaunar da ita yayi kusa da shi yace "miye na d'aga hankali dan Allah ki
kwantar da hankalinki

bafa wata bace face Meenat ban san waye ya bata number na ba yau sati d'aya kenan tana
damuna da kira
wai hak'uri take bani kuma dan Allah ita ta amince zata aure ni nayi hak'uri"

cikin sanyin jiki tace "to me kace mata"?

"kema kinsani ko ak'afa aka d'ura mun ita zan cire na yar bare kuma da hankalina ta manta duk
tijarar da tamun da wacce ta maki ne

ai da bazatayi gigin kirana ba tas na mata na kuma fad'a mata ko kyautar ta akabani banayi
akai kasuwa

kuma tun daga ranar ban sake d'aga kiranta ba amma tak'i zuciya ta k'yaleni sai kirana take da
nambube barkatai da na d'aga naji muryarta zan katsi kiran"

kwantar da kanta tayi a k'irjinsa cikin sanyi tace "Habibi dan Allah *KAR KA GUJE NI* saboda
wata"

gashin kanta da yasha gyara ya dinga wasa da shi kafin yace "bana fatan zuwan wannan ranar
Aishana har abada bazan tab'a guje maki ba mun zama anta da jini

ke kad'ai kin ishe ni rayuwa banda burin zama da macci fiyi da d'aya ballatana ma har na d'auko
wacce zata sa na guje ki

sai dai ban san ikon Allah ba idan yayi zan zauna da maccin da tafi d'aya banda ja sai dai nai
addu'an kar Allah ya had'ani da wacce zata rabani da farin cikina

Meenat kowa ko ahanya bana fatan had'uwarmu ballatana aure Insha Allahu"

sai da ya tabbatar ta natsu sannan yayi mata sallama zai je ya lek'a kamfaninsu.


ranar litinin suka dira Kaduna agidansu da ke malali suka sauka wanda Dady yasa ank'ara
gyara masu sosai har kayan d'akin an sauya mata

ko hutawa basuyi ba suka fara shirye shiryen biki Yaya Saif da Halima 'yar kauye wacce da
k'yar ya ciyo kanta ta karb'i soyayyarsa

Lawal kuwa 'yar gida za ayi Salma k'anwar Al'amin au na manta Hakeem

duk gidan Dady za ayi komai.

bayan an gama biki ankai amare gida jansu Lawal anan Malali gidan da dai kuka sani sai dai
ank'ara masa girma da gyara kamar na Hakeem wanda Abbu ne ya saye filin da ke kusa dasu
yasa aka k'ara fad'in gidajan aminan da k'ayata shi.

Saif kuwa abuja aka kai amarya Dan acan aka tanbatsa masa gida naji da gani 'yan k'auyen su
Halima sun koma gida da santin gidan Halima.


bayan kwana biyu da gama biki
ta had'a kayanta sai Zariya da abubuwab arzik'in da Dady da Saif da kuma Hakeem suka bayar
akawu mata sosai Aunty tayi murnar ganin 'yartata

Bety kamar ta had'iye d'an Aunty Muhsin d'an watanni.

kwananta biyu ta dawo KD sai shirin kumawa India suke tana kitchen tana aikin abinci tajiyo
sallama

fitowa tayi tana amsa sallama ganin Zee yasa ta buga tsalle suka rungume juna

sai da suka natsu Bety tace "ashe dama zan sake ganinki Zee"?

harararta tayi kafin tace "ban sani ba 'yar rainin wayo wai Bety kin san inda naki amma kikasa
nemana"

langwabar da kai gefe tayi kafin tace "ayya Zee ba haka bane had'uwata da Meenat ne baimun
dad'i ba shiyasa nazata ko ke hakan zata faru wannan yasa ban nemeki ba

amma wallahi kina raina"

"me 'yar iskar ta maki hala"?

nan ta kwashi yanda sukayi har bibiyar Hakeem da ta dingayi ta bata labari

"him Meenat ai bazanyi mamaki ba dan zata iya tunda kwad'ayayya ce nifa tub bayan barinki
makaranta alak'armu tayi nisa dama danki nake tare da ita saboda tafiya kwad'aye da ruk'o kice
baki gani halinta

sai da ta nuna maki amma ai tayi butulci kuma kanta tayiwa

Dan shekaranjiya nakejin labarin tayi aure sai dai ta had'u da wanda ya fita

yazo yana ta mata k'arya motoci da naira duka kwanansu goma da had'uwa akayi auren ba
binciki ba komai iyayan suka biye mata in fad'a maki Ashe wankin mota ne sana'arsa

yanzu satinsu biyu da aure matsaluli sun kunnu kai Fa'iza khamees sabuwar k'awarta ke
fad'amun da muka had'u wajan salon agunta ma nasamu adris d'inki tace kun had'u wajan bikin
su Yaya Saif"

"oh lallai kuwa mun had'u da ita dan tace matar Yaya Saif 'yan uwansu ne na can k'auye

wallahi Meenat taban tausayi Allah ya kawu mata mafita"

"ke mubar zancin kwad'aye da dugon buri ya janyo mata ina 'yata"?

"tana gun Ummy ygd ya bayan rabuwa"

"wallahi sai alkhairi"

"bara na kawu maki ruwa na barki sai zuba muke"

bayan ta kawu mata abunsha da danbun nama tace "bisimillah kafin na k'arasa giriki wai Zee
aure fa"?

"Wata biyar da aure na harda d'an yaron cikina"

"Wow gaskiya na maki murna Allah ya raba lafiya"

"amin"

da yamma *Hakeem* ya dawo yasamu bak'uwarsu sosai suka gaisa da 'yar fira kafin ya shige
d'akinsa.

sai dare Mijinta Alk'asim yazo d'aukarta suka rabu da alk'awarin zasu kawu masu ziyara kafin
su koma India inda mazajan sukayi musayar number.

Bety na hango tana turo ciki tafiya da k'yar *Hakeem* yana zaune kan kujera yana wani binciki
a laptop d'insa zama tayi kusa da shi tare da mik'o masa madarar da ke cikin cop karb'a yayi
yace "nagode maman biyu"

harara ta kaimasa cikin turo baki tace "tab d'ayanma ya akaji da ita bare biyu kama daina mun
fata"

dariya yayi kafin yace "hum haba madam nasan wannan himman da na bayar ya wuci d'aya sai
biyu kima shirya rainun 'yan biyu"

duk ta kaimasa cikin shagwaba kamar zatayi kuka da k'yar ya rik'i hannunta tare da rungometa
ta baya yana dariya yace "yi hak'uri na daina amma kinsan me

bank'i kibani yara ukku ukku ba ina son yara da yawa Aishana"

"nima Habibina Allah ya kawu mana masu Albarka"

"amin Aishana k'anwata matata uwar 'ya'yana farin cikin rayuwata"

"I love you Yaya *HAKEEM* hasken rayuwata"

"I love you too Aishana"


*Alhamdulillah anan na kawu k'arshin littafina mai suna KAR KA GUJE NI kuskuren da nayi ciki
Allah ka yafe mun Masoyana aduk Inda kuke ina alfahari daku ina k'aunarku k'auna irin sosai
d'innan*


*ina alfahari daku 'yan Uwana jinin jikina A Yabo Famili*

*ina alfahari da ku 'yan REAL PML Allah ya k'ara had'a kanmu amin*



daga marubuciyar

*AMAL*
*MUKULA 'YAN MATAN ZAMANI*
*KAR KA GUJENI*

sai kun sake jina awani sabon Littafi na mai Suna
*MA AURATA*


Insha Allah
?

_mai k'aunar Ku har kullum_

� *Aisha A Yabo*�

Fulani _Visitwww. Nafiunafson@mywapblogs.com_

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login