Showing 27001 words to 30000 words out of 41150 words

Chapter 10 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2881

kana d'an k'ank'ani bayan wannan ba wata alak'a ta 'yan uwan taka ko
zumunci,

to atak'aici dai muna buk'atar gida mun Baka nan da kwana biyu rak ka tashi kabamu gida
muna kuma fatan zaka mana kyakyawar fahimta"

Al'amin da tunda suka fara maganar kansa yaki aduni zuciyarsa na masa suya idanunsa har
sun sauya kala d'aguwa yayi ya kallesu cikin girmamawa yace "to Kawu Baffa na fahimce ku
Insha Allahu zanyi k'ok'ari na baku gidan cikin lokace nagode sosai"

"yawwa d'an albarka ai mune da godeya da ka fahimce mu"

daganan sukai masa sallama suka wuce suka barshi zauni cikin tashin hankali da rashin
madafa.


_mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

Fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*

_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_



#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*HAK'IK'A BA ABUN DA ZAKA SO KAYI FARIN CIKI FACE RASULU S.A.W SON SANE
HAK'IK'ANIN K'AINA BEGENSA NE HAK'IK'ANIN SHAUK'I ALLAH YA BARMU DA K'AUNAR
MA'AIKI S.A.W DARE DA RANA ZAFI DA SANYI AKOWANI YANAYI AKOWANI LOKACI DUK
BUGUN NUMGASHI DUK GUDANYAN JINI.DANGE ANNABIN DAI*


*140 to 150*

Ya jima zaune yana sak'a da warwara sai dai ya rasa mafita haka ya tashi ya nad'e tabarma ya
shiga cikin gida.

tana kwance tana game da wayarsa taga ya shigo jikinsa asanyaye da saure ta ajiye wayar ta
mik'e tsaye tana tambayarsa "Habibi lafiya na ganka haka me ya faru"?

rik'e hannunta yayi suka zauna kan kujera d'aura kansa yayi kan kafad'arta ya lumshi idanunsa
hannunta ta d'aura kansa tana wasa da sumar kansa


ba tare da tace dashi komai ba ya jima ahaka ganin yak'i
yayi magana yasa cikin sanyin murya tace "Habibina kasani adamuwa fa wai me ke faruwa ko
wani ne bashi da lafya ko mutuwa akayi"?


ajiyar zuciya yayi kafin yace ba ko d'aya Aishana zan fita ki tayani addu'a kinji karki damu"

ya k'arasa maganar yana murmushi dan kawar mata da damuwar da yagani kwance afuskarta

taimasa Allah ya tsare ya bada sa'a ba dan ta gamsu da ba komain ba.



bayan layinsu yaje shagon Sani ya sayar da wayarsa zatayi dubu d'are Yayan Lawal ya saya

masu iri d'aya dawowarsa Dubai amma yanzu da k'yar yasamu aka saya dubu talatin yana
karb'ar kud'in yaje yayi masu sayayyar abinci dai dai k'arfinsa

ya bawa Walid mak'wabcinsu ya kai masa gida daganan ya hau acab'a zuwa kasuwar barci har
bakin gurin da Kawu yake sana'arsa aka ajiyeshi.


bayan sun gaisa cikin rashin sakin fuska Kawu yace "Aminu lafiya dai ko"?

gyara tsuguninsa yayi kafin yace "lafiya k'alau Kawu dama alfarma nazo nema gurin....

cikin sauri Kawu ya katseshi ta hanyar d'aga masa hannu "kaga Aminu idan dai kan maganar
gida ne karka ma suma dan ba zaiyu mu barma ba baka da gadonsa ba zumunci atsakaninmu
sai taimkon da marigayiya tama ihin"

cikin jan numfashi yace "hakane Kawu nasani ba wai ina nufin zaku barmun kyauta bane Aa
zaku mun alfarma ne kubani haya ne har zuwa sanda Allah zai hore mun sai na tashi"


Kawu ya d'anyi jim kafin yace "to naji zamuyi shawara ko me kenan zan neme ka"

"nagode sosai Kawu" daganan sukayi sallama.


tasha ya nufa ya dingayin dako da zarar motar matafiya ta tsaya zai zo ya d'auki kayansu zuwa
gurin ababin hawa ko bakin titi har idan lokacin Sallah yayi jam'i baya wuce shi sai yamma lik'is
yanufi gida.


gajiyi ya isa gida yana zuwa ya fad'a kan katifa yana "wash Allah"

kallonsa tayi cikin tausayawa tace "Sannu Habibina"

lumshi idanunsa yayi kafin yace "yawwa Aishana ya gidan"?

"lafiya k'alau Habibi" ruwan randar Inna masu sanyi ta d'ebomai sannan ta kawo masa abinci

tashi zauni yayi yana fad'in sannu Aishana Allah yayi maki albarka"

"amin Habibi" kallonsa ta dingayi yanda yake cin abin cin gwanin tausayi

bayan ya gama ci ta kai masa ruwan wanka.

bayan Sallah Isha yana kwance tana masa tausa tace "Habibi amma yau tunda kafita bakaci
komai ba ko"?

murmushi marar sauti yayi kafin yace "me kika gani Aishana"?

"yanayin ka ya nuna mun hakan"

mirginawa yayi yana kallonta yace hasashen ki ne kawai"

"Hum Habib... "kiyarda dani" ajiyar zuciya tayi kafin tace "Habibina munga kayan abinci
mungode Ubangiji Allah ya k'ara bud'i da lafiya"

"amin Aishana" yayi maganar yana mai janyota jikinsa bakinsa yakai cikin bakinta ya dinga aika
mata sak'wannin soyayya duk k'ok'arinsa na kawar da dukan wata tambayar da yasan zata iya
yimasa daganan aka fad'a sunnar Ma'aiki S.A.W. wannan kenan


*kuyi hak'uri da wannan banda lafiya I love you all FNS*

_mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�
Fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*


_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_

#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*Soyayya wacce ba juya baya ba danasani ba kaicu sai tsantsar farin ciki da annashuwa samun
natsuwa itace Soyayyar Annabi MUHAMMAD S.A.W dangi mu saki kowa mukama Annabi da
iyalan gidansa da jikukinsa dangi Annabin dai*



*150 to160*


Washe gari da wuri ya shirya ya bar gida gurin wani Abokinsa yaje ya koyi sa'a ya tarar dashi
yana wankin mashin d'insa bayan sun gaisa yace

"Al'amin ya garin kwana biyu ka b'uya daga kai har Lawal" Al'amin dake jingina jikinsa da
kusurwar gidan yasa hannun shi d'aya cikin aljihu

yayi murmushi kafin yace "wallahi lafiya k'alau Alhamdulillah Lawal yayi tafiya shiyasa kadaina
ganinsa"

"au kardai kace mun tafiyar sa Abuja ta tabbata"

"eh wallahi Amma dai bazai jima ba zai dawu"

"bai samu aikin bane"?

"yasamu akwai abun da zaizo yayi sai ya koma ga ba d'aya"

"Allah sarki gaskiya namasa murna Allah ya taimaka muma Allah yasamu a danshin sa"

"Amin summa amin Sagir nazo ne na tambaye ka ko zaka mun hanyar da zan samu Mashin na
dingayin acaba"?



"ah sosai ma kuwa akwai wani da naji yana neman wanda zai dinga yi masa haya da mashin
saboda wanda ke masa bayada gaskiya wannan yasa ya karb'i mashin d'in idan dai har zaka
iya baka da matsala"

cikin farin ciki yace "ai dan zan iya na nema nagode sosai Sagir"

"haba Al'amin ba komai ai ana tare"

sun d'an tab'a hira kafin sukayi Sallama da juna.


da ganan yaje gurin 'yan buga bugansa sai magarib ya dawo gida kai tsayi masallaci ya nufa
sai da akayi Isha sannan ya shiga gida.


Bety tun fitarsa take kwanci sam bata jin dad'in jikinta kwana biyu haka take wuni da zazzab'e
da tashin zuciya

haka take jure wa ta gyara gidan idan
da akwai abun da zata girka tayi komai cikin dauriya take yinsa


yauma hakan tayi sai dai yau wahalce ta wuni komai takasa ci ko k'amshin abincin bata so haka
tayi girkin tana amai

da k'yar taga ta gama sannan tayi wanka ta shirya cikin k'ananan kayan da Lawal ya sayo
mata ita da Al'amin (Allah ka had'amu da Abokai na gari)


tana jin Sallamarsa tafito da gudunta tana zuwa ta fad'a jikinsa shima da murnar sa ya
rungumeta yana kiss d'inta.

bayan sun natsu yayi wanka yaci abinci yake fad'a mata ya samu mashin gobe da safe zai fara
fita kamar yanda Sagir yakira ya fad'a masa

sosai tai murna da Adu'an Allah ya sanya Alkhairi da albarka aciki.


su Kawu sun amince zasu bashi haya amma da alk'awarin zai dinga biyan kud'in haya cikin
lokaci.


acikin d'an k'ank'anin lokaci abubuwa suka sauya musu sosai Allah ya san yawa sana'ar
albarka.

Bety yau ta tashi da ciyon kai sosai ko d'aga kan bata iyayi hankalin shi ya matuk'ar tashi haka
yaje yasamu adai daita sukai asibiti


bayan tambayoyi da aune aune aka tabbatar da tana da juna biyu

wai zo kuga murna gun Al'amin kamar ba gobe sai Hamdala yakewa Ubangiji magani suka
rubuta mata sannan suka sallameta.


soyayya ce da tsantsar kulawa Bety take samu gun Al'amin wanda zata iya cewa ba maccen da
takaita sa'ar miji.


watansa d'aya da fara acab'a mai mashin ya karb'i abunsa tare da bashi hak'uri anmasa
barazana ne shiyasa ya karb'e ba dan baya jin dad'in aikinsa ba.

ranar haka ya dawo gida zuciyarsa ba dad'i sai dai sam bai bari Bety ta fahimci halin da yake
ciki.


washe gari ya kwaso wankenta da nashi ya zauna yanayi kamar yanda yasaba tunda tazo ko
pant d'inta bata tab'a wanke wa ba, shi ke wanke mata duk yanda tayi nacin ya barta tayi
hanata yakeyi


tana zauni kan kujera tsugune ta d'aura kanta a kafad'arsa tace "Habibi yau bazaka fita bane ka
d'auko wanke"?


"uhm yau ina so na zauna da iyalina idan kuma Aishana bata buk'atana to sai nasan gurin
zuwa"

ya k'arasa maganar cikin tsokana dariya marar sauti tayi kafin tace "lallaima ai ni bank'i muyita
zama tare karka fita ko ina har Illah Masha Allah ba"

matsi rigar da ya wanke yayi ya ajiye cikin wani bokiti kafin yace "Aishana matata Uwar 'ya'yana
in banda abunki idan ban fita ba me zamuci da kuma me zamuyi d'awainiyar kanmu da na
yaranmu idan Allah ya kawomana"?


far tayi da idanunta kafin tace "Soyayya zata ishemu komai"

kallonta yayi cikin shauk'i yace "Allah Aishana"

"Allah kuwa Habibina"

"nayarda Aishana Allah ya barmu tare har a Aljanna fiddausi"


"Amin Habibina Mijina Uban 'ya'yana".


rashin aikinyi yasa Al'amin ya koma ma buga bugarsa har watarana ya yanki shawarar zai fara
sana'ar sai da gwanjo ya nemi shawarar Bety ta k'arfafa masa gwaiwa

ya had'a 'yan kud'ad'ansa yayi jari dasu alhamdulillah Allah ya san yawa sana'ar Albarka.


cikinta nada wata bakwai abubuwa suka fara ja baya yanzu sam babu ciniki watarana haka zai
dawo gida ba cinikin ko sisi


bangarin abinci kuwa watarana sukan samu su dafa sau d'aya awaini shinkafa fara da mai ko
ya sayo masu dawa ko masara suyi tuwo tun bata iya ci har tasaba.

wani lokacin da kyar yake samun kud'in da zai sayo mata abincin da zatace baya ta kansa idan
dai taci to falillahi

dai dai da rana d'aya bata tab'a nuna gazawarta ga sauyin rayuwar da ta tsinci kanta ba hakan
ya kan matuk'ar k'ara masa soyayyarta da tausayinta aransa.


kwana ukku kenan yanda ya fita haka yake dawowa ko taro bai samun ba

sai dai ya ciyo bashin garin kwaki da k'ule ayi kwad'o

kantin Hamisu ya shiga bayan sun gaisa yace "Malam Hamisu dan Allah adai k'ara hak'uri
damu abani shinkafa gwangwani d'ayaya da mai na naira hamsin Insha Allahu zanyi k'ok'ari na
kawoma kud'inka gaba d'aya"

cikin rashin walwala wanda aka kira da Malam Hamisu yace "gaskiya kayi hak'uri Al'amin
bashinnan yafa yi yawa naira dubu nake binka kusan sati biyu kuma yanzu kazo na dad'ama
wani

Aa gaskiya da sake inama laifin ace ka rage bashin ne amma baka rage ba kace na k'arama

idan dai ba so kake ka karyani ba mu taru mu zama d'aya"


Al'amin cikin damuwa yace "dan Allah Malam Hamisu kayi hak'uri wallahi ina nan ina k'ok'ari
naga kud'in sun samu na biyaka kud'in ka amma ba fatana na b'atama jari ba kataimaka mun
dan Allah"

"aifa sai kayi" ya joya kan wacce tun zuwan Al'amin take tsayi yace "yi hak'uri baiwar Allah me
za abaki"

Murmushi tayi kafin tace "ayya bakomai su Malam Al'amin talaucin naku har ya kai ga cin
bashin abinci

Allah sarki Bety wallahi har tabani tausayi ko da yaki ai ita tajawa kanta tana cikin gatanta ta fita
ta zab'i tsiya

bayan talauci ga rashin asali waya sanima ko shig...

afusaci ya d'aga mata hannu cikin b'acin rai yace "ya isa haka Meenat wai nikam me natare
maki ne arayuwa?

kike neman tozartani aduk inda kika ganni bana shiga lamarinki meyasa kike neman shigarmun
rayuwa

na rok'iki dan Allah kifita rayuwata da ta iyalina tun baki kaini bango ba"!

cikin shewa tace "ahayye nanayi dama talaka marar asali yana da wani katab'us ne ai wallahi
ba abunda ka isa kamun matsiyaci kawai"!

hannu ya d'aga zai mareta ko me yagani sai ya fasa kawai ya juya yabar kantin ba tare da ya
kula tijarar da Meenat take masa ba

mai kantin sai hak'uri yake bata da k'yar yasamu tabar kantin.

daga lokacin unguwar ta d'auka Al'amin shegeni baya da asali ba damar ya fita sai a hau
nuninsa ana zagensa

yayi kukan zuci yayi na fili harya godewa Allah.


Bety sam batada labarin abunda ke faruwa kasancewar ba fita take ba ko yaushe tana gida
Al'amin kuma bai fad'a mata ba

sai dai damuwar da take gani a fuskarsa ta alak'anta ta da rashin sana'ar yine da rashin madafa
shiyasa ko yaushe take k'ok'arin kwantar masa da hankali.


tana zaune tsakar gida tana gyaran k'umbar hannunta wata yarinya tashigo "salamu ailaikum
wai ance ana wa mai gidannan sallama"


"bayanan ya fita kice waye ne"

"to" yarinya tafita da gudu sai gata ta dawo "yace Lawal ne"

da murnarta tace "ji kice da shi ya shigo"

hijab d'inta da me sarkafi a k'aure ta janyo tana sawa ya shigo da sallamarsa

kujera ya janyo ya zauna suka gaisa cikin girmamawa tace "Yaya Lawal saukar yaushe"?

"Wallahi yanzunnan ko gida banje ba nan na fara zuwa"

"ayya sannu andawo lafiya"?

"lafiya k'alau wai me yasami wayar Al'amin inata nemansa bana samusa"?

"ai wayar ce ta lalace shiyasa"

"ayya to ni zan wuce gida amma anjima zan dawo dan Allah idan ya dawo kice dashi ya jirani"

"to Insha Allahu zan fad'a masa ko ruwa ban kawoma ba Yaya Lawal bari ba kawoma"

"haba karki damu ba komai nagode".


bai jima da fita ba Al'amin ya dawo da gudunta taje gurinsa ta fad'a k'irjinsa rungumeta yayi
cikin kulawa tace

"Aishana bakya jin magana ko"?

cikin shagwab'a tace "uhm Habibi me nayi na rashin ji"?

fuskarta ya d'ago suna kallon juna yace ba na hanaki gudu ba ko kin manta yanzu ba ke kad'ai
bace"

ya k'arasa maganar yana shafar cikinta b'oye fuskarta tayi cikin k'irjinsa tana murmushi

zaiyi magana yaji ana sallama cikin sanyin jiki ya janyeta tare da yimata kiss a goshi yace da ita
yana zuwa bayan ya mik'a mata ledar da ya shigo da ita.

kamar yanda ya zata d'in hakane Baffa ne tare da Kawu "ah Baffa sannunku da zuwa"

"kaga rik'i gaisuwarka ba ma buk'ata kasani ka sab'a alk'awari wata biyu kenan Baka biya
kud'in haya ba Dan haka yanzu ba sai anjima ko gobe ba ka tattara inaka inaka kabar
gidannan"

durk'usawa yayi cikin muryar Lamar zaiyi kuka ya fara rok'onsu da suyi masa lamuni zuwa sati
biyu zai biya su kud'insu

amma fir sukak'i haka ya koma cikin gida zuciyarsa a cunkushi



_Mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

Fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*


_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_

#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*WA ZAI SO UBA YA K'YALE D'IYA INA BAZAIYU BA SOYAYYA BATA CIKA SAI KASO UBA
DA 'YAY'YANSA SAYYADA 'YAR SAYYADI SHUGUBA 'YAR SHUGABA SAYYADA FAD'IMATU
ZAHRA BINTU RASULULLAHI S.A W AMUNCE MUN KI YARDA DANI 'YAR MUTAN YABO
WALLAHI BANDA ABUN K'AUNA BAYAN ABANKI K'AUNAR SA CE TASA NAKE SON
FAD'IMA, BAKI DA ZUCIYA BAZA SU IYA MISALIN TSANTSAR K'AUNAR DA TAKE MUKU BA
KI YARDA DANI KISAN DA ZAMANA HAR KULLUM INA TA K'OFARKI SAYYADA INA MAULA
NA SANI KYAUTA HALINKI NE GADON KI NE, BA KWA JEKA KADAWO ANAN TAKE KO KE
BADA KYAUTA, ZAUNA DA LAFIYA SHALE LE TA ANNABI TAKAWARKI LAFIYA 'YAR
SAYYADA SHUGABAR MATA NANA KHADIJA SANNU SANNU JIKA GA SAYYADI
ABDULLAH DA AMINA*

*NA GAIDA MAHAIFIYAR HASAN DA HUSAIN LAMUNCE MUN KI RIK'E HANNUNA DA
HANNUNKI MAI* *ALBARKA KI KAINE HAR GURIN MAHAIFIN KI DAFA KAINA KI SANYA
MUN ALBARKA DA BAKIN DA BAI TAB'A SAB'O BA, IDAN KIN* *YARDA DANI NASA NI
ALLAH DA MA'AIKI ZASU YARDA DANI, ALLAH KA K'ARA NARKAR DAMU DA ZUKATAN
MU DA RUHINMU DA GANGAN* *JIKINMU ACIKIN SOYAYYAR ANNABI MUHAMMAD S.A.W
DA SAYYADA FAD'IMA DA IYALAN GIDANSA DA* *JEKUKINSA SHEHU AHMAD TIJJANI DA
SHEHU IBRAHEEM INYES, HAK'IK'A* *KUNE GATANA SHURAFA'U DA* *BAZARKU NAKE
RAWA* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃



*150 to 160*

Zaune take ganin yanayin da ya shigo yasa ta saurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login