Showing 21001 words to 24000 words out of 50006 words

Chapter 8 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf

30 Mar 2025

6150


Da sauri ya miƙe ya fita ƙofar ɗakin ya tsaya, jim kaɗan ta fito sam rikicewa ya sa ta manta ba ta
fito da hijabi ba sai hular dake kanta kawai mu raga-raga irin ta bacci, sa'arta ɗaya kayan a sake
suke basu fito da surarta ba.

Tsayawa ta yi jikin bango ta na satar kallonshi, ita wallahi kunyar kallonshi ma take ji, amma shi
da alama ba haka ba tunda har ya zo inda ta ke, ɗan matsowa ya yi kusanta yace "Saleee.."

Ba ta bari ya ƙarasa ba ta ja baya tace "Ka ga ka faɗa min komai daga nan."

Murmushi ya yi ya ɗan ƙarewa surarta kallo, to ai kayan da ke jikinta wanda bai san mace ba ne
kawai ba zai fahimci irin kayan alatun da ke ɓoye a cikin suturar ba, amma shi da ya gama
sanin sirrin ya gama hango komai, cikin sakin fuska yace" Saleema, abunda kika gani ɗazu na
ke so ki manta dan Allah, sam ba abinda kike tunani bane, kuskure ne wallahi kula jiya ne ya
fara faruwa, amma na miki alƙawarin ba zai sake faruwa ba, kuma dan Allah ki min alƙawarin ba
za ki faɗa ma kowa ba?"

Wani kallo ta jefo masa da mamakin kalamansa tace" Kuskure? Mu'awwaz zina ka kira
kuskure? Kasan kywa da Allah ma cewa ya yi karmu kusanceta bare har mu je ga inda take, kai
ka je kusa da ita kuma ka abka, amma za ka ce kuskure?"

Girgiza kai tayi cike da takaici ta sake kallonshi tace"...



*Allah ya na tsare duk wanda ya kamalta kare kanshi daga aikata alfasha.*



*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍
*BAIWATA*
‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍‍❤️‍



*NA*


_SAMIRA HAROUNA_


*SADAUKARWA GA*


*AHALINA*



*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)* ��
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️


_Bismillahir rahamanir rahim_


_10_

Girgiza kai tayi cike da takaici ta sake kallonshi tace "Mu'awwaz abunda ka aikata zunubi ne
babba, sai dai har yanzu kana da damar tuba a wajen Allah, game da ni kuma kar ka ɗaga
hankalinka, ba zan tona abinda Allah ma ya rufe ba, ni ma kuma ina so ya rufa min asiri
duniyata da lahirata, na maka alƙawarin babu wanda zai ji wannan maganar, amma fa idan ka yi
alƙawarin kai ma na farko kenan kuma na ƙarshe."

Cike da yaudara yace" Na miki alƙawari Saleema, na farko kenan kuma na ƙarshe, wallahi ba
zan sake ba."

Jinjina kai tayi tace" Shikenan, Allah ya sa."

Raɓashi tayi ta wuce tana faɗin" Sai da safe." Da kallo ya bi bayanta yana ɗan taune leɓenshi
na ƙasa, abunda zuciyarshi ke raya mishi shine" Lokacin da ka san wata a ranar ka ke ganin
wata sabuwar halittar."

Murmusawa kawai yayi ya sauka daga matakalar ya kama hanyar ɗakinshi da tunanin ba ma
zai iya da Saleema ba, ba wai dan ta fi ƙarfinshi ba, sai dan gani yake ko aura masa ita aka yi
wannan za ta fi ƙarfin iyawarshi saboda suffarta, amma kuma wani ɓangare na zuciyar nuna
masa yake zai iya tunda dai mace ce.


*Washe Gari*



Kamar daga sama ta ji ana sallame salla, a zabure ta tashi zaune ta na rarraba ido, dubanta ta
kai ga agogo dan ganin lokaci, sai dai inda agogon take babu haske sosai bare ta fahimci,
hannu ta kai ta ɗauki wayar Hameeda ta duba, rufe baki tayi cike da rashin jin daɗi tace "Kenan
dai sallah ce aka idar?"
Da sauri ta aje wayar ta sauko a gadon tana daddaɓa Hameeda, a ƙala sai da ta daddaɓata sau
biyar kafin ta motsa tana faɗin "Ummm! Wai me ye?"

Da sauri tace "Ki tashi har an gama sallah."

Ta na gama faɗin haka ta nufi ban ɗaki dan rabon da ta tuna ranar da ta rasa sallah irin haka
har ta manta, ma fi yawan lokuta dama Mamanta ke tashinta daga bacci, sauran lokuta kuma ita
ke tashi da kanta da taimakon wayar Mamanta, juyowa tayi ta kalli Hameeda da ta sake gyara
kwanciyarta tace "Dan Allah ki tashi Hameeda, ki tashe su suma su yi sallah."

Shigewa ban-ɗakin ta yi ta gabatar da abinda za ta yi ta fito a gaggauce, yanda ta barta haka ta
sameta, ganin za ta ɓata lokaci wajen tashinsu ita ta makara su su rasa yasa kawai ta canza
kayanta ta kabarta sallarta, duk da farilla ce a kanta yanzu, amma saida ta fara yin raka'atanil
fijir saboda ta ji fatawar da aka ce indai ka saba yin raka'a biyu kafin fitowar alfijir, to ba laifi idan
wani dalili ya sa sallah ta kubce maka ka yi kafin ka yi ta farilla, har ta idar da sallata su
Hadeeya ba su motsa ba, cike da takaici ta miƙe ta koma ban-ɗakin ta ɗauko ƙaramar buta da
ruwa a ciki, dan su ne kaɗai za su iya tashinsu, ta na zuwa kam ɗaya bayan ɗaya ta dinga
watsa musu suna tashi a zabure kamar waɗanda aka firgita.

Cike da tsiwa da rashin kirki Ummee tace "Malama me ye haka? Wannan wane irin jahilci ne?
Ya mutane suna bacci za ki tashesu da ruwa? Ba ki da hankali ne?"

Ɗan cije leɓe Saleema ta yi ta lumshe idonta, hakan ya bata damar haɗe abunda ke ranta kafin
ta buɗe ta kalleta tace "Ku yi sallah, lokaci na wucewa."

Hadeeya ce tace "Saboda hakane ki ka tashemu? Dan baki san darajar ɗan adam ba."

Da alamu irin na ba ta jin daɗin maganar ranta kuma ya fara ɓacewa ta kawar da kanta kaɗan
tace "Da sallah ku ka je kuka gabatar ya fi muku alkairi."

Juyawa tayi tana cire hijabinta Ummee tace "An ƙi a yi sallar to, dole n..."

Fauuuu! Cikin zafin nama Saleema ta kashe fuskarta da mari, a kiɗime Ummee ta dafe kunci
tana kallon Saleema, Hadeeya da Hameeda ma a tsorace da kuma mamaki suke kallon
Saleema, yo ko su dake ƙannenta ba ta taɓa marin ɗaya daga cikinsu ba, hasalima ko faɗa irin
wannan na yara ba su cika yi ba. Girgiza kai Saleema tayi cikin jin haushi tace "Kin gani, kin
hassalani, kina ƴar musulma ne za ki furta wannan kalmar? Kin kuwa san hukuncinki a wannan
lokacin?"

Ummee da takaici ya gama kasheta a mugun haukace ta nuna kanta tace "Ni kika mara?"

A tausashe ka rantse ba ita ce ta mareta ba tace "An mareki, ki rama mana."

A harzuƙe Ummee ta sauko daga kan gadon ta yi hanyar fita tana faɗin "Na zan rama da kaina
ba, amma zan kira wanda zai rama min."

Taɓe baki Saleema tayi da tunanin Allah yasa ma rayuka su ɓace ta samu damar tafiyarta daga
wannan gida mai cike da kuraye ta ko ina, wa ya sani ma ko gado sukayi? A nutse ta gyara
ɗaurin ɗan-kwalin doguwar rigar da ta saka ta jawo silifas ɗinta ta saka, ta kala hanya za ta fita
ta juyo ta kalli su Hadeeya da har yanzu ke kallon kamar ba sa hayyacinsu tace "Sallar fa?"
Da sauri Hameeda ta sauko daga gadon ta nufi ban-ɗakin da alamar ta tsorata, Hadeeya kula

saida ta murguɗa baki kafin ta sauko ta nufi ban-ɗakin ta tsaya tana jiran fitowar Hameeda.
Murmushi tayi da ke nuna "Ku shiga hankalinku tun wuri."

Za ta fita a ɗakin amarya ta banko kai cike da masifa hannunta riƙe da hannun Ummee, a
bayanta kuma Alhaji Auwal ne da Hajia babba a gefenshi.

Kallon kallo suka dinga yi kafin amarya ta nuna Saleema tace "Ke! A kan wane dalili ki ka marar
min ƴa?"

Saleema dake mamakin ganin yanayinsu dukansu, kayan da ke jikinsu bai nuna alamar su
kansu sun yi sallah ba, dama-dama ma Hajia babba da alamar ruwa a jikinta, wataƙila alwala ta
yi dan ko hular kanta bata ɗora dai-dai ba, cike da kunya ta kalli amaryar a ladabce tace "Aunty,
sallah na tashesu su yi ba su tashi ba, shi ne ita ta ke faɗin wai an ƙi a yi sallar, shiyasa na
mareta."

Da ɗumbin mamaki amarya tace "Shiyasa kika mareta? Ke baki san fuska daraja ne da ita ba?
Kawai sai ki mareta dan ta ce an ƙi."

Da mamaki Saleema ta kalleta tace "Fuskar ce ke da daraja? Wa ya faɗa?"

Cike da sababi amarya tace "Ai ko a wa'azi ana faɗa cewa babu kyau dukan mace a fuska
saboda tana da daraja."

Wani ɗan murmushi Saleema tayi cike da raha tace "To aunty ai wanda ya ba fuskar daraja shi
ne kuma ya ce shi kaɗai yake so a turmusa fuskar nan ƙasa dominshi, kenan ya dace ta ce ba
za ta yi ba?"

A hassale amarya ta sake nunota da yatsa tace "Ke Saleema! Tunda kika zo gidan nan dama
na fahimci wani tsageran iskanci kike ji, to ni bana son irin haka, ki tsaya a matsayinki kawai,
amma ya za ki zo gidan uban yarinya kuma ki mareta, ina aka taɓa haka?"

Gyara tsayuwa Alhaji Auwal yayi wanda da farko jikinshi ne yayi sanyi, duba da an mari ƴarsa
akan ba ta yi sallah ba, to ya kenan shi idan ta ji bai tashi ba sai kukan Ummee ne ya tasheshi
shi da uwar Ummeen? Cikin nutsuwa ya kalli Ummee yace" Ke je kiyi sallah."

Sai kuma ya kalli Saleema yace" Shikenan ya wuce, kowa ta je ta yi sallah."

Cike da damuwa Saleema tace" Ni na yi sallah Abba, amma dai ka faɗa musu su dinga tsayar
da sallah a kan lokacinta, kamar Ummee da su Hadeeya idan aka umarcesu suyi sallah su ka ƙi
kuma ba tare da wani uziri ba, sannan sun yarda babu abun bauta da gaskiya sai Allah, kuma
Annabi Muhammad Manzon Allah ne, aka tabbatar sun yarda da duka shika-shikan musulunci,
to fa wasu suna ganin kashesu za'ayi ta hanyar cire musu kai, wasu kuma suna ganin a'a za'a
jinkirta musu ne su yi sallar sannan ya kashesu..."

Tausasa murya tayi sosai sannan tace" Abba, yanzu duk lamarin da aka tanadar wa wannan
hukuncin bai kamata mu riƙeshi iya ƙarfinmu ba? Manyan Malamai magabata akwai masu
fahimtar wanda duk ya bar sallah ta kubce masa da-gangan to ya zama kafiri, idan har zai yi
sallah ta gaba ko ya ranka wannan sallar to a ganinsu sai an kuma bashi kalmar shahada, inda
wasu malaman ke ganin a'a ba ka kafirta ba, sai dai ko kayi sallar ba lallai ubangiji ya amsheta
ba saboda kayi kan lokacinta ba, dan haka wasu suke ganin kar ma kayi shi ya fi."

Raunana murya tayi kamar za ta fashe da kuka tace" Ta ya bayan na san wannan zan zuba ma
ƴan uwana ido suyi wasa da sallah, bayan dukaninmu nan mun san ita ce kawai ta bambamta
mu da kafiri, indiyawa su na azumi dan buƙatunsu da al'adunsu, mu ma musulmi munayi, krista
suna raba dukiyarsu ga mabuƙata, akwai daga cikin waɗanda ba su da addini da suke zuwa
ziyarar ɗakin Allah, imma dan buƙatarsu ko kuma ganin al'ajabin wurin da ɗaukar rahoto,
sannan kafirai dayawa sun yarda akwai Allah kuma shi ya haliccesu kamar dai mu, sannan sun
yarda Annabi Manzonsa ne, imani da shi ne kawai ba su yi ba, to ku faɗa min a nan me ya
rabamu da su? Sallah ce kawai ko arne ya ga mai yin ta zai sa wannan musulmi ba tare da ya
yi tambaya ba."

Kallon Ummee ta yi da jikinta ya mutu sosai tace" Ki tsayar da sallarki, za ta zame miki haske a
ƙabarinki, sannan idan sallarki ta yi kyau a sikelin lahira, to hisabi ma bai zama lalle gareki ba."

Ita kanta amarya da bala'i ne ya kawota sosai jikinta mutu ta ji zuciyarta na dukan tara-tara
tunawa da yanda ita ta ɗauki sallarta, sai kawai ta juya jiki a sanyaye ta bar ɗakin, haka Alhaji
Auwal da Hajia Rabi ma suka fita suna jin gaba-ɗaya yarinyar ta gama ɗauresu da wasu
manya-manyan igiyoyi da ba zasu iya kwance kansu ba.
Ganin haka Saleema ta fita a ɗakin ta hauro ƙasa tare da Hajia babba wacce yanzu ɗakinta ke
ƙasa sablda wuyar da hawa saman ke mata, cikin ladabi ta tabayeta "Mama, zan iya shiga
madafa?"

Murmushi ta sakar mata tace "Me zai hana Saleema, ki shiga ki ɗauki duk abinda kinke so."

Girgiza kai Saleema tayi tace "A'a Mama ba dan buƙatata ba ne, abun kari zan haɗa, na ga mai
aiki ba a nan take kwana ba."

Girgiza kai tayi ita ma tace "A'a Saleema, ki bari na gama sallah sai na ɗora, dama sai rana ta yi
take zuwa, iya shara da wanke-wanke da sauran ayuka take yi, amma girki mu ke yi sai dai ta
taimaka mana da wani abun kawai, dan Alhaji baya son cin abincin mai aiki."

Ƴar dariya tayi tace" Hakan ya yi kyau, kamar Babana shi ma haka yake, amma ki bari ni zan
ɗora, idan da buƙata ku sai ku ɗora na Abba idan kun ida sallah."

Faɗaɗa murmushi tayi tace" Nagode Saleema, Allah miki albarka."

Da fara'a ita ma ta amsa da" Nagode Mama, amma me za'a dafa?"

Da fara'a tace" Saleema ko me kika dafa ma ai ya yi, ki duba a madafar akwai duk abun buƙata,
idan kuma kin rasa wani abun ki min magana."

Jinjina kai tayi cike da ladabi ta wuce madafar inda ta fara da abinda ta gani kuma ta iya
sarrafawa. Hajia Rabi na idar da sallah ta fito za ta shiga wajen Alhaji dan tambayarshi abinda
zai ci, Mu'az ne ya shigo gidan dan bai kwana a gida ba, tsaye tayi har ya ƙaraso yana gaisheta
da "Ina kwana Mama."
Na wasu daƙiƙu ta fara zuba masa ido kafin tace "Ba'a gida ka kwana ba ko?"

Ba tare da damuwar komai ba ya amsa da "E Mama."

Ba alamar wasa a tare da ita dan bata so ya kawo mata wargi duba da tambayar da za ta mishi
ba ta taɓa kwatanta yi masa ita ba sannan tace "Ina ka kwana?"

Da sauri ya saka idonshi a cikin na ta kamar wanda aka ba wa tsoro, sai kuma ya saka fuskar
mamaki yace "Mama, me ya sa kika tambaya? Wani abu ya faru ne?"

Sake haɗe fuskarta tayi tace "Sai wani abu ya faru zan tambayeka?"

Ɗan girgiza kai yayi yace "E to Mama, na ga dai haka bai taɓa faruwa ba ai."

Tsareshi tayi da ido tace "Amsar tambayata?"

Ɗan matse bakinshi yayi yace "Abinci na fara ci a restaurant, sannan na wuce majalisarmu, ba
mu tashi a nan ba sai ƙarfe uku na dare, daga nan mu ka ƙarasa gidansu *Zeid* a can na
kwana."

Wani sakaran murmushi ta yi tace "Ka kwana ko ka rintsa? Ai ka gama kwananka tun a
majalisa."

Gyara tsayuwa ta yi tace "Sallah da, ka yi sallah kafin ka shigo?"

Ƙanƙance ido yayi yana mata kallo mai kama da hangen nesa yana so ya gano me ke damun
Mamanshi yau? Cikin mamaki yace "Na yi sallah Mama."

Harara ta galla masa tace "Yanzu ka yi ko?"

Sosai ƙeya yayi alamar kunya bai ce komai ba, girgiza kai tayi tace "Allah ya shirya."

"Ameen Mamana." Ya faɗa yana binta da kallo, ganin za ta yi nisa ya matsa kusanta yace
"Mama."

Juyowa tayi tana kallonshi amma ba ta ce komai ba, da ɗar-ɗar din amsar da za ta bashi yace
"Mama wani abu ya faru ne?"

Da mamaki tace "Me ka gani?"

Sunkuyar da kai ya yi yace "Na ga ai kina ta min wasu tambayoyi ne kamar ƙaramin yaro ko
wata mace."

Wani kallo ta mi shi tace "Au! Ina matsayin mahaifiyarka ba zan tambayeka ba tunda ka wuce
munzalin?"

Girgiza kai yayi yace "A'a Mama ba haka nake nufi ba, abun dai ne ya zo min wani iri, baki taɓa
haka ba fa Mama."

Jim! Ta yi ta kalleshi kuma ta san gaskiya ya faɗa, gyara tsayuwarta ta sake yi tace "Gaskiya
kam, ni ma kuma na san tambayoyin da na maka sabon abu ne, amma dan Allah da na
tambayeka ba ka ji daɗi ba?"

Murmushi ya sakar mata tare da dafa duka kafaɗunta ya ɗora haɓarshi a wuyanta yace "Na ji
daɗi sosai Mamana, hakan ya nuna min yanda ki ka damu da ni."

Turo ɗan bakinta tayi gaba cikin shagwaɓa tace "Zuwan yarinyar nan ya zamar mana alkairi,
daga jiya zuwa yau ta haska mana abubuwa da dama da suke shige mana duhu, musamman
ma a kan sallah da ta tunatar da mu yanzun, sai na ji kamar zan zauna na yi ta kuka saboda
kurakuren da muka tabka a baya, amma in sha Allah na ɗauki niyyar gyarawa da wannan
nasihar da ta mana."

Hannu ta zura ta bayanta ta shafi kumcinshi a shagwaɓe sosai tace" Gaskiya yarinyar kirki ce,
ina ma za ta zama surukata?"

Da mamaki ya ɗaga kanshi kaɗan yace" Mama, wacece wannan?"

Hararan wasa ta jefa mi shi tace" Wa fa ban da Saleema."

Wani ƙasaitaccen murmushi ya saki tare da maida haɓarshi a kafaɗarta, haka kawai ya ji wani
shauƙi da daɗi na sunan da ta ambata, shiru ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login