Showing 33001 words to 36000 words out of 41150 words

Chapter 12 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2876

godewa Allah ba Wanda me kula shi.


ya dawo gidansa da ke malali gurin iyalinsa idan dai ba tafiya yayi ba yana tare da su sai dai ya
rame yayi duhu damuwa ta masa yawa ga fushin da iyayan sa keyi da shi ga wani irin son
Zainab da ke d'awainiya da shi

zai iya cewa a rayuwarsa bai tab'a son macce yanda yake son Aunty ba

ko yaushe cikin zarya zariya yake amma ko sau d'aya ba abari ya ganta ba

yau da yamma ya shiga zariya sai da ya biya masallaci yayi sallah la'asar sannan ya k'arasa
gidan


yana zuwa kawu na fitowa gidan ai kuwa ya murtiki fuska kamar yaga kashi da sauri Dady ya
fito mota durk'usawa yayi har k'asa "Barka da yamma kawu"

cikin tsawa Kawu yace "rik'i gaisuwarka bana buk'uta na kuma godewa Allah da ya kawo ka ina
nan

duk zaryar da kake inada labari ina so daga rana ta yau karna koma ganin k'afanka ak'ofar
gidannan in dai Zainab ce ko bayan raina ban yafe ba idan ta komawa auren ka

sannan idan dai gida dan yana naka zaisa kana mana zarya to zasu tashi subar ma tsiyar ka"!

fau ya wuce afusace yabar Dady durk'ushi agurin ba tare da ya saurari maganar da Dadyn keyi
ba

hawaye nagani suna zarya afuskar Dady turk'ashi Lallai wani abun sai so ba ruwansa da tsofa
ko yarinta.



*kuyi hak'uri da wannan FNS INA Buk'atar addu'an Ku banda lafiya*


� *Aisha A Yabo*�

Fulani����
�����

������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*


_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_



#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*TAKAWAR KA LAFIYA SAYYIDUL WUJUDI GATAN KOWA ALFAHARIN KOWA GARKUWAR
KOWA K'AUNAR KA DA'IMAN BA GUDU BA JA DA BAYA ZUCIYA DA JINI KAUNAR KA
SUKE BURINA NA KASANCE DA KAI DUNIYA DA LAHIRA SOYAYYAR KA TABI JINI DA JIKI
BABU MASAK'AR TSINKI DA'IMAN SAI ANNABI* *MUHAMMAD S.A.W* RAINA *FANSA NE
GARE KA YA NABIYU RAHAMATI*
*DANGI ANNABIN DAI!!!*

*180 to 190*

Haka ya mik'i tsaye jiki ba k'wari baiyi zuciya ba ya nufi cikin gidan yana ta k'wala sallama

ya d'an jima yana sallama sai can ya jiyo muryar Inna tana amsa sallamar

"amin alaika salam waye ne"?

tayi tambayar dai dai sanda ta k'arasu surun tana ganinsa ta b'ata fuska tana fad'in "lafiya"?

sunkuyawa yayi gabanta yana fad'in "Inna mun wuni lafiya"?

"lafiya ya akayi ne"? ta amsa gaisuwar atak'aici

cikin k'ara k'ask'antar da murya yace "dan girman Allah da Ma'aiki Inna ayi hak'uri hak'ik'a Inna
nasani abun da nayi ban kyauta ba

kuma wallahi nayi nadama Dan Allah kuyi hak'uri Zainab ta koma d'akinta"


cikin sanyin jiki Inna tace

"bakomai yawuce ai dama bawa bai isa ya kwaucewa k'addararsa ba

Dan haka mun yafe ma amma zan cin komawar Zainab ba ahannuna take ba tana gunta da
kawun ta ni bazan ja da ikon Allah ba"


"nagode Inna Allah ya saka maki da Alkhairi"

"amin ba komai ka shiga d'aki bara na turo Zainab d'in"

"nagode Allah ya k'ara girma".


Inna ta shiga cikin gida d'akin da Aunty take ta nufa tana zaune tana duba littafin addu'oi

jin shigowar Inna yasa ta ajiye littafin gefenta cikin murmushi tace "Inna sannu"

"yawwa Zainab Alhaji ne yazo yana son ganinki"

b'ata fuska tayi kafin tace " wanne Alhaji Inna "?

"ah Baban su Bety ki tashi kije ni bazan maki dole ba amma kisani kowani bawa da k'addararsa
Allah yarubata sai hakan ta faru bawa bai isa ya canza ba,

sannan idan Alhaji na da laifi to kema da naki laifin ya fad'a maki gaskiyar abun da ke zuciyarsa
kin nace zaki zauna saboda yara

wanda banga dalilin cutawa kanki akan yaransa ba dan haka kiyi hak'uri kije ban kuma ce ki
wulak'anta sa ba

domin gudun aikin da nasani dan baki san abun da zai faru agaba ba"

cikin sanyin jiki tace "to Inna".

dama da hijab ajikinta d'akin da yake ta nufa

bayan sun gaisa ya fara bata hak'uri cikin sauri tace "nifa ban rik'e ka da komaiba wallahi na
yafema"

ajiyar zuciya yayi kafin yace "nagode Auntyn yara ina Neman wata alfarma da ki amince mun
amaida auren mu"

cikin murmushi tace "kayi hak'uri bazan iya koma wa auren ka ba kawai mubarwa Allah zab'e,

ya wajan Bety tana lafiya"?
ta d'auko zancin Bety dan takawar da zancin

"Uhm bana ce tana lafiya ko akasin hakan ba saboda banda labarinta ban san gidan mijin nata
ba

amma ina nan ina bin cike har Allah yasa adace"

sosai lamarin ya tab'a zuciyarta addu'a sosai tayi akan Allah ya bayyana ta

daga haka ta mik'i zata wuce yaciru kud'i ya bata tak'i karb'a tayi shigewarta gida.

haka yabar gidan jiki ba k'wari.


a cikin wata ukku da fitowarta gidan Dady Allah ya kawo mata miji Malamin islamiya yana da
mata da yara hud'u

ko wata basuyi da had'uwa ba akayi auren su suna zauni lafiya da maigidanta da abokiyar
zamanta.


lokacin da Dady yasamu labarin Auren Aunty yanki jiki yayi ya fad'i asumi iscs d'insa ne suka
kai shi asibiti

sannan suka kira gida suka fad'a cikin tashin hankali Ummy da iyalanta suka k'arasu asibiti sun
tarar yana barcci sai dai kallo d'aya zaka masa ka fahimci yana jin jiki

office d'in Dr d'insu ta nufa bayan sun gaisa tace "Dr me yake damun Mijina"?

"gaskiya hajiya damuwa ta yiwa Alhaji yawa da har ya haifar masa da ciyon zuciya

dan haka shawarar da zan baki kuyi k'ok'arin guji duk abunda zai b'ata masa rai ko sanya shi
damuwa

hakan zai sa maganin da muka d'urashi akai suyi tasiri akansa cikin yardar Ubangiji

dan gaskiya idan yaci gaba da sa damuwa aransa komai zai iya faruwa"

godeya ta masa tare da tabbacin za su kula haka ta komawa d'akin da yake

yaran suna ganinta sukak'i fara tambayarta "Ummy me yake samun Dady"?

"kuyi masa add'u'a kunji"?

"to Allah ya bashi lafiya"
"amin".


kwanansa hud'u aka sallame shi bayan yayi wanka yaci abinci Ummy ta kora yaran

bayan fitarsu cikin hikima take tambayar sa abunda ke damunsa da har ya janyo masa ciyon
zuciya

nan take ya bata labarin abunda ya faru abaya

kallonsa tayi cikin wani yanayi kafin tace "gaskiya Alhaji baka kyauta ba kuma wallahi ko nice
bazan dawo maka ba

kama godewa Allah da Ta yafe ma da abun yafi haka

kuma nikam ina buk'atar ka kaini gurn dangin ka saboda yarana da kuma abun da gaba zata
haifar"!

tana gama fad'a ta mik'e tsaye zata fita yayi saurin rik'o hannunta cikin damuwa yace

"haba Ummyn yara kar ki juyan baya alokacin da nake buk'atar tallafin ki

hak'ik'a nayi matuk'ar nadama akan abun da na aikata kuma Insha Allahu acikin satinnan zan
shirya mana tafiya Sudan"

komawa tayi ta zauna tayi cikin tausayin sa tace "shikenan Allah ya nuna mana ka daure kaciri

damuwa k'addara ce bawa bai isa ya kauce mata ba sai dai k'arfin addu'a yasa ta zowa mutum
da sauk'i

ka nem gafarar Ubangiji da neman sassauce agurin sa"

haka ta zauna tana kwantar masa da hankali da lallab'ashi.

acikin satin suka nufi Sudan gidansa da ke Sudan suka sauka sai da suka huta sukaci abincin
da 'yan aiki suka girka masu

sannan suka nufi gidan iyayansa yaran sai murna suke zasu ga kakannin su da sauran familin
Dady

Ummy kuwa damuwa ce fal aranta da tunanin waci irin tarba zata samu a gun sarakanta?

Dady ma kusan tunaninsa d'aya da Ummy ya zasu karb'i zancin shikam yasan mai laifuka ne
agun iyayansa da familinsa addu'a d'ai yake Allah yasa komai yazo masa da sauk'i.


_Mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

Fulani����
�����
������
*KAR KA GUJE NI*
������
�����
�����


� *Aisha A Yabo*�

�fulani�


*®Real Pure moment of life writers*


_We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_

#WWW.PMLWRITERS@GAIMAIL.COM
#IG PML ERITERS
#http://www.facebook.com/PML_-Writers-FNS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


*Son Annabi ne mafita Mustapha Babban Bango d'aha rik'e ni Dan nasamu rabauta babba
k'aunar ka nake dare da rana Begen ka nake ya khairil khanzillah shugaba aso ka aji dad'i
ak'ika akasan ce cikin k'unci wallahi komaina naka ne ya Habibullah ya Shafi'ullah Allah k'ara
kusan tamu da narkar damu acikin Ma'aiki S.A.W* *DANGI ANNABIN DAI*!!!

*200*


Lokacin da suka isa Baffa baya nan sai Hajiyar sa ganin shi da bak'in fuska yasa ta tare su da
fara'a sai dai zuciyarta fal da mamakin

yaran da taga suna matuk'ar kama da Dady tambayoyi ne aranta amma haka dole ta hak'ura
tasa aka gabatar masu da abinci

basu wani ci da yawa ba saboda a k'oshi suki

cikin ladabi yace "Hajiya Baffa na gari nata neman wayarsa bata shiga"?

"eh yana gari nasan yanzu yana hanyar dawowa gida"

ko rufi baki batayi ba Baffa yayi sallama d'akin bayan yasa mu guri ya zauna Hajiya tamasa
sannu da zuwa

ya amsa yana kallon yaran da mamaki yace "Ikon Allah wad'annan yarafa masu kama da
yaran gidannan"?


"uhm nima mamakin da nake yi kenan tare suki da Sufyan"

da sauri ya kai duban sa gun Dady wanda sam bai kula da shi ba sai yanzu Dady yace "Baffah
mun same ku lafiya"?

"lafiya" Baffa ya amsa masa atak'aici Ummy tazo gabansa cikin ladabi ta gaishe shi ya amsa
mata da sakin fuska suma yaran haka suka gaishe shi

bayan sun gama gaisawa Dady yasa 'yar aikinsu ta shiga dasu Ummy d'akin bak'i

bayan fitarsu Dady ya fara basu hak'uri sannan yayi masu bayanin aurensa da yaran da suka
samu

nisawa Baffa yayi kafin yace "bazan ja da Ikon Allah ba, ba kuma zank'i karb'arsu ba amma
kasani baka kyauta ba kanuna wa duniya mu iyayanka ba abakin komai muki ba

tunda har zaka iya aure tsawon wannan shekarun ba tare da sanin mu ba

ka cutawa Zainab ka danni hakk'inta akan wani dalili marar tushe ka godewa Allah da bata
shiga wani hali na aikata zina ta silarka ba"

fad'a sosai Baffa da Hajiya sukayi masa kafin daga bisani suka yafe masa.

ko kafin kace me maganar ta yad'u cikin famili kowa sai jinjina lamarin yake sai dai hakan bai
hana su nunawa Ummy da yaran ta soyayya da kulawa ba.

Yaya Saif yana Mumbai yaji labarin aikuwa 'yan ransa yayi dubu ya b'ace wannan yasa yayi
fushi da Dady da kowa na gida

har suka dawo Nageria baizo ba sai da Dady yayi da gaski da nuna b'acin ransa sannan yazo
cikin ikon Allah yana ganin 'yan Uwansa yaji k'aunarsu ba kad'an ba

Dady da sauran 'yan Uwa sai addu'a suke akan Allah ya bayyana masu Bety.


Al'amin Alhamdulillah likkafa taci gaba ko wata da fara aiki baiyi ba Yaya ya saya masa Mota
bud'i ya samu hankalinsu akwanci

basu da damuwa sai fatan Allah ya sauke Bety lafiya

sai damuwar da take ransa wanda ko Bety baya barin ta fahimta rashin sanin iyayensa da
familinsa wannan na matuk'ar damunsa ko yaushe yana addu'a akan Allah ya bayyana masa
familinsa

abunda bai sani ba babu ranar da zata fito har ta fad'i Bety bata yi addu'a akan Allah ya
bayyana dangin Habibinta ba.


yau kam ta tashi jikin sai ahankali ko karin kumallo da kyar ta iya had'a masa bayan fitarsa ta
koma ta kwanta

har zuwa azahar bata gyara gidan ba batayi girki ba sallah ma da kyar ta iya yinta

tana zaune kan darduma tana salatin Annabi S.A.W taji shigowar mai gidan


yana k'wala mata kira "Aishana Ashana"

"Na'am Habibi ganinan zuwa" tayi maganar tana mai mik'ewa tsaye falon ta nufa tsaye ta tarar
da shi ransa b'ace aikuwa yana ganinta ya hau fad'a

"miye haka Aishana yanda na fita nabar gidannan haka na dawo na tarar da shi ba shara"!

cikin kwantar da murya tace "kayi hak'uri Habibi wallahi tun fitar ka ina kwanci banda lafiya
shiyasa amma yanzu zan gyara kayi hak'uri kaji"

ta k'arasa maganar ciki lallami

"me yasa baki fad'an ba kafin na fita ko ki kirani awaya"?

"kayi hak'uri nayi kuskure bazan sake ba da yardar Allah"

janyota jikinsa yayi cikin kulawa yace "ya jikin"?

"da sauk'i"
"Allah ya k'ara sauk'i zauna bara na gyara gidan kinci abinci"?

cikin shagwaba tace tun fitarka komai fa banyi ba"

"ayya sannu idan kinji baki da lafiya ki daina yin shiru idan ba haka ba zamu b'ata"

kanta ta kad'a alamar to

cikin d'an k'ank'anin lokaci ya gyara gidan ko ina yayi fis sannan ya girka masu farar shinkafa
tunda dama tana da Soyayyar miya

sai da sukaci abinci sannan sukayi wanka

suna zaune a falo kwanci take ajikinsa shikuma yana kall idanunta suna lumshi ciyon mara take
ji can taji tana jin fitsari

ta tashi ahankali zata wuce ya kalleta yana fad'in "me nine Aishana"?

"zan shiga ban d'aki ne"

"OK"

tana shiga ciyo yace salamu alaikum durk'usu tayi tana nishin wahala

Al'amin jin shirun nata yayi yawa yasa shi bin bayanta yana zuwa kukan Baby ya fad'a kunninsa
arud'i ya fad'a ban d'aki yana kiran

"Aishana haihuwa kikayi"?

cikin murmushin k'arfin hali ta gyad'a masa kai tana fad'in "wayata na kan firij kakira Ummy"

da sauri ya fita yana fad'in "to to sannu"

yana kiran Ummy ya fad'a mata ai ba awani jima ba ta zo gidan d'akinsa ya koma dan yana
matuk'ar jin nauyin Ummy

cikin d'an k'ank'anin lokaci Ummy ta gyara Baby da Uwar Baby ta wanki kayan ta gyara ban
d'aki tare da Fishe ko ina da turare ko ina sai k'amshi yake


tei mai kaure ta had'awa mai jego ta kai mata d'aki

"Sannu d'iyata ungu wannan maza shanye"

karb'a tayi cikin jin kunya tace "nagode Ummy Allah ya saka maki da mafificin Alkhairin sa"

"Amin ba komai ai d'a na kowa ne ina jinki kamar yanda nakejin su Ihsan karki damu kinji"

d'aukar jaririya tana fad'in "Sannu d'iyata barakallah masha Allah wannan girma na kishiyata
ai kam kinyi fama"

Bety dai kumai ta kasa cewa sai murmushi take Ummy tace "bara na tafi gida Dadyn Ku na
hanya yau zai dawo"

"Allah ya dawo da shi lafiya"
"Amin inawa Baban Beby barka"

"to Ummy zai ji Insha Allahu"

yana jin fitar Ummy ya shigo d'akin yana zuwa ya rungometa cikin tsananin farin ciki yace

"sannu Aishana Allah yayi maki Albarka Allah ya faranta maki fiye da yanda kika faranta mun"

"amin" ta amsa cikin jin dad'i d'aukar Babyn yayi yana mata addu'a sosai sai kallonta yake ciki
da k'auna

su Ilham suka shigo gidan suna hayaniyar murna basu ko jira an amsa sallamar su ba suka
fad'a d'akin

"lah Yaya yi hak'uri ba musan kana nan ba"

dariya yayi kafin tace "karku damu 'yan k'annena Ku k'arasu ga 'yar taku"

har rigin rigin ake wajan d'aukar Babyn "Woww Aunty kyakyawa har tafiki"

"kai Ihisan Ilham Ku fad'i dai gaskiya Ku ciri son kai" cewar Bety

"Allah da gaski Aunty"

haka dai Al'amin ya fita ya barsu suna ta murna

ba ajima ba Autan Ummy ya kawo mata abinci da farfesun naman rago.

kwana ukku da haihuwa Lawal ya dira garin da abun arzik'insa ko shi akaiwa haihuwar
muranar da ya nuna sai haka.

daga Al'amin har Bety basu da bakin yiwa su Lawal da su Ummy godeya sai dai kawai suyi
masu addu'a

domin sun tsaya masu akan komai sun zame masu iyaye 'yan uwa.

ranar suna aka rad'awa Baby sunan 'yar shugaban Halitta Fad'ima shugabar mata (Allah ya
k'aramana soyayya da kusance amin)

ana kiranta da (sajida)


ko yaushe tana gurin Ummy sosai suke k'aunar Baby Dady son da yakewa sajida har mamaki
yake baiwa Ummy indai yana gidan zaisa ad'auko ta

yayi ta yi mata wasa idan ya fita ko yayi tafiya tsarabar ta dabance.


Ranar asabar Al'amin yana gida kwanci yaki kan kafet ya d'aura Sajida 'yar wata hud'u akan
cikinsa yana mata wasa

sai dariya take Bety na kitchen tana masu girkin rana taji yana kiranta da sauri ta fito kitchenn
hannunta rik'i da Pleat d'in da ta yanka masa furut ajiyewa tayi gefensa tana fad'in

"yi hak'uri Habibi na tsaya sauki miya ne"

"OK ungu Sajida ki d'utata a fu naji tana nishi k'ila kashi zatayi karta mun ajiki"

karb'arta tayi kafin tace "idan tayi ma ba sai kaji yanda nakeji ba"

"Aa ai ku dama aikin ku ne bana mu ba"
ya fad'a yana dariya

"him lalle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login