Showing 39001 words to 42000 words out of 50006 words
Chapter 14 - Baiwata Book Complete by Samira Harouna.pdf
da ba karatun ka ke
ba kuma ɗinki ka ke yi, kana ganin hakan ya yi dai-dai? Ba ka tsoron ulcer ɗinka ta tashi?"
Kallonta ya yi a ladabce yace" Ki yi haƙuri Mama, in sha Allah zan kiyaye, ai komai ya zo ƙarshe
tunda an gama."
Cike da tabbaci tace" An gama, amma jiran tsammanin sakamakon shi yake jefaka a halin
tunanin nan, me zai hana ka bar wa Allah zaɓi, idan ka yi nasara ka gode masa, idan ba ka
samu ba ka gode masa ka kuma duba wata hanyar ka bi."
Ajiyar zyciya ya sauke ya jinjina kai yace" Hakane Mama, in sha Allah zan yi yanda ki ka ce."
"Allah yasa." Ta faɗa tana kallon kwanon abincin tace "Maida hankali ka ci abincin."
"To Mama." Ya faɗa yana jawo kwanon dan ba ya son yin musu da ita, saida ta ga ya fara jefa
abincin kaɗai ta bar ɗakin tana sake jadadda masa za ta zo ɗaukar kwanon da kanta, maza ya
cin ye duka kafin ta dawo.
Ƙarar da wayarshi ta yi yasa ko amsa mata baiyi ba ya du a wayar, wani iska ya feso daga
bakinshi ganin Sharhasila ce, ƙurawa lambar idanu yayi da tunanin ya ɗauka? Dan tun da ya
fara zana jarabawar nan bai kirata ba saboda zafi da kanshi ya yi, yau ne ya gama yake tunanin
zai je gidan dan su haɗu saboda ƙara ƙaratowar lokacin bikinsu, gashi kuma ta kira bai san dalili
ba.
Ɗauka ya yi ya kara a kunne yana sallama, a taƙaice ta amsa wa "Alaika salam, Baby shine ka
manta da ni ko kirana ba ka yi?"
Lumshe idanu yayi kamar ba zai amsa ba, sai kuma ya numfasa cikin nutsuwa yace "Ban
manta da ke ba, zan zo gidan yau."
Cike da shagwaɓa da kuma sakarci tace "Ka ga ni zan zo, zan zo gidan na ku, ina son ganinka
ne."
Waro idanu yayi a sauƙaƙe yace "Gidanmu kuma?"
Turo baki tayi ta amsa da "E, gidanku, na yi kewarka Baby."
Dafe gaban goshonshi yayi yace "Ba sai kin zo ba, ni zan zo anjima, kin ji?"
Cikin shagwaɓa tace "Ka yi alƙawari?"
"Na yi." Ya faɗa a tausashe, murmushi tayi wanda saida ya ji sautinsa a kunnuwa tace "To Baby
ka taho mana da ice cream, ni zan ba ka wani abu idan ka zo."
Rufe idanu yayi yana mamakin wauta irin ta Sharhasila, "To." Kawai ya faɗa yana ɗauke wayar
daga kunnenshi ya aje ya ci gaba da cin abincin.
*Ga mai son shiga grp ɗina ya tuntuɓi wanda ke musu post zai samu kanshi a ciki in sha Allah.*
*Alhamdulillah.*
24/05/2022 à 14:11 - Mom Lateef: ❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*BAIWATA*
❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️
*NA*
_SAMIRA HAROUNA_
*SADAUKARWA GA*
*AHALINA*
*GAMAYYAR MARUBUTAN NIJAR (ASSO.)*
_(Burinmu d'aga muryoyinmu sama domin anfanar da al'umma had'e da ciyar da adabin
hausa.)_
☆ *[G. M. N. A]* ☆ ️
_Bismillahir rahamanir rahim_
_16_
Fitowarta kenan daga wanka tana tsane jikinta da babban towel, su Hadeeya ta samu suna ta
mitar aikin da sukayi na gyaran ɗakin Papi wanda har kayan abinci sai da Alhaji Auwal ya sa
aka canza musu wuri aka maidasu madafa, Ummee haushi kamar zai kasheta da tana aikin,
yanzu haka duk a gajiye suka kwanta har ƙarfe 11:00 ta yi.
Kayan baccinta ta saka ta zauna bakin gado tana addu'o'in da ta saba yi, ta shafe jikinta kenan
za ta kwanta aka ƙwanƙwasa ɗakin, miƙewa tayi da niyyar buɗewa dan Hameeda tsaki ta ja
tana faɗin "Daren ma ba za'a bari mu huta ba."
Ta kai hannu za ta ɗauki hijabinta aka turo ƙofar, ido huɗu sukayi da Mu'az da yayi turus yana
kallonta daga ƙasa har sama, bakinshi buɗe ya kasa furta ko a, hankali ya lalubi idanunshi ya
rufe dan in ba haka ba zai mutu a tsaye. Sa'a ɗaya ta yi saurin rarumo hijabi ta rufe jikinta ba
tare da ta sanya ba, sosai kunya ta kamata ta sadda kanta ƙasa, riga da wando ne jikinta na
bacci, rigar ta na da hannaye iya damatsenta, saidai ta fito mata da surarta, haka ma wandon
duk da bai kamata ba, amma tsayinshi iya bakin gwiwoyinta ne.
Hadeeya da ta miƙe zaune ce tace "Yaya, lafiya?"
Buɗa idanunshi ya yi ya kalleta sai kuma ya yi gyaran murya yace "Ughym! Umm..ammm...!
Dama jarabawarku ne ta fito, na zo na ji lambobinku ne dan na duba muku."
Da sauri Hadeeya ta taso tana faɗin "Yawwa, Yaya ni lambata 4452..."
Saida ya saci kallon Saleema da ta wanka masa harara ta ja tsaki ta koma ta zauna kan gadon
kafin ya turawa abokin na shi lambar da sunan Hadeeya ya duba masa, cikin ƙanƙanin lokaci
aka faɗa masa Hadeeya da Ummee sun samu har ma da Hameeda da ita ta zana jarabawar ne
kawai amma ba ta kai ga ajin ba (candidate libre), cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin ya hargitse da ihu
da shewa na ƴan matan, da gudu suka fita dan sanar da iyayen da har yanzu suke zaune a falo
suna kallo suna hira.
A hankali ya tako ya zo gabanta cikin sanyin murya kamar mai tsoronta yace "Saleema,
lambarki?"
A zafafe tace "Ba na buƙata malam, ka ga shigo mana ɗaki da ka yi ma ba tare da an baka izini
ba ya isa, dan haka kar ka hassalani dayawa."
Kawar da kai tayi tana sake haɗe fuska sosai ita dole ya ɓata mata rai, durƙusawa ya yi niyyar
yi dan ci gaba da bata haƙuri, haka kawai ya ke jin ranshi ba daɗi saboda ranta ya ɓace, da
sauri ta jaye ƙafafunta dake kusa da shi tana ɗan galla masa harara, miƙewa yayi tsaye yace
"Ki yi haƙuri Saleema, na shigo ne dan na ga baku jima da shigowa ɗakin ba bare a ce har kun
kwanta, amma ai na ƙwanƙwasa ƙofa, kuma sai da na ɗan jinkirta kafin na shigo, tunanina
hakan ya ba wa wacce ke farke damar kimtsa jikinta."
Sake marairaicewa ya yi yace" Saleema, ni fa ba kowace mace ke birgeni ba, ba kuma kowane
tsiraici na ke son gani ba, tunda na ke a rayuwata ban taɓa jin ina son wata ƴa mace ba sai ke,
ke ce mace ta farko da na ji ina so na yi rayuwar aure da ita, ke ce macen da na ji ina sha'awar
ta zama uwar ƴaƴana, Saleema..."
Yanda ya kira sunanta yasa ta ɗaga kai ta kalleshi, ci gaba ya yi da cewa" Tabbas ƙarya na faɗa
idan har na ce surarki ba ta birgeni, amma ki sani na yi tarayya da mata da suka fi ki kyau da
wayewa, sai dai ba su min ba saboda sun rasa *aji*, a gareki ne na fahimci duk wata mace mai
aji, to tana tare da *kamun kanta*, wallahi abu ɗaya ya sa na ke sonki da aure, wannan abun
kuma shine *tarbiyya*, ina da yaƙinin tarayyata da ke za ta zama tsanin hawana hanya
madaidaiciya, kamar yanda na ke da tabbacin zuri'ata indai ta tsatsonki za su fito, to za su
zama abun alfaharin kowa, sannan na zama uba ma fi dacen ƴaƴa a duniya."
Da sauri ya durƙusa gabanta yayi tsugunno irin na maza yana kallon fuskarta kamar yadda ita
ma take kallonshi da ƙyar take ƙyaftawa yace" Saleema, ki nemi zaɓin ubangijinki a kan
lamarina, kar kiyi gaggawa dan ni ma ba zan yi ba, duk da kuwa ina matuƙar son yin aure
saboda wani babban dalili, idan har kika ji kin gamsu za ki aureni, to ki sanar da ni a ko da
yaushe, ni kuma na miki alƙawarin faɗa miki komai a game da ni, har da ma wanda iyayena
kansu ba su sani ba, dan bana so mu fara zama na gaskiha ba tare da kin san wannan abun
ba, dan gaskiya ba na jurar matsala daga abun da na ke so, musaman ma..."
Saida ya yi ƙasa da kanshi kafin yace" Musamman ma ke, wallahi zan iya miki kuka idan kina
hushi dani."
Da sauri ya ɗago ya kalleta yace" Kin gane? Ni kwata-kwata ban saba da rayuwar wahala ba,
ban taɓa jin abu ya birgeni lokaci ɗaya ba kamar yadda kika shiga raina, an reneni cikin gata da
bani duk abin da na ke so, dan Allah Saleema kar ki hana min kanki a karon farko na rayuwata."
Buɗa ido tayi da kyau tana kallonshi, ɗan jan hijabinta tayi ta ƙara rufe ƙafafunta da take jin ta
kamar a tsirara, ba tare da ta ɗauke dubanta gareshi ba tace" *Aku*, aku sarkin surutu."
Laƙace mata hanci yayi yana dariya yace" Ke ma da kin aureni za ki koyi surutu."
Da sauri ya miƙe tsaye yana sake faɗin" Yanzu bani lambar ta ki kema na sa a duba miki?"
Girgiza kai tayi tace" Gaskiya a'a, ina ji a jikina ma ban ci ba, ba sai ka wahalar da kanka ba."
Da mamaki yace" Me yasa? Ya za ki cire rai haka?"
Cike da jimami tace" Ka share kawai, nagode da kulawarka."
Ɗaga kafaɗa ya yi yace" Shikenan, bari na canza kaya sai na je na dubo miki."
Da mugun sauri ta miƙe tsaye har tana sakin hijabin ya zube ƙasa ta yi ram da rigarshi tana
faɗin" A'a, a'a dan Allah kar k..."
Sai kuma ta saki rigarshi ta ja baya tana durƙusawa ta ɗauki hijabin kanta ƙasa cike da kunyar
abun da ta aikata, ganin ta yi shiru babu ma alamar za ta ce ƙala sai kawai ya fita shima ya na ji
a ranshi lallai lallai dole ya dinga nisantar yarinyar nan dan gudun samun matsala, dan in dai zai
dinga ganinta a haka, sannan har wani dalili ya sa su haɗa jikinsu, to fa tabbas komai na iya
faruwa a yadda yake tsananin son yin aure dan ya ci halalinsa.
Da farin ciki Hameeda ta shigo ɗakin tace "Abba ya ce ki zo."
Ba ta amsa mata ba ta miƙe bayan Hameeda ta fita a ɗakin, zane ta ɗaura a kan wandon
sannan ta saka hijab ɗin ta fito, falon ta samesu suna ta murna inda ta ji Ummeeta na faɗin
"Gaskiya Abba ni dai ƙaton sa za'a yanka min, ƙawayena su ci nama su ƙoshi."
Tana ƙarasowa ya kalleta yace "Saleema ke ba ki faɗa mana sakamakonki ba?"
A sanyaye tace "Abba da safe zan je da kaina na dubo."
Da mamaki yace "A'a, me yasa to? Gashi a sauƙaƙe Yayanku na diba muku."
A ladabce tace "Abba na fi so na duba a can."
Kallon Amarya ya yi yace "Ai ina tunanin ƴan Bac ma gobe ake fito musu da sakamako?"
Saida ta yatsina fuska ta kalli Saleema tace "Haka ake saka rai."
Jinjina kai yayi yace "To shikenan, Allah kaimu goben sai ki je tunda haka kika fi so."
Juyawa tayi ta koma ɗaki ta kwanta gabaɗaya take ji a jikinta kawai ba ta samu ba, amma dai
za ta je dan ta samu tabbacin haka.
*Washe gari*
Ta jima wajen Papi suna hira tana faɗa masa wani abu da ya zo kanta daren jiya kafin bacci ya
ɗauketa, ganin ta samu goyon baya ɗari bisa ɗari sannan ta fito daga ɓangaren na shi ta nufo
falon dan ɗaukar jakarta ta tafi makaranta dubo sunanta. Kai tsaye madafa ta nufa ta samu
Nafissa da amarya suna aiki, ɗan kama musu tayi saboda Nafissa take so ta ma magana, tana
ganin Amarya ta buɗa mangaza ta raɗawa Nafissa abu a kunne, kallonta tayi da mamaki tace
"Kin tabbatar?"
Lumshe ido tayi alamar e tace "Ki yarda dani, ki ƙwarara kanki."
A tsorace ta furta "Gaskiya ina jin tsoro."
Girgiza mata kai tayi ta riƙe hannubta tace "Ki ji tsoron Allah kawai, yana tare da mu kuma zai
taimakemu, saboda niyyarmu mai kyau ce."
Jin amarya na fitowa yasa Saleema raba hannunta da na Nafissa tace "Yawwa ni na tafi, sai na
dawo."
Jinjina kai tayi tace "A dawo lafiya."
Da harara amarya ta bita tana ayyana "Allah raka taki gona, na san ma ba samu zakiyi ba tunda
ba karatun ne a gabanki ba."
Amarya na idar da girki ta kira Ummee, tana zuwa ta bata abincin Papi ta ce "Ki kaiwa Baba
ɗakinshi."
Wani yatsina fuska tayi tace "Papi kuma? Ba ga Nafissa nan ba."
Rai ɓace amarya tace "Ke in za ki karɓa ki karɓa, doka ce kuma ubanki ya ɗorata, in ba za ki
kai ba na kira Mu'az ya kai sai na faɗa masa ke kin ƙi."
Da sauri ta finciko kwanon ta juya kamar za ta cira bakinta tana bubbuga ƙafafu ta nufi ɗakin
cike da takaicin me ye sai ita za ta kai masa abinci, tana shiga ɗakin ba sallama dan ta nuna
bata so ba fa, ajewa kawai ta yi ba ko ina kwana duk da yana zaune falon haka ta juyo ta fito,
da kallo ya bita kawai ya girgiza kai a ranshi yace "Allah ya shiryaku."
Tare da dreba suka tafi makarantarsu, a kam ta samu ɗalibai da dama da suma suka zo duba
na su sunan, ba ta ;ata lokaci ba wajen fara duba sunayen da suka fara da harafin H, shiru
babu alamar na ta sunan, haka ta dinga dubawa daga farko har ƙarshe amma babu, jiki a
sanyaye ta koma gefe ƙofar wani aji ta zauna ta tangale kanta da ginshiƙin wurin, sannu sannu
ta ji idanunta sun fara kawo mata ruwa, kamar an daketa sai kawai ta fashe da kuka.
Cikin ƴan ajinsu ne wata ta dafa kafaɗarta tace "Saleema."
Ƙin ɗagowa tayi saboda ita kaɗai ta san me take ji, ganin haka yasa ta sake faɗin "Saleema, ki
yi haƙuri idan ba ki samu ba, kinga ni ma ban samu ba kuma ban damu ba, saboda na san
akwai gaba kuma haka Allah ya tsara, kinga dayawa ma basu samu ba amma kowa ya haƙura,
wannan shekarar jarabawa ta zubar da ɗalibai dayawa, ki ƙwarara kanki in sha Allah wata
shekara sai ki ga kin samu."
A hankali ta rage kukanta jin ba ita kaɗai ba ce akwai dayawa, share hawayenta tayi ta miƙe
tsaye ta kalli budurwar tace" Nagode Chafa'atu, nagode sosai, Allah ya sa haka shi ya fi zama
alkairi."
"Ameen." Ta faɗa tana murmushi, da sauri Saleema ta nufi hanyar fita ta samu dreba na jiranta
ta shiga suka tafi, haka kawai ta ji zuciyarta ta bushe da tunanin hukuncin da mahaifinta zai
mata, a ganinta idan ma duka ne ai ba yau ne farko ba, ya jima yana dukanta tun bata san
ciwon jikinta ba, dan haka za ta ɗauka idan ma dukan ne, ai dai ba zai ɗauki ranta ba idan ba
Allah ya nufi hakan ba, kyauta kuma ya ba wa su Hadeeya duk abin da ya mallaka bai dameta
ba, in dai bai hukunta mahaifiyarta da laifinta ba to komai ya yi.
Cikin takon nutsuwa ta shigo falon, a hankali ta shiga bin kowa na ɗakin da kallo saboda yanda
ta ga sunyi zugum-zugum, babban abin da ya ɗaga hankalinta shine ganin mahaifinta a gefen
Alhaji Auwal zaune fuskarshi yanda kasan hadarin gabas, sai dai kuma a gefe da ta ga Nafissa
durƙushe tana kuka ƙashirban sai ta ɗan murmusa kamar hankalinta a kwance yake.
Duk da arnan kallon da mahaifinta ke aika mata bai hanata ƙarasawa kusa da shi ba ta zauna
ƙasa irin zaman tahiya tace "Abba ina kwana."
Ɗauke kanshi yayi daga kanta da mamakin ita yarinyar nan ba ta gane ɓacin rai ne? Kusanshi
fa ta zo bayan ta san zai iya tattakata, Alhaji Auwal ne ya dawo da shi daga tunanin da yake ta
hanyar faɗin "Ƴata ya batun sakamakon?"
Kallonshi tayi sai kuma ta sunkuyar da kai a hankali ta girgiza kanta alamar ba magana, da
sauri ya kalli Alhaji Yusuf da zai yi magana a zafafe ya masa alama da ido ya yi shiru, haɗewa
ya yi yana jinjina kai kamar zai tashi sama, a tsanake ya kalleta yace "Ƴata, kar ki damu kanki
kin ji, faɗa min ya kike so? Kina son samun kanki a aji na gaba ne? Ko kuma kina so nan da
awa ɗaya ki ga sunanki a kafe a wata takardar?"
Kallonshi tayi tace "A'a Abba, nagode da karramawarka, amma na fi so na samu dalilin
ƙoƙarina, idan akayi haka an zalunci dayawa wanda ba su da yanda zasuyi."
"Kuma har abada ba za ki samu ba indai da ƙoƙarinki ne." Cewar Alhaji Yusuf har da saka ƙafa
ɗaya ya tureta daga kusanshi, sai da tayi kamar za ta yi sujada dan abun bazata ne, gyara
zamanta tayi sanda Alhaji Auwal ke faɗin "Ka ga kar ka kuma dukar min yarinya, karatun ba na
Allah ba ne? Ko dabararta za ta bata ne?"
Cije leɓen ƙasa Alhaji Yusuf ya yi kamar zai ciji iska, Alhaji Auwal kuma kallon Nafissa ya yi da
ke ta sharar hawaye yace "Zan nemeki, ki bamu wuri yanzu."
Miƙewa ta yi ta nufi madafa, kallon Hajia Rabi da amarya yayi yace "Dan Allah ku bamu wuri za
mu tattauna?"
A kasalance suka miƙe musamman amarya da ta bi Saleema da