Showing 3001 words to 6000 words out of 41150 words
Chapter 2 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
wucewa yaga abun da ya faru ya sasu motarsa da wusu mutane Ukku
suka nufi kaduna dan kaisu Asibiti.
ko Kaduna basu kaiba Uncle yace ga garinku hankalin mutanin ya matuk'ar tashi Momy cikin
tsananin jin jiki tace dan Allah kukira mun mijina ga numbersa tafad'a masu number cikin jin
azaba anyita kiran wayarsa bai d'auka ba har suka shiga Kaduna wanda zuwa lokacin Momy
tafita hayacinta suna isa asibiti aka wuce imagns da ita.
_mai k'aunarku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJENI*
*Na Aisha A Yabo*
fulani
*Pure moment of life writers*
_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_
#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#http://www.Facebook.com/Pml_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*20 to 25*
Ana shiga da ita ta fara kalmar Shahada tana idarwa numfashinta ya d'auke Doctor ya duba ta
yana gama dubata yaja mayafi ya rufeta kafin ya kalli wa d'an da suka kawota yace "sai dai kuyi
hak'uri Allah ya karb'i Abarsa"
*Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" suke ta furtawa kafin mai motar yace "yanzu ya zamuyi ma
sada mamattan ga iyalansu"?
"ranka ya dad'e me zai hana asake kiran number da baiwar Allah ta bayar" cewar d'aya daga
cikinsu
"hakane bari na sake gwada kira Allah yasa wannan karan ya d'aga" ya fad'a cikin jimami.
Dady fitowarsa kenan daga wurin meeting da wasu turawa akan wani kamfani da yake so ayi
masa gini anan legos harya sayi fili, duk wani iri yake jinsa ga wani irin sanyi da yake ji cikin
wannan yanayin wayarsa ta dinga k'ara alamar neman agaji kasa d'aga kiran yayi sai cewa PA
d'ine da yake tattara faels ya d'aga kiran
sanda PA yaji bayanin da aka masa hankalinsa ya matuk'ar d'agawa cikin sassauta murya
yanda Dady bazaiji shi ba ya kwatanta masu gidan Dady tare da sheda masu basu gari amma
yanzu zasu biyu hanya
bayan ya gama waya ya dawo kusa da Dady yace "yallab'ai dama hajiya ce takira tace suna
asibiti Bety bata da lafiya" aransa yace "gara na fad'a masa haka yafi da dai gundarin zancen"
cikin tashin hankali Dady ya mik'e yana fad'in "me yasa meta me yake damunta!?"
cikin tsananin tausayin uban gidansa yace yallab'ai abun da tafad'a kenan"
"maza ka kira K'asim ya shirya mana tafiya Kaduna yanzunan" cikin ladabi yace "to yallab'ai".
lokacin da sukayi duk abun da ya kamata suyi sannan aka basu gawawakin sukayi gida dasu
uhm fad'an irin tashin hankalin da wannan familin suka shiga alk'alamina ba zai iya ba iyakar
tashin hankali sun shiga
Dady abun kamar hauka ya zame masa Aunty sai da ta kwanta asibiti.
bayan adu'ar sati Umminsu Safna taso ta d'auki Bety da Saif Dady yak'i bazai iya rabuwa da
yaransa ba
Umminsa tace "kai da ba zama kake ba taya za abarma yara dole kayi hak'uri kabarsu
hannunmu ko ka tattara ka koma Sudan"
"Ummi kuyi hak'uri narasa Safna bazan iya juran rashin su Saifullah ba Zainab tana tare damu
nasani zata kula dasu" ya k'arasa maganar cikin zubar hawaye
Baffan Dady yace "in banda abunka Zainab d'in zatai ta zama ne batayi Aure ba ko kuma zata
cigaba da zama gidannan daga kai sai ita"?
cikin sauri Zainab da take gefi tana kuka wacce rashi biyu ya dake ta miji da Uwar d'aki tagari
tace
"Baffa dan Allah karku tafi dasu wallahi zan iya kula dasu har iyakar rayuwata bazan iya jure
rashin su AISHA ba"! ta fad'a cikin kuka kamar numfashin ta zai d'auke
dukansu sukayi shiru kafin daga bisani sukace shikenan suje an sallame su bayan fitar su Dady
iyayan da yayyinsu sukayi wata maganar da duk k'wak'wata nakasa jiyo me suke fad'a daganan
taro ya tashi washe gari 'yan Sudan suka wuce aka bar Ummin Dady tare dasu Aunty.
saif tun yana fitinar akaishi gun Momy ayita lallashi yau da gobe har ya daina Bety kuwa Sam
bata san me ke faruwa ba.
*bayan Wata biyar*
Baffan Dady dana Safna yayyansu sukazo bayan sun huta Baffa yace
"Sufiyan ba komai ne yasa nazo tare da Baffanka da kuma 'yan Uwanka ba sai kan maganar
Yaranka idan har kana Son abarma su to dole zaka amince da zancen mu idan baka amince ba
to lalle zamu d'auke Su Aisha"
ba tare da tunanin komai ba yace "Baffa ko miye ne nayi maku alk'awarin zanyi matuk'ar bai
sab'awa addini ba" ya fad'a cikin ladabi
Murmushi Yaya Sumayya tace "Sufiyan ba komai bane face ka amince da Auren Zainab saboda
zamanku hakan ba zaiyu ba sannan munyi tunanin dukanku ba kwason rabuwa da yaranku
wannan yasa akayi shawarar had'aku aure"
zuciyarsa ce ta dinga bugawa da sauri da sauri nan take yayi sharkaf da gumi ya zaiyi ya riga
ya d'aure kansa wani b'angari kuma yana buk'atar yaransa
ba tare da dogon nazari ba kawai ya amince yana furtawa ya bar falon inda ya barsu suka
cigaba da tattaunawa dan kuwa sun yaba da halin Zainab da yanda take kula da yaran kamar
d'iyan cikinta.
washe gari da Abban Zainab ya zo daga k'auyensu da yake cikin zariya lokacin da Abban
Zainab ya fad'a mata maganar Auren hankalinta ya matuk'ar tashi
kamar ta d'aura hannu aka taita rusa ihu take ji "ya ma za ayi ta aure uban gidanta mijin Momyn
da tamata dukkan halaci gaskiya Abba bazan iya ba"!
"ba komai Zainab bazan maki dole ba amma dai ki sani kakannin yarannan zasu karb'esu zamu
tafi dake gida"
shiru tayi tana kuka "wayyo ni Zainab ya zanyi? bazan iya rayuwa ba kuba banda mafita bayan
na amince Momy kiyi hak'uri ki yafeni dole tasa amincewa"!
ranar Juma'a bayan an sauko sallah Juma'a dubban al'umma suka shidi d'auren Dady da Aunty
sai fatan Allah ya bada zaman lafiyada zuri'a d'ayyaba.
iyaye da 'yan uwa sun masu nasiha sosai kafin suyi masu sallama akabar ango da amarya sai
yaransu.
da dare Dady na hango d'akin amarya wanda tuni ankawota b'angarinsu bayan ancanza komai
na gidan da d'akunan duk cikin umurnin iyayansa
ina ganin ya shiga da guduna nabi bayansa dan kar ayi bani sai dai kash ina zuwa na tarar
harya kullo k'ofa na manna kaina ga k'ofa ko zan jiyo sai dai kash komai banji ba nabar gurin
kamar zanyi kuka☹
tunda Saif yaji Autynsu ta Aure Dady ya tsaneta baya shiga lamarinta sam bata damuwa da
wulak'anci da gorin da yake mata ita dai lallab'ashi take wannan dalilin ne ya kawo rashin jituwa
tsakaninsu Dady yana sane amma bai tab'a damuwa ba yana matuk'ar son yaransa shiyasa
yake lallab'asu yanda suke so.
Saif yana kammala sakandiri Dady ya kaishe INDIA gidan Uncle Muhammad (yayan Momy
Safna acan yake aiki yayi Aure acan yana zaune Mumbai)
acan yayi Digiri har masters d'insa lokaci lokaci yana kawo masu ziyara ko suje masa.
Bety an girma anzama 'yan mata kyakkyawa ce ajin farko tana da diri da gashi dai dai
gwargwadu wankan tarwad'a sak larabawan Sudan tana da kyan hali da Yakana duk da
kasancewarta 'yar gidan masu hali gaba da baya ga gata da ya sata a gaba hakan baisa ta
wulak'anta talakawa ba ko wad'anda suke k'ark'ashinsu
tana da tausayi da taimako ga yawan fara'a duk suffa da halin Momynta ba wanda tabari
shagwab'ab'iya ce tak'ar she zan iya cewa shagwab'a ajininta taki
sab'anin Yaya Saif yana da masifar ji da kai bai d'auki talaka abakin komaiba bayan su nemi
taimako a gunsa ya d'auka ya basu halin Dady sak.
lokace lokace sukan je Sudan har Aunty idan sun kwana2 su dawo Bety bata san ba Aunty ce
ta haifeta ba sai bayan da ta gama sakandiri Saif ya fad'a mata tare da nuna mata hotonan
Momynsu ranar kam tasha kuka da k'yar Aunty ta lallasheta
sai dai wannan baisa ta sauyawa Aunty fuska ba saima k'aunarta da takejin ta fiye da da.
tayi saukar alk'ur'ani mai girma a islamiyarsu da ke unguwar har tafara karatun littafan addini
k'awarta d'aya tun furamari Zainab Alk' asim tana matuk'ar ji da zee saboda sunan Auntyn ta.
tana shekarar farko a A.B.U anan suka had'u da Meenat duk da kasancewarta d'iyar talakawa
basa wulak'anta ta jininsu ya had'u sosai suna taimakunta sosai akan harkar karatun ta.
har zuwa wannan lokacin da Bety take da shekara goma sha takwas Yaya Saif baiyi aure ba
anyi fad'a anyi nasiha har angaji anzuba masa ido dan acewarsa har yanzu baiga matar aure
ba.
daga Dady har Yaya Saif duk basa yawan zama agida yau sune waccan k'asar gobe sune a
wacan k'asar yana da kamfanuni da yawa acikin jahuhin nageria har k'asashin turai yana da
gidajan mai sosai a nageria *WANNAN KENAN*
*CIGABAN LABARI*
_kuyi hak'uri da wannan banda lafiya Insha Allahu idan nasamu sauk'i zanyi maku tpyng anjima
ko gobe ina baran Adu'a_
_mai k'aunar ku_
*KAR KA GUJENI*
*Na Aisha a yabo*
Fulani
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*GAREKI ZHARA MUHAMMAD SURBAJO MAGANAR GASKIYA BANSO NASHIGA CIKIN
MAGANARKI BA DOMIN DUK WANDA YAYI NAGARI KANSA SAI DAI KIN FAD'I WATA
KALMA DA BAZAN IYA SHIRU BA. KINCE YANDA AKE FAD'AN SURBAJO KO ANNABI
S.A.W BA AFAD'A HAKA GASKIYA WANNAN KUSKURE NI KI GYARA FURUCINKI ANNABI
S.A.W YA WUCE KO SANNAN YA WUCE KWATANCIN MAI KWATANCIN SHI SONSA DA
AN BATARSA DUK BUGUN NUMFASHI NE DA GUDANYAR JINE YA WUCI MISALI DAN
HAKA DAINA KWATANTA KANKI DA SHI TSAYA IYA KE DA MASU YI DAKE DA FATAN ZAKI
FAHIMCE NI KI DINGA SANIN INDA FURUCINKI ZAI TSAYA.*
_Wannan shafin na sadaukar da she ga duk maccen da take samun matsala da 'ya'yan mijinta
sunyi aure ma baza su barki ki huta ba sai sun wanko k'afa daga gidan mijinsu sunzo taya
uwarsu kishi Ubangiji Allah ya k'ara maku hak'uri da jureya yayi maku sakayya ta alkhairi_
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_
*25 to 30*
Kwanci taki tana chatin fira take acikin GRP d'in Aisha A Yabo suna calanji da Zainab KT taji
sak'o ya shigo hakan yasa ta fita GRP dan ta d'auka Zee ce ba k'uwar number ta gani tana
shiga ta fara karanta sak'on
" _Aslm barka da dare ma abociya kyau da sanyin hali tun ranar da na fara ganinki Zuciyata
ta abka acikin k'aurki k'auna Marar misiltuwa ga d'an bawan Allah da k'ok'on baransa ki karb'e
ni ba danne ba sai dan Asalin soyayya_ *ANNABI MUHAMMAD S.A.W*
_mijinki Insha Allah mai k'aunar ki A.A_"
ta mai maita sak'on ba adadi ba wai dan ba a saba turo mata sak'wanni irin wad'anan ba Aa
hakanan kawai take jin wannan daban da na kowa ita dariya ma ya bata wai mijinta ba ko dad'in
ji
kashi data tayi tare da ajiye wayar tayi kwanciyarta adu'an kwanciya barcci tayi ba awani jima
ba sarkin b'araye yayi awun gaba da ita.
kusan sati biyu kenan kullum A.A sai ya turo mata sak'wanni na safi daban na rana daban na
dare daban tun bata damuwa har tazo ta fara jin kalamansa na mata tasiri a zuciyarta
sak'wannin sa sun zamo masu d'ebi mata kewa da faranta ranta.
yau kwana ukku kenan bai turo mata sak'o ko d'aya ba ga ba d'aya bata cikin natsuwarta har
Aunty ta ganu damuwarta
suna zauni da yamma Aunty tace "Bety mi ya ke damunki ya nayinki duk ya canza"?
murmushi tayi tare da kwantuwa jikin Aunty kafin tace "lah Aunty ba komai fa kawai karatu ne"
"uhm um Betyna ban yarda ba fad'amun gaskiy"
"da gaski fa nake Aunty ba abun da ke damuna"
tabar maganar ba Dan ta yarda ba dan tasan halin Bety da zurfin ciki idan zasu kwana ba zata
fad'a mata ba zata bita da adu'a Allah ya yaye mata damuwarta.
yau gajiyi ta dawo makaranta wanka kawai tayi tabi lafiyar gadu dama tana hutun sallah
kid'an wayarta ce ya tashe ta barcci sai da tashiga ban d'aki tayi burush sannan tafito ta duba
wayar sak'onni ne har hud'u duk na A.A duk cikin sak'onnin na k'arshin yafi sauran tsaya mata
a zuciya ga abun da ke ciki
_naso najurewa nisanta kaina da k'aunarki saboda sanin nisan tazara da ke tsakanina da
ke sai dai Zuciyata ta kasa juran hurun da nake mata, bazan b'oye maki ba ni d'in talaka ne
marar wadata sai dai Alhamdulillah ni mai wadatar zuci ne, ina maki Soyayyar gaskiya bana
kallon komai naki bayan tsantsar k'auna ki bani dama na gabatar da kaina gareki"._
kwanciya tayi rairan tare da lumshi idanunta "A.A nima zan so na ganka kariga ka saci Zuciyata
da tsadaddin kalamanka sai dai lokacin had'uwarmu baiyi ba"
tajima kwanci tana tunanin A.A kafin ta tashi d'akin Aunty tanufa ta tarar tana karatun k'ur'ani
zama tayi kusa da ita bayan takai aya sukayi adu'a tare
bayan Aunty ta ajiyi k'ur'ani ta dubeta fuskarta d'auki da murmushi tace "Bety na antashi barcin
shigata biyu d'akinki"
"wallahi yau gajiyi nadawo shiyasa Auty yunwa nakeji me aka dafa a gidannan"?
"tuwo mukayi" ta fad'a tana linki hijab d'int b'ata fuska tayi kamar zatayi kuka tace " ni dai Aunty
gaskiya kisan yanda zakiyi dani yunwa nakeji kuma bazan iya cin tuwo ba"
rik'o hannunta Aunty tayi tana dariya tace "da wasa fa nake maki jalof d'in kuskus nayi sai
farfeson ragon ruwa"
ajiyar zuciya tayi kafin tace "yawwa Aunty yanzu naji zance" tabar d'akin da gudunta Aunty ta
nufi kitchen.
tana gama d'ibar abinci a plet tabi Aunty kitchen tana ci suna fira da Aunty da ladidi Aunty tace
"Bety ki daina biyiwa Yayanki ke macci ce Aure zakiyi ba kisan wani irin miji zaki aure ba mai
kud'i ne ko akasin haka shiyasa nake so ki kuyawa kanki cin ko wani irin cima"
"Aunty ya zanyi Allah bazan iya cin tuwo ko wani kala ne ba kuma ko baya da kud'i ai muna da
Dady ga Yayana ga Auntyna ai bamu da matsala"
"uhm Bety yarinta na damunki an fad'a maki namijin kirki zai zauna iyayan matarsa na d'aukar
nauyinsa garama ki sauya tunani run wuri"
ladidi tace "uwar d'akina gaskiya Aunty ke fad'a maki duk namijin da bai da zuciyar nema sai dai
jiran abashi hak'ik'a ba mijin Aure bane"
cikin sanyin jiki tace "to zanyi k'ok'arin koya" daga haka bata saki cewa komaiba tabar kitchen
d'in su Aunty suka cigaba da tattaunawa.
ranar asabar k'arfe ukku na yamma tayiwa Aunty Sallama tanufi Unguwar ma'azu.
bata wani jima gurin Meenat ba tace "kefa zuwa nayi ki kaini gidansu Faruk' "
cikin mamaki tace "wai dama baki manta ba"?
ta hararita cikin wasa kafin tace "ga zahiri nan kin gani ni Dan Allah tashi muje kiraka ni"
ta fad'a tana mik'ewa tsayi tare da gyara mayafinta
Meenat ta d'auko hijab tasa suna fituwa tsakar gida ta kalli Inna da take zaune cikin rumfa tana
sak'ar rigunan sanyi (sana'arta kenan)
tace "Inna zan raka Bety"
"to sai kin dawo Aisha ki gaida iyayan naki"
"zasuji Inna"
suna fituwa k'ofar gida Meenat tace "ina kuka ajiye mota"?
"ni kad'ai nazo mota na ajiyeta farkon layinnan saboda ruwa sun kwanta ahanya"
suna zuwa k'ofar gidan tace "to ga gida nan ni zan koma"
"ban gani zaki koma ba na d'auka tare zamu shiga"
"kiyi hak'uri aiki zanyi kije kawai sai mun had'u makaranta" tabar gurin da sauri
Bety tabita da kallo ciki da mamaki bata wani tsaurarawa kanta tunanin dalilin k'in shigar
Meenat ba ta fad'a gidan bakinta d'auki da sallama
Lawal ne zaune akan tabarma yana cin kwad'un k'anzo da zogala Al'amin na gefe yana koyawa
Faruk' karatunsa na islamiya
Inna ta amsa mata sallamar cikin fara'a tace "maraba shigo Lawal da yakai loma bakinsa dai
dai nan idonsa ya fad'a kanta ai kuwa ya k'ware sai tare idanunsa sun firfito sunyi jajir sabo da
wahala da tsoro.
_na gode sosai da adu'anku gare ni_
_mai k'aunar ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJENI*
*Aisha a yabo*
Fulani
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_
*30 to 35*