Showing 30001 words to 33000 words out of 50006 words
Chapter 11 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
Wata harara ta wanka masa tace "Ni? Allah ya tsareni, me zan yi da kai?"
Murmushi ne ya suɓuce masa tare da ɗan sunkuyar da kan shi, yo in ba haukan yarinyar nan
ba, shi ne za ta ce me za ta yi da shi? Ta dubeshi da kyau mana, ko ƴar uwarta Hadeeya ba ta
fishi jar fata ba duk da ta na mace, a haka ma dawowarsa ƙasar nan ne rana ta fara lalata masa
fata, sannan ya na da ilimi da kuɗi, to me take nema a jikin namiji? Da ba za ta samu a wurinsa
ba.
Hijabin da ke jikinta ya nuna da yatsa yace "Me ya sa ba kya cire wannan abun ko dan ki huta?"
Murguɗa masa baki tayi tace "Saboda shi ne mutumcina."
Kallon tuhuma ya mata yace "Me ye mutumcin gaba-ɗaya?"
Cikin ido ta kalleshi tace "Shi ne kimata."
Taɓe baki yayi yace "Me ye ita kimar ke nufi?"
Numfashi ta feso ta ƙanƙance ido tace "A wajena kimata ita ce madogarata."
Da mamaki na fasahar harshen yarinyar yace "Madogara? Me ye ita kuma?"
Ba tare da shayin komai ba tace "Aƙidata."
Tsareta ya yi da ido kamar ba zai yi magana, dan abun da ya fahimta ba za ta rasa abun faɗa
ba, sai kuma ya numfasa yace "Me aƙidarki ke nufi?"
"Addinina." Ta faɗa kamar dama jira take ya sauke maganar ita ta ɗauka, da mamakin amsarta
ta ƙarshe ya nunata daga sama har ƙasa yace "Idan na fahimce ki dai-dai kina so ki ce ke
karan-kan ki ke ce addinin?"
Da sauri ta girgiza kai tace "A'a, ba ni ba ce, nufina a nan shi ne, duk wani da yake amsa sunan
musulmi, to ya kamata q na ganinshi gaba-ɗayansa a ga musulunci, a tattare da musulunci
kuma akwai, imani da tauhidi."
Girgiza kai yayi yana murmushi yace "Maganarki nan fasa min kai take, na fahimci wasu
kalaman na ki amma ban gane wasu ba."
Rumgume hannayenta tayi a ƙirji tace "Ka yi imani da Allah?"
Cike da tabbaci yace "Sosai ma, ko shirka ban taɓa kwatanta yi ba."
Kallon fuskarshi tayi da ɗan jin ya birgeta ta wannan fannin sannan tace "Ka yi ƙoƙarin tsayawa
a kan wannan saiɗarar, dan laifin shirka shi ne laifin da Ubangiji ba ya gafartawa mai yi idan har
ya mutu bai daina ba, sannan ranar ƙiyama idan har ba'a samu da-idai da ƙwayar zarra na
shirka a aikin bawa ba, sannan aka samu sallarsa cikakkiya, to akwai yiwuwar ya zama ɗaya
daga cikin waɗanda Allah zai saka aljanna da rahamarsa ba tare da hisabi ba."
Wani kallo ya aikawa fuskarta mai cike da birgewa yace" Sallah..." Sai kuma ya sauke numfashi
ya ɗan sosa ƙeya yace" Zan yi ƙoƙarin tsayar da ita a kan lokacinta, babu sallan da ke kubce
min, matsalata ɗaya wasu lokuta sai lokacinta ya kusa fita ko ma ya fita na ke gabatar da ita."
Waro ido tayi tace" Subhanallah! Kasan kuwa illar da ke cikin yin hakan?"
Cike da rashin sanin babban abu ya ke aikatawa yace " Ai ina yi ba wai ba na yi bane, kawai
dai..."
Dakatar da shi tayi da cewa"...
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_13_
Dakatar da shi ta yi da cewa "Hakan ai babbar matsala ce, in har da gangan ka ke bari sallar sai
lokacinta ya wuce, to ya za ka ji idan aka ba ka tabbaci wannan sallar da ka yi ba a kan
lokacinta ba Allah ba ya karɓa?"
Ɗan buɗa baki ya yi da yanayin mamakin nan sai kuma ya yi murmushi yace" Danƙari, da an
samu matsala babba ai."
"Dan haka sai ka kiyaye." Jinjina mata kai yayi da fara'a yace "Zan kiyaye."
Ɗan murmushin yaƙe ta mishi ta raɓa za ta wuce, da kallo ya bita yace "Nagode."
Juyowa ta yi tace "Akan me fa?"
Da murmushi a fuskarshi yace "A kan komai ma."
Ɗaga girarenta tayi sama sannan ta yi shigewarta, sai da ya ga shigarta kaɗai ya kama
gabanshi shi ma ya na jin yarinyar na ƙara shiga gaba-ɗaya zuciyarsa, ruhinsa da ma gangar
jikinsa.
______________
Bayan sun gaisa sosai a tsanake ta fara da "Ƙawata, dama wata shawara na ke so mu yi da ke,
ban sani ba ko za ki yi amanna da abin da na zo miki da shi."
Duk da ba gabanta take ba amma fuskarta a sake tace "Haba ƙawata, ai tsakaninmu babu
haka, ki faɗa ko ma menene ni na san zan amince, saboda ra'ayinmu na zuwa ɗaya a mafi
yawancin lokuta."
Numfasawa amarya tayi tace "Hakane, dama Mu'awwaz ne ya nuna sha'awarsa ta son auren
Hameeda, shine na ce ya bari na fara tuntuɓarki da maganar, dan na san burinki a kan yaran
nan, ba yanzu ki ke so suyi aure ba har sai sun cimma wani matsayi na rayuwa, amma na ce ya
bari yanda mukayi sai ya ji."
Wani daɗi ne ya ziyarci Ardiya har saida ta dafe ƙirjinta ta waina ido tamkar ta na gaban mijinta
cike da farin ciki tace" Haba ƙawata, wannan abun arziki har sai kin nemi shawarata? Kai tsaye
fa kina iya turowa a nema masa aurenta, ai Mu'awwaz ɗana ne kamar yanda Hameeda ta ke
ƴarki, duk so na burina kuma in dai a kan ki ne ai zan iya ruguje shi, sannan fa karki manta
Mu'awwaz yana da ilimi sannan ya san mahimmancin boko da ribar da ke cikinta, ina da
tabbacin ba zai hana Hameeda ci gaba da karatunta ba."
Da farin ciki amarya tace"Tabbas haka ya ke ƙawata, ai ko bai tsaya mata ba ni mai taimaka ma
ta ce a kan karatunta har mu ga ta tsaya da ƙafafunta, kuma na ji daɗi sosai, hakan na nufin
zumuncinmu zai ɗore ta hanyar sake zama surukan juna."
Da haka sukayi alƙawarin sanar da mazajen na su idan suka dawo sukayi sallama kowace
ranta fess tamkar an mata bushara da aljanna, domin kuwa burikansu ne za su cika ta hanyar
haɗa auren nan na *ƙwarya* ta bi *ƙwarya*. Ardiya a ganinta nasararta ce kuma sa'ar ƴarta ce
samun namiji kamar Mu'awwaz, matashi mai matasan shekaru, ga kazar-kazar da birgewa, ga
shi kuma ɗan babban gida, a ko ina Hameeda ba za ta ji kunyar nuna mijinta ba musamman a
cikin ƙawaye.
Tana kwance kan doguwar kujera ta gama waya da Mamanta tana ɗan wasa da wayar Nafissa
ta fito daga madafa ta tsuguna gaban Hajia Rabi tace "Hajia na idar, ki kawo saƙon."
Fuskarta ba yabo ba fallasa ta jawo ƙaramar jakarta a gefenta tace "Yawwa, har kin gama
duka?"
"E." Ta faɗa a ladabce, kuɗi Hajia ta fito da su ta bata tana faɗin "Yawwa gashi, kuma dan Allah
ki yi sauri ki dawo, sannan ki shiga ɗakina akwai rigata wacce aka kawo ranar da ta yi yawa a
wuya, ki kai masa sai ya rage min ita."
"To Hajia." Ta faɗa tana miƙewa ta yi hanyar ɗakin, jim kaɗan ta fito hannunta riƙe da leda,
Saleema na ganin haka ta aje wayar ta tashi zaune tace "Mama zan iya zuwa tare da ita?"
Kallonta tayi ta kalli Saleema tace "Me ya sa za ki tafi tare da ita? Wajen mai ɗinki ne za ta je."
Amariraice tace "Mama na gaji da zaman ne ni kaɗai, kuma ai na ga ba ƙasa za ta tafi ba."
Ba wai dan ranta ya so ba tace "Shikenan, tashi ku tafi, amma kar ku jima." Dan ita a ganinta
ƴar aiki ba tsararta ba ce da za su fita har su jera tare a gansu. Cike da zumuɗi Saleema ta
shiga ɗakinsu ta ɗan fesa turare sannan ta ɗauki hijabinta kalar ruwan ƙasa mai hannayen roba
da hula mai kallabi, tsaf ta ɗaure abunta a baya inda a baya kuma har ƙasa ya ke ja idan ta na
tafiya saboda tsayi, fitowa tayi ba tare da ɓata lokaci ba suka kama hanya dreba ya ja su zuwa
shagon.
Ganin irin tafiyar da aka yi yasa Saleema kallon Nafissa tace "Wai yanzu tun daga can su Hajia
ke kawo ɗinki har nan?"
"E, ya yi nisa ne?" Nafissa ta faɗa tana kallonta, girgiza kai tayi tace "Gaskiya akwai nisa,
wannan ya za su yi idan mai ɗinkin ya saɓa musu alƙawari? Sai a yi ta kai da kawowa kenan?"
Dariya Nafissa ta yi tace "E to gaskiya sai na ce mi ki ba'a saɓa musu alƙawari, bai taɓa min
ɗinki ba bare na bayar da shaida, amma dai daga yanda Hajia babba da Hajia ƙarama suke sa
ni zuwa karɓo musu ɗinkinsu, ya tabbatar min da shi ɗin mai alƙawari ne, dan ban taɓa zuwa ya
ce bai ida ba, shiyasa ba na zuwa da fargabar abin da zan tarar."
Jinjina kai Saleema tayi ta ɗan maida dubanta ga titi. Dammmm! Ta ji gabanta ya yanke ya faɗi,
da sauri ta wara idonta a ƙofar da tunanin ko wani abu ne ke faruwa a wajen, sai dai ba abin da
ta gani kuma ba ta ga fuskar da ta sani ba, a hankali ta sulale ta jingina kanta a madubin ƙofar
ta na ci gaba da kallon hanya, a can ƙasan zuciyarta kuma a nutse ta ke jin gabanta na ci gaba
da bugawa zuciyarta kuma na harbawa a tsanake. Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta lumshe
ido tare da furta "Hasbunallahu wani'imal wakil, La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum mina
zalumin!
Daga cikin kwana dreban ya faka motar suka fito saboda rashin sarari a inda shagon yake,
hakan yasa suka ɗan tako a ƙafa suka tsallako titi, daf da titi shagon yake ga kuma samari da
ke zaune ƙofar shagon da alama ma har da maɗinka, amma a haka kuma gida na kallon shago
sai ƙaramin masallaci a gefen gidan, Nafissa ce ta kalli samarin da ke zaune tace "Sannunku."
"Yawwa Sannu." Suka amsa mata, ƙarasawa sukayi da sallama a bakunansu suka shiga ana
amsa musu. Ɗan tsayawa ta yi tana sake buɗa idonta dan tabbatarwa kanta abin da take gani,
tabbas dai shine tunda gashi shima ya mata kallon sani duk da ya ɗauke kanshi kamar wanda
aka tsorata, dogon bencin da ke cikin shagon ta zauna kamar yanda Nafisa ta zauna ta na faɗin
"Ina wuni malam Huzeifa."
Taushin muryarshi da yanda ya amsa ba wani sakin fuska da irin rahar nan ta samari ya sa ta
ɗan saci kallon fuskarshi, kan gemunshi ta sauke ido da ke baƙi-ƙirin ya masa kyau a fuska duk
da duhun fatarshi, ta na ji Nafissa na tambayar an ida, da sigar ban haƙuri yace "Ki ɗan yi
haƙuri kaɗan Nafissa, shi na ke ƙarasawa yanzu, idan akwai in da za ku je za ki iya tafiya sai ki
dawo."
"A'a zamu jira, ba in da za mu je." Ta faɗa tana gyara zamanta, jinjina kai ya yi yana rintse
idonshi da ƙarfi sosai, to fa a dole zuciyarshi da sheɗan ke son fizgar idonshi ya kalli yarinyar da
fitina ce kallonta a wurinshi, shiyasa ba ya so ya kalleta bare ya ji irin abin da ya ji ranar, dan ya
fahimci abun a jikin *wannan kaɗai ya ke ji*, dan suna haɗa ido farkon shigowarta gabanshi ya
faɗi tsikar jikinta ta yamutsa.
Shiru shagon ya ɗauka, Saleema ƙarewa komai na shagon kallon take, ji take ina ma tana ɗaya
daga cikin maɗinkan shagon nan, garin kalle-kallen har ta juyo da kanta ta sauke a kan shi ya
na ɗinkinshi a nutse da tela ta lantarki da ko ƙararta ba'a ji sosai. Ba tare da saninta ba ta saki
baki cike da birgewa take kallon yanda ya ke ɗinkin ta na jin kamar ta ƙwawa masa
*BAIWARSA*.
Tunda ya lura shi take kallo jikinshi ya ɗauki makyarkyata yake ji ina ma yana da ƙarfin halin da
zai iya kallonta yace "Dan Allah sarara min haka, kawar da idonki a kaina."
Sai dai jikinshi ɓari yake sosai ta yanda idonshi suka fara disashewa yana neman yin abin da
bai dace ba a ɗinkin mutane, Allah ne ya ji tausayinshi ta hanyar jefo ɗaya daga cikin samarin
da ke zaune ya na faɗin" Sannunku."
Da sauri ta juyo sai kuma ta ɗauke kanta jin Nafissa ta amsa masa har suna ɗan hira yasa ta
sake maida hankalinta gareshi ta na kallon aikin da yake, cike da tsokana matashin nan yace"
Ustaza ba gaisuwa? Da alama sarauniyar jan aji ce ko?"
A hankali ta juyo ta kalleshi sai kuma tace" Sannu." Kawar da kai tayi tana yatsina fuska, hakan
yasa matashin faɗin" Sai da na roƙa? Wai me yasa ƴan matan yanzu ba ku san gaishe da
mutane idan kun gansu?"
A take yanayinta ya nuna sam ba ta jin daɗin takuratan da yake neman yi, ta nutsu tana kallon
abin da ta jima ba ta yi ba kuma take kwaɗayi, amma sai wani canzen iska yake mata.
Cike da jin haushi tace "Ciwon kawunanmu ne mu ka fara sani, ta ya kawai za mu yi arhar da
maza zaune a titi za mu wuce sai mun gaishesu? A cikin can akwai Yayana ne? Ko akwai
Kawuna a ciki? Ko kuma Baffa na? Ba ko ɗaya? To a kan me sai na bayyanar da al'aurata
gareku dan na birgeku?"
Irin a ɗan zafafen nan ta ɗauke kanta daga gareshi, karaf! Suka haɗa ido da Huzeifa da ya
dakata da ɗinkin yana kallonta da mamakin dama akwai ƴan mata ma su irin wannan tunanin?
Ganin sun haɗa ido a tare suka kawar da dubansu kowa na ɗan ƙyafta ido, matashin ya kalla ya
wanka masa harara mai cike da gargaɗin da ya fahimta ya kuma juya ya fice a shagon.
Kallonshi Saleema ta sake yi cikin nutsatsiyar murya da taushi sosai tace "Malam, am... Na ce,
a nan kuna koyar da ɗinki ne?"
Kallon fuskarta ya yi yana mamakin ashe dai ta ganeshi? Ya ɗauka ta manta shi shiyasa shi ma
yayi kamar bai ganeta ba, a hankali ya fara girgiza mata kai sannan ya maida dubanshi ga
aikinshi yace "A'a, ba ma koyarwa."
Cikin sigar rarrashi tace "To amma ai kai ka iya ɗinki, ba za ka koya min ba? Ina son koyon ɗinki
sosai."
Wani *sahibin* kallo ya aika mata yace "Kin taɓa koya ne a wani waje?"
Cike da zumuɗi Saleema ta gyara zama tace "Na taɓa koya amma tun ina yarinya, amma kuma
ban manta abubuwan da na koya ba, sai dai shekara takwas kenan yanzu, ina buƙatar koyon
irin ɗinkin zamani."
Wani malalacin murmushi ya yi a ganinshi wannan ɗin mai kama da ƴaƴan masu kuɗi, ita ce za
ta koyi ɗinki? Ganin bai kulata ba ya ci gaba da abin da yake ya sa ta ƙara cewa "Malam, ka
faɗa min ko na wa ake biyanka sai na biya ni ma ka koya min?"
Kallonta ya sake yi ba ko ƙyaftawa, a kunyace ta sadda kanta ƙasa da mamakin kallon me yake
mata haka? Nan ma dai bai amsata ba, dan haka ta ɗaga idonta tare da wanka masa harara...
Sai dai tana fara hararan na shi na jin haushin ya ƙi kulata caraf suka haɗa ido, da sauri ta juya
kanta tana kallon titi cike da kunyar kamata da yayi.
Nafissa da tunda suka fara magana ba ta tanka mata ba cewa tayi "Haba malam Huzeifa, ba za
ka koya mata ba?"
A hankali ya girgiza kai ba tare da ya kalleta ba yace "Ba na koyawa mata ɗinki."
"To amma me yasa?" Cewar Saleema da sauri tana juyowa, satar kallonta yayi da tunanin wai
me zai yi da za ta fahimci ba ya son suna doguwar hira ne? Ta kasa gane akwai wani abun
al'ajabi a cikin nutsatsiyar muryarta wanda yake sa wa gaɓɓan jikinshi na amsawa zuciyarshi na
dokawa da sauri, tsoro ya ke kar ya biyeta su dinga zancen ne har ya kauce ƙa'ida. Ƙura masa
ido da tayi alamu ne na amsarshi take jira, a hankali ya ɗauke dubanshi daga gareta cikin
sanyayyar murya kamar wanda ba ya da lakka yace "...
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_14_
A hankali ya ɗauke dubanshi daga gareta cikin sanyayyar murya kamar wanda ba ya da lakka
yace "Haka kawai."
Ɗan taɓe baki tayi ta kalli Nafissa da ke faɗin "To amma ai za ka iya fara