Showing 42001 words to 45000 words out of 50006 words
Chapter 15 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
harara, har yaran ma duka ya
korasu sannan ya kalli Alhaji Yusuf yace "Bari na nuna maka wani abu game da ƴarka."
Kallon Saleema ya yi a tsanake yace "Matso nan Baby."
Miƙewa tayi ta koma kusa da shi ta zauna ƙasa, a nutse ya kalleta yace "Saleema, wannan
yarinyar Nafissa ta zo min da wata magana yanzu, amma ban yarda da ita ba saboda na san
ɗana..."
Gyara zamanshi ya yi yace "Ta faɗa min wai Yayanta ne ya ke so ya kashe min ɗana Mu'awwaz
saboda ya gano akwai wata mummunar alaƙa tsakaninshi da ita Nafissa, kuma ta tabbatar da
zai aikata saboda Yayan na ta ɗan daba ne, shi ne ta tsorata take sanar dani wai na yi wani abu
a kai, da fari ma ƙin faɗa ta yi sai da na yi da gaske ta faɗa min dalili, to magana ta gaskiya na
ɗan taɓa ganin abin da ya sani zargin Mu'awwaz, sai dai ba na jin zai iya neman ƴar aikin gidan
nan, to yanzu ke ya kike gani? Na tura Mu'awwaz wata ƙasar ne? Ko kuma na sanar da
hukuma su shiga tsakaninsu."
Da sauri Saleema da dama komai shirinta ne ta kalleshi tace" A'a Abba, kar ka yi ko ɗaya."
Da alamar tambaya ya tambayeta da" Me yasa?"
A nutse cike da hankali tace" Abba, ta min bayani akan Yayan nan na ta, ɗan shaye-shaye ne
da babu abin da yake sai zaman banza, ba ya da tunanin kansa bare ya yi tunanin rayuwar
wasu na shi, a ganina idan ka shigar da maganar wajen hukuma, to kamar mun daɓawa kanmu
wuƙa ne, dan shakka babu za'a san abin da Mu'awwaz ya aikata, idan kuma ka fitar da
Mu'awwaz ƙasar waje, to fa wannan ɗan daban zai iya fallasashi da tunanin ya gudu ne saboda
tsoron kar ya ɗauki fansa, idan kuma har maganar ta fito fili, to hukumar kare haƙƙin mata da
yara ƙanana za su iya saka ido a kan lamarin, idan haka ta faru kuma za'a ce a gudanar da
bincike, a ƙarshe kotu za ta shiga lamarin da ƙorafin Mu'awwaz na ɗaya daga cikin ma su cin
zarafin mata musamman marasa galihu."
A sanyaye sosai kamar za ta yi kuka tace" Abba, kuma ka san hukumar kare haƙƙin mata ba ta
wasa da lamari irin wannan, za su ɓata lokaci da kuɗi har ma da iko wajen ganin sun kayar da
mu wannan shari'ar, gwamnati ma ba ta ja da su Abba, dan su suna da goyon baya daga
turawa ne."
Ta ƙarashe maganar da sigar dake nuna tana son tsoratar da shi, ai kam a tsorace Alhaji Auwal
yace" Hakan na nufin mutumcin gidan nan zai zube kenan?"
Cikin raɗa kamar za ta yi dariya tace" Abba, ai har siyasarka ta shekaru ma lalacewa za ta yi,
abokan hamayya sun samu abun tsokanarku da shi, gaskiya a duba wata hanyar."
Riƙe haɓa Alhaji Auwal ya yi ya kalli Alhaji Yusuf da ya kafe Saleema da idanu da mamakin ina
duk ta san wannan abubuwan? Wa ya bata wannan hikimar? Cike da jimami yace" Ya ka ke
gani Alhaji Yusuf?"
Ɗauke idanu yayi daga Saleema yana ɗan matse fuska yace" Gaskiya ne Alhaji, a duba wata
hanyar daban."
Jinjina kai ya yi yace" To kenan ya kake gani?"
Kallon Saleema ya yi yace" Ke shiga ciki."
Jinjina kai tayi ta fara yunƙarawa a kasalance za ta bar wurin, inda shi kuma ya kalli Alhaji
Auwal yace" Ina ganin a kira yaron sai a bashi kuɗi ma su yawa da zai sa ya bar maganar
kawai, kuma ma yarinyar ai ba fyaɗe ya mata ba, da son ranta haka ya faru tunda ba
karan-kanta ta zo ta faɗa ba."
Da sauri Alhaji Auwal ya juya ga Saleema da ke tafiya a hankali tana jin me mahaifin na ta ke
faɗa, ta na ganin idan ɗaya daga cikinsu haka ta faru, shin haka zai faɗa? Kiranta ya yi yace"
Dawo zauna."
Dawowa ta yi ta zauna yana kallonta yace" Kin ji me mahaifinki ya faɗa, ke me kike tunani?"
Saida ta saci kallon mahaifinta dake ta hararenta tace" Abba, mu fara tabbatar da gaskiyar
maganar ta hanyar tuntuɓar Mu'awwaz."
Jinjina kai yayi yace" Wannan ma magana ce, amma yanzu ke mu ƙaddara an tuntuɓeshi kuma
gaskiya ne abin da aka faɗa, me ye mafitar?"
Ƴar dariya tayi ta girgiza kai tace" Abba, gaskiya a wautar kasancewata ƴar fari kuma mace mai
rauni, idan a ra'ayina ne sai na ce mu aura masa ita, kunga kenan ko da daga baya maganar ta
fito, to sai a ɗaukeshi kawai soyayya ce irin ta masu ƴanci, tunda dukansu sun haura shekara
sha takwas, dan idan kuɗi mu ka bashi hakan zai iya sa wa ya dinga yaudararmu ta hanyar
karɓan kuɗi lokaci lokaci (blackmail), kunga kenan babu hutu kuma ko yaushe dai asirin zai
tonu, amma idan ta zama matarshi babu mai ɗaga maganar."
Bubbuga cinya Alhaji Auwal ya yi ya washe baki yana dariya yace" Wannan yayi, wannan
shawara ta yi, hakan shi ne mafita."
Sai kuma ya kalli Alhaji Yusuf da mamaki ya sakashi zuba musu idanu kawai ya nuna mishi
Saleema yace" Ka gani ko, abinda na ke so ka fahimta kenan, wannan ita ce *BAIWAR
ƳARKA*."
Kallonta yayi yace" Tashi ki shiga ciki Baby, amma zan fara shawara da Baba na ji me yake gani
game da hakan, dan yanzu bana komai sai da shawararshi."
Murmushi ta saki ta miƙe kawai dan ta san ta wajen Papi ma ba za'a samu matsala ba, dan ta
gama da shi tun kafin ma ta kitsawa Nafissa abin da za ta yi.
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_17_
Tunda Papi ya fara magana bayan sun faɗa masa abin da ke faruwa Abban Saleema ke
kallonshi kamar a tsorace, to sak shawarar da ƴar ƙaramar ƴarsa ta bayar shi ma yake maimaita
duk da ba su faɗa masa sun tattauna da kowa ba, har sai da Alhaji Auwal ya taɓoshi yace "Ka
gani ko, ya kamata ka saka ido akan yarinyar nan, tunda ta zo gidan nan abubuwa masu kyau
ke faruwa, sannan rayuwata da ta iyalina ta fara hawa kan saiti, wallahi babbar *kadara* Allah
ya baka, ka kula da ita yanda ya dace, idan Allah yasa ba ta cikin wanda za su ci moriyar boko,
to ka tambayeta abin da za ta iya yi bayan wannan, za ka sha mamakin yarinyar nan idan na
faɗa maka watarana ni da kai za ta iya yi mana alfarmar da duk ikonmu da iliminmu ba za su
sama mana ita ba."
Maida dubanshi yayi ga Papi yace" Baba, tunda kai ma abin da ka gani kenan, ina ga anjima sai
mu je gidansu yarinyar, ko ba komai ni a ganina ya kamata Mu'awwaz ya shiga hankalinshi, dan
abin da yarinyar ta zo da shi ya tabbatar min da zargina a kan shi, Baba kamar Mu'awwaz na
kamashi da kororn roba (comdom) a motarshi, amma da na yi magana ya dinga min
kame-kame, yanzu kam na yarda da abin da ke faruwa a gidan nan, tunda shi ya lalata mata
rayuwa, to shi ya kamata ya aureta ko ba ya so, idan ta auri wani a haka za ta iya fuskantar
tsananin rayuwa da ƙiyayya, idan mun yi sa'a auren ya yi ƙarko to za ta rayu cikin tsangwama,
amma idan shi ne da ya fara, bai da bakin aibatata dan shi ya fita lalacewa."
Kallon Alhaji Yusuf ya yi dake tunani kan abin da Alhaji Auwal ya faɗa masa, a ganinshi me ye
ya kamata a ce kamar Saleema na so bayan karatu? Ai sai dai in soyayya take, ko kuma aure
take so? A gaskiya ba ya jin zai iya taimaka mata da komai in dai ba abin da ya shafi karatu ba,
to me ya fi ilimi a duniyar nan? Idan ba ka da ilimin nan na boko wani baƙauye ka ke zama,
ƙaramin misali sau tari zai yi magana da yaran da harshen faransanci su mayar mi shi, amma
ita ko ya yi niyyar yi mata sai ya dakata dan ya san ba za ta san me ya ce ba bare ya samu abin
da yake so. Dafashi Alhaji Auwal ya yi yace "Muje ko?"
Ɗan zabura ya yi sannan ya miƙe yana kallon Papi yace "Baba sai an jima."
Da haka suka fita farfajiyar Alhaji Yusuf na faɗin "Yanzu sai yaushe za'a turo min yaran? Ina
buƙatarsu a gidan nan wallahi, gaba ɗaya mun yi kewarsu."
Nauyayyar ajiyar zuciya Alhaji Auwal ya sauke yace "Ka yi ƙoƙari ka sama musu ƙannai mana,
ka ga fa duk sun zama ƴan mata nan gaba kaɗan aurar da su za ka yi."
Murmushi ya yi yana shafa wuyanshi yace "Alhaji ai... Ina ga sun isa haka, dama namiji ne
muke ta fatan Allah ya bamu, kuma na fi so ya fito daga wajen mahaifiyar Saleema, amma Allah
bai nufa ba har yanzu."
Murmushi Alhaji Auwal ya yi yace "Da alama kai kanka ka fi yarda da tarbiyar da Safiya ta ke ba
wa na ta yaran?"
Sadda kanshi yayi ƙasa bai ce komai ba, murmushi Alhaji Auwal ya sake yi yace "Shikenan ba
komai, zan turosu da yamma, akwai tsarabar da nake son haɗa musu ne, sannan da dare zan
zo gidan na ka akwai maganar da na ke so muyi da kai a kan ita Saleema da kuma Hameeda."
Da sauri ya kalleshi yace "Lafiya dai ko? Ba wani abu sukayi ba?"
Girgiza kai yayi yace "Ba abin da suka aikata, idan na zo za ka ji ko menene."
Jinjina kai yayi yace "Shikenan Alhaji, Allah kaimu."
Musabaha sukayi ya bar gidan da tunanin wace magana kuma zai zo mishi da ita a kan
Hameeda da Saleema? Da haka ya isa gida ya shaida ma Safiya Saleema ba ta samu ba
kamar dai yanda tun farko ya je makarantar ya dubo musu, saida ta yi ƙwalla na rashin jin daɗi
da fatan Allah ya nuna mata ilimin da ke cikin hakan.
Idar da sallah azahar ɗinta kenan ta samu Hajia babba tace "Mama, dan Allah wayarku za ku
ara min na kira Mamana."
Da fara'a ta nuna mata wayar da ke kan gado tace "Gata nan, idan kin ida kuma sai ki faɗawa
su Hadeeya su shirya, Alhaji ya ce zaku fita tare siyayya."
"To Mama." Ta faɗa a ladabce tana ɗaukar wayar, fitowa tayi daga ɗakin tana ɗora wayar a
kunne, jim kaɗan Mamanta ta ɗauka suka gaisa a tsanake, ɗorawa tayi da "Mama lambar
Khairat za ki duba min a wayarki, ina so zan yi magana da ita."
Numfashi Safiya ta sauke har tana jin sautinshi kafin tace "Shikenan, amma me zai hana ki bari
har ki dawo, tunda anjima za ku zo."
A shagwaɓe tace "Mama, magana ce ta gaggawa, kwana huɗu ya rage saukar makaranta, ina
so na tambayeta wani abu ne."
"Shikenan." Ta faɗa tana cewa "Bari na duba na gani."
Har za ta kashe wayar Saleema ta yi saurin cewa "Mama."
Dakatawa tayi tace "Ina jinki."
Cikin ladabi tace "Abba bai miki faɗa ba a kan rashin samun jarabawata?"
Murmushi Safiya tayi tace "Bai yi ba Hajia, dake tun jiya ma kwance na ke ban da lafiya, amma
yanzu da sauƙi."
Hankali tashe Saleema tace "Ayya! Mama baki da lafiya, ki yi haƙuri jiya ban kiraki ba, ya jikin
na ki?"
A tausashe tace "Da sauƙi sosai Saleema, kuma har da rashinki a kusa dani, amma yau na ji
ƙarfi sosai da aka ce za ku dawo."
Cike da tausayin mahaifiyar ta ta tace "Zan zo Mama, shiyasa nake ta miki addu'a Allah ya sa ki
min ƙane, ko hakan zai sa ki sassauta soyayyarki a kaina."
Muryarta ɗauke da sautin jimami da rawar murya tace "To ya na iya Saleema, ke kaɗai Allah ya
bani, dole na tattara duka soyayyata na ɗora a kan ki, idan so samuna ne Saleema mahaifinki
ya miki aure tun yanzu, ta hakane zan saka ran ganin jikoki daga gareki."
Kunya ce ta kamata kamar tana gabanta, rufe fuska tayi da tafin hannunta ɗay tace "Kai Mama,
dan Allah ki daina ni bana so."
Safiya ma murmushi tayi daga inda take tace "To shikenan na daina, amma idan kika zo zamuyi
maganar dan ki tabbatar ina buƙatar hakan daga gareki."
Ɗan matse bakinta tayi tace "To Mama, karki manta lambar."
"To." Ta faɗa tana kashe wayar dan turo mata lambar, ƙarasawa tayi ga kujera ta zauna tana
jiran shigowar saƙo, kamar an ce ɗaga kanki kalli ƙofa sai kal suka haɗa idanu ita da Mu'awwaz
dake shigowa falon da sauri kuma da alamar ɓaci rai da tashin hankali. Kai tsaye ita ya nufo da
mugun sauri, sai da ya zo gabanta ya tsaya, juyawa ya yi dama da hauni ya ga ba kowa sai ita
kaɗai, maida dubnshi yayi gareta yace "Ke, me kika faɗawa Abbana?"
Wani kallo da take jifanshi da shi ƙasa da sama kamar ta ga abun ƙyama, ƙarshe ma ɗauke kai
tayi ta taɓe baki tace "Me ya ce masa na faɗa mi shi?"
Sunkuyowa ya yi kamar zai yi ruku'u yace "Na tabbata akwai abin da kika faɗa masa, yanzu
yake tambayata wai me ye tsakanina da Nafissa."
Kallonshi tayi ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya tace "In tambayeka mana? Me yasa ka min ƙarya a
waccen ranar?"
Rarraba idanu yayi yace "Ƙarya kuma? Yaushe na miki ƙarya?"
Nunashi tayi da yatsa tace "Ranar ka faɗa min shi ne farko, ashe wata uku kenan ka na anfanar
ƴar mutane kamar wata matarka, yanzu ka ƙaddara kai ne mijinta ka sameta a haka, ya za ka
ji?"
Taɓe baki yayi ya yatsina fuska cike da shaƙiyanci yace "Sam, ki ma daina kwatanta ƙazamar
can da zamowa matata, kuma abin da ya faru ai biyanta na ke, ba dole na mata ba."
Cike da takaici Saleema ta miƙe tsaye tana riƙe wayar hannunta da kyau wacce ta ji shigowar
saƙo tana kallonshi tace "Ka sani alƙawarin Allah ba ya tashi, wallahi kai ba ka isa ka lalata
rayuwar ƴan mata ba son ranka, sannan idan ka tashi aure kace kamila nutsatsiya ka ke
buƙata, dole ka girbi abin da ka shuka, ɓarnar da ka fara kuma kai ne za ka ƙarasata."
Sama da ƙasa ta dalla masa harara ta juya za ta bar wurin, cak ta tsaya saboda idanu da suka
haɗa da Mu'az na tsaye a bayansu, ganinshi tsaye ya sa Mu'awwaz shiga taitayinshi ya fara
sadda kai ƙasa yana kame-kame da sosa ƙeya.
Haɗe fuska ta sake yi ta ɗaga ƙafa da niyyar wucewa ta barsu, sai kuma Mu'az da fuskarshi ta
nuna alamar tashin hankali ya fara takowa da sauri yana nufota, irin yanda yake tahowa
gabaɗaya sai take ganin kar dai ya rumgumeta, baya ta fara ja a hankali amma ya na ci gaba
da nufota, ba tare da sani ba ta kai wa Mu'awwaz karo a bayanta da sauri ta juya ta kalleshi, sai
kuma ta juyo a hassale inda Mu'az yake cike da ɓacin rai tace "Mu'az wai me ye haka? Ka na
l..."
Nuna mata Mu'awwaz ya yi fuskarshi ɗauke da fushi yace "Me ye tsakaninki da wannan yaron?"
Da mamakin tambayarshi ta wara idanunta kaɗan a saman fuskarshi tace "Kamar ya me ye
tsakaninmu? Me ka gan..."
Tsawar da ya daka mata ta hanyar nunata da yatsa yace "Ke!!!" Ya sa ta ruf da bakinta ta rintse
ido, sai kuma ya shaƙo wuyan rigar Mu'awwaz ya fincikoshi gabanshi yana kallonshi yace "Me
ye tsakaninka da matata?"
Turnuƙe fuska Mu'awwaz ya yi yana son ƙwatar kansa yace "Ni ba komai tsakanina da ita,
magana kawai muke."
"A kan me kuke maganar?" Ya faɗa a tsawace, Saleema da ta koma gefe tana kallonsu ce tace
"Amma ai bai shafeka ba."
Gam-gam! Ya sake matse wuyan rigar Mu'awwaz bayan ya kalleta sannan ya kalleshi yace "Me
ka ke faɗa mata?"
Cikin jin haushi Mu'awwaz yace "Wai me ye haka? Na faɗa maka ba komai, me zan mata ne a
tunaninka?"
Cikin ɓacin rai yace "Saboda na san halinka, na san duk iskancin da ka ke a garin nan, zuba
maka idanu na yi kayi saboda rayuwarka, amma ka ga wannan?"
Ya nuna masa Saleema dake gefe sannan ya ci gaba da cewa "Matata ce, wannan ta fi ƙarfin
ka mata iskanci Mu'awwaz, wallahi idan ka kwatanta yin haka sai na fizge abin da ka ke taƙama
da shi a jikinka wajen faɗawa ƴaƴan mutane."
Hankaɗashi ya yi da ƙarfi har saida ya faɗa kan kujera, har zai juya sai kuma ya sake juyowa da
ƙarfi ya sake fincikoshi ya miƙar da shi tsaye, taɓe masa baki ya yi ya ɗan matsa fuskarshi sosai
kusanshi ya shinshina bakinshi har zuwa wuyanshi, Mu'awwaz na ganin ya fara shinshinarshi
ya fara sissine kai a tsorace, da maɗaukakin mamaki Mu'az ya kalleshi sosai yace "Mu'awwaz
sigari ka fara sha?"
Da sauri ya girgiza kai yace "A'a wallahi."
Sakin wuyan rigarshi ya yi tare da fara