Showing 24001 words to 27000 words out of 41150 words

Chapter 9 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2882



bayan ta ajiye kayan ta d'auko ta barma ta shimfid'a masu sannan ta d'ebu ruwan randar Inna ta
kawo masu

"sannu Aishana yayi magana ahankali yanda ita kad'ai za taji
murmushi tamasa tare da komawa gurin Inna ta zauna

bayan sun gaisa da Inna yake nuna mata sayayyar da yayu kayan abinci ne da kayan kitchen
da risho

sai akwati d'aya da take mak'il da sutara da kayan kwalliya dai dai k'arfin talaka yaba Inna wata
leda atamfa da les ne aciki ya saya mata

Inna sosai ta yaba tana ta samasu albarka.

Lawal bai jima ba yayi masu sallama bayan sunsa kayan d'aki

Al'amin ma d'aki ya shiga Inna ta kalli Bety da take wasa da zoben hannunta tace "Humaira
tashi kibi mijinki"

"to" tace cikin jin kunya ta wuce d'aki tana zuwa ta tarar dashi kwanci ya rufe fuskarsa da
tafukan hannunsa

tana zuwa ta kwanta ak'irjinshi rungumeta yayi cikin shauk'i yace"ai na d'auka bazaki zo ba"

hannuta takai fuskarsa tana wasa da sajan fuskarsa da ya kwanta tace "ai ban isa ba sannu da
k'ok'ari nagode sosai Ubangiji Allah ya saka da Alkhairi Allah ya k'ara bud'i"

"amin Aishana nagode da kika yaba"

tashi zatayi yasaki rungumeta yana fad'in "ina zaki"?

"zan kawuma abinci ne"?
"Inna tayi girki ne"?

"Aa Faruk ne ya kawu daga gidansu Yaya Lawal"

"Allah sarki angode kinga ina can inata tunanin na barki da yunwa Allah Allah nake mu dawo
gida na dafa maki ko Indome Allah ya saka masu da Alkhairi"

"Amin".


da daddare ma sai da Inna ta kurata da k'yar ta tafi dan harga Allah tana jin kunyar Inna

tun adaren take ta yimasa kukan Dady da Aunty da k'yar ya lallasheta da Alk'awarin gobe za
suje.


washe gari bayan sunyi sallah ta fito ta gaida Inna sannan ta taya Inna suka gyara gidan duk da
Inna ta hanata amma tak'i

ita ta had'a masu abun kari wainar k'wai ta masu sannan ta dafa masu ruwan te sai da ta
kaiwa Inna da Faruk nasu sannan ta kai nasu d'aki

tana ajiyewa ya janyota jikinsa yana mammatsa mata jikinta sai sannu yake mata cikin tausayi
ganin tayi aikin da bata Saba ba.

ba halin ya taimaka mata tunda Inna na nan ko afuska bata nuna masa tagaji ba haka sukayi
karin kumallo cikin tattalin juna

banyan sunyi wanna sun shirya ya fita ita ta zauna gurin Inna.



bayan sallah isha ya aro mashin d'in Lawal ya d'auketa suka nufi gidansu Bety koda ya fad'awa
Inna inda zasu bata hana ba sai adu'an da taraka su da ita.

abunda suka tarar ya matuk'ar d'aga masu hankali.


_mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

�fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*


_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_



#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS

#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com

*LALE MARHABABIKI YA IBNATEE Ubangij Allah ya raya mana ke bisa sunna*


*FNS ina mai baku hak'uri na jina shiru da kukayi sabgogeni suka mun yawa amun afuwa*



*1020 to 1030*


Jikinta ya fara rawa tana so ta k'waci kanta sai dai gangan jikinta sunk'i su bata had'in kai
sak'onni ya shiga aika mata


Al'amin jikinsa ne ya fara shock d'aurata yayi kan katefa ya mirgina kanta inda yayi mata rumfa
da faffad'an k'irjinsa

nan ya shiga aika mata sak'onnin soyayya ga baki d'aya sun fita hayyacinsu sun jima a cikin
yanayi na shauk'i

kafin daga bisani ya mirgina gefe yana maida numfashi idanunsa a lumshe

Bety ta runtsi idanunta tana jinta wani iri d'aya gefen wata irin kunyar Al'amin takeji

hannunsa ya kai ahankali ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sauki ajiyar zuciya

d'ago fuskarta yayi yana so su had'a ido tak'i yarda sai b'oye fuskarta take ak'irjinsa dariya yayi
marar sauti kafin yace


"Aishana ba dai kunyata kikeji ba amma ba laifinki bane laifina ne da nabarki da ita zanyi k'ok'ari
nacire maki ita"

komai takasa iya cewa da shi sai murmushin da takeyi.


da dare bayan sun shige barcci ya umurceta da ta yo alwala cikin sanyin jiki tace "ina da Alwala
kumafa nayi sallah"

murmushi yayi kafin yace "eh nasani"

bata sake cewa dashi komai ba nan ya jasu jam'i sukayi nafila cikin kuyarwar Ma'aiki S.A.W ga
dukan sababbin ma'aurta ya jima sosai yana masu adu'a bayan sun shafa yayi mata tambayoyi
gami da addini Alhamdulillah tabashi amsa dai dai baiyi wani mamaki ba sanin yanda take da
sun ibada kuma tana koyawa Faruk karatunsa,

bayan sun gama cin gasasshiyar kaza da madara mai sanyi sunkayo burush Al'amin ya shiga
wanka

Bety da dama tun bayan magrib tayi wanka k'ara shafi jikinta da turaruka tayi sannan ta d'auko
rigar barcci marar nauyi tasaka ta d'auko zumbulilin hijab tasaka
kwanciya tayi rub da ciki tare da lumshe idanu zuciyarta

sai lugude take yau kam wannan rawar jikin da Habibi keyi tasan yau sai yanda Allah yayi da ita

yana fitowa ban d'aki idanunsa suka sauka kanta ganin hijab d'in da tasaka sai ta bashi dariya
murmushi kawai yayi ya cigaba da shirinsa,

hawowa yayi kan katefa ya d'ura rabin jikinsa abayanta yana lek'in fuskarta cikin muryarsa mai
dad'i yace

"Aishana wannan hijab d'infa bakya jin zafi?"

cikin shagwab'a tace "eh ni zafi nake j... au sanyi zance"

ta k'arasa maganar tana rufe baki da hannunta

dariya yayi yaja hancinta kafin yace "shikenan ai kin riga kin fad'i gaskiya"

cikin dabara yaciri hijab d'in yana tsokanarta da wasanni su Bety fa ido ya fara raina fata lo😜

ni dai daganan na rufu masu k'ofa dan kar idona ya ganemun abunda yafi k'arfin ganinsu.


tun adaren ya taimaka mata ta zauna cikin ruwan zafe sai kuka da shagwab'a take masa
shikuwa ya biye mata sai lallab'ata yake da samata albarka

bayan sunyi wanka ya sauya masu zanin gado sannan suka kwanta rungume take ak'irjinsa
tamkar zai maidata ciki wani irin sonta yake k'ara huda zuciyarsa da jinin jikinsa sai k'ara
godewa Allah yake da ya mallaka masa Bety amatsayin matarsa

duk da azabar da tasha hakan baisa ta tsani Habibinta ba saima soyayyarsa da take k'araji da

farin ciki yanda take ta samun Albarka da kalaman soyayya masu tsada daga gun Habibi.

tun k'arfe hud'u ya tashi ahankali ya zame jikinsa dan karya tasheta zanin gado ya wanki ya
shanya a k'ofar toilet sannan yayo wanka tare da d'auro alwala

bayan yayi nafila ya zauna yana karatun k'ur'ani sai da akayi kiran farko sannan ya tasheta.


bayan sunyi sallah asuba ta kwanta akan darduma tayi filo da cinyoyinsa cikin kulawa da k'auna
yace "sannu Aishana barccini" idanunta alumshi ta girgiza masa kai

gyara mata kwanciya yayi ajikinsa yana lallab'ata har tayi barcci.

bayan ya gama lazaminsa ya kwantar da ita kan katefa sannan yafita

d'aki ya tarar da Inna bayan sun gaisa take tambayarsa Bety cikin jin kunya yace "ai bata da
lafiya ne shiyasa bata fito ba"

"ayya Allah ya bata lafiya"

"amin Inna bara naje nai mana abun karin kumallu"

"haba Al'amim barshi kawai nayi ji ka kula da matar ka"

zaiyi magana tace "bana son musu" tashi yayi yabar d'akin cikin jin kunya yana susa kansa ko
bata fad'a ba yasan Inna taganu abunda yafar.


yana zuwa ya kwanta tare da janyota jikinsa ba ajima ba barcci yayi awun gaba dashi.


zaman nasu gwanin sha'awa soyayya aminci da girmamawa ne atsakaninsu rashin aikinsa bai
hana suka rasa cima mai kyau ba cikin taimakon Inna da Aboki nagari Lawal

bayan wata d'aya yasamu aikin gini ta hanyar wani mak'wacinsa duk da aikin mai wahalane
haka ya jure saboda Inna da Bety

ko sati biyu da fara aikin baiyi ba aka koreshi duk akan maganar farko hankalinsa ya matuk'ar
tashi shikam waye wannan me yamasa yake masa bita da k'ulli?

tambayar da yayi ta yiwa kansa kenan yarasa mai bashi amsa.

sau biyar yana neman aikin hannu sai yasamu har yafara mura sai akure shi

haka yau ya dawo gida ransa ajaguli sanadin kurarsa da akayi wajan 'yan walda da duka baifi
sati d'aya da samun aikin ba

yau ya fita da zummar yasamu 'yan canjin ya kai Inna asibiti da jiya ta wuni da zazzab'i mai zafi
yau dai ko da ya barta da sauk'i

sai dai ya fita da k'udirin idan ya dawo ya kaita asibiti sai ga wannan bak'in cikin ya sameshi duk
da nisan da suke dashi daga gurin 'yan walda zuwa Unguwarsu haka ya taku sayyada zuwa
gida

dan dama d'are ya tashi dasu canjin cefanin da yayo masu da zai tafi ya hau acab'a.


haka ya k'arasu gida agajiyi gashi ya kwasu k'ishin ruwa dan yau ana tsuga rana agarin Kaduna

abun da ya gani k'ofar gidan ya matuk'ar d'aga masa hankali jikinsa yayi sanyi har ya kasa
d'aga k'afansa daga gurin da yake tsayi.


*FNS kuyi hak'uri da wannan nayi bak'i shiyasa ban samu nayi maku da yawa ba*


_mai k'aunar ku_

� *Aisha A Yabo*�

fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_



#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*1030 to 1040*

Tun bayan fitarsa jikin Inna ya tashi Bety tana gefenta cikin damuwa sai sannu take mata

cikin jin jiki Inna ta rik'e hannun Bety tace "Aisha kiyi hak'uri da sauyin rayuwar da kika sami
kanki ki rik'i mijinki karki barshi duk runtsi Aminullah maraya ne baida Uwa bai da Uba"


cikin firgici Bety tace "Inna kefa wacece agareshi"!?


Murmushin k'arfin hali tayi kafin tace "Karki tashi hankalinki Aisha nima mahaifiyarsa ce amm...

tarin da ya tarnik'ita ne ya hanata k'arasa maganar ta sai sannu take mata cikin sark'ewar
murya tace "Allah yayi maku albarka ya albakaci aurenku da zuri'a mai albarka"

daganan ta fara Kalmar shahada Bety da take tallabi da ita taji Inna duk ta saki ga wani irin
nauyi da taji ta mata

kuka tafashi dashi itakam duk a tunaninta zafin ciwo ne yasa Inna bata ko iya motsa jikinta

ahankali ta zame jikinta ta kwantar da Inna akan shimfid'a tana tunanin yanda zatayi wa zata
kira?

tana haka sai ga matar Baffa Baba Furaira tazo cikin mamaki Baba Furaira tace "Aisha lafiya
kike kuka ina Innar Al'amin"?

cikin Kuka Bety tace "tana d'aki kwanci bata da lafiya sosai kuma gashi Yaya bayanan"

"Subahanalillah muje d'akin tun yaushe ne bata da lafi... kasa k'arasawa maganar tayi lokacin
da idanunta ya kai inda Inna take kwanci

cikin sauri ta k'arasa bakinta d'auki da salati bayan ta duba Inna da kyau sai ta hau " *Innalillahi
wa Inna ilaihi raji'un* shikenan Inna antafi gidan gaskiya"

"iye Baba mutuwa fa kike nufi"!!

Bety tayi maganar da k'arfi

jin Baba na kuka ta kasa bata amsa yasa ta sulali k'asa tana wani irin kuka gwanin tausayi.


Baba takira Baffa ta waya ba ajima ba sai gashi yazo cikin tashin hankali anta kiran wayar
Al'amin bai d'aga ba abun da basu sani ba ya manta wayar gida shima kawu ba ajima ba yazo

cikin d'an k'ank'anin lokaci aka shiryata da taimakun mak'wabta.

sanda Al'amin ya k'arasu k'ofar gida yaga jama'a wasu suna tsaitsaye wasu na alwala


wannan yasa yaji ya kasa d'aga k'afansa zuciyarsa ta tsinki Kawu ne ya hangoshi ya tahu
gurinsa "sannu Al'amin ka dawu"?

cikin rawar murya yace "Kawu me ke faruwa"?

rik'o hannunsa Baffa da ya k'arasu yayi yana fad'in "mushiga ciki Al'amin"

haka ya dinga bin Kawu har cikin gidan inda yaga mata zazzauni masu kuka nayi masu tagumi
nayi

har d'akin Inna cikin tausayawa Kawu yace "Al'amin sai dai mu d'au hak'uri da dangana
mukumayi imani da duk abun da Allah yayi shine dai dai

*KULLI NAFSIN ZA IKATUL MAUT* dukan mai rai zai d'and'ani zafin mutuwa"

sai da yayi masa nasiha sosai kafin ya sanar da shi Rasuwar Inna

fad'ar irin tashin hankalin da Al'amin ya shiga bakina ko alk'alamina ba zasu iya ba.


wunin ranar zukata ba dad'i Bety ranar sam batasa Al'amin a idonta ba sai dare

tana kwance d'akinsu haryanzu kuka take idanunta duk sunyi hushi kanta na mata ciyo yau
komai ta kasa sawa cikinta dukuwa da lallashi da banbaki da su Baba sukai mata

bak'aramin jin mutuwar Inna tayi ba tana jinta tamkar mahaifiyarta

sam bataji shigowarsa ba sai jin hannunsa tayi abayanta cikin sauri ta tashi fad'awa tayi jikinsa
tana k'ara fashewa da kuka

rungomota yayi shima yana zubar hawaye da k'yar ya iya had'iye kukansa ya fara magana
ahankali cikin lallashi yace "yi hak'uri Aishana kukan ya isa haka adu'a Inna take buk'ata
agurinmu kukan bashi da amfani"

da kyar ya samu ya lallasheta ta daina kukan tashi tayi ta d'auko filaks d'in ruwan zafe da kayan
tea wanda duk suna cikin sayayyar da yayo masu jiya

tea ta had'a masa mai kauri ta matsa kusa da shi ta nufi bakinsa da Cop d'in "Habibi nasan
bakaci komai ba kasha tean sai na kawuma abinci"

rik'i hannunta da take rik'i da tean yayi ya kai bakinta yana fad'in "nasani kema ba komai kika
ci ba"

haka suka ciyar da Kansu sai da suka k'oshi sannan suka kwanta barcci yak'i d'aukar su sai
tunani da kowaninsu keyi alwala suka je suka yi suka fuskanci Ubangiji dan nemawa Inna da
dukan musulmi rahama agun Mahaliccinmu.



*BAYAN WATA D'AYA*

ahankali suka fara sabawa da rashin Inna Faruk ya koma gun Mahaifinsa duk da Al'amin yaso
abarmasu shi uban yak'i

sosai yanayin rayuwar ya sauya masu abincin da zasu ci yana neman gagararsu ya rasa
aikinyi wannan na matuk'ar d'aga masa hankali ba kansa yakeji ba Bety

yana matuk'ar tausaya mata yanda tasaba rayuwar jin dad'i da hutu bata san babu ba abunda
da tafi k'arfinsa
yau shine yafi k'arfinta.


Bety tun tana wahala na rashin irin cimar da tasaba har yazame mata jiki dai dai da rana d'aya
bata tab'a nuna masa gazawarta ba sai zallar k'auna da tausayi da take nuna masa hakan ya
k'ara k'aunarta da k'ima azuciyar Al'amin.


kwanci yaki daga shi sai vets da wando 3kwata ya rufe idanunsa tunani yake ina zai samu wa

Bety abunda zatayi kari yau ko kwabo bai tashi dashi ba

har ta zauna dab dashi bai sani ba hannunta takai fuskarsa tana shafa sajen da yake kwanci
afuskarsa gwanin sha'awa cikin damuwa tace

"Habibi nasani ba barcci kake ba bana son ina ganinka cikin damuwa da tunani Allah baya
d'aurawa bawansa abunda yafi k'arfinsa

dukkan d'an adam da kalar jarabawarsa mu tamu jarabawar kenan muyi fatan mu cinyeta
muyita rok'on Ubangiji da kaimasa kukanmu,

nasan damuwarka bazai wucini ba har kullum ina fad'ama ina tare da kai da dad'i da babu
banda damuwa idan har ina da ita to naganka cikin damuwa"

janyota jikinsa yayi ya rungometa yana jin wutar k'aunarta na k'ara ruruwa azuciyarsa cikin
tsantsar k'aunarta yace "Aishana har kullum ina godewa Ubangiji da ya mallaka mun ke a
matsayin matata hak'ik'a kin kasance macce tagari irin wacce Annabi S.A.W ya kwad'aitar damu
da mu aura,
kinzamu mun macce tagari idan ina cikin damuwa kallonki kad'ai ya kan gusarmun da
damuwata kikan sakani farin ciki da murmushinki kin bani dukan soyayyarki cikin gaskiya da
amana,

Aishana banda bakin yi maki godeya Ubangiji Allah yayi maki Albarka Allah yasa ki zamu Uwar
'ya'yana kikasan ce matata har a Aljanna Fiddausi ki kasance shugabar matana na Aljanna"

cikin tsantsar farin ciki ta amsa da "amin mijina farin cikina abun alfaharina"

sallama sukaji anayi k'ofar gidan Bety tace "Habibina kamar muryar su Baffa"

"eh nima kamar shi naji d'auko mun rigana"

"to" ta fad'a tare da tashi tsayi bayan ta d'auko tasa masa yayi mata kiss a goshi sannan ya fita.


"ah Baffa kawu sannunku da zuwa ku shigo daga ciki kun tsaya awaje"

"haba bakomai nan d'inma yayi ya iyalin naka"?

"lafiya k'alau bari na d'au ko maku shimfid'a" komawa yayi cikin gida ya d'auko masu tabarma
bayan sun zauna suka saki gaisawa Kawu yace

"to Aminullah bakomai ne ya kawumu gurinka ba sai maganar gidannan da kake ciki sanin

kanka ne gida ya zama na magada kuma Inna bata da magadan da suka wuce ni da kuma
Baffa gashinan zauni

saboda bata bar d'a ko d'aya ba, mune 'yan Uwanta kuma shak'ik'anta ko ba haka ba Baffa"?

Baffa ya gyara zamansa kafin yace "sosai kuwa sanin kanka ne bayan alak'a ta musulunci da
rainunka da tayi tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login