Showing 6001 words to 9000 words out of 41150 words
Chapter 3 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
Inna tayi saurin mik'ewa ta d'ebu ruwa a randa ta kawu masa "sannu ga ruwa kasha ko zai
lafama"
hannunsa na rawa ya karb'i ruwan yana sha cikin ikon Allah taren ya lafa masa Al'amin ya dube
shi cikin tausayi yace "sannu Kaine baka cin abu a hankali cin abincin ma sai kasa garaji aciki"
shi dai Lawal komai baice ba sai kallon Bety dan iyakar gaskiyarsa tsoraci yaki
Al'amin ya kai dubansa inda Lawal ke kallo sai da Zuciyarsa ta bada dum! "me ya kawota
gidansu? kenan ganinta yasa Lawal kwarewa mts Lawal akwai kayan tak'aice shegin tsoro
wallahi ko wata macci albarka"
mts tsaki ya sakiyi fuskarsa tamau sam ba annuri ya cigaba da yiwa faruk' karatu
Inna tace "oh 'yar albarka yi hak'uri na barki tsayi ina zuwa bari na d'auko tabarma"
Bety da ga bad'aya jikinta yayi sanyi ganin marar tausayinan a inda bata tsammani ba duk sai
taji dama bata shigo ba
Murmushin da bai kai ciki ba tayi kafin tace "lah Inna ba komai wallahi nanma yayi" ta fad'a tare
da janyo kujerar tsugguni da ke ajiye gefin Inna ta zauna
cikin ladabi ta gaishe da Inna, Inna ta amsa cikin fara'a kafin tace "sai dai ban sheda fuskar ba"
"hakane gaskiya dama ranar ne nashigo unguwar nan na yarda wayana a kantin wannan ta
nuna Lawal kafin tacigaba da fad'in
shine Faruk' ya kawoman gaskiya naji dad'in haka wannan yasa nayi alk'awarin idan nasaki
dawowa zanzo mu gaisa"
cikin jin dad'i Inna tace "Allah sarki sannu da k'ok'ari mun gode sosai"
ta kallo Faruk' tace "Faruk' baza ka gaida Aunty ba"?
tasowa yayi cikin fara'a da ladabi yace "ina wuni Aunty"
"lafiya k'alau Faruk' ya karatu"
"Alhamdulillah" yana fad'a ya koma gurin Al'amin tashi yayi ya shige d'akinsa yana fad'in Faruk'
bari sai da dare sai mucigaba"
"to Yaya"
itama mik'ewa tayi tana fad'in "Inna na tafi sai na saki shiguwa"
to "har kin tashi gashi ko sunanki baki fad'an ba"
murmushi tayi kafin tace "sunana Aisha Humaira amma amfi kirana da Bety"
"to Humaira mun gode ki gaida gida"
"zasuji" tafad' tana rik'o hannun Faruk' suna zuwa mota tabashi kayan k'walama da tasayo
masa yak'i karb'a
sai da tab'ata rai kafin tace "idan nabaka abu ka daina cewa bazaka karb'a ba kaji"?
"to amma Inna za tayi fad'a"
"Aa baza tayi ba ungu maza kaje"
karb'a yayi yana godeya sai da yaga tafiyanta sannan ya shiga gida.
Bety na fita Inna ta harare Lawal cikin fad'a tace "kaima kazama irinsa ko? ina laifin wanda ya
so naka sabi da Allah uhm
kai kazuba mata k'walak'walan idanunka kamar zasu zazzago k'asa amma ko uhm bakace da
ita ba
shikuma ya wani d'aure fuska ya tashi ya shige d'aki yana ya tsinar fuska kamar yaga kashi"
Lawal da ya kasa natsuwa da maganar Bety gani yake kamar da wata manufa a alak'arta da
Faruk'
ganin fad'an Inna bazai k'are ba cikin kwantar da kai yaci
"Inna kiyi hak'uri ni wallahi duk a tsoraci naki itace fa yarinyar da nake fad'a maki Al'amin ya
mara ranar da zamuje gidan kawu salmanu daganinta 'yar masu kud'i ce ina tsoron karta ce
d'aukar fansa za tayi ta hanyar Faruk' "
Al'amin da fitowarsa kenan yace "waye ya fad'ama kawai tunaninka ne haka amma ba wani
d'aukan fansa"
cikin harara Lawal yace "itace ta fad'ama hakan"?
"bata fad'an ba amma kasan abun da na karanta ko"?
Inna za tayi magana yayi saurin zaunawa kusa da ita ya rik'o hannunta cikin lallashi yace "Dan
Allah Inna kiyi hak'uri Allah tun ranar da abun ya faru nayi nadama yanzun ma kunyar abun da
na mata ne yasa na shige d'aki batare da na mata magana na"
cikin fushi tace "ba zan yarda kayi nadama ba har sai ka bata hak'uri"
"Inna idan dai hak'uri ne na maki alk'awarin duk inda na ganta zan bata hak'uri ni dai karkiyi
fushi dani"
"shikenan Allah yayi maku Albarka"
"amin Inna nagode" Faruk' na shiguwa da Maya Inna ta hau fad'an me ya karb'a shi dai hak'uri
ya shiga bata shima Yaya Al'amin yayi masa fad'an kar ya koma karb'an duk abun da ta bashi
ko wani ya bashi".
tun bata tura masa amsa har tazo ta fara tura masa sak'o sukanyi waya lokaci lokaci cikin
k'ank'nin lokaci sukayi shak'uwa ta ban mamaki sai dai har zuwa wannan lokacin basu tab'a
had'uwa ba.
yau ma kwanci taki kan kujera suna waya "Aishana me yasa duk lokacin da zan maki maganar
ga batar da kaina gidanku kike k'i?"
cikin shagwab'ab'iyar muryarta tace "nifa bak'i nayi ba"
"to naji ko baza su bawa talaka aurenki ba"?
"haba sam ba haka bane"
ajiyar Zuciya yayi kafin yace "Aishana ina so ki bani dama na gabatar da kaina gidanku amma
kafinnan ya kamata kisanni kisan waye ni"
shiru tayi tana nazari kafin tace "shikenan ba damuwa duk sanda ka tashi zuwa ina maraba"
cikin farin ciki yace "yawwa Aishana gobe da yamma zan zo sai dai ina tsoron kiganni
mummuna ki *GUJE NI*"
"kenan baka yarda da son da nakema aganina soyayyar gaskiya ba ta duban komai kyau kud'i
ko wani muk'ami,
soyayyar da nakema ta wuci na *GUJE KA*aduk yanda kaki ina Sonka *KARKA GUJE NI* Duk
rintsi"
"Aishana na yarda da k'aunarki gareni ina Sonki burina ki kasance matata uwar 'ya'yana ke d'in
rayuwata ce bazan iya guje maki ba duk rintsi"
sun jima suna waya cikin nuna tsantsar k'auna wa junansu suna gama waya taji an fara kiran
sallah azahar alwala taje tayi bayan ta idar da sallah ta saki shiryawa ta nufi gidansu Faruk'
bayan ta fad'awa Aunty.
zuwa yanzu sunyi sabo sosai da Inna tana jinta har cikin ranta jinta take tamkar Momynta.
haka Inna tana Son Bety tun zuwanta na biyu ta bata hak'uri kan abun da Al'amin ya mata ta
nunawa Inna ba komai ya riga ya wuce.
sai dai duk zuwan da take basa had'uwa da Al'amin sai dai wani lokacin ta kanga Lawal a cikin
kantinsa ko gidan Inna su gaisa.
tana zuwa ta tarar Inna nawa wata kitso zama tayi kusa da Inna tana fad'in
"lah Inna Ashe kin iya kitso"?
murmushi Inna tayi kafin tace "na iya Humaira yanzu like tafe"?
"eh wallahi Inna nayi kewarki kwana2 makaranta ta hanani zuwa na ganki ina Faruk' d'ina"?
cikin kulawa tace "nima kullum sai nata jajin rashin ganinki Faruk' yaje gidan Abbansa sai jibi zai
dawo"
duk sai taji ba dad'i matar da akewa kitso tace "Inna ina kika samu 'ya kyakyawa haka"?
dariya Inna tayi kafin tace 'yata ce"
"gaskiya inawa k'anena kaminta"
"babbar magana to gaki gata idan zata so shi"
Inna ta fad'a tana dariya "diyar Inna ki so shi ai ko shima kyakyawa ne kamarki"
"Uhm" kawai tace tabar gurin d'akin tai shigewarta ta kwanta kan gadon Inna mai rumfa da ke
matuk'ar burgeta ga d'akin a tsabtaci.
_mai k'aunar ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJENI*
*Aisha a yabo*
Fulani
® *REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_
*INA MATUK'AR GODEYA DA JIN DAD'IN ADU'AN KU GARENI FNS ALHMDLH NA SAMU
SAUKI NAGODE ALLAH YA BAR K'AUNA*
*35 to 40*
Sun jima suna fira bayan tafiyar wacce akaiwa kitso sai k'arfe biyar na yamma tayiwa Inna
sallama.
daga gidan Inna Supermarket ta wuce dalema ake malali dan canne gurin sayayyarta
bayan ta fito an samata kayanta a bayan mota har zata shiga mota wata mata tana bara
matar ba zata haura shekar 30 ba tazo da yara d'ayan a goye d'aya a hannunta
Bety ta kalleta cikin tausiyi tace "ke kuwa baiwar Allah me yasa da sauran k'arfin ki da
k'urciyarki zaki na yawon bara ga yara k'anana"?
cikin karyar da kai ta fara magana kamar za tayi kuka tace "hajiya nima ba a son raina nake
baran nan ba
ni d'in na tasu marainiya ba uwa ba uba ina gun k'anin babana na tashi cikin wahala da k'unci
ga talauce ga tsangwama matar kawuna da yaranta
a haka dai Allah ya kawo man mijin aure bayan aurenmu muna son junanmu matsalar talauce a
haka dai muke rayuwa cikin rashi da rashin taimakon dangi
kwatsam k'addara tasame mu Allah yayiwa mijina rasuwa sanadin ciwon ciki na dare d'aya ya
barni da yara goma wad'annan 'yan biyun tun suna wata takwas Babansu ya rasu rashin
mataimaki ya sani shiga sana'ar bara"
ta k'arasa maganar cikin kuka Bety ma hawaye ne suke zarya a fuskarta
shiga motar tayi cikin tsananin tausayi baiwar Allah tace "shiga mota na kaiki gida"
cikin d'an firgi ce matar tace "anya hjy ayi haka"?
"karki damu ki shigo ba zan cuta maki ba Allah yaga zuciyata taimakonki nake so nayi"
haka matar ta kwatanta mata gidanta da yake ba wani nisa da gurin,
ganin yanayin gidan kad'ai zai tabbatar ma da masu gidan suna cikin k'agin talauci,
kud'i masu yawa ta d'auko cikin jakka "ga wannan ki rik'i kafin gobe Insha Allahu zan dawo"
matar ta karb'a cikin rawar jiki sai godiya taketa zubawa kamar harda 'yar kwalla,
ita dai Bety bata tsaya jin godiyar ba tai shigewarta mota tare da yiwa motar key tabar unguwar
ciki da tausayin matar.
sanda ta shiga ta nunawa yaranta Alkhairin da suka samu sunata murna da shewa Bety Albarka
ko da babbar 'yarta Nafisa 'yar shekara 13 ta k'irga kud'in dubu hamsin ne nan fa murna ta karu
kowa sai fad'an abun da za asaya mai yake.
sai da tayi wanka sannan ta shiga d'akin Aunty itama fituwarta kenan daga gurin wanka
zama tayi kan gado tana fad'in "wash Aunty na gaji wallahi"
"da ki kayi me"? tayi mata tambayar tana saka rigar barci
"Uhm Aunty ko driving ai aiki ne"
ta harareta cikin wasa tace "gun raggaye ba kuma ai ke kika sa kanki tunda da drvnki kikace ke
zakiyi"
cikin turo baki irin na shagwaba tace "nifa Aunty ba komai kesa nace ni zanyi drvn ba zugar isct
d'innan ke ban haushi wallahi"
Auty ta zauna kusa da ita tana fad'in to Bety ya zakiyi kin dai San halin yayanki duk randa ya
ganu bayan makaranta kina zuwa wani gun ban san yanda zamu kwashe ba musamman ne
tawa sai tafi zafi kin sani"
cikin sanyi tace "ayya Aunty kiyi hak'uri ba fa wani gurin nake zuwa ba"
"to naji ina kike zuwa kwana biyun nan? gashi yau kinyi dare abun da baki sabayi ba
ina tsoron idan Betyna ba wasu k'awayen kika samu ba suke son sauya halinki ba"
d'ura kanta tayi akan kafad'ar Aunty cikin murmushi tace
"wayyo Auntyna Betynki nan yanda kika santa tarbiyar da kika d'aurani akai ba abun da ya
sauya
dama shigowar nan da nayi na fad'amaki sai gashi kin mun magana"
anan tabata labarin had'uwarsu da su Inna har abun da ya faru yau ta k'ara da cewa
"Aunty ina son na taimaki su Inna Amma komai na basu basa karb'a sai dai tace dani k'aunar
da nake masu ta wadatar dasu
ina so nasa Faruk makaranta saboda zuwan da nake na fahimci baya zuwa boko ina so
*Salfanamoh college* dake Unguwarnan
Amma ban san ta yanda zan tunkari Inna ba ina tsoron karta ce Aa"
ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka
Aunty ta rungume ta cikin farin ciki tace "Betyna 'yar Albarka ba inda kika bar Momy gurin kyan
hali wannan yasa nake alfahari dake"
nan take ta bata shawarar yanda za ta taimake su Inna ba tare da samun wata matsala ba
tabar d'akin cike da jin dad'in shawarar Aunty.
washe gari da yamma Babbar mota ce cike da kayan masurufi tayi parking daidai kantin Lawal
driver ne tare da macci d'aya suka fito motar kai tsayi kantin suka nufa kamar yanda Bety ta
umurce su
Lawal kad'ai suka tarar Sallama sukai masa bayan sun gaisa drvn yace
"sunana Muhusin wannan da muke tare sunanta hajara mun zo k'ark'ashin gwamnati ne muna
bin unguwanni muna raba kayan abinci da abun da ya sawwak'a
har dai yau Allah ya kawomu wannan Unguwar ko zaka taimaka kayi mana jagora gurin rarraba
kayan"?
cikin fara'a yace haba me kuwa zai hana sannunku da zuwa"
cikin taimakon Lawal suka dinga rarraba buhun shinkafa da carton d'in taliya da man gyad'a da
manja da dubu goma wajan gida goma sha biyar suka samu har gidansu Meenat
duk gidan da aka sallama idan mai gidan bayanan sai hajara ta shiga tabawa matar gida
Muhusin yace "Abokina baka nunan gidan naku ba"
ya fad'a yana murmushi shima Lawal murmushi yayi kafin yace Ayya gidan namu yana da d'an
nisa da nan amma ga gidansu
Aminina nan kusa da dama yanzu nake shirin magana"
"OK ba damuwa suka ciri buhun shinkafa biyu taliya carton biyu mai ma biyu biyu da ✉ dubu
hamsin ne aciki
yace "ga naka" ya karb'a yanata godiya gidansu Al'amin komai hud'u hud'u tare da dubu d'ari
hud'u wai zo kuga murna Addu'a kam da albarka sun shata agun Inna da mutan Unguwa.
Bety da kanta taje gidansu baiwar Allah ta kaimata kayan abinci da kud'i masu yawa har kuka
sai da tayi tana shimata albarka da kyawawan addu'oi.
haka ta koma gida cike da farin cikin sauke nauyin da take ganin ya hau kanta.
cikin mayar da zancen kiran Dady ya shigo wayarta cikin murna ta d'aga kiran
"DADY I MISS YOU yaushe zaka dawo Yaya ma ya tafi yayi zamansa"
ta k'arasa maganar kamar za tayi kuka
murmushi Dady yayi kafin yace "nima ina k'ewar ki sosai cikin satinnan Insha Allah zan dawo
kuna dai lafiya ko"?
"lafiya K'alau Daddy idan kadawo akwai labari mai dad'i da zan baka"
"Uhm Betyna fad'amun yanzu harna k'agara naji"
cikin shagwab'a tace "Aa Dady sai kadawu zan fad'ama kaji Dadyna"
sun jima suna fira kafin yace "Bety naga kinciri kud'i masu yawa
mi kikayi da kud'i da yawa haka"?
"Ayya Dady kayi hak'uri inaso na fad'ama mantawa nayi" nan tayi masa bayanin abun da tayi
dasu sai dai bata nuna masa tana zuwa gunsu Inna ba,
"kin kyauta Allah yayi maki Albarka amma dai ki kularmun da kanki bana son kina huld'a dasu
tsakaninki da talaka taimako"
"to Dady" ta fad'a cikin sanyin jiki sun d'an tab'a fira kafin daga bisani sukayi sallama.
Al'amin dawowar sa kenan daga gurin sana'arsa ya ga kayayyaki a k:ofar Inna
ya k'arasa d'akin Inna bakinsa d'auki da tambayoyi Faruk kawai ya tarar yana shan fura
"Faruk ina Inna"?
"Yaya sannu da zuwa Inna tashiga ban d'aki"
"OK kayi Alwala kafin na fito wanka muwuce masallaci"
da ganan yawuce d'akinsa.
a hanyarsu ta dawowa daga masallaci Lawal yake baiwa Al'amin labarin alkhairin da suka samu
yau
Al'amin ya dubi Lawal cikin mamaki yace "yanzu kai me ka fahimta?
kyautarka tafi ta sauran mutan Unguwa tamu ta shafi ta kowa kai dole akwai ayar tambaya
acikin al'amarinnan" ???
"mtsw kaifa wallahi kana da matsala to miye aciki kowa rabonsa yake ci kawai malam kaciri
komai aranka Allah ne ya kawo mana d'auki dan haka mugode masa mu kuma godewa wanda
yayi mana wannan taimakon"
"Uhm shikenan tunda kace hakan" da ganan sukayi salama Lawal ya wuce gida Shima ya
shige gida.
Yana cin abinci suna mayar da zancin da Inna "Al'amin nace tunda Allah yasa ansamu kud'i me
zai hana asa Faruk makaranta"?
"Inna maganar makarantar Faruk tana raina dama k'udirina idan nayi kwasar adashe na zan
saka shi kuma wannan satin Insaha Allahu zan karb'a"
"duk da hakan tunda Allah yasa ansamu asashi d'in idan ka karb'o adashen sai ka had'a da
wad'annan kayi jarin kanka"
cikin sauri yace "amma Inn... saurin katsi shi tayi ta hanyar d'aga masa hannu bana son musu
kayi yanda nace"
numfasawa kafin yace to Inna Allah ya saka da alkhairi" da ganan ya wanki hannunsa da
bakinsa yasha ruwa sannan yace "Inna zan d'an fita amma ba jimawa zanyi ba"
"Allah ya tsari"
"amin Inna".
Bety tariga ta gama shirin tarba bak'onta tun sanda ya kirata ta masa kwatancin gidansu
tana son ta fad'awa Aunty sai dai tana jin kunya
tana cikin tunanin yakira yana fad'amata ya k'arasu Bintu ta Kira tace ta shigo dashi d'akin bak'i
bayan fitar Bintu tasa hijab tanufi d'akin Aunty cikin jin