Showing 18001 words to 21000 words out of 41150 words

Chapter 7 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf

20 Mar 2025

2873

Dady karka biyewa Bety yarinya ce sam bata san inda yake mata ciwo ba"

"Saif kayi abunda nace" cikin tashin hankali Bety ta matsa kusa dashi cikin muryar da taci kuka
tace "Dady kayi hak'uri kamun rai wallahi banje da wata manufa ba ko dan nak'iyin biyayya
gareka ba dan Allah Dady kayafe mun wallahi zan aur... tsawar da ya daka mata ne yasata

had'iye sauran maganar batare da ta shirya hakan ba

"bana buk'atar wata magana kiyi abunda nace idan ba haka ba wallahi kinji na rantse zan bada
ke sadaka ga kowaye"

da ganan ya tashi ya nufi d'akinsa yana fad'in "Zainab ki sameni d'aki"

Fa'iz mik'ewa yayi yabar falon cikin damuwa ya sani zaiji jiki na rashin Bety sai dai hakan da
yayi shine dai dai ba zai iya aurenta ya kasance gangan jikinta ne kad'ai atare dashi Zuciyarta
na gun wani ba zaiyu ba.


Aunty ta wuce d'akin Dady cikin fad'uwar gaba da tunanin me zai faru?.

Yaya Saif ya kai mata rank'washi aka wanda yasa tasaki k'ara cikin jin haushin ta yace "kika
kuskura kika nacewa auren fak'irinnan Allah dagani har Dady Zamu ciri hannunmu acikin
al'amurranki banza marar tunani yana talaka me yaci me ya baki

kirasa abun so sai talaka wanda idan ya samu na yau da k'yar tunananin inda zai samu na
gobe zaiyi"

fad'a sosai yayi mata kafin yaje ya d'auko mata wayar ya jefa mata ajiki yabar falon yanata meta

ita dai komai bata iya cewa dashi ba sai kukanta take oh dama ya lafiyar kura ballatana an
tab'ota

tarik'e wayar tana tunanin mafita "takira Al'amin kokuwa? idan kuma tak'i kiransa Dady zai
had'ata da kowa ma kai gara kawai takirashi da dai ahad'ata da wanin kuma wai sadaka tab"!

haka dai ta zauna tana sak'awa da warwarewa.

ahankali Aunty ta tura k'ofa yana tsayi abakin window ya goya hannayansa abaya yaba k'ofa
baya


ahankali ya fara magana ba tare da ya jiyo ba "Zainab abun da kika mun kin kyauta kenan? da
saninki Bety taje d'akin sauraye sannan nazo na tambayeki kimun k'arya idan 'yar da kika Haifa
ce zakiyi mata irin wannan tarbiyar amanar da na barmaki kenan"?


cikin rawar murya Aunty tace kayi hak'uri kuskurena d'aya da na b'oyema gaskiyar magana
Amma wallahi tallahi ban San fitar Bety ba nima dubawa nayi naga batanan

ban kuma b'oyema dan wata manufa ba sai dan gudun karkayi fad'a amma kasan bazan tab'a
cewa da Bety taje wani gun da zai iya zama illa ga rayuwarta ba

banci amana ba ba kuma zan tab'a ciba kasani"

jiyowa yayi suna fuskantar juna kafin yace "bazan tab'a yarda da wani zancinki ba domin tun
farko kin tabbatar mun da saninki ta fita

kin karya Alk'awarin da mukayiwa juna
ina so ayau d'innan ki bar gidannan na *SAKE KI SAKI D'AYA*duk da kin b'ata mun rai hakan
ba zaisa na manta alkhairan da kikayiwa yarana ba"

janyo wata 'yar akwati k'arama mai kyau ya mik'o mata "ga wannan kirak'i k'adarurin da ke ciki
zasu ishiki komai awannan rayuwar"


murmushin takaici tayi kafin tace "karik'i kayanka bana buk'ata amma kasani ni ban karya
alk'awari ba kaine ka karya alk'awari idan ka manta bara na tuna ma"


*BARI MU D'AN WAIWAYA BAYA KAD'AN*


zauni take kan gado fuskarta lullub'e da mayafi kuka take sosai tana tunani taya zata zauna da
Uban gidanta kuma mijin Momy wacce tarik'eta tamkar 'yar da ta Haifa,


shigowarsa ce tasa ta saurin sauka daga kan gado ta sunkuya cikin girmamawa tace dashi
"sannu da zuwa"

"yawwa" ya amsa bayan ya zauna gefen gado ya d'an kalleta kafin yayi gyaran murya yace


"Zainab ina so ki bani hankalinki nan muyi magana ta fahimta kinji"?

gyara zamanta tayi kan kafet cikin natsuwa tace "eh yallab'ai"

"kiyi hak'uri da maganar da zan fad'amaki magana ta gaskiya bazan iya zama dake amatsayin
mata ba,

ina maki kallon kamar yanda marigayiya tanemi na d'auke ki d'iya har yanzu ahakan na d'auke
ki,

na amince wa aurenki saboda ina so na rayu da yarana kema nasan saboda ba kyaso arabaku
kika amince,

wannan yasa na yanki hukuncin zamu zauna da juna kamar da ba tare da kowa ya sani ba,

duk lokacin da kikaso rabuwa da yaran ashiryi naki da na sallameki yaya kin amince"?

yayi mata tambayar yana mai zuba mata idanu

ko kad'an bataji haushin maganarsa ba dan tasan gaskiya ne ya fad'a hakan yayi mata dad'i
hannunta tasa tana mai share hawayen dake ta zarya afuskarta

batare da dogun nazari ba tace "ba komai na amince amma ina so kamun alfarmar barina
gidannan har sai ranar da Bety tayi aure aranar nayi alk'awarin zan barku"

cikin mamaki yace Zainab shekararki 15 Bety shekararta hud'u da 'yan watanne amma kike
maganar zaki zauna ba tare da abokin rayuwa ba tsawun wannan shekarun"?

"karka damu zan iya ai shiyasa na nemi hakan saboda ban san wace irin mata zaka aure ba kar
tazo ta k'untata masu aranar da Momy zata rasu kafin su tafi tabar mun amanar su Aisha ya
zama dole na rik'i wannan amanar duk rintsi" ta k'arasa maganar cikin shishshik'a kuka

ganin ta dage yasa ya bar maganar yayi mata saida safe

bayan fitarsa tayi shirin kwanciya hankalinta kwanci duk wani damuwa da zullumi ya gushe
azuciyarta taso ta d'auko Bety su kwana tare sai dai gudun tambayarta dalili yasa dole ta
hak'ura tayi barccin ta ita kad'ai.

kwanci yake tunani ya hanashi sakat anya yayiwa yarinyarnan adalci amma ya zaiyi dole ne
yayi wannan hukuncin Allah yagani baya jin sonta ba kuma zai iya cin amanar marigayiya ba ta
d'auki Zainab tamkar 'yar cikinta hakan yasa shima yake d'aukarta a wannan matsayin har gobe
bazai iya rayuwar aure da ita ba haka dai yayita tunani har barcci yayi awun gaba da shi.

tana matuk'ar kyautatawa su Bety k'auna ce take nuna masu tamkar ita ta haifesu Saif ne kawai
ke d'an bata matsala rashin kunya da tsiwar da yake mata yana damunta amma sam bata biye
masa tsakani da Allah take sonsu.


tana yawan ciyon Mara musamman lokacin al'adarta haka take daurewa har tayi taji sauk'i
batare da tabari kowa nagidan ya sani ba ko yaushe cikin azumi take

tsakanin ta da Dady kowa gaisuwa ne sai girkin da take masa idan yana gari ko yaushe zaka

ganta cikin hijabi.

iyaye da 'yan uwa kuwa tun suna damuwa da rashin haihuwarta har aka hak'ura aka dage da
adu'a sai dai suna matuk'ar tausayinta aganinsu gara shi yana da biyu itace dai ko d'aya bata
da

wannan yasa sanda yajewa iyayansa da zancin zai k'ara aure suka hanashi saboda suna son
Zainab suna tausayin rashin haihuwarta file ya hak'ura ba dan ya so ba.


*bayan shekara ukku*

Dady ya k'ara aure ba tare da Zainab da iyayansu sun sani ba 'yar nan Kaduna ce suna zaune
a malali yaransu hud'u

Farhan Safna da taci sunan Momyn Bety ana kiranta da (Ilham) sai Zainab da taci sunan Aunty
ana kiranta (Ihsan) sai auta Isma'il ko yaushe Mamy na damun Dady ya kaisu gun danginsa
kodan yaransu da kuma halin rayuwa

duk san da tamai maganar hak'uri yake bata zai kaisu sudai k'ara hak'uri. wannan kenan.


*ci gaban labari*

"ina fatan ka tuna dan haka ban karya alk'awari ba kaine dai ka karya alk'awari"

daga haka bata sake cewa komai ba tabar d'akin.

Bety da take zaune a inda Aunty ta barta cikin damuwa tama rasa tunanin yi shin farin cikin
samun Al'amin zatayi ko bak'in ciki saboda Al'amarin ya zo mata ba yanda taso ba, ba kuma
yanda ta zata ba

tana cikin wannan yanayin ne taga fitowar Aunty a hargitsi ta nufi d'akinta hakan ya matuk'ar
d'aga mata hankali tashi tayi da sauri tabi bayan Aunty.


_mai k'aunar Ku_

� *Aisha A Yabo*�

�fulani����
�����
������

*KARKA GUJENI*
������
�����



� *na Aisha a yabo*�

*Fulani*�


*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*







*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*


_Wannan sune shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_


*90 to 100*


Gurin wadrobe ta tatarar da Aunty tana fito da kayanta cikin sauri ta k'arasa gurinta tana fad'in
"Aunty lafiya naga kina had'a kaya"?

"lafiya k'alau Bety" ta bata amsa ba tare da ta juyo ba "dan Allah Aunty fad'amun me kefaruwa
yanayin ki kad'ai ya tabbatar mu da ba lafiya ba"

rik'o hannunta Aunty tayi suka zauna bakin gado ta fara magana cikin muryar da ko yaushe
zata iya fara kuka

"Bety banji dad'in abun da kikayi ba Allah ya gani banmaki irin wannan tarbiyar ba meyasa zaki
biyewa zuciyarki kije gun saurayi"?

cikin kuka tace "Aunty koda kowa zaik'i yarda dani ban zaci kema zaki k'i amincewa dani ba
wallahi summa tallahi banje gun Yaya Al'amin da wata manufa ba,

kawai naje ne dan nayi masa sallama na kuma fad'a masa abunda ke faruwa dan kar yaji awani
gurin ya kalleni amatsayin mayaudariya"


"ni bance banyarda dake ba amma meyasa kafin kije baki nemi shawarana ba sannan ga waya
me yahana ki ki kirashi"?

"Aunty kinfa san ank'wace mun waya taya zan kirashi sai dai kuskure na rashin fad'a maki da
banyi ba kiyi hak'uri dan Allah Aunty"

ajiyar zuciya Aunty tayi kafin tace "shikenan koma dai miye yariga da ya faru sai dai akiyayi
gaba"

"Insha Allahu Aunty ya zanyi kibawa Dady hak'uri nifa bance bazan aure zab'insa ba"

"uhm Bety kinfa san halin Dadynki kaifi d'aya ne tunda ya yanki wannan hukuncin ba makawa
kika k'i kowa ma zai iya had'aki dashi

ko auren ki da Fa'iz da kiga ya hak'ura dan dai shine yace ya hak'ura dan haka shawarar da zan
baki ki turo Al'amin d'in"

kad'a kai tayi ciki da gamsuwa sai dai aranta tarasa farin ciki zatayi ko bak'in ciki


"Aunty meyasa kike had'a kayanki"?

Aunty ta kawar da kanta gefe cikin rawar murya tace "Bety Dadynki ya *Saki ni*saboda yana
ganin na gaza gurin tarbiyarki"

Bety ta rungumi Aunty tare da fashewa da wani irin kuka cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa
inna ilaihi raji'un na shigesu ni Aisha ya zanyi?

Aunty dukan alkhairan da kekamun kin soni kin bani kulawar da uwa ke baiwar 'yarta tun ban
san kaina ba har zuwa wannan lokacin

na rasa sakayyar da zan maki sai na zamo silar mutuwar Aurenki

wayyo Aunty ki yafemun zanje nabawa Dady hak'uri ya janye *Sakin*"!

ta mik'e da sauri zata bar d'akin Aunty ta janyo ta jikinta

"kiyi hak'uri Bety baki da laifi aciki dama ko hakan bai faru ba lokacin barina gidannan yayi"

da mamaki Bety ta d'ago fuskarta tana kallon Aunty kafin tace "Aunty kamarya lokacin barinki
gidannan yayi"?

murmushi Aunty tayi wanda yafi kuka ciwo kafin tace "eh ina nufin Allah ya k'addarta rabuwar
mu kuma lokace yayi dan haka karki damu"

"Aa Aunty kiyi hak'uri dan Allah zan bawa Dady hak'uri dan Allah"

da k'yar Aunty ta lallasheta tabar maganar inda ta k'ara k'arfafa mata gwiuwa da ta aure Al'amin
shine miji mafe Alkhairi da tajima tana mata adu'a tasamu,

tana kuka tana taya Aunty had'a kayanta

lokacin da Aunty zata fita Bety d'akinta tashige tana kuka kamar ranta zai fita kacokan ta d'aura
laifin sakin Aunty akanta.


bayan tafiyan su Bety d'akinsa ya koma ya kwanta zuciyarsa ba dad'i adu'a yake tayi Allah yasa
kar wani abu ya sami Aishan sa

dan yaga yayanta yana da zafin rai wani b'angare na zuciyarsa yana ciki da zullumi da
tambayar ina zata tafe da take cewa bankwana tazo masa

haka yawuni cikin damuwa Allah Allah yake ayi la'asar ya tafe gurinta dan jin me kefaruwa.


Dady da tun fitar Aunty d'akin ya koma ya zauna kan kujera yana jin ba dad'i azuciyarsa lallai
hukuncin da yayiwa Zainab ba dai dai bane bai kyauta ba bai mata adalci ba haka yayita tariyu
zamansu da ita ko yaushe cikin kyautata masu take

dai dai da rana d'aya bai tab'a sauki hak'inta ko d'aya da yake kansa da ya shafe zaman
takewar aure ba

kansa yaji yana masa wani irin ciwo kamar zai rabu biyu haka ya janyo wayarsa ya kira Dadyn
Fa'iz

bayan sun gaisa Dadyn Fa'iz yace "Alhajin Allah yanzu nake shirin kiranka sai gashi ka kirani"

"hakane dama gami da maganar Fa'iz da Bety ne"

Dadyn Fa'iz yayi saurin katse shi yace "Fa'iz ya fad'amun komai karka damu muyi fatan Allah
yasa hakanne mafe Alkhairi

dama can ba matarsa bace mutum kuma baya auren matar da ba tasa ba amintarmu tana nan
basu suka had'amu ba ba kuma zasu rabamu ba"

cikin jin dad'i Dady yace "gaskiya naji dad'i sosai da ka fahimceni Allah yasa hakan yafi alkhairi"

daganan suka d'ura wata firar kafin daga bisani sukayi sallama.


Aunty tana fitowa ta d'auki motarta ta d'au hanyar zariya zuciyarta a cunkushi

sanda ta isa gida Mahaifiyarta ta tare ta da murna sai dai yanayin da taga Aunty yasa jikinta
yayi sanyi bayan sun gaisa Inna tace "Abu anya zuwannan na lafiya ne"?

Aunty tasa hannynta tana share hawayen da suka zubu mata cikin kuka Taiwan Inna bayanin
sakin da Dady yayi mata da dalilin Sakin sai dai ta b'oye mata gaskiyar zaman da sukayi da
Dady

Inna ta dinga tafa hannu tana "LA ilaha illallahu Mahammadu Rasulullahi S. A.W ni Fad'ima
naga Rasulu yanzu sabida Allah da Ma'aiki Alhaji bai saki ki da k'urciya ba sai yanzu da girma
yazo ya kuma ga k'asa yarufe idon Mahaifinki

akan laifin da 'yarsa tayi bake ba zai huce kanki ai shikenan Allah ba azzalumin bawa bane ki
kwantar da hankalinki karki sawa kanki damuwa Allah yasa hakan shi yafi zama alkhairi

tashi kije kiyi Sallah la'asar kizo kici abinci"

Aunty ta tashi ta nufi tsakar gida tana fad'in "Inna inasu Abulkhairi"

"suna iskamiya anjima kad'an zaki gansu".


zaune take akan darduma ta idar da Sallah la'asar tayi kuka harta godewa Allah shiguwar Dady
ne yasa ta saurin d'ago kanta tana duban k'ofa

zama yayi kan kujera fuskarsa sam ba annuri cikin tsoro tace "barka da wuni Dady"

"kiramun saurayin naki" yayi mata magana ba tare da ya amsa gaisuwarta ba

cikin kuka tace Dan Allah Dady kayi hak'..
katseta yayi cikin fad'a yace "zaki kirashi kokuwa sai na b'abb'allaki"?

cikin rawar jiki ta mik'i ta d'auko wayarta da ke ajiye kan madubi cikin sa'a tana kira number ta
shiga mik'awa Dady wayar tayi ta rakub'e gefe tana 'yan Matan hawayenta.

Al'amin da fitowarsa kenan daga masallaci yaga kiran Aisha abun ya bashi mamaki d'azun ta
fad'a masa yayanta ya kwace wayarta to miye zai kirashi ko cin mutunce zai masa na d'azun bai
ishe shi ba lallai kuwa idan hakane zaiyi da nasanin kiransa

da wannan tunanin ya d'aga kiran amsa Sallamar da Dady yayi masa yayi cikin ladabi dan jin
muryar babban mutum

Dady yace "kana magana da Mahaifin Aisha idan har da gaske kake inaso nan da k'arfe biyar
naganka tare da waliyanka koda minti d'aya ka k'ara akai zan d'aura da wani"

bai jira amsar Al'amin ba ya katsi wayar tare da cillamata wayar yana fad'in "kin dai ji abunda
nace idan ya k'ara minti d'aya ko waye zan d'aura aurenki da shi"

kifa kanta tayi akan gado tana kuka mai cin rai da danasanin biyewa zuciyarta zuwa gun Al'amin
gashi Dady yak'i fahimtarta

"Dady ina son Al'amin amma banso na aure shi ba da son ranka ba Dady"

ringing d'in wayarta ne ya katse mata tunani tana dubawa taga Al'amin d'aga kiran tayi sai dai
ta kasa magana sai shishik'ar kuka take

hakan ya matuk'ar d'aga masa hankali "Aisha na dan Allah ki taimake ni kiyi hak'uri ki daina
kukannan fad'amun me ya faru"?


cikin kuka ta masa bayanin abunda ya faru tun sanda akayi maganar auransu da Fa'iz da
dalilinta na zuwa gurinsa har zuwa abunda ya faru bayan dawowarta

"Innalillahi wa inna iIaihi raji'un Aishana kin aminci nazo adaura dani idan na rasaki komai ma
zai iya samuna"

kad'a kai tayi kamar tana gabansa tace "na amince Al'amin"

da zumud'i yace "nagode Aishana sai munzo" daganan ya kashi wayar

gida ya shiga Faruk ya tarar da shirin islamiya "Faruk me kakeyi har yanzu baka tafe islamiya

ba"?

"yaya harfa naje wani malamin mu ne yarasu yau akace baza azauna ba sai bayan kwana
ukku"

"ayya Allah ya jik'ansa da rahama da dukan musulmi amin ina Inna"

"bayan tafiyanka masallace mijin Aunty uwaliya yazo ya d'auketa"

cikin tashin hankali yace ina zasu" Faruk da ya tsorata da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login