Showing 15001 words to 18000 words out of 41150 words
Chapter 6 - Kar ka Gujeni Book Complete by Aisha Yabo Fulani .pdf
d'an iska mai lalata 'ya'yan mutane to bara kaji k'anwata tafi k'arfinka
tawuci ajinka idanma kwad'ayi ne da son abun duniya yasaka cusa kanka inda Allah bai kai ka
ba to tun wuri kaiwa kanka nasiha
kafita hanyar k'anwata idan ba haka ba wallahi tallahi ba kaiba kaf danginka kajanyo masu
masifa"!
"Uhm gaskiya ne ni talaka ne amma ba mai zuciyar kwad'ayi ba ba kuma mai nakasassar
zuciya ba k'anwarka naganta ina so
soyayya ta gaskiya ba dan na lalata mata rayuwa ba dan ba halina bane ba kuma zan fara kan
abunda nakewa k'auna ta fisabilillahi ba
dan haka wannan tunaninka ne kawai ban sota dan kud'inku ba, ban kuma b'oye mata ba
tayarda dani ahakan ta soni
dan haka maganganunka bazasu sa na daina sonta ba ko na *GUJETA* sai dai idan ita da
kanta tace bata yi dani
dole zan barta ba dan naso ba, sannan kai baka isa kamun abunda Allah bai nufi ya sameni ko
dangina ba"
cike da takaici Yaya Saif ya nufi bayan Al'amin zai janyota tayi saurin ja baya tana fad'in "dan
Allah Yaya kayi hak'uri kaje yanzu zandawo wallahi magana kawai zamuyi"
ta k'arasa maganar cikin kuka "Wallahi Bety idan bakizo muntafi ba ranki zai b'aci zan
b'abb'allaki fa dan kinga muna lallab'aki shine zaki nemi ki rainamu
akan wannan d'an iskan talakan ko"?
"wayyo Yaya pls kadaina zaginsa miye laifinsa dan Allah dan kawai ya soni shine laifinsa miye
banbancin talaka da mai kud'i duk fa d'aya ne agun Allah sai wanda yafi bautamasa shine ya
zarce talakan ko mai kud'i
kadaina wannan Yaya sam ba kyau kuma ni ba komai ya kawuni nan ba gobe zamu bar k'asar
bankwana kawai fa nazo muyi
dan Allah Yaya kabarni muyi magana dan Allah"
a fusace ya kaiwa bakinta bugu Al'amin yayi saurin janyota jikinsa hakan yasa bai sameta ba
cikin sanyi Al'amin yace "kayi hak'uri zata bika ba sai ka daketa ba"
yana gama fad'a ya rik'o hannunta suka fito d'akin sai da suka kai k'ofar gida yace "ina motar
taki"?
ta nuna masa da d'aya hannun sai da ta zauna yace "Aishana kiyi hak'uri kije gida anjima k'arfe
biyar na yamma zanzo amma sai dai ki fito
saboda naje mai gadinku yace ance karya kuma barin na shiga gashi kuma ba asamun wayarki
meyasa"?
kallonsa tayi kafin ta sunkuyar da kanta cikin muryar kuka tace "Yaya ya k'wace wayar kuma
au......
tsawar da Yaya Saif yayi matane ya hanata k'arasa maganar "Wallahi Bety idan baki bar
gurinnan ba ranki zai b'ace zansa a hallakar da wannan d'an iskan da yake hure maki kunne"!
da sauri ta rufe k'ofa tare da yimata key tabar Unguwar tana kuka kamar ranta zai fita.
"na dawo gareka ba dai kai d'an iska ba gaka talaka sai fad'in rai da nuna isa zaka san ka
tabka babban kuskure shiga gonar da ba taka ba"
yabar gurin afusace ya shiga motarsa suka bar Unguwar Fa'iz da tun faruwan al'amarin ya kasa
cewa komai tsabar takaici da kishi sun rufeshi
"dama rufeshi sukayi yarinya bashi take soba tana da wanda take so har d'akinsa take zuwa
lallai ai ko autar mata ce ya barta
dan atsarinsa bayada burin auren macen da bata sonsa dan baiga ribar hakanba da aurensa
ma sai tadinga huld'a da saurayin kai ina ba zaiyu ba dole ne ma nasan abunyi"
Saif ya d'an kalleshi kafin ya maida hankalinsa ga hanya yace "Fa'iz ka kwantar da hankalinka
kar wannan ya tayarma da hankali Bety bata isa tak'i aurenka ba
shikuma wannan d'an iskan yau zansa ayi masa hankali sai yayi nadamar da ko wani yaga zaiyi
soyayya da 'yar masu kud'i zai hana"!
Fa'iz murmushi yayi cikin takaice yace "Saif kenan meye laifinsa itafa takai kanta gurinsa bashi
ba dan haka idan dai dan nine karkayi masa komai dan Allah"
daga haka ba wanda ya saki cewa komai har suka isa gida kowa da kalar nazarin da yake.
Aunty ta shiga d'akin Bety da plate d'in abinci a hannunta ta tarar bata nan ajiyewa tayi tare da
zama kan kujera tana jiranta dan azaton ta tana band'aki
jin shirun yayi yawa yasa tayi tunanin lek'awa band'akin taga ko lafiya
_
tana turawa taga wayam ba kowa lamarin ya tsorata ta
ko ina na gidan ta duba bata ganta ba hakan yasa ta fito harabar gidan ta tambayi ma aikatan
aka tabbatar mata da anga fitarta.
haka ta koma d'akinta ta zauna tana tunanin inda Bety taje tana cikin jimamin Dady ya dawo
har zai wuce d'akinsa ya fasa ya nufi d'akin Bety ya tarar bata nan hakan yasa yayi sashin
Aunty
da sallamarsa ya shiga Aunty ta mik'i tsayi tai masa sannu da zuwa cikin ladabi
"ina Bety? naje d'akinta batanan"
cikin fad'uwar gaba tace "ta d'an fita nan amma ba jimawa zatayi ba "
ya fara magana cikin fad'a "saboda me zaki barta ta tafita bayan kinsan na hanata fita"
"kayi hak'uri wajan zainab taje"
fau yafice ba tare da ya saki cewa da ita komaiba
ajiyar zuciya tayi aranta tace "gara haka da dai tace dashi batasan fitarta ba bari zatayi zuwa
anjima tagani idan bata dawo da wuri ba sannan tasan abunyi"
maganar Dady tajiyo sama sama yasata fitowa taga me ke faruwa
Dady yana fitowa Babban Palo ya had'u da Bety ta shigo da gudu tana kuka cikin sauri ya
rik'ota suka zauna kan kujera yana tambayarta
"Bety lafiya kedawa waye ya tab'amun ke"?
lafewa tayi jikinsa tana cigaba da kukanta batari da tace dashi komai ba
hakan ya d'aga masa hankali matuk'a Allah yasa 'yar tasa ba gamu tayi ba
fitowar Aunty yayi dai dai da shiguwar su Yaya Saif
da sauri Dady yace "yawwa Saif zo ka tambayar mun ita abunda ke damunta tak'i tamun
magana sai kuka take"
zama yayi kafin yace Dady k'yaleta kukan rainin hankali ni kawai take agidan saurayinta
naganta dan na kurota shine take wannan kukan"
nan ya basu labrin abunda ya faru Dady ransa ya matuk'ar b'ace zuciyarsa ta rufe har baisan
sanda ya rufeta da duka ba da k'yar Aunty da Fa'iz suka k'waceta hannunsa fad'a yake sosai
"Aisha kincuceni kinci amanata tarbiyar da naginaki da ita kenan zuwa d'akin saurayi"!?
Bety da take jikin Aunty tana kuka tunda tae da wayonta Dady bai tab'a dukanta ba kai ita bata
tab'a sanin zafin duka ko fad'a ba sai akan wannan auren
sai dai maganganun Dady sunfi komai d'aga mata han Kali wanda yasata yin da nasanin
biyewa zuciyarta zuwa gurin Al'amin
duk da tasani bada wata mummunan manufa taje ba kamar yanda suke zato amma taya zata
fahimtar dasu?
maganar Fa'iz ce ta dawo da ita daga tunanin da take
"Dady ina Neman alfarma dan Allah dan Annabi kayi hak'uri kabarta ta aure wanda take so
idan dai dan nine wallahi na hak'ura kuma zanyiwa abbana bayani zai fahimta
karka zargi Bety da komai kuskurenta d'aya zuwa d'akinsa da tayi bayan wannan bana tunanin
da wani abu kayi hak'uri Dady ka fahimceni kakuma gafarce ni idan na b'atama rai"
daga haka bai saki cewa komaiba ya sunkuyar da Kansa k'asa saboda irin kallon da Dadyn ke
masa.
_tofa shin Dady zai amince kokuwa?í ¾í´” to kudai biyu 'yar mutan yabo Dan jin yanda zata
kasance_
_mai k'aunar Ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJENI*
*Aisha a yabo*
Fulani
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_
*80 to 90*
Gyaran murya Dady yayi kafin yace "ba zanga laifinka ba Fa'iz ba kuma zan tilastama ba zanyi
magana da Abbanka"
ya juyo da kallonsa ga Bety cikin fad'a yace "kin kyauta Aisha kin nuna ban isa dake ba ban isa
nasaki ko na hanaki ba shikenan sai ki turoman yaron yau inaso na ganshi
Saif kabata wayarta"
"haba Dady karka biyewa Bety yarinya ce sam bata san inda yake mata ciwo ba"
"Saif kayi abunda nace" cikin tashin hankali Bety ta matsa kusa dashi cikin muryar da taci kuka
tace "Dady kayi hak'uri kamun rai wallahi banje da wata manufa ba ko dan nak'iyin biyayya
gareka ba dan Allah Dady kayafe mun wallahi zan aur... tsawar da ya daka mata ne yasata
had'iye sauran maganar batare da ta shirya hakan ba
"bana buk'atar wata magana kiyi abunda nace idan ba haka ba wallahi kinji na rantse zan bada
ke sadaka ga kowaye"
da ganan ya tashi ya nufi d'akinsa yana fad'in "Zainab ki sameni d'aki"
Fa'iz mik'ewa yayi yabar falon cikin damuwa ya sani zaiji jiki na rashin Bety sai dai hakan da
yayi shine dai dai ba zai iya aurenta ya kasance gangan jikinta ne kad'ai atare dashi Zuciyarta
na gun wani ba zaiyu ba.
Aunty ta wuce d'akin Dady cikin fad'uwar gaba da tunanin me zai faru?.
Yaya Saif ya kai mata rank'washi aka wanda yasa tasaki k'ara cikin jin haushin ta yace "kika
kuskura kika nacewa auren fak'irinnan Allah dagani har Dady Zamu ciri hannunmu acikin
al'amurranki banza marar tunani yana talaka me yaci me ya baki
kirasa abun so sai talaka wanda idan ya samu na yau da k'yar tunananin inda zai samu na
gobe zaiyi"
fad'a sosai yayi mata kafin yaje ya d'auko mata wayar ya jefa mata ajiki yabar falon yanata meta
ita dai komai bata iya cewa dashi ba sai kukanta take oh dama ya lafiyar kura ballatana an
tab'ota
tarik'e wayar tana tunanin mafita "takira Al'amin kokuwa? idan kuma tak'i kiransa Dady zai
had'ata da kowa ma kai gara kawai takirashi da dai ahad'ata da wanin kuma wai sadaka tab"!
haka dai ta zauna tana sak'awa da warwarewa.
ahankali Aunty ta tura k'ofa yana tsayi abakin window ya goya hannayansa abaya yaba k'ofa
baya
ahankali ya fara magana ba tare da ya jiyo ba "Zainab abun da kika mun kin kyauta kenan? da
saninki Bety taje d'akin sauraye sannan nazo na tambayeki kimun k'arya idan 'yar da kika Haifa
ce zakiyi mata irin wannan tarbiyar amanar da na barmaki kenan"?
cikin rawar murya Aunty tace kayi hak'uri kuskurena d'aya da na b'oyema gaskiyar magana
Amma wallahi tallahi ban San fitar Bety ba nima dubawa nayi naga batanan
ban kuma b'oyema dan wata manufa ba sai dan gudun karkayi fad'a amma kasan bazan tab'a
cewa da Bety taje wani gun da zai iya zama illa ga rayuwarta ba
banci amana ba ba kuma zan tab'a ciba kasani"
jiyowa yayi suna fuskantar juna kafin yace "bazan tab'a yarda da wani zancinki ba domin tun
farko kin tabbatar mun da saninki ta fita
kin karya Alk'awarin da mukayiwa juna
ina so ayau d'innan ki bar gidannan na *SAKE KI SAKI D'AYA*duk da kin b'ata mun rai hakan
ba zaisa na manta alkhairan da kikayiwa yarana ba"
janyo wata 'yar akwati k'arama mai kyau ya mik'o mata "ga wannan kirak'i k'adarurin da ke ciki
zasu ishiki komai awannan rayuwar"
murmushin takaici tayi kafin tace "karik'i kayanka bana buk'ata amma kasani ni ban karya
alk'awari ba kaine ka karya alk'awari idan ka manta bara na tuna ma"
*BARI MU D'AN WAIWAYA BAYA KAD'AN*
zauni take kan gado fuskarta lullub'e da mayafi kuka take sosai tana tunani taya zata zauna da
Uban gidanta kuma mijin Momy wacce tarik'eta tamkar 'yar da ta Haifa,
shigowarsa ce tasa ta saurin sauka daga kan gado ta sunkuya cikin girmamawa tace dashi
"sannu da zuwa"
"yawwa" ya amsa bayan ya zauna gefen gado ya d'an kalleta kafin yayi gyaran murya yace
"Zainab ina so ki bani hankalinki nan muyi magana ta fahimta kinji"?
gyara zamanta tayi kan kafet cikin natsuwa tace "eh yallab'ai"
"kiyi hak'uri da maganar da zan fad'amaki magana ta gaskiya bazan iya zama dake amatsayin
mata ba,
ina maki kallon kamar yanda marigayiya tanemi na d'auke ki d'iya har yanzu ahakan na d'auke
ki,
na amince wa aurenki saboda ina so na rayu da yarana kema nasan saboda ba kyaso arabaku
kika amince,
wannan yasa na yanki hukuncin zamu zauna da juna kamar da ba tare da kowa ya sani ba,
duk lokacin da kikaso rabuwa da yaran ashiryi naki da na sallameki yaya kin amince"?
yayi mata tambayar yana mai zuba mata idanu
ko kad'an bataji haushin maganarsa ba dan tasan gaskiya ne ya fad'a hakan yayi mata dad'i
hannunta tasa tana mai share hawayen dake ta zarya afuskarta
batare da dogun nazari ba tace "ba komai na amince amma ina so kamun alfarmar barina
gidannan har sai ranar da Bety tayi aure aranar nayi alk'awarin zan barku"
cikin mamaki yace Zainab shekararki 15 Bety shekararta hud'u da 'yan watanne amma kike
maganar zaki zauna ba tare da abokin rayuwa ba tsawun wannan shekarun"?
"karka damu zan iya ai shiyasa na nemi hakan saboda ban san wace irin mata zaka aure ba kar
tazo ta k'untata masu aranar da Momy zata rasu kafin su tafi tabar mun amanar su Aisha ya
zama dole na rik'i wannan amanar duk rintsi" ta k'arasa maganar cikin shishshik'a kuka
ganin ta dage yasa ya bar maganar yayi mata saida safe
bayan fitarsa tayi shirin kwanciya hankalinta kwanci duk wani damuwa da zullumi ya gushe
azuciyarta taso ta d'auko Bety su kwana tare sai dai gudun tambayarta dalili yasa dole ta
hak'ura tayi barccin ta ita kad'ai.
kwanci yake tunani ya hanashi sakat anya yayiwa yarinyarnan adalci amma ya zaiyi dole ne
yayi wannan hukuncin Allah yagani baya jin sonta ba kuma zai iya cin amanar marigayiya ba ta
d'auki Zainab tamkar 'yar cikinta hakan yasa shima yake d'aukarta a wannan matsayin har gobe
bazai iya rayuwar aure da ita ba haka dai yayita tunani har barcci yayi awun gaba da shi.
tana matuk'ar kyautatawa su Bety k'auna ce take nuna masu tamkar ita ta haifesu Saif ne kawai
ke d'an bata matsala rashin kunya da tsiwar da yake mata yana damunta amma sam bata biye
masa tsakani da Allah take sonsu.
tana yawan ciyon Mara musamman lokacin al'adarta haka take daurewa har tayi taji sauk'i
batare da tabari kowa nagidan ya sani ba ko yaushe cikin azumi take
tsakanin ta da Dady kowa gaisuwa ne sai girkin da take masa idan yana gari ko yaushe zaka
ganta cikin hijabi.
iyaye da 'yan uwa kuwa tun suna damuwa da rashin haihuwarta har aka hak'ura aka dage da
adu'a sai dai suna matuk'ar tausayinta aganinsu gara shi yana da biyu itace dai ko d'aya bata
da
wannan yasa sanda yajewa iyayansa da zancin zai k'ara aure suka hanashi saboda suna son
Zainab suna tausayin rashin haihuwarta file ya hak'ura ba dan ya so ba.
*bayan shekara ukku*
Dady ya k'ara aure ba tare da Zainab da iyayansu sun sani ba 'yar nan Kaduna ce suna zaune
a malali yaransu hud'u
Farhan Safna da taci sunan Momyn Bety ana kiranta da (Ilham) sai Zainab da taci sunan Aunty
ana kiranta (Ihsan) sai auta Isma'il ko yaushe Mamy na damun Dady ya kaisu gun danginsa
kodan yaransu da kuma halin rayuwa
duk san da tamai maganar hak'uri yake bata zai kaisu sudai k'ara hak'uri. wannan kenan.
*ci gaban labari*
"ina fatan ka tuna dan haka ban karya alk'awari ba kaine dai ka karya alk'awari"
daga haka bata sake cewa komai ba tabar d'akin.
Bety da take zaune a inda Aunty ta barta cikin damuwa tama rasa tunanin yi shin farin cikin
samun Al'amin zatayi ko bak'in ciki saboda Al'amarin ya zo mata ba yanda taso ba, ba kuma
yanda ta zata ba
tana cikin wannan yanayin ne taga fitowar Aunty a hargitsi ta nufi d'akinta hakan ya matuk'ar
d'aga mata hankali tashi tayi da sauri tabi bayan Aunty.
_mai k'aunar Ku_
*Aisha A Yabo*
fulani
*KAR KA GUJENI*
*Aisha a yabo*
Fulani
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*
*#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*
_Wannan su ne shafukan mu da zaku dinga ziyarta dan neman nvl d'in mu. fatanmu Allah ya
baku ikon zuwa amen_
*80 to 90*
Gyaran murya Dady yayi kafin yace "ba zanga laifinka ba Fa'iz ba kuma zan tilastama ba zanyi
magana da Abbanka"
ya juyo da kallonsa ga Bety cikin fad'a yace "kin kyauta Aisha kin nuna ban isa dake ba ban isa
nasaki ko na hanaki ba shikenan sai ki turoman yaron yau inaso na ganshi
Saif kabata wayarta"
"haba